Showing 3001 words to 6000 words out of 20427 words
Chapter 2 - INDA BA KASA by Ummu Maher (miss green).txt
sune don su ɗauke musu kewa,don masu aiki maza da mata sunfi Goma agidan,duk kuma suna sanye ne da uniform ɗinsu gwanin sha'awa.
Ummita na ganin shigowarsu ta miƙe ta tashi,tana ɗan sosa ƙeya don ita aganinta a'i abin kunya ne wannan.
Baby kuwa kai tsaye ta shige banɗakin,ta koya wa Khairat komai ita kuwa ƴar girman kan tana ɗaki ta kasa zuwa taga komai.
Baby ta fito abinta,tana tsokanar Ummita ta fita waje,Ummita na ganin ta fita ta matso kusa da Khairat ta ce"ni wallahi Kunyar Babyn nan nake ji wallahi,musamman ma yanzu da kika sa ta gane mu ƴan ƙauye ne".Khairat dai bata ce mata komai ba ta fara cire kayanta tana ɗaura wani tawul alamar zata shiga wanka.
Ganin hakan yasa Ummita ta wuce banɗakin da gudu tana cewa"tunda an kunna fanfon a'i ba komai,bari inyi wanka na wankan da ban taɓayi ba,don taro kyakkyawa Baban Baby".
Ita dai Khairat kasa magana tayi,saboda yadda take nuna abu afili babu wani ɓoye ɓoye,Baban Baby shi kuwa wata irin macece bai taɓa gani ba?tunda yanzu ma wataƙil daga garin turawa xai dawo?."
Wani irin mugun ihu Ummita tayi,da gudu ta fito tana ihu tana cewa"wayyo Allah na fuskata,na ƙone Wallahi fuskata ta ƙone don Allah Khairat ki duba min"?.
Abinka da ɗan uwa da sauri Khairat ta fara duba mata fuskar,da yake Ummita fara ce sai ga wajen har ya ɗashe yayi jawur..sai kuma lokacinne Khairat ta tuno Baby ta ce mata fanfan na ruwan zafi ne,ga bokiti nan idan tana son ta haɗa ga fanfan sanyi nan gana Zafi,idan kuma da shower zasuyi gashinan,duk ta koyawa Khairat komai ita kuma ƴar girman kai bata tsaya ta koyi komai ba,ita dai abinda ta sani girman kai da kuma Buri.
Sosai Ummita ke kuka,Khairat tayi rarrashin har ta gaji sannan ta miƙe ta ce"Kizo muje in nuna miki yadda ake amfani da komai,don naga ke har yanzu baki san komai ba amman kuma girman kai ya hanaki ki koya".
Babu yadda Ummita za tayi,dolenta ta shige gaba suka shiga banɗakin don itama tana son koya,ko don gaba tunda sunzo gidan ne bada niyyar yini ba.
Khairat ta nuna mata komai sannan ta fito daga banɗakin,Sosai Ummita tayi wanka kamar zata canja fatar jikinta,tana yi tana santin ruwan da kuma sabulun,saboda ruwan wani irin mugun daɗin wanka ne dashi,ga sabulun da mugun ƙamshi gami da kumfa kamar kamfanin sabulu.
Ta ɗauki mintina da dama tana wannan wankan,har Khairat ta gaji taje bakin banɗakin tana bugawa,amman Ummita ko ajikinta sai da ta gama tsaf sannan ta fito,alokacin har Baby ta iso kuma lokacin bai fi mintina ya sauka ba.
Baby ta ce"kash!har yanzu baku gama ba?Momy na ta jiranku?to bari mu tafi saboda wallahi sun kusa sauka,gwara muje kuyi haƙuri yanzu zamu dawo".
Ummita ta kasa magana saboda tsabar baƙin ciki,ji take kamar ta kamo Baby ra daka taso ace yau ɗaya sunje filin jirgi amman Baby ta hana faruwar hakan,a cewarta wannan a'i baƙin ciki ne don kada aga Babanta.
Ita kuwa Baby taba fitowa ta samu Halima har ta shiga danƙareriyar motarta tana jiransu,Securities suna tsai tsai suna jiran su shiga su rufe.
Baby na shiga kuwa suka rufe,Halima ta ce"Baby lafiya kika taho ke kaɗai?ko basu shirya bane"?.
Baby ta ce"eh Momy basu shirya ba,kuma kinga Dadyna ya kusa sauka."
Halima ta ce"haka ne gaskiya don yanzun ma sai dai muyi sauri".
Halima na bada uder ɗin su tafi,motocin suka biyo bayansu wasu agabansu wasu a bayansu haka suka tafi Filin jirgin Baby sai murna take ita dai za taga Dadynta.
Halima kuwa duk bayan mintina sai tayi murmushi,yau wata biyu kenan rabonta da ta saka gwarzon mijinta a idonta,tana masifar son mijinta da kuma ƙaunarsa,bata son duk wani abunda zai shiga tsakaninta da mijinta,tana addu'ar Allah ubangiji ya barta da mijinta har abada.
********
. . .kai tsaye Indo gidansu ta wuce,tana shigowa gidan ta iske Innarta na tankaɗe,Indo ta zumbuɗo baki gaba sanan ta ce"gettere ! Yauma tuwon zakiyi Inna?gaskiya ni bazanci ba".?
Ko kallonta Innar bata yi ba,ta cigaba da tankaɗenta,Yayar Indo Aminatu nata wanke wanke,ta ce"don Allah Indo zo ki ƙarasamin zanje Makarantar Allo in bada hadda"?.
Indo ta ce"oh ni sai akace miki gantali nake ko?to zauna ki ƙarasa kayanki,kije kuma kisha bulalar malam Modibbo".
Aminatu tayi rau rau da idanuwa sannan ta ce"Inna kice mata ta tayani Allah za'a dake ni,ita kuma kinga ba zuwa take ba yanzu".
Inna ta kalli Indo sannan ta ce"ke yanzu Indo sai ance miki ki taya yayarki aiki?ke kullum babu abinda kika iya sai shegen yawo?babu arabi babu boko"?.
Indo ta zumɓuro baki sannan ta ce"Allah don Inna ta saka bakine da babu abinda zanyi,tunda ke kin iya haɗa mutum da iyayensa."
murmushi Amina tayi kawai ba tare da tace komai ba,don Idan Indo na da kunya baza ta ce mata wai tana haɗa ta da iyayenta ba,don mahaifinsu yana masifar son Indo akaf cikin ƴaƴansa,yana son Indo sosai son da shi kansa baya yiwa kansa,bai ƙi yarasa komai ba indai zai buɗe idanuwansa ya gansa gashi ga Indo.
Aminatu ta wuce kawai ta sanya hijabinta,sannan ta ɗauki allonta ta wuce abinta,Indo kuwa sai harararta take ita kuwa Inna sai kallonta take sannan ta ce"idan kin gama hararar ƴar uwar taki sai ki wuce kiyi wanke wanken".
Indo ta zauna ta ƙarasa wanke wanken,tana roƙar ubangiji Allah yasa wani ya shiga gonarta yaji jiki,ai kuwa akayi sa'a sai ga Matar Babanta ta fito daga ɗaki,wacce ake cewa Inna Harira ta ce"Indo yau kuma ke ce da wanke wanke?duk rashin kunyarki?duk yadda akayi wani rashin mutuncin kike so ki ƙulla".
Indo bata kulata ba ta cigaba da wanke wankenta,Innar Indo kuwa Murna take Indonta ta fara hankali,tunda gashi an kulata don ayi rigima kuma taƙi kulawa.
Daman matan Mahaifin Indo Huɗu ne,Kuma mahaifiyarta ce uwar gida ammanfa mahaifin Indo mutun ne me auri sake,ya auri mata yafi sai a irga,wasunsu akan Indo ake sakinsu wasu kuma wani dalilinne,su Indo suna da yawa a ƙalla zasu kai Su ashirin da biyar wasu yaran suna gidan wasu kuma suna wajen iyayensu,Indo ƴar gata ce sosai awajen mahaifinta,ko da mahaifiyarta ne kuwa zai iya yin kacaca don yana masifar sonta kamar ruhi.
Indo ta kammala wanke wankenta ta kai ɗaki ta ajje,Allah ya taimaketa Inna ta gama Tuwonta da wuri.
Inna Harira ta kalli Mahaifiyar Indo a wani wulaƙance sannan ta ce"yauwa Idan kin sauke zan ɗora ruwan zafi".Innar Indo ta ce"la babu komai zo ki ɗora Harira".
Inna Harira ta ce"saka Indo ta ɗoramin saboda kaina ke ciwo".Innar Indo tasan babu wani ciwon kai amman saboda kada dai ta bada ita awajen Indo ta ce"Indo zo ki ɗorawa Innarki ruwan zafi".
Nan ma Indo bata ce komai ba ta wuce abinta wuce ta ɗora mata ruwan zafin,Tazo zata shiga ɗakinsu kenan Inna Harira ta watso mata ruwa,sai tayi sauri ta ce"yi haƙuri fa ban sani ba".
Tana faɗar hakan ta tintsire da dariya sannan ta wuce ɗakinta,Innar Indo tana jinta tasan babu wani tana sane tayi hakan,Indo ta shigo ɗakin ko ajikinta ta cire kayanta,agaban Innarta babu ruwanta don ita kullum ganin kanta take ƙaramar yarinya.
Innar ta ce"Indo wai ke haryanzu baki girma bane?a yanzu fa kina da kusan shekara sha huɗu amman baza ki daina wannan haukar taki ba"?.ki kiyaye ni akan kina cire kaya agabana."
Indo ta turo baki sannan ta ce"ba Inna Harira ce take son ta kaini ƙarshe ba?Allah ina tsoron muguntar da zan mata,don wallahi har ta mutu baza ta manta dani ba ehe".
Indo ta faɗi hakan tana cire wasu kaya riga da wando kamar na pakistan,cikin kayan da Baffanta ke siyo mata.tana saka kayan tana murguɗa baki tare da mita.
Innar Indo ta girgiza kanta don tasan Indo baza ta daina abinda take ba,sai kuwa taji Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hhhhhh ho ni Indo magani Hegi da Hegiya maganin ƴar banza da ɗan banza,a taɓoni a taɓo masifa ka barni ka zauna baki alekum".
Innar ta kalleta sosai,ita wani lokacin ma idan Indo tayi wani abun gani take kamar ba ita kaɗai ce tayi ba saboda yadda ta iya zaro maganganu.. . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[27/01, 06:51] 🌈Ummu maher(miss Green)💚: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟫3
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIPORT*
------A hankali ya fara sakkowa daga matattakalar Jirgin, yana tafiya cikin nutsuwa kana ganinshi kasan cewa mutunne me ilimi da sanin ya kamata, don nagarta ce fal a fuskarsa da kuma kamala, sanye yake cikin manyan kaya kamar kowanni lokaci, don shi mutunne me son manyan kaya,da wuya kaga ya saka ƙananan kaya.
Shadda ce ajikinsa kalar sararin samaniya, ɗin kin taxarce a mutunce, ya sanya hularsa kalar sararin samaniya, takalminsa baƙi agogon hannunsa ma baƙi ne sai walƙiya yake.
General Muhammad Aliyu Maska,shine asalin sunanshi Maska kuma shine asalin garin mahaifiyarsa dana mahaifinsa, don mahaifansa duk ƴan gari ɗaya ne dangi ma ɗaya.
Kyakkyawane shi ta ko'ina, idan kayi mai kallon farko wajibine ka ƙara kallonsa, yana da kyau na ban burgewa da nunawa sa'a, yana da ƙwarjini sosai a idon mutane saboda komansa a nutse yake yinsa, sannan Miskili ne shi sosai don ba kowa ke ganin haƙoransa ba, sai wanda Allah yayi zai gani,sai dai duk miskilancinsa agidansa ba haka take ba, don idan ka ganshi da iyalinsa abin sai ya baka sha'awa,don ko bature bai isa ya kama ƙafarsa ba.
Da gudu Baby ta taho tana zuwa ta rungune mahaifinta sosai,shima rungume ƴar tasa yayi sannan ya ce.
"Baby kinyi girma fa yanzu Masha Allah,b azan iya ɗaukar ki ba?don haka a daina rungumeni ni dai tunda yanzu kin girma".
Doka ƙafarta ta hau yi kamar ƴar jaririya,ya lakuci hancinta sannan ya ce"yimin murmushi mana My mom".?
Ya faɗi hakan yana kama kunnensa,Sosai Baby take dariya sannan ta ce"Dady ka siyomin teddy ɗin"??.
Sosai ya fashe da dariya sannan ya ce"yeh!na bada oder ɗinta za'a kawo miki Teddy me girma kamar ke my Daughter".
Halima na gefe tana kallonsu cikin sha'awarsu don tana masifar jin daɗin ganin Baby da mahaifinta a haka,wani tsohon son yayarta ya tasar mata,ta rufe fuskarta kaɗan tana hawaye na tunowa da yayarta marigayiya wato mahaifiyar Baby,har yanzu gani take kamar taci amanar yayarta na aure mata mijinta,sai dai babu yadda za tayi don haka rabbi ya tsara.
Kuma ayanzu baza ta iya rabuwa da mijinta abin sonta ba,tana masifar son MD son da baza ta taɓa iya daina yi masa ba,sonshi acikin jininta yake.
General Muhammad Aliyu ayanzu haka yana neman takarar kujerar gomna,wanda a halin yanzu har an kusa zaɓe,Filin jirgin cike yake da masoya da magoya bayansa,har bai san yawansu ba mutane suna son MD sosai,don ba da kanshi ma ya nemi kujerar ba,mutane ne suka nemar masa saboda da cewarsa,don mutunne me son mutane,maƙwaftansa kuwa ba ƙaramin taimakonsu yake ba,kyaun gidansa da tsaruwarsa kamata yayi ace yana G.R.A unguwar masu kuɗi,amman yana cikin mutane abinsa,don ya taso cikin mutane,don ayanzu haka su goma sha huɗu ne awajen mahaifiyarsu,sannan kishiyarta ba sa guda 8.
Don haka shiyasa ya taso da son mutane sosai,Gashi da taimakon marayu da waɗanda basu da ƙarfi,bai ƙi ya zauna haka ba indai har zai taimaki marayu,duk bayan ƙarshen kowani wata yana zuwa gidan marayu don ziyartarsu,tare da kai musu taimakon abinda ba suda shi,baya ɗora kowa akan taimakon mutane,shi da kansa yake zuwa ya kai babu ruwanshi da girman kai,shiyasa iyalinsa ma suka taso cikin wannan rayuwar,bai nuna musu su daban suke ba,ya nuna musu duk ɗaya suke da Talakawa,hatta ƴarsa Baby makarantar Gomnati tayi,don shi bai yarda makarantar gomnati ba'a samun ilimi me nagarta ba,abinda ya lura dashi makamai ne babu na gari kuma indai aka samu malamai nagari to tabbas za'a samu ilimi na gari.
Sunan Mataimakinsa Dr Aliyu Umar Mashi,shima mutunne nagari don babu ruwanshi da abin duniya da kuma abinda ke cikinta,don abinda ya ɗauka shine duniya ba abar zama ba ce,yau gare ka gobe ga waninka in yau kai ne gobe ba kai bane.
Bayan sunyi musabaha da mataimakinsa suka gaisa da magoya bayansa,sannan ya nufo Inda Halima take,ya rungumo abarsa ya rungume agaban mutane babu ruwansa,don kowa yasan matarsa ce kuma shi fa bai ɗauki runguma awani abuba,don runguma ba turawa ne suka fara yinta ba,larabawa musulmai sune suka shigo da ita da kuma(sumba)wato kiss,ashi ko agaban waye yin abinsa yake ga matarsa don bai ɗauki abin a matsayin wani abuba.
Mota ɗaya suke da matarsa da kuma ƴarsa Baby,Mataimakinsa kuma da sauran mutanensu,sai kuma securities ɗinsu waɗanda suka rakosu.
Kai tsaye gidan mahaifansa ya fara zuwa,Halima tayi shiru tana tunanin haɗuwarta da Hajiyar Maska,surukarta ba tada ta ido ko kaɗan,maƙasudin daya sa mijinta ke yawaita tafiye tafiye kenan,saboda mahaifiyarsa mutunce me matuƙar faɗa da kuma rashin sanin darajar mutane,takan rufe idonta ta yiwa mutun ta tas,shiyasa sam Halima bata son zuwa wajenta,indai ba da mijinta ba shima kuma don babu yadda za tayi ne dashi,don indai yayi tafiya kafin yaje gida sai ya fara zuwa yaga lafiyar iyayensa.
Gidane ƙato me kyau da tsaruwa,gidane wanda ya amsa sunansa gida gashi ƙato sosai,yana da part kusan guda Baƙwai agidan,Ɗaya na mahaifinsa,ɗaya kuma na mahaifiyarsa,ɗaya na kishiyar Hajiyarsa,ɗaya kuma na kakar MD wacce aka fi sani da Hajiya Kaka.sauran part ukun kuma na ƙannensa ne,na mata guda ɗaya na maza kuma guda biyu don maza sunfi yawa agidansu,a haihuwa shine na biyu agidansu.
Gate biyu ne agidan,wanda yake cike da sojoji waɗanda suke a tsaye sun saita bindigunsu kamar zasuyi harbi,ba abin mamaki bane don an samu sojoji agidan ba,don bayan MD ƙannensa goma maza duk sojoji ne kowanne kuma da muƙaminsa,aƙwai major general,aƙwai captain,aƙwai Admiral,aƙwai general da sauransu.
Shiyasa tun daga gate ɗin farko zaka san lallai gidan Sojoji kazo saboda tsaron da gidan yake dashi da kuma yawan sojojin gidan.
A hankali Halima ta fito,duk jikinta a matuƙar sanyaye tana tunanin irin haɗuwar da zatayi da Hajiyar MD,tuni taji zuciyarta babu daɗi,bawai bata son mahaifiyar mijinta bane?a'a abu ɗaya ne yasa take nesa da ita,na komai bane illa gorin rashin haihuwa,wanda ta sanya ta agaba ta hana ta shan ruwa,gorin haihuwa abune me ciwo,wanda ba kowacce macece tasan hakan ba,sai wadda take cikin wannan matsalar,ita kaɗai ce zata iya fahimtar abinda take ji.
Shi kuwa MD tuni ya wuce sashen mahaifinsa,don yaga ƙofar a buɗe ita kuwa Halima kasa shiga cikin gidan tayi,don bata san kalar masifar daza ta haɗu da'ita yau ba,tayi ta gumi a jikin motar har Baby tayi gaba kuma sai ta dawo baya ta ce"a'ah Momy lafiya naga kin tsaya"?.
Halima bata amsa mata ba,don tasan Baby aƙwai kaifin basira,tsaf zata iya gano abinda ya hanata shiga.
Baby ta ce"Momy nasan abinda ya hanaki shiga?Hajiya ce ko?don Allah momy ki cire tunanin Hajiya aranki,bana son kina ɗorawa kanki tunani akan Hajiya,Hajiya fa bata da wuta ba tada aljanna,duk faɗanta sai dai tayi ta gama,kuma don Allah kada kiyi kukan nan da kikewa Hajiya,shiyasa takw miki yadda take mikin,amman idan kika nuna abin bai miki zafi ba sai kiga an zauna lafiya,tunda dukkanku dai babu yadda zakuyi da juna,ita mahaifiyar mijinki ke kuma matarsa,kowaccenku zata iya kaishi wuta,don haka don Allah Momy kada ki nunawa Hajiya wani abu."?
*INDO ƳAR CASKALE*😂
--------Indo na ganin Inna Harira ta shiga wanka,ta sheƙe da dariya sannan ta ce"hhh yau za'ayi allan dungure agidan nan,yau za'aci uwar sabada Inna Harira yau zaki gane kurenki,sai na nuna kiki ni ba kanwar lasa bace,ba'a taɓani abanza sai na rama zansan na haifu".
Shigewa ɗakin Innarta tayi,alokacin tana Sallah Indo tayi dariya ciki-ciki wato ta samu yadda take so kenan,ta buɗe wata samira ta ɗakko wani abu,ta ɓoyeshi a hannunta ta fita a hankali,Dai dai lokacin Amina ta dawo daga makaranta,Indo na ganinta ta harare ta wuce,ashe bata sani ba ledar ta ɗan leƙo ana ganin komai.
Amina ta ce"Indo ke kuma me zakiyi da Yaji me uban yawa"?.
Indo ta ce"gettere zanci wanda Inna tayi,kinsan cinsa dole sai da yaji gwara in ɗan saka yafi