Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 20427 words

Chapter 3 - INDA BA KASA by Ummu Maher (miss green).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

daɗin ci".


Amina ta kalle ta ba tare da tace mata komai ba,sai dai sam bata yarda da Indon ba,don tasan halin ƙanwarta ba tada yafiya ko kaɗan.


A hankali Indo ta ɗan zira hannunta,sai taji ta taɓa bokitin,kuma da alama Inna Harira ta juya bayanta ne,ta buɗe ledar yajin ta juye sa duka aciki.
A hankali ta koma ɗakinsu,ta sheƙe da wata dariya ta ce"wooo ni Indo,yau za'a ga rawar asosa agidan nan,daman na daɗe banga rawar banga ba,yau Allah yasa zan ganta agidan nan."


Inna ta kalleta sannan ta ce"Indo me kika aikata?ke fa bakyason zaman lafiya a rayuwarki?kinsan Allah jikinkine zai gaya miki,saboda bazaki kashe ni ba,tunda ba ke kaɗai na haifa ba kinji".


Indo kuwa kamar mutuniyar arziƙi ta wuce,ta buɗe samirar tuwo tana turo baki sai dai babu yadda za tayi dole taci don Baffanta baya nan.
Don tasan da Baffanta yana nan babu abinda zaisa taci tuwo,da cen bakin kasuwa zai kaita taci abinda take so ta ture.


Tana cikin cin tuwon ta fara jiyo ihu a banɗaki,Ta kasa kunne sai taji Inna Harira tana cewa.


"Wayyo Allah na!wayyo Allah na!!!jama'a a kawo ɗauki zan mutu,yaji zai kashe ni wayyo Allah na".
Sosai take ihu,matan gidan da yaransu duka suka fito don ganin abinda ke faruwa,Indo kuwa ko ajikinta ƙara gyara zamanta ma tayi,ta cigaba da cin tuwonta tana ƙara haɓɓaka muguntarta akan duk wanda yayi gigin shiga sabgarta.


Da ƙer Inna Harira ta samu ta sanya zaninta sannan ta fito,ta cigaba da ihu idanuwanta a rufe tana neman taimako,amman babu wanda ya iya zuwa wajenta,don duk daman haushinta sukeji,saboda yadda take da shisshigi ga kuma muguwar muguntarta.


Ƴaƴanta ne ma sukazo suna kuka suna tambayarta abinda ke faruwa,Da sauri Innar Indo ta ƙaraso tana cewa"subhanalillah sannu Harira?me ya faru?a ina kika samo yaji"?.
Inna Harira ta taƙarƙare ta zunduma wani irin ihu tana cewa"wayyo Allahna mutane ku kawo min ɗauki,fatata zata yage wayyo yaji zai kashe ni".


Mutuniyarku Indo gwalo tayi sannan ta wuce abinta ta sauke ruwan zafinta,sannan ta shiga wankanta bayan ta wanke banɗakin,Harira kuwa da ƙer aka ta aka shiga da ita ɗaki,ta sandare ta koma kamar me aljanu sai surutai take tana ihu,Indo kuwa cewa take"gobe ma kya sake muguwa kawai me mugun nufi,aini duk muguntarki a tafin hannuna kike,tayi wata shewa ta ce"woo ni Indo uwar mugu da muguwa,Wooo sai ni Indo ƴar gidan Baffa sango Woo ni Indo".


Ita kaɗai take abinta tana shafa mai,Amina ta kalleta sannan ta ce"amman gaskiya Indo bakya kyautawa wallahi,ai kome Inna Harira tayi miki bai kamata kiyi mata haka ba,ke sai kace me zuciyar fir'auna ace mutum yana musulmi amman baya yafiya?gaskiya Indo ki canja ɗabi'a wallahi,wannan ba ɗabi'ace ne kyau ba,kema fa kina yiwa Allah laifi kuma ya yafe miki".


Tunda Ta fara maganar Indo ta tsaya tana kallonta,kai kace wata ta Allah sai kuwa ta ce"ni dai wallahi Yaya Amina da masallaci ma kika koma kika fara wa'azi da ba ƙaramar jama'a zaki tara ba,don haka tun wuri ma gwara a fara kiranki da ya sayyada".


Tana faɗar hakan ta kyakyale da dariya,tana janyo gazal ɗinta tun daga gefen ido har kunne,sannan tazo tayi ɗiso ɗiso irin nasu na ƴan ƙauye,ta tashi ta sanya kayanta irin na fulani,har da sarƙar ƙafa tayi wani irin mugun kyau,duk da yanayin ƙwalliyarta.


Taraba gashin gida biyu irin yadda akewa yara,yayi mata bala'in kyau tamkar sarauniya sannan ta kitse abinta da kanta,duk Amina na kallonta amman bata isa tayi magana ba,yanzu sai cibi ya zama ƙari shiyasa taja bakinta tayi shiru,don ita kanta ma Indo ba kyaleta tayi ba.
har Indo ta fita sai kuma ta dawo da baya,ta ɗan leƙo ɗakin Inna Harira,ta hango Innarta tana haɗa manshafawa da farar hoda tana shafawa Inna Harira,don daman shine maganin Wannan raɗaɗin,musamman na yaji don haka sai shafa mata take ta yi,wasu wajajen kuma tana bata tana shafawa da kanta.


Sam Indo bata ji daɗin hakan ba,taso acean barta ta ɗanɗana kuɗarta,ba da wuri haka ba amman hakanma ko yaya ta ɗan gane karon fa da wuya,kuma ta gane shayi ba ruwa bane gobe ma ta ƙara shiga harkarta.
Tuni Innarta ta ganta don haka ta ce"Indo lafiya kike leƙowa"?.


Ganin anganta yasa ta shigo,tayi kalar tausayi sannan ta ce"ayya sannu Inna Hari Allah ya baki lafiya?Inna akira mata Malam na soro yayi mata ruƙiyya".?


Inna ta wurgamin wani kallo sannan ta ce"liman zaki kira kinji?mara kunya kawai ni dai ina faɗa miki Indo kibi duniya a sannu wallahi,idan ba haka ba wataran sai kinyi nadama me yawan gaske".


Indo ta sosai ƙeya sannan ta ce"ni dai na tafi dandali don nasan yanzu su Surbajo na nan suna jira na".


Tana faɗar hakan ta fita da sauri,don tasan ba tada gaskiya ta tsaya a soro ta dinga dariya kamar wata mahaukaciya.
Inna Harira Tayi shiru tuno da wani abu yasa ta tashi da sauri tana ce wa.


"Wallahi tallahi bazan yarda ba,aradun Allah bazan yarda ba sai an ƙwatomin Hakkina Hegiya Indo ina kike ......✍🏾😂😂


Ni kuwa Ummy maher nace ki bita dandali tana cen,Indai Indo Ƴar Caskale ce dai dai take da ke😩😂😂😂




*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.


Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻


07068606171
08104335144
08179523215


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_




*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_




*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_




_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_




1 500
2 700
3 1000


_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank


_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._




_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171


*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*


0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171




*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*




_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_


*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[27/01, 06:52] 🌈Ummu maher(miss Green)💚: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*


_(Littafi na 1📃)_



NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*


*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------




*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*


_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894


*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*




Page🟪4


---------Babu yadda za tayi haka tabi Baby suka shiga sashen Hajiya gabanta sai faɗuwa yake,suna shigowa ɓangaren Allah ya taimakesu Hajiya bata falon,Sosai hakan ya faranta ran Halima ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a danƙareren falon Hajiya.


Ta cewa Baby"bana son in shiga ɗakin Hajiya don ina tunanin ko ba ita kaɗai bace,in kin shiga Baby sai kice tare muke don wataƙil ko Baba yana nan don naga sashensa abuɗe".


Baby ta ce"to Momy bari in shiga sai in gaya mata,amman ni wallahi da nayi zamana anan,don bana son masifar wannan jarababbiyar tsohuwar".Baby ta faɗi hakan tana chono baki gaba don ta tsani duk wanda baya son mahaifiyarta,don ita fa haryanzu gani take Halima ce mahaifiyarta,don bata taɓa nuna mata wani abu da zaisa ta san ita ba mahaifiyarta bace,kuma ko gorin da akewa Halimar ma cewa take'wai su Momy basu san sanda kika haifeni bane?ko don sunga har yanzu baki sake haihuwa bane'?.


Sosai maganar ke dukan zuciyar Halima,sai dai babu yadda za tayi don tasan ba itace ta haifi Baby ba,amman har aranta tana jin kamar itace ta tsugunna ta haifi Baby,tunda yayarta ce ta haife ta.
Baby na shiga ta iske Hajiyar Maska na waya,tana ganinta ta kashe wayar tana cewa"sai da Safe Hajiya Talatu".


Baby ta ce"Hajiya Ina wuni".?


Hajiyar ta kalleta sannan ta ce"lafiya klau Taƙwarata,ya gidan?yau uwar baƙin halin ta barki kizo inda muke?saboda kada mu cinye ki?amman a'i kina zuwa gidan Hajiya Xulaiha ko?tunda ita wannan kakarki ce ta wajen uwa ko"?.


Baby ta zumɓuro baki gaba tamkar zatayi kuka ta kalli Hajiya da Lulu Eyes ɗinta ta ce"Hajiya ni fa Momy bata hanani zuwa nan gidan,nima makaranta ce ke hanani zuwa wajenku".


Hajiya ta ce"ni zaki faɗawa makaranta?babu weekend ne?ke dai kawai kice uwar riƙonki ta koya miki baƙin hali?to a'i kuwa idan kika ce halin wannan zakiyi zakisha wahala sosai".


I'ta dai Baby bata ƙara magana ba,don Allah Allah take ta fita daga ɗakin,sam bata san taji wani ko wata yana zagar mata mahaifiya,kuma ta tsani kalmar nan da mutane ke faɗa mata a kullum wai Mimynta ba mahaifiyarta ba ce.


Tana cikin wannan halinne taji Hajiya na cewa"kinzo kin tsaya min aka kamar wata sandar ba'are,ke idan an faɗi laifin uwar riƙonki sai ki hau cika kina batsewa kamar zakiyi duka ko?".


Baby ta fara magana a ƙage ta ce"Hajiya don Allah abar wannan maganar,ni da Momyna ce ita tana falo,kuma mun rako Dadyna yau ya dawo daga tafiyar da yayi".
Hajiyar Maska ta fara magana cikin faɗa.


"Oh aiko ki tayi kizo ki jawo ni ki kai ni?bata san ɗakina ba?ko kuwa yau ma ranin tazo ta gwadamin?to wallahi Halima ta kiyaye ni,idan ba haka ba zata san tayi da ƴar garin Maska".


Baby kuwa tsabar fushi kasa tsayawa tayi,ta fice fuuu cikin fushi sai taji sam bata san ganin matar,saboda yadda ta tsani mahaifiyarta dama ta hana kowa zaman lafiya,Alhali ita ta zauna lafiya da mijinta,don Hajiya kaka ba mutum ce me tsaurarawa ba,duk da dai tana da faɗa amman faɗanta sai an taɓa ta sannan takeyi ba haka kawai irinna Hajiyar Maska ba.
Baby na fita Hajiyar Maska ta ce"Ni wallahi al'amarin Baby yana bani mamaki?Yarinya kamar wacce aka yiwa asiri?kullum ana gaya miki ga hanyar da zakibi don ki cusgunawa wannan mayyar data liƙewa ubanki,ammanke kullum kare ta kike?to ni nasan abinda zanyi don yau ɗinna ba sai gobe ba,zan nunawa Halima cewar ita bata isa ta dinga haɗani da ɗana ba."


Itw kaɗai dai take ta faɗanta.


MD yana shigowa ya ce"a'ah Ya kuma kika zauna anan Halima"?.


A hankali ta ɗago don kanta ne yake sara mata,haka take ita bata iya saka abu aranta ba,yanzun nan sai kaga ta rame ta zama abar tausayi.
"Hajiyar na ciki ne shiyasa ban shiga ba,ba jira ta fito amman Baby ma tace ita kaɗai ce,yanzu ma shiga zanyi mu gaisa".
Bai ce mata ƙala ba ya wuce abinsa,don shi ba mutunne me magana ba,shiyasa wasu suke ganin kamar yana da girman kai,kuma shi haka Allah yayi sa aƙwaishi da miskilanci,wannan kuma halin mahaifinsa ne,don shima ba ruwansa ba komai ya kewa magana ba,sai dai yana da zuciya sosai,don ko su Hajiyar Maska suna shayinsa sosai.
Yana shiga Hajiya tayi masa banza kamar bata san Allah yayi ruwansa ba,yana ganin hakan yasan lallai aƙwai abinda ya faru,sai dai bai kawo komai ba ya tsugunna har ƙasa,sannan ya fara gaida mahaifiyar tashi cikin girmamawa.


Hajiyar Maska ta kalleshi sannan ta ce"yanzu Muhammad har nayi lalavewar da za'a rainani haka?matar ka ta zauna min a falo sannan ta ce wai inzo mu gaisa?tasan kuwa ni wacece awajen ta?Muhammad kana neman aljanna kuwa?kana son ka gama da duniya lafiya kuwa?".


Da sauri ya kalli Hajiyar tasa sannan ya ce"Hajiya wallahi ban san abinda ke faruwa ba?na tambayeta yanzu tace abinda yasa bata shigo ba ta ɗauka ba ke kaɗai bace,shiyasa bata shigo ba amman kiyi haƙuri Hajiya".


Da sauri Hajiyar Maska ta ce"inyi haƙuri Muhammad?saboda an cuce ni?sai ka zuba ido yanzu matarka tana wulaƙantani?ta inda Salis ya fika kenan?matansa guda biyun nan bai yarda kowaccensu ta nemi rai nani ba,amman kai sai ka tsaya mace na juya ka kamar sitiyarin mota".
Kasa magana yayi,amman kana ganinsa kasan ransa a matuƙar ɓace yake amman ya daure ya sunkuyar da kansa.


MD mutunne me mugun haƙuri,sai dai yana da zuciya sosai saboda haka bai fiya son zaman garin ba,saboda Tashin hankalin daya ke ciki,tsakanin matarsa da mahaifiyarsa,yasha zama yayi tunani akan abinda yake haɗa mahaifiyarsa da matarsa amman bai taɓa gano komai ba,kawai dai abinda ya gane abune guda ɗaya shine matuƙar Halima zata zo inda Hajiya take,to dole sai an samu matsala idan kuma bata zo ba shima matsalar ne,tunda matan ƴan uwansa duk suna zuwa gidan,bai kamata ace matarsa ce kawai bata zuwa ba,saboda wani dalilin ɓatawarta da Mahaifiyarsa,shi kuma ya rasa yadda zaiyi a samu maslaha.
A hankali ya tashi tsaye duk karsashin daya zo dashi sai yaji yanzu duk babu shi saboda ɓacin rai,haka ya fito zuciyarsa na masa wani irin zafi.


Ko daya ke yanzu dai idan akayi duba na tsanaki,za'a ga tabbas Halima ce da laifi saboda a'i ita ya kamata taje har inda Hajiya take,ba Hajiyar ce zata zo inda take ba.
Halima na ganin fuskarsa tasan lallai Hajiya ta haɗa ta da mijinta,sai dai koma menene ta shirya ƙarɓarsa tunda yau tazo inda Hajiya take,kuma tasan dole sai wani abin ya faru.


"Halima me yasa bakya son zaman lafiya ne?me yasa kullum kike son haɗani da Hajiyata ne?ne yasa bakya son in zauna lafiya da mahaifiyata?kina son in shiga aljanna kuwa?Halima bana son inyi miki abinda zakizo kina dana sani ne,shiyasa nake kyale ki kullum ina ɗorawa mahaifiyata laifi,akan wannan matsalar da muke ciki,amman ke bakya ganin duk wani ƙoƙarina?zan amshi raganar duka al'umma yanzu,kina son in shiga tashin hankalin da zan kasa biyawa mutane buƙatarsu,waɗanda suka ɗauramin nauyi?Halima ina son ki shiga har ɗakin Hajiya yanzu ki bata haƙuri,haƙiƙa abinda kika yimin yau ya ɓata min rai sosai."


Halima kuwa tunda ya fara magana ta sunkuyar da kanta,ta kasa ɗagowa ma ta haɗa idanu dashi duk da daman idan Mijinta na mata magana ko haɗa idanu bata yi dashi,don dai ta bashi girmansa na mijinta tare dayi masa biyayya.


Wasu hawaye ne masu zafi suka fara zubo mata,ita da Mijinta zata iya irga sau nawa suka taɓa yin faɗa,tasan mijinta ba shida matsala zasu iya shekara ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba,kullum cikin zaman lafiya suke gwanin sha'awa.
Hajiya na tsaye duk tana kallon diramar dake faruwa,duk da haka bata ji daɗin yadda Muhammad ya yiwa Halima ba,taso ace yaci mata mutunci sosai idan ma har da dama ya haɗa mata da takaddar saki,don ita ayanzu babu abinda take farin cikin gani irin taga an saki Halima,amman shiru duk abinda take haɗa mata bata ji sakamako ba.
Hajiya ta ce"Muhammad a'i ni har yanzu baka burgeni ba,saboda daman irin wannan faɗan da kake mata kamar wani lusari shiyasa take rai na ka,amman babu komai ni nasan matakin da zan ɗauka.


Wata irin tsawa ya yiwa Halima yana cewa"Halima!ba cewa nayi kije ki bawa Hajiya haƙuri ba?me yasa kike son ɗoramin magana ne?me yasa bakya son zaman lafiya ne"?.


Halima ta tashi a hankali,jikinta har kakkarwa yake saboda tsawar da MD yayi mata,ta je har gaban Hajiya ta tsugunna sannan ta ce.
"Hajiya don Allah kiyi haƙuri,in sha Allah bazan sake miki makamancin haka ba,ki yafe min don Allah"?.


Hajiyar Maska ta kalle ta sannan ta ce"sai anyi magana ki dinga sunkuyar da kai,daman irinku haka kuke Ni dai Allah ya haɗa ɗana da masifa ta aurenki,aure kusan shekara goma sha amman babu ɓatan wata har yau."






*****---*****


. . .Inna Harira ta miƙe tana masifa tana ce wa"Wallahi bazan yarda ba,wannan shaiɗaniyar yarinyar ce ta sanya min yaji acikin ruwa,wallahi bazan yarda ba hegiyar yarinya mara kunya,wacce bata aan mutuncin mutane ba Allah ya isana wallahi".
Ta faɗi hakan tana kuka kamar ƴar ƙaramar yarinya.
Ita kanta Innar Indo ta gane ƴar tata ce tayi,amman tasan ta inda zata biyowa Indon,don daman mahaifinta ke ɗaure mata gaba don ta raina kowa.


Inna Harira dai ranar masifa ta dinga yi,matan gidan kuwa ko kallon arziƙi bata ishe su ba don daman tuni sun daɗe da yin faɗa da ita,don bayan Innar Indo itace me fawa agidan,don su ƴan kallo ne agidan,don ko Innar Indo darajar ƴarta take ciki ne gidan yake ɗaga mata ƙafa,amman Inna Harira ita ce me gidan sai yadda ta dama haka ake sha,sai dai fa Indo ƙadangaren kan tulu ce,bata fito ba sai da ta shirya don babu inda bata je ba,akan a haɗa Indo da mahaifinta amman sai suce mata su baza su iya ba,don sun gano wani babban al'amari a tsakanin Baban Indo da ƴar tasa.. . . .✍🏾




*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.


Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻


07068606171
08104335144
08179523215


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_




*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_




*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_




_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_




1 500
2 700
3 1000


_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank


_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads