Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 23384 words

Chapter 1 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jun 2024

313

Ads at the middle of Article

*🟣 SIRIKAR ZAMANI🟣*



*NA MARUBUCIYA*


*SAMHA*
*Y'ARMACE*
*KISHIYACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND KNOW*
*SIRIKAR ZAMANI*




*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)🖌*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/








WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD ( MRS BASAKKWACE)*






GAJEREN LABARI👌


*DUK-KAN YABO DA GODIYA SUN TAB-BATA* *GA ALLAH MA DAUKA-KIN SARI,WANDA YA HALICCI MUTUM* *KUMA YA SANAR DASHI GAME DA ALK'ALAMI YA SANAR DASHI ABINDA* *BAI SANI BA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TAB-BATA GA* *MAFI-FICIN HALITTA SHUGABAN MU ANNABI* *MUHAMMAD DA ALAYEN SA DA SA HABBEN SA BAKI D'AYA TARE DA DUK WA Y'ANDA SUKA BISHI* *DA KYAUTA-TAWA HAR ZUWA RANAR SAKAMAKO.*


*LABARIN SIRIKAR ZAMANI LABARI NE AKAN WATA MATA MAI BIBIYAR GIDAJEN AURAN Y'AY'AN TA TAGA MAI YAKE GUDANA TSAKANINA SU DA MAZAJEN SU.*






*PAGE 1*








*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI.*








Can cikin baccin su suke jiyo bugun ƙofar ɗakin su kamar za'a b'alla, mik'e wa yayi tare da jan gajeran tsaki wanda ko wacce take kusa dashi ba zata jiyo ba,ya dubi matar sa da take kwance tayi tsumu-tsumu da ido don ta san ko shakka babu mahaifiyar ta ce ke bugun ƙofar nan,cikin kasalaliyar murya yace," Umaimah ki tashi ki bud'e nasan Mama ce".






Uhm tace,"kafin tace,Allah yau ba zan bud'e ma Mama ba na gaji da halinta ba ta da aiki sai zuwa gidan y'arta babu k'wak'k'waran dalili haba Baby wallahi na gaji da ana canja uwa da na canja Mama wallahi".










Had'e rai yayi yace,"uwan kice ai ba tawa ba,kuma san-nan uwa-uwace duk munin halin mahaifiyar ki gwamma naki da na wasu,don haka ki tashi kije ki bud'e ƙofar nan ta shigo ki soya mata k'wai da bread,ki had'a mata tea mai kauri".








Mik'ewa tayi badan ranta yaso ba ta fita a bedroom d'in ta nufi falon gidan taje ta bud'e ƙofar tana turo baki,Mama dake tsaye k'ik'am bakin ƙofar ta rik'e k'ugu ta wani dunk'ule hannu ta watsa mata dak'uwa tace,"dan uwar ki kinsan ina da ciwon k'afa kinaji ina bugu kin k'i kizo ki bud'e min,ba wan-nan ba ba zama nazo yi mai kika tara jeki d'ebo min in tafi wallahi bashi yamin yawa Maman gaje d'ari takwas take bina,haka D'an Ladi mai kanti naci bashin d'ari biyar kishiga ki sauri dan Allah".








Tunda ta fara magan Umaimah ta wani bud'e baki tana kallonta,Mama ta k'ara mata dak'uwa tace,"dan ubanki baki zaki wage kina kallo na".








Zumb'ura baki tayi ta juya tana k'unk'unai itako Maman k'ara gyara zanin ta tayi, Umaimah koh shiga ɗaki tayi tace,"tou Baby kud'i takeso bazata shigo ba wai bashi ake binta",yace,ki bud'e drawer kid'au 10k ki bata,amma kice tai hak'uri ta shigo",tace," owk",bud'e wa tayi ta fita ta inda ta barta nan ta isketa kan ta mik'a mata ta wafce tafara irgawa, Umaimah bud'e baki tayi tana kallon ta,saida ta gama irgawa kafin tace,tou Umaimah na wuce sai gobe ya muku albarka",bata jira mai zatace ba tasa kai tai gaba.








Umaimah komawa ɗaki tayi ta zuna gefen gadon ta ta rafka tagumi, matsowa yayi ya dafata yace,"kiyi hak'uri mahaifiya ce dole mubi abinda suke so,don mu gama dasu lafiya,tashi muje kitchen in tayaki aiki", mik'ewa tayi suka fita tare.










Mama koh da tafita gidan Umaimah kai tsaye gidan Fateema ta nufa,tana zuwa ƙofar gidan ta wani fashe da kuka wi-wi-wi-wi-wi-wi, Fateema na jiyo kukan ta ta dafa goshin ta k'irjin ta ya buga da sauri ta mik'e ta fito ta tare ta tana fad'in ,"lafiya Mama?.............!










*TOU FA MAI MAMA ZATAYI ANAN KUMA,SAINAGA COMMENT D'INKU*


COMMENT
VOTE
ND
SHARED.






_typing_🖌️






*🟣 SIRIKAR ZAMANI🟣*



*NA MARUBUCIYA*


*SAMHA*
*Y'ARMACE*
*KISHIYACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND KNOW*
*SIRIKAR ZAMANI*




*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)🖌*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/








WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD ( MRS BASAKKWACE)*






GAJEREN LABARI👌








*TRUE LIFE STORY*






*PAGE 2*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*










Mama ta kama saleb'en hijjab d'inta ta fyace majina ta kar-kace tace," Fateema daga gidan Umaimah nike,kinsan bata da mutunci duk bugun ƙofar su da na rik'a yi tana ji da ita da d'an iskan mijinta ba wanda ya bud'e balle suji maine-ne matsalata gashi d'ari na kenan na hau mashin naje gidan su k'arshe tunda ga gidan ta na taho a k'afa harnan wajenki d'ayan albarka".








Fateema cike da ma-makin ta tace," Umaimah?,Mama tace," sosai-sosai kinsan halinta halin malan Garba ubanku",tace,"uhmm Mama ba wan-nan ba mai ya kawo ki,kinsan ina da kishiya banison yawan zaryan nan da sas-safe,don Maman Saudat akwai gori, Mama cike da masifa tace,dalla rufa min baki,duk yawan nan da shige da ficen da nike saboda wa nike in ba saboda shegiyar kishiyar ki d'in-nan bane,ba ma kice in shiga ɗakin ki in huta gajiyar da na d'ebo tun daga abakwa har unguwar rimi a k'afa ba,kin isheni da surutun tsiya,tace,Mama ina zaki shiga wallahi tsaya nan Alhaji nanan bari inje in tat-taro miki abinda na tara kwana biyu",washe hauru tayi tace,yauwa y'ar albarka Allah yasa sunkai dubu goma ko tara", cike da ma-maki tace,Mama dubu goma kuma,tou ai ni ko dubu biyu ban dashi Alhaji bai bamu sisi na cefane,komi siyowa yake duk wata yana ajewa, d'an kud'in break d'in si Firdausi nake hanasu nike tat-tara wa shine suka kai dubu daya da d'ari da hamsin......,"dalla min shiru sakaryan banza sai kace ba mace ba Mama ta katse mata magana taci gaba da fad'in,tsayawa zaki sai ya baki in ya shiga wanka la-luba aljihun sa ki kwashe kud'i,in za'a buga a raya kice ba ke bace sai mi",Fateema gwalalo ido tayi tace,"Mama da kanki kike sani sata?, dak'uwa tayi mata tace,"satan uwar ki,komi kika d'auka na mijinki halal ne ba haram ba,don haka je ki kwaso min y'an canjin raba mugu da makami ibada ne,ma raina kad'an b'arawo",tace,uhm kede Mama wallahi,bansan mai kike da kud'i ba wallahi,bari in d'auko miki,kitafi tunkan ki tara min jama'a",tace, "yauwa maza Allah shi albarka ba duk da ba haka aka so ba k'anin miji yafi miji kyau",juyawa tayi cike da ma-makin halin mahaifiyar su,bata san komi ba kullum ta k'wam-mace ta rink'a zubar musu da mutunci musam-man ita da take da kishiya a dai-dai ƙofar falon suka had'u da Alhaji ya fito zai tafi aiki ,ja baya tayi,ya k'arasa fitowa tace,"harka fito?,yace,"eh wallahi,ina kika je?, baki shirya su Walida ba da mun wuce tare",nuna mai inda Mama tayi da hannunta yayin da tai ƙasa da kanta saboda kunya,yace," a'a Mama ce,koki shigo da ita kya barta waje".










Sosa kyeya tayi cikin rashin gaskiya tana ƙasa-ƙasa da ido tace,"ita tace bazata shigo ba yau', cike da ma-makin shi yace,"Maman a yau?,tace,"eh",yace,"tou bari in k'arasa mu gaisa dan Allah kiyi sauri ki shirya yaran nan su wuce",tace,"tou Allah ya tsareka sai ka dawo",yace, "Allah yasa", yai gaba ya isketa tsaye ya duk'a har ƙasa yace,"ina kwana Mama?,washe hauru tayi tare da cewa,"lafiya k'alau Alhaji, ya kwanan iyalan?,yace,"lafiya k'alau, ya baki shiga ba kika tsaya anan?,tace, "wallahi kuwa sauri nake shiyasa,kuma mun gama tattaunawan abinda ya kawo ni anan",yace," mashaAllahu, bari inbaki na goro da na motor ",tace, "a'a Alhaji ayi haka,Allah yayi albarka",yace,amin tare da mik'ewa ya sa hannu a aljihu ya dank'o kud'i y'an d'ari bib-biyu sa babbi ya mik'a mata,jikin Mama har rawa yake ta karb'a kud'in,tana ta zuba ruwan godiya kamar sabuwar marok'iya, sallama ya mata ya nufi inda motor shi yake ya shige mai gadi ya bud'e masa get ya fice,cike da ma-makin surukar shi da bata jin kunyar zuwa gidan y'ay'an ta abin haushin ma tunda farar safiya,yanzu bai cire tsam-manin duk ta gama karade gidajen k'anan Fateema kafin tayo nan Allah keda kullum sai ta bi-biye gidan y'ay'an nata.










Duk abinda suke Fateema na jikin window tana hango su har ya bata kud'i ya fice,fitowa tayi da y'an canjin a hannu ta nufo Mama tana tafiya tana had'awa, tana ƙaraso wa Mama batai wata-wata ba tasa hannun ta ta wafce kud'in,turo baki Fateema tayi tace,"Mama miye haka,wallahi kin fiye son kud'in tsiya,wai mai kike da kud'i?,Mama tace,"idon matam bayi,kuna da d'an shinkafa da indomie ki d'ebo min?, Fateema ta waro ido tare da bud'e baki , dak'uwa Mama tai mata tare da cewa ,"ko bazaki bada bane?,tace,ko d'aya Mama zan bada ni na isa na hanaki ,kije gida zan aiko a kawo miki karki jawo min magana gun kishiya, kuma dan Allah Mama na rok'e ki alfarman annabi da alk'urani,kiyi sati bakizo gidan nan ba,wallahi kunya nikeji,tunda nazo gidan nan ban tab'a ganin iyayen Maman Saudat sunzo ba,ko Yayan ta kika gani a gidan nan tou haihuwa tayi amma ke kullum kina han.......sarin katse mata maganan tayi tace,"ke banza ance miki hakanan banza ne basa zuwa,duk d'iyar da kika ga iyayenta da y'an uwanta basa bibiyar ta musam-man iyaye tou bata gama dasu lafiya bane,ba y'ar albarka bace",cike da k'osawa da magan ta Fateema tace,"nide naji kitafi zanzo muyi maganan kuma zan aiko miki da shinkafar",tace,"tou nayi no gidan Zainab",cike da ma-maki tace,"gidan Zainab kuma Mama dan Allah kije gida ki huta haka Zainab da take kabala zaki kama hanya?,tou tab-batatta mai baki tsuntu ni nayi gaba",bata jira mai zata kuma cewa ba tai gaba abinta,da ido Fateema ta bita cike da ma-makin halin uwarsu da bai raguwa saide ya k'aru.












