Showing 18001 words to 20427 words out of 20427 words
Chapter 7 - INDA BA KASA by Ummu Maher (miss green).txt
dafa ƙafa ta ya ce don Allah Indo ki yafe min,don kinsan tunda ya taɓoni sai yasan ya taɓoni don wallahi bazan yarda yaci bulus ba.
Bintu ta ce"Hmm ke kam Indo kin fi ƙarfina wallahi,ni ban ma san abinda yasa na tafi gida na dawo wajenki ba?".
Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hegiya Bintu wato kin gano amfani ko?daman idan kaga kare na shinshina takalmi to yasan abinda ya hango,da bani da amfani da tuni kin fita a harkata."
Bintu taja hannun Indo wai au tafi gida,Indo ta fizge hannunta ta ce"ke Bintu kyale ni a'i dole sai naje naga yadda abin zai kaya,ko so kike in tafi gida banga yadda zasu kaya ba"?.
Ta fisge hannunta tayi gaba abinta,Bintu ta kalli ƙawarta kallon tausayi don ita yanzu Indo tausayi ma take bata,ayi mutum bai da aiki sai tsokanar mutane da son tashin hankali?ita Indo wacce irin mutum ce?babu yadda zatayi da halin Indo,kuma baza ta iya rabuwa da Indon ba don son Indo azuciyarta yake,sai dai kullum addu'arta Allah ya shirye ta.
Sailuba na zuwa ƙofar gidansu Lami ta hango mijinta Sunusi,sai tsara Lami yake ya kafo hularsa a gaba yana mata daɗin baki.
Sailuba ta wuce ta tsaya a tsakiyarsu tana kuka ta ce"wallahi She Allah ya kamaka mugu azzalumi kawai,macuci maci amana yau Allah ya toni asirinka."ta faɗi hakan tana kuka sosai,jin tana kuka sai ɗan tama ya fara kukan sosai.
Sunusi yayi tsuru,kamar kazar da ƙwai ya fashewa aciki,ya buɗe bakinsa xaiyi magana Sailuba ta ce"yimin shiru Sunusi,babu abinda zaka ce min ashe daman wajen wannan ƴar iskar karuwan kake zuwa?wajen wannan shaiɗaniyar ka tare?so kake ka ɗebomin masifa da ƙazanta ka kawo min gida?Allah ya wadaran Halinka Sunusi".
Sunusi ya kasa magana,saboda iya kunya yau dai ya jita kuma yasan halin Sailuba da mugun taurin kan tsiya,ba tafiya za tayi ba tunda taja ta tsaya ɗinnan.
Lami ta kalli Sailuba kallon sama da ƙasa ta ce"kan uba ni kike antayawa zagi haka?to wallahi baki isa kisha ruwa ba yau,sai na cire miki haƙoranki kaf kin kasa tauna ko da abinci ne,tunda ke agidanku ba'a koya miki tauna magana ba".
Ta kawowa Sailuba wani mugun naushi,don Lami irin manyan matan nanne masu ƙiba ta ko'ina.
Da sauri Sunusi ya kai hannunsa don ya tare dukan da Lami ta kaiwa Matarsa Sailuba,ji kake ƙum-ƙum an buge Sunusi a bakinsa.
Indo ta sau dariya a inda take har tana riƙe ciki tana ce wa"Hegi Sunusi yau sai anyi maka ruwan zafi". . . . . . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[27/01, 06:52] 🌈Ummu maher(miss Green)💚: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟫10
---------Halima ta ce"Baby yanzu fa muna hira su Ummita na zaune anan?amman yanzu in juyo sai naga suk basu nan"?.
Baby ta ce"Momy ni fa gani nake kamat basa son gidan nan?musamman ma Ummita, don na sha kamata tana kuka sai tace min wai babu komai?ni dai ina ganin ko muna musu wani abunne wanda basa so"?.
Halima ta ce"to Allah dai ya gani Baby, ni da ban taɓa cutar dasu ba yadda kike awajena haka na ɗaukesu, amman in Sha Allah zan tambayesu sai inji inda matsalar take."?
Baby bata ce komai ba ta wuce makaranta,tare da kaiwa mahaifiyarta kiss, sannan ta wuce makarantar jami'a wacce bata fi wata ɗaya da farawa ba.
Halima da kanta ta ɗaura abinci, saboda ta bar su Ummita su huta, tana cikin girkin Khairat ta shigo tana murmushi ta ce"Anty wallahi Ummita ce ba tada lafiya, ciwon kai ne me zafi ya rufe ta shine nazo ko za'a samu paracetamol."?
Halima ta juyo da mamaki ta ce"wai me ke samun Ummita ne?ko bata son zamam gidan nan ne?ki faɗamin Khairat ke fa ƴar uwarki ce?nasan zaki san komai na ta"?.
Khairat ta sunkuyar da kanta kawai,saboda bata san me zata ce wa Halima ba?ce mata za tayi ciwon son mijinta ne ya kamata?ko kuwa ce mata za tayi Ummita bata son zaman gidan"?.
Khairat ta ɗago da kanta a hankali sannan ta ce"Anty ni kai na ban san me ke damunta ba?amman ina tunanin ke zata faɗa miki dukkanin gaskiyar abinda ke damunta"?.
Halima ta ce"to Allah ya sauwaƙe, muje in duba ta idan da yiyuwar aje asibiti gwara a kaita kawai,amman ni abinnan yana damuna?yarinya tazo gidansu lafiya amman yanzu ace ta haɗu da lalura har da hawan jini?.
Halima ta wuce ɗakinsu Ummita kai tsaye,a bakin gado ta samu Ummita ta haɗa kai da guiwa,tana kukanta a hankali kana kallonta kasan tana cikin wani hali.
Halima ta dafa Ummita,da sauri ta ɗago tare da sauke ajiyar zuciya, sai dai tana ganin Halima ce sai ta sunkuyar da kanta, tana ji azuciyarta da zata iya to da tuni ta shaƙe Halima ta kashe ta, saboda yadda ta yi mugun tsanarta don gani take tamkar Halimar ce zata hanata auren Baban Baby.
Halima ta zauna a bakin gadon sannan ta ce"Ummita idan har kin ɗauke ni ƴar uwa ki faɗamin damuwarki?tabbas ina cikin wani hali akan wannan matsalar da kike ciki?a iya sanina ni dai babu abinda nake muku ku dukanku,muna zaune lafiya daku Baby ma ba tada matsala akan hakan,don Baby tafi kowa son taga gidan nan ya cika da baƙi,bata son ganina ni ɗaya agidan nan bayan ta tafi makaranta, don Allah Ummita ki faɗamin damuwarki"?.
Ummita taji kamar ta ɗago ta tsinkawa Halima mari,don waɗannan maganganun da take yi tamkar tana daɓa mata wuƙa ne acikin cikinta,burinta bai wuce ta ganta ga ta da Baban Baby ba.
Halima ta ce"shikkenan Baby tunda baza ki iya gaya min ba?ni nasan baki ɗaukeni a matsayin ƴar uwa ba."
Ta faɗi hakan tana tashi tsaye ta fice abinta,Khairat ta matso da sauri sannan ta ce"gaskiya Ummita baki yiwa kanki adalci ba,a'i ni aganina ko da kina son mijinta haƙuri ya kamata kiyi ki danne,amman ba ki zauna kiyi ta fama da tunaninsa aranki ba,shi kuma wanda kike yi donshi bai ma san kina yi ba".?
Ummita ta ɗago jajayen idanuwanta ta ce"Khairat ina tsoron inyi miki abinda zaisa kiyi nadamar faɗar waɗannan maganganun a kaina,ina ji araina zan iya rasa komai saboda Baban Baby,zan ita rabuwa da kowa saboda shi, zan iya ɓatawa kowa saboda shi, ke bari ma kiji zan iya komai indai akansa ne,don haka ki iya bakinku tun kafin in miki abinda zaki daɗe kina jinyarsa."
Khairat ta zaro ido tana ce wa"na shiga uku na ni Khairat? Wannan wani irin mayan so ne?wani irin so kike masa da har zai sa ki saɓawa mahaliccinki? Duk abinda kike Ummita ki dinga tunawa da halacci,ki janye wannan son da ki kewa bawan Allahn".?
Tana cikin maganar taji an janyo ta da ƙarfin gaske,Ummita ta gani tana zaro ido idanuwanta sunyi jawur tamkar an hura wuta,ta shaƙe Khairat a jikin bango sannan ta ce"kada ki fasa gayamin duk maganar da zakiyi,tunda naja miki kunne akan ki daina shiga harkata akan wannan lamarin amman kinƙi,to duk abinda nayi miki ke kika ja."
Tana faɗar hakan ta wancakalar da Khairat a wajen, ta yi wucewarta abinta zuwa banɗaki,Khairat ta matsa maƙogaranta tana jin wani mugun zafi, sosa sosai ta miƙe tsaye, ta daɗe a wajen tana tunanin mugun halin da ƙanwarta take,yanzu a matsayinta na yayar Ummita tayi mata haka?ina ga wani kuma?.
Ƙwanansu kusan uku babu me cewa kowa komai,tsakanin Ummita da Khairat sosai kowane ɓangare ya ɗau zafi,don ko Halima ma yanzu har ta haƙura ta daina tambayar Ummita abinda ke damunta,number Adama da take ta bugawa ba'a ɗauka, don tana son faɗawa Adama duk abinda yake faruwa akan Ummita, don tana tsoron abinda zaije ya dawo akan matsalar da Ummita ke ciki, gashi kuma taƙi faɗawa kowa abinda ke damunta.????
Khairat na linke kayansu tana jerawa a sif,sai ta jiyo muryar Ummita na ce wa"Khairat yanzu daman zaki iya gana dani har na tsawon ƙwana huɗu? kiyi min uzuri mana? don Na ce kawai ina son Baban Baby? Me makon ki tayani neman yardarsa sai kuma ki dinga neman rabani dashi?alhalin zuciyata babu namijin da take so sai shi?
In dai don Anty Halima ne kike wannan to ki daina,don nazan taɓa iya daina sonshi ba,zan cigaba da sonshi har in samu amincewar zuciyarsa". . . . . .
Saurin gimtse maganarta tayi,a lokacin da taji an shigo ɗaki ta tashi da sauri don ganin wanda ya shigo?????.
Wani irin bugawar zuciya taji,ba ita kaɗai bama har ita Khairat ɗin,khairat ta zaro idanuwa sosai na tsoron ganin wanda ya shigo . . . . . .
-----*****-----
. . . .Sosai wajen ya kaure da faɗa da hayaniya,Sunusi dai ya kasa karɓar matarsa a hannun Lami,Shima kansa Sunusin yasha duka sosai daga bisani kuma ya koma gefe,don yaga alamar indai bai matsa ba to tabbas zai sha dukan da zai kasa tashi, ita Lami irin matan nanne kamar samudawa, ga jiki ga tsayi shiyasa ba kowa ke haɗa hanya da ita ba.
Indo tana cen gefe tana cin dariya,ta ce"Hegi Sunusi dama Lami ta ɗaga ta tayi allan dungure da kai."
Sailuba tasha duka sosai, sai dai itama Lamin taci na jaki don duk da haka itama tana da na ta ƙarfin,daman tuni ta yadda goyon ta hau tiƙar dambe,shi kuwa Sunusi tuni ya ɗauke ɗansa ya rungume, ya koma gefe ya zama ɗan kallo.
Mutane suka taru duk da dare ne,da ƙer aka rabasu daga damben don kowaccensu bata so rabuwarsu ba,sunfi son a ƙyalesu suci karansu babu babbaka kamar yadda Sunusi ya yi.
Mutanen suka Dinga Allah wadai da halin Sunusi daya kasa raba faɗan Lami da matarsa.
Sai da Indo ta gama kallonta sannan ta kamo hanyar gidansu,babu kowa a layin na su saboda daren fara yi.
Tana cikin tafiyar taji kamar ana binta a baya,ta juya a hankali don taga ko menene?amman sai taga babu komai, ta cigaba da tafiyar tsoro fal aranta gashi kuma daga gidansu Lami aƙwai ƴar tazara zuwa gidansu.
Ga Indo babu arabi babu boko,ballan tana ma har tayi wata addu'ar ta neman tsari, tafiya ta ƙaraji a bayanta ta daure taƙi juyowa ta cigaba da tafiya sai taji ana yowa ta inda take da ɗan sauri-sauri.
Ta rintse idanuwanta,me xa tayi?da gudu ta falla sai gida hankalinta a matuƙar tashe don abinda zai bawa Indo tsoro to ba ƙaramin abu bane.
Innar Indo hankalinta ya tashi sosai, ganin daɗewar da Indo tayi yau gashi har yanzu bata dawo ba.
Amina ta ce"ni wallahi Inna abin Indo mamaki ya ke bani?sam bata da tsoron dare?ga tsokar tsiya kamar ƴar aljanu?????."
Wani irin bugawar ƙirji taji,a lokacin da ta tuno da wani ɓoyayyan sirri, wanda suke ɓoyewa akan Indo amman tasan komai daren da ɗewa, dole asirinsu zai to nu kuma tana tsoron faruwar wannan al'amari. . . . . . . ✍🏾.✍🏾✍🏾✍🏾✍🏾
*Tirrrrrrrrr ƙashi*
Hmmmm ko me su Ummita da Khairat suka gani?daya firgita su haka?wanene ya shigo ɗakin da suke?.
Baby ce? Ko Halima ce? Ko MD ne?ko kuma Hajiyar Maska ce?????
To ko ma dai wanane sai a littafi na biyu zakuji komai.
Sannan menene abinda ya firgita Innar Indo???menene wannan ɓoyayyen sirrin da suke rufewa ita da Baffan Indo???.
Sannan menene yake biyo Indo???.
Wannan amsoshin naku duk sai a nan gaba,don wannan tafiyar yanzu aka soma ta,don wannan littafin yana da pages kusan ɗari,wannan kaɗanne daga cikinsa.
Domin siyan ƙarashen wannan littafin ku neme ni a number ta kai tsaye👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
07068606171
don samun na ka,da abaka labari gwara ka bayar don wannan littafin salon na dabanne.
Wannan littafin Naira ɗari biyar ne kacal,ki biya sannan ki karanta cikin sauƙi da lumana.
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN👉🏾👉🏻*