Showing 18001 words to 20540 words out of 20540 words
Chapter 7 - BOYAYYEN SIRRI Book Complete writing by Chamsiya Laouali Rabo.txt
tsaida shi in ta tashi zamu sake yi mata scaning in kuma mijin ya zo ace ina neman shi dan shi ma yanada laifi mace mai ciki ba ko da yaushe ake zuwan mata ba,in yayi ganganci cikin na iya zubewa"......
Jikar Rabo ce🌚
[18/07 à 15:40] Matar Sadauki💞: *ƁOYAYYEN SIRRI*💞
By Chamsiya Laouali Rabo
Page 38-40
Kanta Ammy ke shafawa tana tofa mata addu'a bayan ta sanar da ABDALLAH suna asibiti,kamar an jefo shi ya shigo ɗakin dady na bayan shi."Ammy mike damunta?"cewar ABDALLAH yana mai zama bakin gadon da take kwance "mi fa zai dameta in ba wannan auren naka da ka tsiro ba garai babu dalili,wlh sa'ar ka guda likita yace cikin bai zube ba da ba zan sake maka magana ba"ido ABDALLAH ya fiddo yace "cikiiii?ciki Ammy ?"yadda yayi maganar a ruɗe ya ba Ammy mamaki da kuma haushi sai tace "ka tashi Dr na nemanka inda kana son cikin ai da ba zaka yi ganganci haka ba"sama-sama ABDALLAH ke jinta baby kawai yake kallo yana duba tafin hannunta ganin dagaske cikin dai ne gareta kawai sai ya rungumeta ya sumbaceta a baki,caraf MARYAM ta riƙe mashi lips ta shiga tsutsa sam ya manta da su Ammy ya biye mata.
Da sauri ya cire bakin shi yana fitar da lumfashi ya fara kallon ɗakin wayam babu su Ammy,ƙuri suka yi ma juna dan a lokacin ta tashi.Hancinta ya ja kamin ya ɗora hannun shi kan mararta yana shafawa yana jin son cikin jikinta har ƙasan zuciyar shi,ta ido suke magana sarai ya gane kallon mi take mashi na irin miyasa ka aureta ba tare da ka gayamin ba? sun ɗauki lokaci a haka Dr ya shigo,sérum ɗin ya ƙara ma gudu ya tambayeta abinda take tace babu sannan yayi ma ABDALLAH jawabin abubuwan da bai kamata tayi ba sannan ya ɗaga mata ƙafa har cikin yayi ƙwari.
"Amman Dr nan da 1week ai yayi ko?"turo ƙofa a kayi da sauri duk suka juya Ammy ce take wurgo ma ABDALLAH wani kallo ashe duk abinda ake tana ji "ka shiga hankalin ka in ba iskanci ba kai ma ba likita ba ne ai ka san abinda ya dace "sosa ƙeya ABDALLAH yayi yace "ammyyyy" hararen shi tayi tana mai ƙarasowa gun MARYAM da ke ƙoƙarin tashi,taimaka mata tayi ta jingina a jikin bango.
Kiran sallah la'asar yasa shi fita,a can masjid ɗin ne bayan sun gama sallah Dr ke tambayar ABDALLAH"dama kai na A.A ?"kai kawai ya ɗaga mashi yana murmushi"yau ne na fara aiki a cikin asibitin sai yanzu naji Nurs na firar an kawo Mrs ABDALLAH,to miyasa baka gayamin kai ne ba"cewar Dr "na zata ka sani ne dan ranar da kazo na ga kun fito da Dr LAWAN (abokin dady ne shi ke ɗaukar sabbin ma'aikata)na zata ya gaya maka"cewar ABDALLAH yana murmushi dan sam bai da girman kai irin na ɗiyan masu kuɗi,"ina fa ya gayamin sunan naka ma dan ya kasance sunan asibitin ne"dariya ABDALLAH yayi kamin su wuce ciki suna tafe suna hira.
A ɓangaren RAINA kuwa bayan an gama mata lalle INNANE tai aiko kiranta ta fara gwada mata wasu garin magani yadda za tayi aiki da su saura kayan mata sauran kuma na gidan boka "na cikin robar tun gobe zaki yi amfani da shi ki matsa shi a gaban ki,muddin ya kusance ki ba zai ƙara jin daɗin wata mace ba"cewar BALARABA wacce bata daɗe da zuwa ba tana kwance bisa gado daga ita sai ɗaura gaba kamar gidanta ta wani saki cinyoyi ga fili.Kai kawai RAINA ke ɗagawa dundu INNANE ta kai mata "ba ki magana ne zaki wani rinƙa ɗaga min kai kamar ƙadangare"cewar INNANE "haba irin kunyar nan ce ta amare ki ƙyaleta ƙawa" BALARABA ta faɗa daga can kwance,ita dai RAINA bata ce komi ba ta kwashe kayan ta maida cikin leda,cikin trolly ta sa ledar ta fice waje.
Da sauri INNANE ta yo kan BALARABA tana shafar ta "haba ƙawa irin wannan ai sai kisa na zauce gaban yarinya"ta faɗa tana haɗiyar miyau kamar mayya "dan Allah ki barni na huta duk a gajiye nike zuwa dare sai muyi "cewar BALARABA tana gyara zanenta,wani mugun kallo INNANE ta jefa mata kamin tace "wane irin in bari da dadare?kan ki guda kuwa?ko kin mance da sharaɗin?"INNANE ta faɗa tana mai yaye zanenta suka fara masha'ar su.Sun ɗauki lokaci kamin su tsagaita , rungumeta INNANE tayi tace "nayi missing ɗinki sosai ko ranar nan da kyal nayi barci da ban same ki ba,dan Allah nan gaba kar kije da MOCTAR in zaki fito"ɗan tureta BALARABA tayi tace "ni jarabar kice ban so na kusa gama aikina na rabu da wannan banzan auren da aka jona mani"tana maganar ne tana mai sabka daga gadon,duk da INNANE taji zafin maganar dannewa tayi tace "ina ne zaki wai?"
"Wanka zani yi in yi sallah"cike da mamaki INNANE tace "yaushe kika fara sallah ban sani ba?ko kin musulunta ne?"cikin jin haushi BALARABA tace "yo da kafira ce ni?"
"A'a ban ce amman miye matsayin wanda rabon shi da ya dubi gabas an fi shekara..."hayayaƙo mata BALARABA tayi "ko ma dai minene ai ke kika ja min ni wlh duk cikin abinda aka gindiya min ba abinda yafi ɓata min rai kamar na barin sallah"ta ida maganar cikin tausayi,dariya INNANE ta sheƙe da ita "toh in banda abun ki ina kika taɓa ganin wanda aljanu zasu biye maka suna maka abinda kake so kuma su yarda kayi alaƙa da Allah ?"ɗan shiru BALARABA tayi tana nazarin maganar INNANE kamin ta fice.
***
Shiri ake kamar za a kaita wajan gasa,wata fitinaniyar gizner ce fara sol wadda aka mata aiki na jan zare da perle,sosai ɗinki ya amshi jikinta.
Ƙamshin jikinta kawai ni'ima ce dan ɓarin turare INNANE tayi mata kamin su taru ita da BALARABA suyi mata nasiha wacce da ita da babu duk ɗaya dan babu zancen kiyi ma mijin ki biyayya ko ki zauna lafiya da abokan zaman ki sai dai akasin haka.
Motoci kan amarya wasu vide ma suka tafi dan INNANE ba tada yarda balle har tayi wasu mutane dayawa.Gida na gani na faɗa ne aka kai RAINA ƙawayenta ƴan ƙarya sai ɗaukar hotuna ake ana azawa a statut .
Bayan kowa ya watse aka bar amarya ita ɗaya,cilli tayi da mayafi ta je bakin madubi tana kallon kanta kamin ta cire kayan ta shiga toilet.Wanka tayi ta shirya cikin wasu arnan kayan barci wanda da su da babu duk ɗaya,feshe jikinta tayi da turarukan boka sannan ta hauda parfum tare da shafa man da BALARABA ta kawo mata na matsi.
Turo ƙofa aka yi tare da yin sallama sai dai bai ƙarasa yinta ba sauran ta laƙe a maƙoshi sakamakon arba da idon shi suka yi da kyakyawar surar RAINA,yawu ya haɗiye ya ida shigowa ciki yana mai ajiye ledar hannun shi.
Tsaye tayi ƙiƙam tana kallon réaction ɗin shi kamin ta fara takowa tana girgiza jiki,suman tsaye ABDALLAH yayi lokacin da ta tsaya gaban shi tana zagaye bakin shi da yatsa.Ajiyar zuciya ya sauke jin turarenta mai kashe jiki da sanyaya zuciya masoyi, juyawa tayi ta nufi ƙofar fita yabi bayanta da kallo yadda shap ɗinta suka fito.Dawowa tayi da ƙaramin tray a hannunta,ledar da ya shigo da ita ta jawo ta juye gasasun kajin Madougou sai turiri suke,abinda ango ya kamata yayi ma amarya ita tayi ma angon shine ciyar da shi da hannu har suka ƙoshi.
Tana lura da yadda yake samun canji amman ta share sai ma wanke bakinta da tayi ta haye bed, ABDALLAH ya koma kamar wani sakarai ya kasa taɓuka komi da kyal ya rage kaya ya shiga wanka.
Dariya RAINA ke yi ƙasa-ƙasa ganin yadda towel ɗin jikin shi ya toni asirin shi na halin da yake ciki,sallah ya so suyi amman sam bai ji zai iya daurewa ba.Hutar ɗaki ya kashe ya zo ya kwanta yana mai jawota a tare suka sauke ajiya zuciya,lumshe ido RAINA tayi tana karɓar saƙonnin da ta daɗe tana jira kamin ta fara maida mashi .Sosai ya samu nutsuwa sai sa mata albarka yake kamin ya fara rarashinta, munafukar luf ta laye cikin ƙirjin shi tana shasheka wani barci yayi awon gaba da su.(🥱asubah ta gari)
***
Kallo guda zaka yi mata ka gane tayi kuka kuma tana buƙatar yin barci sai dai hakan ne taƙi samuwa"ina kwana Ammy "ta furta da muryar ta da bata fita murmushi Ammy tayi kamin ta amsa mata tana mai haɗa mata lipton wanda yasha karamfani,karɓa tayi tana kurɓawa a hankali har ta shanye ta kwanta bisa salon Ammy kuma ta koma kitchen.
"Yanzu yana can rungume da ita ƙila ma yana mata wanka dan na tabbatar ABDALLAH ba zai ɗaga mata ƙafa ba tunda daman shi ko can bai kwanan banza"MARYAM ta faɗa a zuci tana mai goge hawayen da suka zubo mata,sai kuma tayi murmushi"RAINA burin ki ya cika kin auri irin mijin da kike so na san mijina ya haɗa komi abu guda da baki so kuma shi Allah ya bashi shi dayawa gashin ƙirji"duk a zuci ne take wannan maganar kamin kuma ta miƙe zauna "Allah sa kar ta aske shi "ta faɗa a fili ,fitowa Ammy tayi tace "magana kike?ko a baki abinci kamin nayi maki taiba ɗin?"kai ta girgiza tana mai tashi ta nufi ɗaki.
Wani tausayinta ne ya kama Ammy sai taji ƙwalla ta cika mata ido.
Ɗaki ta shige ta kwanta kan bed ta rungume matashin kai a ƙirji tana jin wani irin son mijinta da kishin shi na taso mata,a haka barci yayi awon gaba da ita.
Gashin kanta wanda yake a barbaje taji ana shafawa a hankali ta buɗe idonta ta sauke su kan ABDALLAH wanda ke zaune cikin ƙananan kaya ,da sauri ta tashi zaune shi kuma ya jawota jikin shi yana shafar bayanta.Ɗan janyewa tayi daga jikin shi ta ɗora hannunta ga rigar shi ta shiga ɓalle maɓalen bai dakatar da ita ba har ta gama,ajiyar zuciya ta sauke tana mai zura hannunta cikin ƴar farar ƙaramar rigar shi ta ciki "ina son wanga abun please kar ka aske shi"ta faɗa muryar ta na rawa,"na sani shiyasa na hana ta askewa"da sauri ta kalle shi "har tace ka aske ko?"
"A'a ta dai ce bai burge ta"hannunta ta fiddo tana shirin sabka ya maidata "kwanta ina son ganin lafiyar bébé junior"kwantawar tayi ya ɗaga rigarta yana shafar cikinta daga bakin ƙofa suka ji Ammy na cewa "wannan shirun yayi yawa ABDALLAH uwar mi kake da baka fito ba?"kallon juna suka yi kamin yace "Ammy gamu nan zuwa"ya faɗa yana mai maida mata rigarta daidai.
Falo suka dawo Ammy ta gabatar masu da abun karyawa,shi ke ba MARYAM a baki har ta ƙoshi.
A ɓangaren RAINA kuwa ba ƙaramin haushi taji ba da ABDALLAH ya banzatar da maganarta da tace mashi ta tsani gashin ƙirji sai bai ce mata komi ba yayi kamar bai ji ba ma,abun ƙarin haushi ko ƴar kyautar nan ta amare bai bata ba.
Fitar shi ma tun da safe taji haushinta sai dai babu yadda zata yi, INNANE ta kira bugu biyu ta ɗauka bayan sun gaisa ne INANE ke gaya mata zasu zo ita da BALARABA ganin ɗaki........
💞💞💞💞💞
Ƙyaƙyaf da ido AMIRA ta fara yi sai hawaye sharrr,shashekar kukanta ce tasa malam NURA sanin kuka ne take da sauri yace "tashi ki tafi"AMIRA na fitowa bata zarce ko ina ba sai gida.
A zaune ta tarar da Anna tana gyara waken ƙosai na gobe,ba sallama ta shigo gidan tare da cilli da hijab da niƙaf ɗinta ta fashe da kuka.Cike da tashin hankali anna ta fara tambayar ta lafiya "na gaji!na gaji anna doli ki gaya min wacece ni ko kuma wlh na bar maki gidan ki"dafe ƙirji anna tayi "AMIRA c'est une longue histoire ta yaya ta ina kike so in fara ki bari har ki ƙara girma kinji ƴata"anna ta faɗa tana shirin dafa AMIRA amman ta goce tayi hanyar waje"ki dawo zan baki ciwon da bai barin ka ai gwara ya kasheka ka huta"dawowa AMIRA tayi ta zauna kan tabarma, "AMIRA zan gaya maki kaɗan daga cikin abinda na sani"
*Asalin labarin....*
A damagaram an yi wani shahararren malami mai fatawa mai kuma riƙo da addini,NASIR shine sunan shi wasu kuma suce malam NASIR shaharar shi da tayi yawa yasa aka koma kiran shi da malam mai ruwan ikon Allah domin yana bada magani sosai kuma ana dacewa.
Malam Nasir nada mata guda tal mai suna RUMAISA sai dai dayawan mutane suna kiranta da RUMAI ,tun da suka yi aure sun kwashe shekara goma ko ɓatan wata RUMAI bata taɓa yi ba.
Son da malam NASIR ke yi mata ne yasa bai ɗauki wani abun babba ba sai dai yace lokaci ne bai yi ba,duk surutain mutane basu damun shi dan wasu har magana suke yaɗa mashi "in kura na maganin zawo tayi ma kanta"shine habaicin da ake mashi haka ma matar shi.
"Ni ban ga abun kuka a nan ba komi fa nufin Allah ne,ta yiyu kuma Allah ya jarabce ni ne dan ya gwada imani na sanin kanki ne mutane dayawa wurina suke amsar maganin haifuwa kuma sun dace"cewar malam NASIR yana rarashin matar shi da tun da garin Allah ya waye take kuka,"to malam sai muje wani gun mu nema mana ga MABARUKA nan sai baiwa mata magani take suna haifuwa ni ka..."saurin katseta yayi "Allah sawaƙe da in barki ki kisha maganin ƴan bori "
"Ai kam maganinta na yi ka san gado tayi"
"In bori gaskiya tayi ma kanta maganin da zata samu miji mana"cewar malam yana mai ficewa makarantar rana wadda yake koyar da almajirai.
Fitar shi ke da wuya ta zumbula hijab bata zarce ko ina ba sai gidan MABARUKA,wani gida ne na jar ƙasa tun daga soron gidan zaka gane sun yi bankwana da hanyar Allah ƙawonni ne irin na manya bisashe da ƙwanƙwamaye☠️💀 sai wani hoton ƙaton aljani jawur da shi ya fiddo haƙora waje da zaratan akaifu.
Zuciya na bugawa ta ƙarasa ciki tare da yin sallama "ba ayin wannan abar a nan gidan kibar kawo mamu Allah cikin gidan mu,ki cire takalmi ki shigo"taji wata murya daga can cikin wani kutuɓu na faɗa,takalmi ta cire ta shiga tana mai fidda niƙaf,dariya MABARUKA ta kece da ita kamin ta tsagaita "matar malam da kanta hhhh dama na rantse doli sai kun zo neman taimako na tunda yace zai ja da mu sai mun ga bayan shi"
"A'uzubillahi minna shaitanun rajim"RUMAI ta furta "keee!ba anan gidan ba ke matar malam da ke da shi duk sai mun yi maganin ku"cewar MABARUKA tana zaro ido waje "ta Allah ba taku ba eh gaskiyar malam da yace in bori gaskiya kiyi ma kanki maganin samun miji"RUMAI ta faɗa tana mai cigaba da ambaton sunan Allah .
Da ta dawo gida kuka ta fashe da shi tana danasanin zuwa,maganar MABARUKA kuma ya tabbatar mata da akwai wani *ƁOYAYYEN SIRRI* da malam ke ɓoye mata shiyasa bai son ko sunan unguwar da MABARUKA take a ambata.
Tana cikin wanga zulumin taji kamar an gitta ta gabanta an wuce,sai kuma taji kamar ana jan hijab ɗinta wani tsoro ne ya ɗarsar mata lokacin da taji kamar ana mata bincike cikin ɗaki.
Ta zabura ta diba sai taga tsintsiya ta miƙe da kanta tana shara "kwayat-kwayat" tukunyar da ke bisa murhu na buɗe kanta ta rufe kuma,da gudu ta nufi hanyar waje ƙyauren gida ya bada gammm ya rufe.......
Ƙarshen book one sai mun haɗe a part two
*Duk mai son cigaba zai iya tuntuɓar wannan number* +22795045822