Showing 1 words to 3000 words out of 19859 words
Chapter 1 - RAYUWA SAI DA KE Complet by Mimi queen.txt
RAYUWA SAI DA KE!
By
Ummu Ramlat @2020*
*Allah ubangiji muna rokon ka ka tsare mu daga wannan Annobar data kunno mana ta damemu ta corona virus. Allah ubangiji ka mana tsari da covid19 dan darajar sunayenka tsarkaka Allah ka nisantamu da ita ka mana tsari da ita (Amin ya rab)
*Littafin Rayuwa seda ke Sadaukarwane ga Manazarta writers Association
*Amin Afuwa da kyautar pages da zanyi*
*Special greeting tareda fatan Alkhairy zuwa ga manyan Aunties dina*
*Aunty Hamdiya (Maman husna)*
*Aunty Momy (Maman salman)*
*Aunty Rabi'a maiwa*
*Aunty Khadeejat (Maman yesmeen)*
*Aunty zee (Maman sajjad)*
*Aunty Ameena (Maman zuhrah)*
*Sis Ummi (Maman sajida).........*
Da dai sauran wa'inda ban lissafoba *I want you to know that u makalize in my heart.*
*Labari ne daya kunshi tsantsar soyayya kunci tareda farin ciki tausayi dadai sauran su dan haka kukasance tareda ni Bintu Isah danjin abinda ke ciki*
*Littafin RAYUWA SEDA KEE is a true life story labari ne daya faru dagaske ba kagagge bane kuma ba'a yishi dan cin zarafi ko batanci ga waniba dan haka dan Allah dan Allah aguje zargi kuma idan yazo daya da rayuwarka ko littafin ka please amana afuwa anyine bisa rashin Sani*????
*Nagode*????
Page 1& 2
*Tana* sanye cikin English Attire riga da skirt pink and blue Wanda yai bala'in kamata rolling tai da karamin veil Wanda yake Shara Shara tayi parking dogon gashinta Wanda yasha gyara da pink band,
kafafunta na sanyeda high hill blue mai masifar kyau farace tas siririya wacce ko baa fadaba yanayinta xe tabbatar maka dacewa shuwa arabce, tanada shape din coca cola tanada manyan ido da karamin baki mai dauke da pink lips....huh in short dae kyakykyawace ta akin farko
bazata wuce shekara goma sha bakwaiba amma inkaganta zakace takai 20 don akwaita da cika ido, a hankali take tapiya kamar me tsoron kasa ta shagwabe fuska tanadan yarfe hannu da alama agajiye take,tana gama saukowa daga staircase din tayi tsaye agefe tana duban agogo da alama wani take jira,
Ji tayi andafata tabaya tajuya da sauri tareda sakin karfaffan ijiyar xuciya dan ganin kawarta Ferryce, murmushi ferry tayi tace " *SABREENA* mekikeyi anan."? takara shagwabe fuska tace " *Bobby* nake jira"
murmushi ferry takumayi tareda fadin "why not bazaki tari abin hawa kitafiba dole saikin jirashi" Sabrina tabata fuska "how kike tunanin xantafi bayan yana hanya so kike yaxo be sameniba....."
bata rufe bakiba tajiyo kamshinshi na dindindin dan haka takara shan kunu, ferry ce tace "to Sabrina gadan halak dincan"
juyawa tayi Tamara daure fuska tana kallonshi, yana sanye cikin kananun kaya red wandon chinos da blue shirt bakaramin kyau yayiba,
kallo daya xaka mishi kaga kama kwance afuskarshi shida sabreena kuma shima yanayinshi da komae yanuna cikakken shuwa arabne infact dai gayen ya hadu sosae Wanda kallo days xakayi mishi kasan dan hutune kuma komai nasa a natse take yinsa,
tundaga nesa yasa hannayenshi Yakama kunnuwanshi harya kariso gabanta ya marairaice fuska cikin sigar lallashi yace"I'm really sorry Mimi please pardon me"
yanda ya marairaice ne yabata dariya har saida murmushinta me kara bayyanar da kyanta ya kufce a labbanta Wanda ya haddasa lotsawar kumatunta ta shagwabe fuska "bobby u keep me waiting since"
yakara riko kunninshi "am sorry wallahi excuse ne yarikeni amma tundaxu na taho a hanya motana ta samu Marsala shine nasa aka kawomin wata but am sorry Mimi" tayi murmushin shagwaba "ok let go" yasaki kunnin yakai hannu ya Karba jakar hannunta, murmushi ferry tayi data xama photo tace " *AMJAD* manya kokadan bakasan batama sabreena rai"
gaba Sabrina tayi batare dataji amsan dayaba ferry ba dan agajiye take,kafin takarisa gurin mota shima yakariso dan haka yabude mata tashiga shima ya zagaya yashiga
sannan yatada suka day hanya, kallanshi tayi cikin shagwaba "bobby I'm tried" ya dubeta yanda take shagwaba domin yanasan childish behaviours dinnan nata yace "don't worry mimi mun kusa gida" lumshe ido tayi race "kasan last night I'm sleepless" "I know" ya fada sannan ya daura "please kidinga yin bacci sosai Mimi kinji ko" race "air dolena tunda mun kammala exams din yau" da wannan suka karasa gidansu fake barnawa nan Kaduna state, bayan me gadi ya bude musu wagegen gate din suka shige sukayi parking a parking space din gidan India motocine birjik a pake a gurin, ya fito ya zagaya da sauri ya bude mata tafito
sannan suka jera zuwa bangarensu Sabrina ,Karin su karisa a bakin kofa sukaci karo da Abban Sabrina, Amjad da Sabrina suka gaidashi ya amsa yana duban Sabrina "ke kuma me take damunki u look weak?" cikin shagwaba race "Abba I'm tried....." Yayi murmushi "shine kika koma haka?" Amjad yace "Abba Kwana biyu bata bacci saboda exam amma yau suka kammala kasan dole tagaji" Abba yace "to kushiga ciki kabata abinci" suka shige,
mahaipiyarta tana zaune kan cushion tana kallo tafada jikinta "Ammi nagaji" Ammi tadubi Amjad race "xauna mana" gefe ya zauna yana duban Sabrina data lafe jikin Ammi, sukainat ce tashigo ta gaida ammi tareda duban sabreena race "kundawo lpy Aunty didi?" race "lpy sukainat Ina deenah?" "tana daki" tafada tareda duban Amjad race " Yaya mummy tana kira" ya tashi yana duban sabreena yace "ammi bari naje yanxu zan dawo kiba Mimi abinci" daga ido tayi tana kallonshi harya fice , tashi tayi daga jikin ammi ta haye sama, inda tana shiga ta tube ta fada gado.
*Leemcy* ?�ï?
*Comments*
*Share*
*Vote*
*RAYUWA SEDA KEE!!*
*Ummu Ramlat @2020*
Page 3&4
Misalin two Amjad ya shigo yana tambayan Ammi Mimi, tace."tana sama tunda tashiga bata fitoba danko abincima bata ciba." aiko da sauri ya haye sama knocking yayi jin shiru yasa ya murda handle din yashiga tsayawa yayi yana kallonta, tana kwance ruf da ciki ta daura kanta kan pillow gashinta ya barbazu kan filon zuwa gadon idanunta a lumshe suke kamar me bacci ammah idan aka lura da pink teddyn da take shafawa da hannunta a hankali za'agane ba bacci takeba tana sanye cikin pitted gownt pink iya gwiww wacce take Shara Shara, ta dage kafarta sama duk da tasan an shigo batasan wayeba sedai kamshin shi da taji shiya tabbatar mata dako waye amma bata motsaba, kari sowa yayi kusa da ita."Mimi wake up." ta juyo da kai tana dubanshi."Bobby I'm not well kaina kemin ciwo." tayi magananne da shagwaba ya kamo hannunta ya zaunar da ita tareda kai hannu kan wuyanta yanajin yanda jikinta yayi zafi cikin damuwa yace."tashi ki shirya muje asibiti......." da sauri tace."aa bobby banasan allura." huci yasaki me zafi saboda yafi kowa Sanin babu abinda Mimi ke tsoro irin allura, yace."to naji magani kawai za'a Baki." ta shagwabe fuska."aa bobby banasan magani shima." ya sake dubanta."to me kikeso kenan? Aiko dole kizabi daya." ta girgiza kai."banasan ko days." hannunta yaja."to naji tashi muje kici abinci se kisha magani kinji mimina." ba musu ta rikoshi suka fito, kan kujerar dinning ya zaunar da ita ya bude chicken nuggest din da Ammi tayi ya mutsa fuska tayi ganin ya zuba white rice ze zuba chicken din duk da yasan Sabrina bata cika cin abinci ba sedai ta sha quaker oasts,drinks,fruits amma bata cika San cin abinci me nauyiba ya mutsa fuska ta kumayi lokacin daya debo abincin yakai bakinta tabude baki zatayi magana ya hanata ta hanyar lumshe ido yace."just eat bakida karfi sosae kuma kanki na ciwo dan haka kici heavy food first." tayi rau rau da eyes Wanda suka tara kwalla tabude baki ya saka mata, ya bata sau hudu ana biyar yaga kaman batajin dadin abincin dan haka ya ajiye spoon tareda dubanta yace."me kikeso kici."? tace."Bobby." yace."uhmmm." tace."my favorite.
" ya bata fuska tare da janyo basket bowl daya cika da fruits kala da kala ya dauko kankana ya balla ya saka mata a baki, lumshe ido tayi a haka ya dingi bata tasha sosai sannan ya zuba quaker oasts saboda shine favorite din nata ya zuba sugar da madara yadingi bata, Ammice ta kariso tana fadin."lallai Amjad kana shagwaba wannan kanwar taka sosai abincin ma bazaka bari taci da kantaba kai zaka bata." Cikin shagwaba tace."Ammi idan be shagwaba niba wazai shagwabani."? amjad ya dora."kuma kinga am only her brother kinga ai dole na shagwaba ta, ko Mimi."? tadaga kai tashi yayi yaje ya dauko kit din magunguna ya dawo, sabreena naganin ya ballo magani tafara kuka janyota yayi yace."oya take it kona miki dure." ta bude baki yasaka mata yabata ruwa ta hadiye tana hadiyewa ta fara kakarin amai, yana dariya yace."ki tayi koma meye dai inbakida lafiya dole kisha magani." cikin kukan shagwaba yace."Bobby ba dadifa maganin." Ammi tace."to ai dama badan dadi ake shan magani ba sedan lafiya." ta turo baki tace."amma bobby kan yadaina ciwo tunda naci abinci." Yace."sorry Mimina kece baki fadamin ba amma bazan karaba." ya kamo kumatunta."than smile." ta washe hakora dariya duk Kansu sukayi Wanda yake kara tono asirin kyansu har saida dimple dinta ya lotsa, lumshe ido tayi ta bude tana kankance ido tana dubanshi ya kalleta."lafiya mimi."? tayi murmushi."Bobby bacci nakeji." ya tashi tareda kamota."to muje seki kwanta." Suka nufi upstairs sun fara taka staircase Ammi ta lura dasu."lafiya amjad meya faru."? yace ."Ammi wai bacci zatayi shine zan rakata." murmushi kawae tayi yayinda suka haye, seda ta kwanta ya rufa mata blanket sannan yace."sleep well mimi bari naje naci abinci." tace."kayi hakuri bobby na kyaleka kai kadai bayan nasan baka iya cin abinci ba tare d." kumatunta ya shafa."don't mind Mimina kedai kiyi bacci da kyau." nan ya fice murmushi tayi ta lumshe ido tana tunanin cousin din nata yana ji da ita sosai yana kula da ita tun tana karama shiyasa itama take nunamai kulawa.
******
Kwance take sanye da sponge bob riga da Yar mitsitsiyar wando iya cinya kanta ba dan kwali amma yasha gyara wayan tane ya hau ruri kallan screen din wayan tayi ferryce amma har wayan ya karaci ruri ya tsinke bata dagaba har na biyu ya shigo infact dai saida tayi mata missed calls biyar amma tana gani bata dagaba saboda tsabar miskilanci, sema tashi tayi ta shiga toilet ta jima Kafin ta fito sanye da dan karamin towel pink iya cinya sannan tana tsane jikinta da karamin towel knocking taji anyi bata kai da bada iziniba aka afko kallan ferry tayi rai bace tace."meye haka ferry zaki fadomin daki ba tare da iziniba."? ferry tace."ke sorry niba wannanba yau nefa event din bikin feenah inata kiranki a waya kinki dagawa, ko baki kusane."? ."Ina gani ra'ayin daga wane banyiba." Sabreena tabata amsa a takaice ferry ta bude baki."ah au yau kuma mulkinne ya motsa kenan."? bata bata amsaba illa mai data fara mulkawa, Ferry tace."to ki shirya ina jiranki." ta sauna gefen bed har Sabrina tagama shafe shafenta dukda ba wani kwalliya takeyiba amma ba karamin kyau tayiba domin fuskarta is ready made ko batai kwalliya ba, wardrobe tabude ta dauko half gownt pink tasaka kallonta ferry tayi sama da kasa Kafin tace."Shuwa wannan dress din beyiba karki manta event din Feenah zamuje ba night club ba." Sabrina ta kalli kanta da kyau sannan tajuyo tana kallon ferry from head to toe tace."meye aibin shigena? kuma da kikace na canza kinsan ni bancikasa manyan kayaba aka Sarima ni bana dasu da yawa." Ferry tace."duk da nasan ba kicika sawa ba ki canza akwai wani pink material a wardrobe dinki ko shine kisha." Ferry ta tashi tabude wardrobe ta dauko mata, duk da bata cika Sa manyan kayaba amma datasa ba karamin kyau tayiba ferry ta tsaya tana kallon yanda ta hadu musamman daurin head dinta ferry tace."Shuwa keda basa manyan kaya kikeba jubi yanda kika daura head din." Sabreena tace."ai dukda ba sawa nakeba ina gani ai kuna daurawa." Ferry tace."Ashefa namanta ke gifted ce kallo daya zakiwa Abu kidauke shi jubi dai yanzu kaman dama can kin saba daurawa." gyale ta dauka da jaka tasa shoe suka fito, kallonta Ammi take cikeda shaawa ta shagwabe."Ammi zamuje patyn nafisa." Ammi tace."to Allah tsare sekun dawo." nan suka fice, suna fita Sabrina tayi hanyar bangaren su Amjad ferry tace."Ina kuma zakije."? tace."Bobby zanje nakira domin kinsan bazana iya tafiya ba tare da Shiba." Murmushi ferry tayi sabreena ta wuce,yana biyu kannin Amjad deenarh da sukainat kawae tasamu a falo suna wasa yaran suna ganinta sukace."Ina wuni Aunty didi."? ta amsa musu tareda nufan dakin amjad, doorbell ta danna jin shiru yasata shige a lokacin yafito daga toilet karamin towel ne a hannunshi kadai yana tsane sumarshi dashi da yikeshi tun a toilet corner yake cire towel da sauri ta juya tana fadin."banga komati ba." murmushi yayi cikin sauri yasa kaya jikinshi seda ta dade a waje Kafin tace."In shigo ka kisha."? yace."uhmmmmm." sannan ta shiga yana kallonta yanda tayi kyau ta turo baki."Bobby kallon yayi yawafa." yana dariya yace."naga kinyi kyaune. Mimina." Cikin shagwaba tace."oh dama can banada kyaune."? yace.
"Aa ba haka nake nufiba sedai maganan gaskiya manyan kaya bakaramin kyau suke mikiba, dan zoma muyi photo." da sauri ta matsa ganin yana matsowa ."no bobby kasa riga tukunna." Se lokacin ya kalli kanshi Ashe besa rigaba towel kadai ya daura a kugu tace."bari najiraka a waje kashirya kafito se muwuce dan kasan ferry na waje tana jiranmu." Kai ya gyada mata daganan tafice, falo taje inda tasamu mummyn Amjad tareda yara takariso suka gaisa, mummy tace."haka Amjad kike jira."? tace."Eh wallahi mummy."tace."to maza zo kizauna yara." takarisa ta zauna kusa da mummy tana kallon su sukainat dasuke Assignment baa jimaba yafito yayi kyau sosai tana murmushi tatashi sukayi sallama da mummy suka fice, zaune suka samu ferry a daya daga cikin resting chairs din haraban gidan ta gaji da jira ta zauna, tana ganinsu tatashi tsaye tana fadin."Ammafa kun shanyani." Amjad ne yace."Afwan farida." murmushi tayi yayinda suka karisa gurin motar amjad blue kirar range robber baya ta shiga yayinda sabreena ta shiga gaba gurin me zaman banza ya tada suka fice suna firarraki da dariyarsu har suka Isa Anayin parking ferry ta fice tana fadin."se kun shigo." Sabreena ta janyo hadaddiyar handbag dinta data cikata fam da kudin manni tace."let go bobby." Kudi ya dauko a one side na motan yan dubu dubu bandir biyu ya daura akan cinyarta yace."Ayi manni."tace."lallai Bobby ni inada kudina Ammi ta cikamin jaka Kafin nafito." hannu yakai yanaso ya dauko jakan yana fadin."to hajiya kawo jakan nagani." tayi saurin daukewa tana dariya yace."ba za'a bani nagani ba."? tace."Eh." yace."to shikenan dauke wa'innan kudaden." dauka tayi ta bude jaka tasaka tareda bude mota tafito shima fitowan yayi, suna fitowa kawar sabreena da suke tsaye su uku tace."yawwa yan halak yanzu muka gama maganan Ku, dama idan anga Zara dole aga wata." murmushi Amjad yayi tareda cewa."Ni nawuce gurin abokaina mimi." yayi gaba ita kuma ta karisa gurin Amarya Feenah dake kan high chair Feenah tace."Se yanzu kika iso."? tace."Eh wallahi bobby na tsaya jira kinsan bana iya tafiya ba tare da shiba."murmushi Feenah tayi tace."lallai Shuwa kaunace me tsanani tsakaninki da Amjad amma idan akace San juna kuke se kidinga musawa." Kallon feenah tayi tace."NA fada miki Feenah ba soyayya tsakanina da bobby illa shakuwa ta jini da amintaka kinfi kowa Sani bobby shine babban Aminina kuma duk family dinmu babu Wanda jininmu ya hadu dashi kamar bobby kokin mantane tare muka taso tun muna yara taya kike tunanin soyayya muke bayan har wanka bobby yamin." Murmushi feenah tayi kawai ferryce ta kariso tana fadin."Shuwa gasu Billy can sunzo."da sauri ta tashi cikeda farin ciki tanufi gunsu rungume juna sukayi, billy na fadin."Shuwa ina Amjad din yaje."? tace."yana tareda Ango kinsan abokin angone." Murmushi billy tayi tace."Wallahi soyayyarku na burgeni gunin ban shaawa." tsaki sabreena tayi tace."wai so Nawa zan fada muku babu soyayya tsakanina da da bobby illa shakuwa kawai."ferryce tace."Ai wallahi Shuwa kallo daya za'a muku daga kee har Amjad din agane tsananin soyayyar dake tsakaninku."billy ce tace."dalla kirabu da ita muzata rainama wayau se kace Wasu yara."daga bayan Sabrina suka ji dance."Mimi." Juyawa tayi tana kallon Amjad ya miko mata freshmilk yace."gashi kisha nasan bakici komaiba." da sauri tace."yawwa bobby zokayi musu bayani sundage akan soyayyane tsakaninmu." Murmushi yayi yana dubansu yace."Allah sarki kudena wannan tunanin domin shakuwa ce kawai a tsakaninmu da yan uwantaka." billy ce tace.
"Seka fadawa Wanda be saniba hakan." Hannunshi Sabrina taja tana fadin."leave them bobby mutafi mu zauna." Suka wuce can gefe suka koma inda ba hayaniya kasancewar duk kansu basa San hayaniya, freshmilk din ya bude ya kai bakinta ta dingi amsa seda taji ta koshi sannan tace."Bobby I'm full." Rufewa yayi tareda tashi yace."bari naje na dawo."ta gyada kai ya wuce ta janyo waya tana daddan nawa, ba'a jimaba taga wani saurayi yazo gurin da take sallama yayi mata a dakile ta amsa yace."An bani dama in zauna."? ."Idan kana so." tabashi amsa har lokacin bata kalli fuskar shiba kanta na waya zama yayi tareda fadin."malama tun dazu naganki inaso inmiki magana sedai kuma kin bacemin yanzu shine na hangoki kina zaune anan, dafatan zaki saurari abinda yake tafe dani."? shiru tayi domin Ya dameta ya luura da hakan hakan yasa yace."da alama bakisan hayaniya."? A tsiwace ta dago tana ."To aidama tunda kaga nazonan na zauna ya kamata kagane banasan hayaniya ne." Ya dubeta da kyau yace."Allah sarki dafatan za'a bani dama nafadi sirrin dake Zuciyata...."? ."kabar sirrin a cikin zuciyarka base kafada ba." tafadi lokacin data hango Amjad yana nufo gurin ta dauki Jakarta tabar gurin tana fadin."Bobby mu tafi,shine kabar ni inata jira."? dariya yayi yace."waye wancan."? tayi tsaki ta juya takalli mutumin da yaketa kallonsu tace."Wai yawani zo yadameni nabashi dama yafadi sirrin dake zuciyarshi ni kuma nace yabar sirrin base ya fadaba.
" Cikin dariya yace."da'an temaka anbarshi yafada kada ya mutu dashi." Hararshi tayi tace."Au hakama zakace ko bobby."? Yace."to me zance zan zuba miki idone kin ki kifito mana da miji musha biki." Cikin shagwaba tace."Ni bayanzu zanyi aureba se naga naka." Cikin zolaya yace."Aiko zaki mutu bakiyi aureba yarinya danni matana na Aljanna." hararshi tayi cikin muryan kuka tace."Allah bobby banasan kalan wasan nan." Yakama kunnuwan shi yace."sorry Mimina." Nan suka samu guri suka zauna, A haka aka gudanar da