A gag-gauce yafito daga falon kallo d'aya zaka mai ka tab-batar da ranshi a b'ace yake yashiga motor shi maigadi ya bud'e masa get ya zo fita ya tsaya inda mai gadi yake tsaye yace,"Baba na baka umurni kar ka k'ara barin ko waye yazo gidan nan ya shiga duk wanda yazo kace,ni mai gidan Alhaji Ahmad na hana shiga koda kuwa mahaifiyar ta ne", Baba mai gadi yace,an gama mai gida,sa kai yayi ya fice,yana da yasanin auran Zainab tun farko auran su yau shekara uku gidan bai tab'a yakewa da bak'i ba daga b'an garen taba,in zai sai buhun shinkafa tou bai yin sati daga ita sai shi kullum,tana kwashewa in uwarta tazo ta bata,in ya aje y'an kud'ad'e ta kwashe daga ita sai shi a gida a ɗaki yanzun dole ya dena kai kud'i cikin ɗaki shida gidan shi yanzun ma fitowan da yayi ranshi b'ace baifi kwana biyar da yasiyo kayan abinci ba amma tace,masa komi babu,saide yasha ruwan lipton bako madara balle siga duk sun k'are baccin yana siyo komi enough amma baya sati dole ya k'ara aure ko zaiyi dace da wata macen ta gari.








Yana fita baifi minti talatin ba sai ga Mama ta sauka akan mashin ta taho da k'arfin ta zata shige gidan y'a taji k'ofa a gark'ame bugu ta farayi baji ba gani, Baba megadi ya lek'o ta y'ar k'ara min b'uli yace," Hajiya Alhaji yace,kar in k'ara bari kishigo kiyi hak'uri ki tafi", tace, "kan kutumar uba ni zaka hana shiga kai awa a mai gadin bakin get kai d'in banza da wofi nasan Ahmed bazai ce haka ba mai hak'uri ne shi don haka ka bud'e min ko kuwa aikin ka yazo k'arshe a gidan nan",yace, kome zakice kice amma baki shigowa,yana gama fad'a ya juya ya shige ɗakin sa ya barta tsaye,bugun get d'in take kamar zata b'alla tana lailayo zagi, Zainab tun da taji ana bugun get tasan Mahaifiyar tane,tacika tai fammm tana tanajin rashin mutuncin da zatai ma Ahmad in yadawo tunda ya wulaqanta mata uwa,Mama ko takai hour guda zaune bakin get d'in mutane na wucewa suna kallonta kaman almajira da taga ba sarki sai Allah haka ta tashi ta tare mashin ta hau tana
ta tsine ma Ahmad,duk da haka bagida ta wuce ba saida tai biye-biye,sai wajen azahar taje gida tana zuwa tayi alwala ta shiga ɗaki ta shimfid'a dad-duman ta ta zauna ta mim-mik'e k'afa wai zatai sallah.








*CABDI LALLAI MAMAN NAN DUK GANTALIN DA TASHA TIN SAFE DA K'AFAFUN TA AMMA ANZO BAUTAN UBANGIJI TA ZAUNA TA MIK'E K'AFA RASHE-RASHE WAI ZATAI SALLAH ALLAH YA KYAUTA.*






COMMENT
VOTE
ND
SHARED.




_typing_🖌️






*🟣 SIRIKAR ZAMANI🟣*



*NA MARUBUCIYA*


*SAMHA*
*Y'ARMACE*
*KISHIYACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND KNOW*
*SIRIKAR ZAMANI*




*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)🖌*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/








WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD ( MRS BASAKKWACE)*






_WATTPAD:_ *KHADYBASAKKWACE*


_FACEBOOK:_
*MAMY BASAKKWACE*




*GMAIL'S*
*khadee241@gmail.com*
*OR*
*muhammadkhadija748@gmail.com*




*WAN-NAN PAGE D'IN SADAUKAR WA NE GA HAJIYA DALA,ALLAH YABAR ZUMUNCI DA K'AUNA,INA GODIYA DA KULAWA.*






_GAJEREN LABARI👌_




*PAGE 3*








*JAN HANKALI DA YAWAN KU KUNA TINANIN CEWA WAN-NAN UWA CE,TABBAS WAN-NAN UWACE, MAHAIFIYAR SU CE DA GASKE,KUMA YA FARU DA GASKE,YANZU ZAMANIN DA MUKE AKWAI IYAYEN DA DAYAWA SON DUNIYA DA KWADAYIN ABIN DUNIYA YA MUSU YAWA, BURIN SU KAWAI Y'AY'AN SU IN SUN AURAN MASU HANNU DA SHUNI,SU RINK'A BIBIYAR GIDAN JEN SU SUNA GANIN MAI YAKE KAWO MUSU SU YAGA RABON SU ,IN BASUJE DA KANSU BA KUWA,ZASU TURA K'ANNAN SU,WASU IYAYEN HAR SATA SUKE SA Y'AY'AN SU,ALLAH DE YASA MU DACE .*








*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI.*








Yanda ta mim-mik'e k'afa yasa y'arta Nafeesa ta dubeta tace, "Mama miye haka kuma?,tace,"uhm kide bari Nafeesa ciwon k'afa", cike da ma-makin ta tace,Mama tun shidan safe kika bar gidan nan da k'afar ki kina ta yawo a gari sai yanzun ki dawo ki mim-mik'e k'afa kice zaki bautawa ubangiji","ke dalla min shiru, y'ar izalan banza kawai,kun fiye wa'azi kabarin ki daban nawa daban in aljanna na Malan Garba sai ku hanani shiga", Nafeesa uhm kawai tace.












Wur-wur ta dungura sallah ta koma ta shigid'e,tana hamma.






"Gafarar kudai masu gida Saratu na nan kuwa",cewar wata dattijuwa da bazata wuce shekarun Mama ba,Mama daga d'aka tace,"Maman Gaje gani yanzun na shigo nai sallah",wacce aka kira da Maman Gaje tace,"ke kinma yi sallah Saratu ni ina nayi aini banma yi ba,samma bana cikin natsuwa ta wan-nan shegen yaron Auwalu ya koro min Hafsatu gida wai tana masa satan hatsi tana kawo min ina saidawa,Mama ta mik'e zumbur tace,"mene Maman Gaje nike ji haka?, Auwalu nan da kike ganin shi dama tun ba yau ba nace ki tashi tsaye kanshi,idon shi a bud'e yake samm bai ganin girman manya,shiyasa da kika ganni nan ban yarda y'ata ta wulaqanta a gidan miji ba daganan har niger nake tafiya nemo musu maganin mallaka bakiga yanda mazajen su suke girma-ma ni ba kamar zasu maida ni cikin su",Maman Gaje tace,kide bari Saratu ki dace surakai na k'warai kuma ke kina samu daga wajen y'ay'an ki da surikan,niko fa Gaje mai faci take aure, Hafsatu kuwa itace ta aure mai gwab'i-gwab'i Malamin makarantan boko tou gashi ya korota wai yana siyan hatsin wata amma bata kai masa,Mama tace,"cabbb ke kika zauna ,kina kallon ruwa kwad'o har zai miki k'afa,kin ganni nan yau tun shida na fita gidan Umaimah na fara zuwa,dubu goma haka ta dunk'ulo min su,da ga nan na tafi gidan Fateema,mijinta duk da yana da mak'o bai basu na cefane saboda bak'in cikin kar tasai fili gwamma yayo cefane da kanshi amma duk da haka innai ido biyu dashi yana bani na goro yanzun haka kud'in da yaban sunkai dubu takwas,nasa dubu d'aya da y'an canji wajen Fateema d'an kud'in break d'in su Waleedah da take hanasu ta-tara,daganan ina fita natafi gidan Zainab amma mai sam mai gadin gidan tsohon banza kawai ya hanani shiga wai Ahmadu yace kar abar kowa ya shiga da na hadon kusan dubu talatin a d'an fitar nan da nayi",kuma shima Amadun zan dai-dai ta masa zama wallahi,sai mun tatse shi kamar nonon sa", Maman Gaje tace ,"aike Saratu keki kai farar haihuwa wallahi,kakan ki ta yanke sak'a wallahi damani inji matar mani",Mama tai dariya tace,kema Maman Gaje kece baki soba,gobe in Allah ya kaimu birnin gwari zan nufa wajen wani malami kishirya muje kawai", Maman Gaje tace,Saratu ni dake da ban-banci,ina ta ciki wani kud'in zuwa gun malamai sai kin dawo,in da kara ai gajen y'ar ki ce ki had'a ki nema musu taimakon",hakade Mama ta rink'a zuga Maman Gaje har ta yarda zata bita gun boka, Nafeesa dake gefe tawani ja dogon tsaki kamar halshen ta zai tsinke tace,zanga uban da ya isa ya rink'a bibiyar min gidan aure wallahi, banza da ita Mama tayi suka ci gaba da hirar su da Maman Gaje.










Mijin Zainab wato Ahmad yana tashi daga office ya nufi kasuwa ya je gun y'an dankalin hausa ya siyo buhu guda,ya sayo buhun garin k'uli,ya siyo buhun gero dana sugar ya siyo buhun masara da rabin buhun kuka,da buhun garin roga yasa mu motor kwasan kaya aka loda a acikin ta ya shiga motor shi yana gaba suna binshi a baya har suka isa gidan shi a haraban gidan yayi parking ya fito ya umurce su da su sauke kayan,bayan sun sauke ya sallame su suka wuce,sa y'an aikin gidan yayi su kwashe kayan su shiga dasu ciki,yai gaba,da sallama ya shiga falon kaca-kaca kamar kullum itama yanda ya barta haka ya isketa da alaman ko wanka bata yi ba kallo d'aya ya mata ya kauda kai zai wuce, mik'ewa tayi ta sha gaban sa,take wani tsami ya dake hancin sa da sauri ya ture ta gefe, dai-dai lokacin mai guga ya shigo da buhun dankali,da kallo ta bishi,har zai shige store don ya aje cikin tsawa tace, kaiiiiiiiiiiii ina zaka shigar min da abincin dab-bobin nan?,fita dasu,ba mai guga ba,hatta Ahmad da yayi gaba saida yayi saurin juyawa jin furi cin ta,taci gaba da fad'in maza kafitar min da abincin a kuyoyin nan anan,ni dabba ce da za'a siyo min dankali,aje akai ma dab-bobi", Ahmad murmushi yayi yace,Isah maida waje,baibi ta kanta ba ya bud'e ɗakin shi ya shige ya sa key,wanka ya shiga zuciyar shi na masa zafi,can yayi murmushi,bayan ya fito ya shirya sai k'amshi yake ya d'au key d'in motor shi da wayar shi ya fito,ba kowa a falon fita yayi haraban gidan ya k'ara sa inda mai gadi yake dashi da Isa mai guga yace, Isa kaje ka nemomin motor in kwashe kayan nan inkai ma dab-bobi kamar yanda Zainab ta buk'ata..............!










*TOFA MAI MURMUSHIN AHMAD YAKE NUFI,KUMA SU WAYE DAB-BOBI DA ZAI KAI MAWA?*






_MORE COMMENT MORE TYPING BAKWA COMMENTS SAM._




COMMENT
VOTE
ND
SHARED










typing🖌️








*🟣SURUKAR ZAMANI🟣*


*بسم الله الرحمن الرحيم*



®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[ ```Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women```]
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*


Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads