Showing 12001 words to 14963 words out of 14963 words
Chapter 5 - DOCTOR NAWWARA Book 1 by Ummu Maheer Miss Green .txt
a idanuwan Alhaji Adam wato Mahaifina.
A hankali Mai Marta ba ya tashi dogaransa na binsa ya mik'omai hannu suka k'ara gaisawa sannan Ya CE".ki rawo min Mahaifinsa awaya muji me ke faruwa?don muna ta zaune kowa kuma yana da inda zaije.
Haka kuwa aka yi Mahaifina ya kirawo wayar Mahaifin Saif ringing 1 ya d'auka suka gaisa sannan Mahaifina ya fara tambayarsa abinda yasa suka yi musu haka?
Nan Mahaifin Saif ya shaida masa wai yanzu Saif ya shaida musu wai ya fasa Auren Nawwara.....
Please kuyi hak'uri ina tyiping kad'an na yi busyne 👏🏼.
Sauran 2page in gama na bati ki hanzarta ki biya naki domin ki karanta wannan littafin domin dad'in yana gaba.
*UMMU MAHER CE*
[12/8, 06:22] Rabiatu🥰Ummu Maher🏕️⛱️: [11/25, 17:30] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: *_⚡DOCTOR NAWWARA⚡_*
NA
(UMMU MAHER) MISS GREEN🍀
Na kusa gama free pages start paying 200 ne kacal ta wannan account number 2212328303 RABIATU BASHIR ZENITH Bank.ko katin Aitel ko na Mtn ta wannan number 07068606171.yanzu za'a fara labari.
16🟩17
..hankalin Mahaifina ya tashi sosai,da Saif yasan bazai Aureni ba ai ba zai tara mutane akan aikin banza ba,Mai Martaba ma yaji haushi sosai akan abinda ya faru,matsowa yayi dai dai kunnen Alhaji Auwal ya rad'a masa wata magana ban san ko meye ba ni dai Ummu Maher naga Alhaji Adam ya fara fara'a nan da nan aka sanar cewa akwai d'aurin Auren da za'ayi kowa ya tsaya,abinda kowa yayi mamaki dashi shine Sarki mai Martaba ne ya d'aurawa d'ansa Auren Nawwara.
Nan fa wajen ya kaure da maganganu wad'anda suka San abinda Yarima Jalal ya ke ciki suka dunga tausayawa Nawwara don wasu har kwalla suka yi mata cewa ita ma ta zama gawa kamar yadda sauran matan nasa suka zama gawa,Mai Martaba ya umarce Alhaji Adam bayan d'aurin Aure akwai maganar da za suyi ta sirri,aka d'aura Aure akan sadaki dubu d'ari.
Bayan an gama d'aurin Auren ne Mahaifin Nawwara ya samu Mai Martaba a babban falon gidanshi Amman ba ainahin gidanshi,Gidan da yake hutawa.
Babu abinda Mai Martaba ya b'oyewa Mahaifin Nawwara komai sai da ya sanar dashi har zuwa yanzu,Mahaifin Nawwara ya yi shiru hankalinsa ya yi matuk'ar tashi,cen kuma ya CE"babu Komai Allah ya shige mana gaba,daga haka suka cigaba da zantawarsu akan matsalar da kuma yadda za,ah tun kari matsalar da shi Kansa angon yadda za'a sanar mishi.
Gidanmu ya cika damk'am bayan y'an d'aurin Aure sun dawo kowa fuskarsa babu fa'a sam,kowa kaga fuskarsa kamar anyi mai alk'awarin shiga wuta.
Yayan Mahaifiya ta ne ya sameta ya fad'a mata duk abinda ya ke faruwa sannan ya ce kada a sanar dani da wuri saboda hankalina zai tashi,Umma ta samu Lanta da Yanyala da kuma sauran y'an uwa ta fad'a musu abinda ke faruwa cikin tashin hankali,kowa da abinda ya ke cikin ransa mamaki da kuma tausayin Nawwara,haka suna ji suna gani aka hana kowa sanar da Nawwara abinda ya ke faruwa.
Ni kuwa haka kawai naji gabana yana fad'uwa don rabona da waya da Saif kwana 1 kenan har yanzu ko da na buga wayarsa baya d'auka,ko gaisuwar iyaye ban sunzo sunyi ba tunda al'adarmu CE yin hakan,na yi matuk'ar damuwa ga shi har yamma ta yi wayarshi switch up.
Na kalli Humaira Y'ar k'anwar Mahaifina na CE"wallahi Humaira narasa me ke damuna gaba ki d'aya zuciyata babu dad'i tun jiya nake kiran wayar Saif a rufe"?na fad'i hakan ina ya mutsa fuska kamar zanyi kuka.
Allah ya Sani ina matuk'ar son Saif bazan iya rayuwa babu shi ba,tunda muka fara soyayya bamu tab'a kwana 1 ba muyi waya ba koda text message ne sai gashi yau aranar d'aurin Auren mu wannan matsalar ta faru.
Humaira ta yi dariya ta ce"kai gaskiya Nawwara kina da zumud'i wallahi kin San wasu angwayen sunfi son hakan sai kinje su jiyar dake farin ciki,don haka ki daina damuwa watak'il angwan naki suna cikin irin wad'annan mutanen.
Ban gama shiga damuwa ba sai da dare ya yi naji babu Wanda ya yi min maganar kai ni d'akin miji,gashi ni kuma babu damar in tambaya?ranar har 10 na dare banyi bacci ba ina cikin tashin hankali sosai.
Ko dai Saif ya mutu ne?ake bb'oyemin in dai har ba mutuwa yayi me yasa ba a gaya min ba?babu tambayar da banyi wa kaina ba Amman na nakasa gano amsar don dole na hak'ura na kwanta bacci b'arawo ya sace ni.
Cikin bacci na na yi wani mummunan Mafarki wai gani a wani daji babu kowa ina ta kuka,wata mata tana bina da wuk'a kawai sai na ga wani kyakkyawan matashi yazo ya hankad'eta ta fad'i k'asa.
Nan matar ta fara ihu tana kuka matashin ya ruk'o hannuna muka tafi wani gida mai kyaun gaske,dai dai na farka a gigice ina kiran sunan Allah,y'an matan da ke d'akin suka fara tambayata ko wani Abu ne ya faru?na ce musu a,ah.
*Yarima Jalal*
Yana kwance a babban farlonsa yana kallon wani kabarai a aljazira,kawai sai yaji kiran mai Martaba a wayarsa ya d'auka cikin girmamawa ya gaishe shi Yace yazo yana son ganinsa yanzu,kafin ya amsa kawai sai ganin Saima akansa tana wani had'e fuska.
D'aga mata gira ya yi alamar tambaya?.
"Wai Jalal dawa ka ke waya ne kake wani kashe murya a farlona"?
" ke kin isa ki hanani waye acikin gida na?ki Sani cewa ita dama 1 ce take zuwarwa mutunm arayuwarshi idan damar ta wuce shikken don haka ki yi taka tsan tsan da rayuwa.
Tashi ya yi ya shiga d'akinsa ya fesa wankansa ya yi matuk'ar kyau Yarima irin mazan Nanne masu zubin k'arfafa irin y'an raatilin d'innan,ga kyau ga kud'i ga kuma ilimin addini sai abin ya bada armashi sosai.
Yana sanye da yadinsa ruwan fari mai shara² ya taje sajensa mai yawa ga shi sai k'elli ya ke yi,yana cikin fesa turare Saima ta shigo ta wani rafka salati"ya juyo ya wuce ta kusa da ita yana tsaki.
Binsa ta yi da kallon mamaki wai yau Yarima ne ya ke yi mata wannan shan kashin,lallai ta yi sake a wannan lokacin don yadda ta saka aka d'aure bakin Yarima sai yadda ta ce ya yi,Amman wai yau ne har da wannan shirin kamar me shirin zuwa tad'i,lallai dole ta yi wani Abu don ba zata tab'a had'a miji da wata mace ba yadda take son Yarima tamkar ranta,kuma za ta iyayin komai saboda ta mallakeshi shi kad'ai.
Tuni ta nemo wayarta ta d'auko wata number hannunta har yana kakkarwa,ringing 1aka d'auki wayar kamar zata fashe da kuka ta fara magana.
"Na shiga ukuna ni Saima domin asirina gab ya ke da tonuwa wai
[11/25, 17:51] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: Ni Jalal ya ke wulak'antawa harda yimin tsaki,daga d'aya b'angaren na jiyo muryar wata mata na cewa"to se me idan yayi miki tsaki kedai kawai ki rik'e mana alk'awari kada ki bari kowa yasan halin da muke ciki don tonuwar asirinmu tonuwar asirinki ne don haka kiki yaye.
Saima bata so hakan ba Amman babu yadda ta iya dole ta yi musu biyayya ko don kwad'ayin abin duniya.
"Jalal ba komai ne yasa na kirawo ka ba magana ce mai mahimmaci don haka ka nutsu kaji me zan CE maka ba umartarka ko Neman izininka na ke yi ba,domin kuwa na Riga da na yanke duk wani abinda zanyi don haka ya zamar maka dole ka yi min biyayya.
Shi dai Jalal kanshi a k'asa ya ke yana sauraron fad'an da Mahaifinsa ya ke masa,don zai iya cewa hakan bata tab'a faruwa a tsakaninsu ba don haka koma menene wannan abin yana da matuk'ar mahimmanci.
Nan Mai Martaba ya fad'a mai duk abinda ya faru har zuwa yanzu da ya D'aura mai Aure ba tare da saninsa ba.
Wani irin razana Jalal ya yi idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sunyi rud'u² alamar b'acin rai sosai a fuskarsa da zuciyarsa,Me yasa mahaifinsa ya yi masa haka?me yasa be nemi shawararsa lokacin aiwatar da wannan babban laifin ba,azuciyarsa kuwa harya fara tausayawa wannan yarinyar domin Mahaifinsa yafi kowa sanin halin da ya ke ciki duk matar da ya Aura sai haka ya faru da ita ma'ana sai ta mutu, Saima ce kawai Allah yasa da sauran kwananta agaba Amman ita ma mafi yawanci tana gaya masa irin mafarkan da ta ke yi lokaci zuwa lokaci.
Shima Mai Martaba tashin ya yi daga zaunen da ya ke sannan ya CE"Jalal nasan abinda ka ke tunani nima na yi wannan tunanin Amman nasan koma menene ajiki na ina jin wannan Auren naka shine zai kawo k'arshen komai Insha Allah.
[11/25, 18:19] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: Zamu dage da addu'ah insha Allah babu abinda zai faru na saka ayi mana saukar alQur'ani mai girma insha Allah babu abinda zai faru kaima ka dage da addu'ah insha Allah wataran ko bayan raina sai ka yi alfahari da wannan Auren,Domin Allah ya Sani har yanzu akwai wani Abu da ya ke cikin raina kuma na ke zarginsa domin nasha mafarki da fuskar mutumin Amman Allah baya bacci ka dage da addu'ah.
Har yanzu hankalinsa bai kwanta ba gani ya ke yi kamar ma ana sane ake had'a shi da mata yana Aura suna mutuwa,ko dai maganar da Saima ta tab'a gaya mai ne akan cewa Kodai iyayensa suna sane suke had'ashi da Mata suna mutuwa,yana son iya yensa sosai bazai tab'a yiyuwa ace sune suke yimai haka ba,don ranar da Saima ta fad'i wannan maganar ba k'ara min fad'a suka kwasa ba don bazai tab'a bawa wata mace damar yiwa iyayensa wani cin zarafi ba don iyayensa sune gaba da komai a rayuwarsa.
*Nawwara*
Wani irin ihu na saka alokacin da Mahaifina ya ke shaidamin duk abinda ya faru ina kuka Lanta na kuka ta rungumeni tana cemin ai Allah ya musanya min da abinda yafi alkhairi tunda gashi yanzu na Auri d'an Sarki,wannan Kalmar ta kaka ta itace ta ke k'ara yimin k'una acikin Zuciyata ban sanshi ba?ban San daga inda ya ke ba kawai sai ace an d'auramin Aure dashi?.
*Ummu Maher CE*
[12/8, 06:22] Rabiatu🥰Ummu Maher🏕️⛱️: *_⚡DOCTOR NAWWARA⚡_*
NA
(UMMU MAHER) MISS GREEN🍀
Na kusa gama free pages start paying 200 ne kacal ta wannan account d'in account number 2212328303 RABIATU BASHIR ZENITH Bank.ko katin Aitel ko na Mtn ta wannan number 07068606171.yanzu za'a fara labari.
Ina y'an kasuwa masu son a d'ora musu kayansu a dukkanin page d'in don samun costumer Ku hanzarta a kud'i k'alilin Naira500 wato d'ari biyar ne zan saka miki a page d'in don samin jama,a ko ina.
🍀🍀🍀🍀🍀
UMMU FU'AD wata shararriyar y'ar kasuwa ce wacce ta shahara wajen kawo muku magunguna da na saka jiki sirrin k'amshi.
_Ina mata wad'anda Mazansu suke wulak'antasu da sauransu ina mata masu son su samu sirrin k'amshi to ga dama ta samu._
Tana kawo kaya kamar haka.
_Turaren jiki mai Sirrin k'amshi da kuma kama jiki wato Jas'ud_
*Nida Mija*
_Akwai turaren da zaki shafa wajen kwanciyar Aure yana k'ara shauk'i da k'ara soyayya wajen kwanciyar Aure,kinsan komai sai da gyara.
Ki kirani ta wannan number
08132506044
*Hawii & first lady*
Wannan shahararren turare mai k'amshin da d'i Wanda idan kika zo waje musamman a taron mata,zaki ga mata na tambayarki wani irin turare kika shafa don tsabar k'amshinsa,kedai hanzarta ki nemi naki ta wannan number.
08132506044
*_Infection_*
Akwai ingantaccen maganin infection Wanda yake fito da sanyi baki d'yansa,don ko wani irin sanyi ne yake damunki insha Allah zaki nemeshi ki rasa,don Duk abinda ke k'ara ruguza Aure to yawanci sanyi ne don haka idan kinsan kina da sanyi to ki hanzarta ki yi maganinsa.
18🟩19🟩20
.... Hankalin Saima ne yayi mummunan tashi ganin inda ta ajje dodon asirinta bata ganshi ba ta duba ko ina bata ganshi ba, ta duba na k'ark'ashin gadonta ma bata Ganshi ba?ta duba na cikin kayan Jalal ma bata ganshi ba,wani irin ihu Saima ta saka sannan ta nemo wayarta ta kira wata number tana kuka.
Salati Saima ta saka sannan ta CE"yanzu Ya gana bokannan yayi tafiya yaushe zai dawo?ban me aka gaya mata ba naji ta saki salati ta Yar da wayar.
Gashi Jalal ya ce mata yayi tafiya Amman bai gaya mata inda zaije ba,Jalal da duk abinda zaiyi sai ya gaya mata,Amman yanzu ya juya mata baya lallai ya zama dole ta nemi mafita,don tasan Mijin ta duk inda ya shiga sai ance ana sonshi kyansa da sa nutsuwarsa ke d'aukar mutane.
...Mahaifiyata kuwa kuka ta ke yi me k'unar rai Y'ar ta guda 1 amman a ce anyi mata Auren sadaka,abin yayi matuk'ar k'ona mata rai sosai don haka bata ce da kowa komai ba kawai ta yi tafiyarta d'aki.
Washe gari da wani irin matsanancin ciwon kai na kwana,ina jin Lanta ta shigo tana tashi na nayi mata banza har ta gama sanbatunta ta tafi,ba a dad'e ba saiga Anty k'anwar Mahaifiyata wai in tashi in shirya da wuri za'a kaini kasan cewar Gidan sarauta basa kai amarya da daddare anfi kaita da rana kowa ya ganta,sai da ta yi da gaske sannan na tashi,ta kaini har ban d'akin sannan ta fara fitomin da kayan da zan saka,gaskiya nayi kuka sosai a band'akin kafin in fara cud'a jikina da k'arfin gaske saboda yadda nake jin zuciyata kamar zata fashe.
Har yanzu a zuciyata tunani nake me ya hana Layla zuwa gidanmu har yau tunda tazo sau 1 bata k'ara zuwa,kodai itama taji abinda ya faru da ni,oho?.
Wata rantsatstsiyar Lifaya ta d'aukomin da atamfa super Y'ar k'arshe da kanta ta shirya ni ina ta kuka kamar raina zai fita daga jiki na ta feshe ni da wani tsadaddan turare mai k'amshin dad'i ,ji nake da ma in mutu in huta don gaba ki d'aya rayuwar duniyar ta fita a kaina yadda muka shirya rayuwar da zamuyi nida Saif abin yana d'aure min kai a lokaci 1a ya janye Aure na,ni kuwa wani irin bak'in jini ne da ni haka?ayanzu inada she kara 24 Amman ban tab'a samun me sona ba,sai Doctor Saif shima yanzu gashi na rasa shi,sai gashi an Aurar dani a banza a sadaka.
Lanta da Yanyala sunyi kuka sosai kamar zasu shid'e sanda akazo tafiya dani Umma na kuwa k'in fitowa ta yi daga d'akin ta k'arshe ma da taji min isheta da koke² sai ta saka k'ira'a ta barmu.
Ko da akazo sakani a mota da k'er aka sakani ina ta kuka me ratsa zuciya,Naji Lanta na cewa akira Mahaifina Amman koda aka duba baya nan,a zuciyata kuwa cewa nayi watak'il yana cen Neman matan da ya saba,dole duk abinda kayiwa Y'ar wasu dole ne a yiwa y'arka wannan abin shike k'ara sakani cikin rud'u da kuma d'imuwa,yanzu ban san mijin da Allah ya zab'amin inyi rayuwar Aure dashi ba,ban tab'a ganinsa ba,ban sanshi ba?yanzu yaya zanyi rayuwar Aure dashi?.
Ina shiga cikin matar naji wani irin k'amshi me mugun dad'i da tafiyar da mutum cikin jin dad'i da annushuwa.
Ko da ba'a gaya min ba nasan cewa akwai mutun kusa dani Amman ban San waye ba?kuma har yanzu ban tsayar da kukan da na ke yi ba,jin zuciyata na ke yi kamar za ta fasa k'irjina ta fito.
Motar mu tana tashi na k'ara fashewa da wani wahalallan kuka kamar zuciyata za ta fashe,tsaki naji a kusa dani Wanda ya tabbatar min da cewa namiji ne a kusa dani,a ta ke wani tsoro ya k'ara d'arsuwa a raina.
Shi kuwa gogan Yarima Jalal yana gefen Nawwara kamar ya faska mata mari ya keji don yadda ya tsani Aurar nan haka ya tsani mutuwarsa,don tun kafin yaga wacece amaryar yaji wani mugun tsanarta.
Ya sani cewa baya son matarsa Saima don itama ba Aurar soyayya sukayi ba,kuma Saima baya kyautatamai ko kad'an kuma bata ganin iyayensa da y'an uwansa da mutunci,Amman zama da Saima ya fiye masa wannan Aurar don ya gaji da kisa da kansa don shi gani ya ke yi duk matan da ya ke Aura shi ya ke kashe su,kuma yasan ta dalilinsa suke mutuwa.
Don haka shi ayanzu yasan wannan Auran da aka k'ak'aba mai na alkhairi bane,kuma bazai tab'a Zame mai alkhairi ba.
Wani burki direban yaci kamar yaga wani abin tashin hankali da sauri Jalal ya CE"kai baka da hankali ne kayi wannan reverse d'in".
Kamar a kunnen Nawwara tabbas tasan wannan muryar Amman ta manta a inda ta Santa,bata gama mamaki ba taji an bud'e murfin motar b'an garen da Yarima ya ke.
Jalal yana fita naji Drivern ya ce min"Gimbiya ki fito ga Mai Martaba ".
Kamar bazan fito daga cikin motar ba,sai cen na fito don tsoro na ke ji yanzu na bar yin kuka.
Mai Martaba ya ce min" Y'ata bud'e fuskarki ki ganni in saka muku albarka"kamar ba zan bud'e ba Amman Dana tuno wani Abu sai na bud'e don ganin su waye wad'annan mutanen?".
Ina d'aga idanuna naga wani kyakkyawan dattijo a gabana yana yimin fara'a na gaisheshi ya amsa cikin fara'a sannan ya ce min yayi mana bizza yanzu zamu tafi k'asar England.
Shi kuwa Jalal gabansa yayi mummunan fad'uwa ganin fuskar Wannan yarinyar Doctor Nawwara wadda suka gani a lokacin da aka had'ashi da ita.
Yanzu wannan yarinyar CE aka aura mai? Yarinya mai nutsuwa da kamala Amman an cuceta an had'asu Aure da ita yana tausayin yarinyar tun bata mallaki hankalinta ba za'a kasheta da sauran k'uruciyarta.
Har mukazo Airport ban bud'e fuskata ba,hankalina a tashe,shin wanene mijin da na Aura?wani irin mutun ne shi?yaya kamanninsa suke?.
To duk wannan sai a gaba zamuji.
Shin wani irin zama Yarima Jalal za suyi da Nawwara?
Shin ita ma zata tsallake ba tare da wani Abu ya same ta ba?
Kuma wannan shine page d'ina na k'arshe ma'ana sai wad'anda suka biya kud'i zasu dinga ganin tyiping.
Idan kina San complete d'in shi to ki nemeni ta wannan number domin labarin sai ma gaba.
07068606171
*Ummu Maher CE*