Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 23384 words

Chapter 7 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jun 2024

319

Ads at the middle of Article

NANAH tatafi makaranta ta nufi kasuwa ta nufi gun masu kayan gwari ta saro kamarsu citta kanufari,tumba,barkono,daddawa ,kuka,kuɓewa bushash-shen tumatur da tattasai da ta rugu maggie gishiri manja man gyaɗa ta sayo,duk siyayyan da tayi taga ko rabin kuɗin ba taɓa ba.










Dawowa tayi ta ƙuƙƙula bayan NANAH ta dawo makaranta da mamaki take kallon kayan ta tambaye mahaifiyarta tace,"UMMU waya baki kayan nan",satowa nayi ta bata amsa a taƙaice.






NANAH tunda taji haka yasa ta kama bakinta tayi shiru ba ta ƙara cewa komi ba,UMMU aiketa tayi maƙwafta ta sanar dasu,aiko gida-gida tashiga tana faɗa,aiko ana zuwa sosai ana saya kuma tana fidda kuɗi harda riba aciki take sayan musu omo abinci da duk abinda NANAH tagani tana so.










Ganin kasuwancin ya haɓaka yasa taje ta siyo buhun masara da gero da dawa dana shinkafa shima ta fara saidawa da sauƙi fiye da shago aiko mutane turu-ruwan zuwa saye suke.










Ganin ta-tara riba sosai yasa ta haɗa kuɗin ta nufi inda taga REEDWAAN ta zauna bata ganshi ba haka ta haƙura ta tashi ta tafi kullum sai tazo tsawan sati ɗaya basa haɗuwa arana na ƙarshe ne taga mai gadi ya leƙo take tambayan shi REEDWAANU take nema,yace shima bai sansu ba baƙine su basufi sati da dawowa ba asalin masu gidan su saida sun tashi,haka ta juya asanyaye ta kama hanyan gidan cike dama kanta alƙawari masa addua tare da adduan Allah ya kuma haɗata da wannan bawan nata.








NANAH ta taso yarinya ce mai hankali da natsuwa akwaita da jan faɗa da rashin kunya bata ɗaukan raini a gun koma waye ba ruwanta da kula ƙawaye ko maza ita kaɗai take alamuranta sabida bata son gulma kace nace bataso ace tace,shiyasa bata kula ƙawaye.








_CIGABAN LABARA._
Yau kimanin wata huɗu kenan da AHMAD yace,"kar ZAINAB ta dawo masa gida...........!






MORE COMMENTS
MORE TYPING
*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*




_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*










NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*










*ƳAR UWA ABIN ALFAHARI ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKI,YA HASKAKE ZUCIYARKI,FARINCIKI DA ANNA SHUWA YA TABBATA AKAN FUSKAN KI DUK ONLINE WRITTERS NAGAMA NAZARI BABU KAMARKI KIN ZAMA ƊAYA TAMKAR DUBU HAƘURI DA KAWAICI ZURFIN TUNANI DUK KE ƊAYA (MY LIPTON GIRL)NA GODE MA ALLAH DA YABANI ƳAR UWA KAMAR KI,ALLAH YA ƘARA HAƊA KANMU,YA TSONE IDON MAƘIYA,AMEEN YA RAB🙏*






_GAJERAN LABARI👌_













_GAJERAN LABARI👌_






*PAGE 38&39*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*








Yau kimanin wata huɗu kenan da AHƁAD yace ZAINAB kar ta dawo gidan sa,hankalin MAMA duk ya gama tashi bata yanzun da lokacin zuwa gidan ƴaƴanta sai nabin bokaye in kaganta gidan ƴaƴanta tou babu kuɗin bin boka saitaje ta tada musu hankali dole suke nemowa su bata taje nemo malamin da zai shawo kan AHMAD amma shiru kuke ji wai ƙeya samu saƙon baya ZAINAB duk tabi tafita hayyacin ta gashi kullum cikin gorin NAFEESA take da ta nema biyar ta rasa zatace itace tun tana biye ta su sha dambe yanzun ko bata iyawa da ganinta abin kamar lokacine amma shiru kake ji wai uwar gulma tayi cikin shege gashi ko ta kirasa a waya bai shiga yayi blocked ɗinta amma duk wata yana tura mata kuɗi ta account sabida yasan bai saketa ba akwai haƙƙin sa akanta ya mata hakane don ta ƙara horuwa da zaman talauci ,itako yanzun ta soma sarewa da aikin bokayen da MAMA takebi don ba yanda zatayi da itane ta ƙyaleta ta zuba mata idanuwanta,MAMA ko duk inda taji labarin boka saita ɓulla ta narka masa ƴan kuɗi tayo gaba amma shiru da yake ba'acikin hayyacin ta takeba shiyasa bata fahimci bokayen gyara miyan gidan su sukeba idonta ya rufe burinta ƴarta ta koma gidan mijinta suci gaba da cin arziki.










Ɓangaren MAMAN GAJE koh abu ya taru mata goma da ashirin ga ƴa a gida da ƙaramin yaro ga wani ciki ya ɓullo ga SANI tunda yazo yaci bai ƙara wai-wayan suba,koda taje gidan iyayen sa akace mata ya jima da tafiya hausa neman kuɗi,ta sanarda su maganan ciki sunyi farinciki sosai amma da yake talakawane suma naci suke nema gari da sugar kawai ta samo ta dawo gida,hakan yasa ta kama aikin wanke-wanke da shara don rufa ma ƴarta asiri ta fita hanyar MAMA don duk ita takaita ta baro da baa samu cikin nan ba duk da gidan aikin wulaƙantata ake hakan baisa tayi zuciyaba inta bari wa zai bata.








Ɓan garen NANAH da AHMAD kuwa soyayya ta kankama ya siye zuciyanta da rikitattun salonsa tun bata kulashi harta fara kula shi,haka REEDWAAN yatasa shi gaba sukaje gun UMMUH neman izinin zuwa zance wajen ƴarta UMMU tayi farin ciki tare da musu addu'an,in alkhairi ne Allah ya tabbatar,NANAH ko farinciki kamar anbata kyautan kujeran makkah,soyayya suke sosai kamar su lashe kansu AHMAD baison inyazo NANAH tai fushi inko tayi fushi bai iya tafiya sai ya tabbatar ta sauka inba haka ba ranan ko wayan shi bata ɗagawa kasacewar ya sai mata waya ƙarama yace inta gama school zai saya mata babba intayi ƙoƙari,don yasan yanzun ya bata babba taji daɗin chart zata manta karatu ko a class chart zatayi NANAH da son kwalliya ai hoto yasa yanzun ta dage da karatu,kullum shike zuwa ya kaita in ya ajeta ya ɗau jakanta ya rakata har bakin class yana goye da jakan wani lokacin har kujera da take zama yake aje jakan ƴanmata suyita kallon shi cike da burgewa da ban sha'awa suji dama sune kalan saurayin da sukeso da mafarkin samu ya zama mijin su,yanzun ƴan maza da matan class ɗin NANAH burgesu take yanda takejan zaranta yanda takeso kowa naso yai mata magana amma babu fuska a tattare da ita ita shigo ba malami takaddan ta take cirowa tai ta karatu ,aduk sanda AHMAD zai aje mata jaka ko a gaban waye ba ruwanta take riƙo hannun sa fuskanta ɗauke da murmushi mai sace zuciyar masoya idanuwanta na kafe acikin nasa kyawawan idaunwan ta masa addu'a kala-kala hakan ba ƙaramin daɗi yake masa ba yana mayar mata da sansanyar murmushi yake cewa amin kafin suyi sallama ƴan class ɗin da malamai kowa mamakin irin soyayyar da suke na kowanne su burin shi ya faranta ma ɗaya baison yaga ran guda ya ɓaci ,hakan da REEDWAAN yagani ko shima baa jin kunyar sa yasa yaje ya sanar da MOMY mahaifiyar AHMAD acewar shi karsu lalace a waje bai nemi shawaran AHMAD ba yai gaba kansa MOMY ko ta kira magabatan shi ta sanar da su sukasa ranan zuwa gidan su NANAH duk abin nan da ake AHMAD baiko saniba don REEDWAN yace ta ma MOMY karta gwada masa ta barshi sumai auran ba zata *LITTAFIN MY LIPTON☕* _(ohhhhhhhhhhhh REEDWANU AKWAI SHISHSHIGI🤔)_.




MORE COMMENTS😃




_typing🖌️_










*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*




_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*










NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*








_GAJERAN LABARI👌_










*PAGE40*


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*








REEDWAAN yace ma MOMY karta gwada masa ta barshi sumai auran ba zata *LITTAFIN MY LIPTON☕* _(OHHHHHHHHHHHHHHH REEDWAANU AKWA SHISHSHIGI ZANGA YANDA ZAAI AURANGA BATARE DA SANIN ANAGOBA🤔)_,nufan gidan UMMU yayi da maganan lokacin NANAH tatafi islamiya,da farin ciki UMMU ta tarbe sa bayan ya zauna yasha ruwa sun gaisa,a ladabce ya ma UMMU bayanin abinda ke tafe dashi,UMMU tayi farinciki matuƙa don burin kowata uwa ta gari taga ta kawar da ƴarta daga gaban ta,duban REEDWAN tayi tace jikinta lokaci ɗaya yai sanyi.








Tace,"REEDWAANU wani hanzari ba gudu ba wallahi ban shirya aurar da NANAH ba nafiso tagama makaranta ta samu aiki kaga munada madogaran da zami mata kayan ɗaki yanzun ko ko cokali ban aje ba da sunan aurar da ƴata,in so samune kubari nan da shekara biyar haka tinda yanzun tana zana jarabawan ta na fita secondry school ne".










Yace,"AUNTY karki damu da wa ƴannan ki addu'a kawai Allah ya bada zaman lafiya ni na miki alƙawari ba za'a ji kunya ba,kimin kwantace gidan kakan nin nata zamuje ranan sunday inshaAllah a biya komi inta gama zana jarabawa basai ai bikin ba".






Yana maganan cikin kwantar da murya tare da lallashin mai sauraro.






Gyaɗa kai tayi tace,"shikenan Allah ya tabbatar da niyan alkhairi".






"Ameen ya Allah".




Yafaɗa yana aje ajiyar zuciya jin bataja maganan da nisa ba.








Nan tayi masa kwatance dangin mahaifin NANAH da suke birnin gwari da number wayar kawunta saida ya gwada ya tabbatar tana shiga kafin ya mata sallama ya miƙe tare da sa hannu a aljihu ya ɗebo kuɗi da baison yawan su ba yace ta ƙara jari godiya ta masa da addu'o'i cike da jin daɗi da farinciki yake amsawa har ya juya yatino ya juyo ya dubeta yace roƙeta alfarman karta faɗa ma NANAH don ko shi AHMAD baisani ba,inko NANAH tasani AHMAD ya sani,batare da dogon tunani ba ta amince masa don itama tana tinanin yanda zata faɗa ma NANAH ta botsare don kullum maganan ta bata isa aure ba.












REEDWAAN zuwa yayi yasami AHMAD da yabashi aron ɗayan part ɗin gidan shi yanaso zai ƙara aure,AHMAD cike da mamaki yake kallon REEDAWAAN don matarsa RUMAISA ba'abin da bata masa,ladabi biyayya tarairayan miji ko shima na yabonta sosai tou miyasa REEDWAAN ya zaɓa ya ƙara mata kishiya,koda yake ko wani namiji kaji yace yana son ƙarin aure da dalili,amma dashi yasamu RUMAISA da bazai mata kishiya ba saide yai ta mata ciki tana haihuwa,batare da yabashi amsaba yai miƙe ya kakkaɓe rigarsa ya barwajen,REEDWAAN murmushi yayi yana binsa da kallo.










REEDWAAN matarsa RUMAISA yaje ya faɗa ma komi akan ƙarin auran da zasuyi ma AHMAD ba tare da sanin saba da yanda yace masa ai ita zai ƙarama kishiya ta rinƙa dariya maƙudan kuɗi yamata transfer ta account yace taje dubai ta haɗo kayan lefe naji da faɗa,kafin nan saida yakaita gidan su NANAH suka sha fira da UMMU taga NANAH don ta gane size ɗinta.








Aranan da sukace zasuje ranan ko suka tafi da kwatance harsuka ƙarasa gidan bayan a vaisa sun sha ruwa ba tare da ɓata lokaci ba suka gabatar da abinda ya kawo su ba kunya ba tsoron ubangiji suka yanke sadaki da gaisuwa aka biya suka amshe saikace su sukai wahalar ƴar,bayan baƙin sun tafi suka ko rabe kuɗin batare da sunyi tunanin sukai ma uwar ƴa haƙƙin ƴarsu ba.










Koda REEDWAAN ya kira UMMU yafaɗa mata anbiya komi sun taso tayi farinciki sosai,duk da tasan ko sisi bata gani a kuɗin sadakin ƴarta don dangin ubanta mayun kuɗine macutane na ƙarshe burinsu kawai ka basu,addua tayi Allah ya kawo mata mafita ta fita kunya.










REEDWAAN ko ɗayan part ɗin gidan AHMAD ya hau gyara ba tare da izinin mai gidan ba ,AHMAD sa masa ido yayi yaga iya gudun ruwanshi don yaga kamar ya fara hauka,abinda ke bashi mamaki ina REEDWAAN ya samu mata da bai taɓa jin labari ba tunda bai nema yasani ba yasa shi ƙara rufe baki yai kaman baison yanayi ba,acikin kwana kaɗan aka gama da yake akwai kuɗi ,aka zuba funitures masu kyau ɗakin ya tsaru iyakan tsaruwa ko ƴar da iyayenta suke da kuɗi ba ko wacce zaa sa mata kayan sa REEDWAAN ya zuba ma NANAH ba,a ɗakinta,duk abida yake AHMDA ɗauko idanuwa yayi ya zuba masa don duk abindaREEDWAAN keyi haryau bai ce dashi uffan ba akan auran da zai ƙara gani yake kamar mafarki amma abin naso yazama gaske,REEDWAAN yasa angyara gidan su NANAH yayi kyau sosai ya ya gyara mata ɗaki,NANAH bata kawo komi ba aranta.










Haka rayuwa taci gaba da tafiya harta gama zana jarabawan kamala babban sakandirin ta,REEDWAAN ko hidiman shi yake batare da sanin AHMAD ba saide wasu abokanan sa sati biyu aka sa akwana a tashi yau saura kwana biyu biki aranan ne RUMAISA matar REEDWAAN tazo ta ɗauke NANAH ta tafi da ita shagon saloon sukaje akai masu lalle da gyaran jiki da gyaran gashi,kuma a ranan ne aka kawo lefen NANAH set uku kowanne mashaAllah ƴan uwan UMMU suka ansa kayan da maƙota,kowa sai sambarka kan kace mi labarin lafen ta yakai saƙo da lungu na unguwan da ma maƙwaftan layin sai turu-ruwan zuwa gani akwati ake kowa na tofa albarkacin bakinsa ƴan gulma nayi masu sa albarka nayi,sai washa gari ƴan uwan mahaifinta suka iso basuzo da komi ba daga rabin buhun masara sai samira uku da ɗari biyar da aka ɗauro a saman samirun,UMMU ko bata gwada musu komi ba illa ansa da tayi tasa ma kayan albarka.






AHMAD jin REEDWAAN zai ƙara aure ya kawo gidan sa yasa yai ma ZAINAB text ta shiryo ta dawo gida,aiko kamar jira ko take MAMA bata nan NAFEESA ma bata nan ta shirya tayo gaban kanta key ta miƙa ma maƙwafta tace in sun dawo ace musu mijinta ya maidata napep ta nema taɗau har ƙofar gidan ta cike da nadaman abubuwan a take ma mijinta a baya ta ɗau alƙawarin gyara duk wani kuskurenta musamman sace-sace da take masa saide suyi tsiya da MAMA amma bata ƙarabata ko sisin ta balle takai ma bokayen banza suci kaji,tana isa taga gidan tsaf kamar da mace aciki zagewa tayi tai girki iyakar iyawanta ta jera a dining tai wanka tana jiran dawowan sa,bai shigo ba sai tara na dare cike da murna ta zo ta rungume shi ta amsa breifcase ɗinsa tana masa sannu da hanya,da ido kawai yake binta don ko da take amarya bata taɓa masa abinda ta masa yau ba ɗakin sa suka shiga ta aje breifcase ɗin ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka tafito yana zaune bakin gado sororo kamar wani dolo,ƙoƙarin cire masa kaya take temaka mata yayi ta cire kayan ta raka shi bakin toilet ɗin saida taga yashiga kafin ta juyo ta buɗe wardrobe ɗin sa ta cirp masa kaya masu sauƙi yana fitowa ta tsane masa jiki da towel ta temaka masa yasa kayan kafin ta feshe masa jiki da turare shiko mamakin sauyawan ta yake lokaci kaɗan ashe dama duk ta iya waƴan nan abubuwan bata masa riƙo hannun shi tayi har dining tai serving ɗinsu su ta rinƙa bashi,saida ta tabbatar ya ƙoshi kafin taci nata in taƙaice muku a wannan daran saida suka gurji juna cikin farin ciki da jin daɗi.






_RANA BATA ƘARYA SAIDE UWAR ƊIYA TAJI KUNYA_
[7/14, 21:03] MRS BASAKKWACE: Yau takama asabar yaune za'a ɗaura auran NANAH da AHMAD,NANAH wacce RUMAISA ta ɗauketa tana gidan ta,AHMAD ko da ƙyar ya amince zaije ɗaura auran REEDWAAN shima saida friends ɗinsu suka bashi kaya kafin ya amsa kayan da REEDWAAN ya kawo masa ya saka,NANAH na gidan REEDWAAN an tsantsara mata kwalliya tasha leshi maikyau da tsada cewar RUMAISA zata rakata bikin ƙanwar tane,itama RUMAISA tasha ado abinta ba'acewa komi,RUMAISA sai hotina take musu NANA ko sai style ake kala-kala hankalinta kwance hakanan yau tatashi cikin farin ciki sosai washe hauru kawai take duk da tana ɗan shiga tunani lokaci lokaci na rashin kiran da AHMAD bai mata ba tasaba shike kiranta kullum safiya gashi yanzun har kusan eleven amma bakira balle saƙo ta tura masa saƙo ba reply ,RUMAISA binta kawai take da kallo itade NANAH na burgeta tabas AHMAD yanzun yayi mata ba wancan buzuwar ba mai shegen girman kan tsiya.






Ƙarfe shaɗaya dai-dai masallacin da zaa ɗaura aure yacika maƙil da mutane AHMAD duk ransa a ɓace yau REEDWAAN ya ƙwace masa waya ya hanashi yaji muryan NANAH sa ya ƙosa agama ɗaura auren ya ƙarasa gidan su NANAH ya ganta don kusane da layin su,kamar daga sama yaji ana ɗaura aure AHMAD BASHEER MAI KAJI da NANAH KHADEEJA AHMAD MUSA ƙara kasa kunne yayi yaji tabbas shi ake ɗaura ma aure fara ware ido yayi nan ya hango baffan sa da sauran ƙannin mahaifinsa da duk bai kula dasu ba tsungulin kansa yayi yana tunanin mafarki yake amma yaga a zahiri ,bai tabbatar da alamarin gaskiya bane saida yaga angama ɗaurin auran anata zuwa taya shi murna da sanyan alkhairi dole yake dariyan yaƙe wanda tafi kuka ciwo ya rasa mai zaiyi farin ciki ko akasin haka jawo hannun REEDWAAN yayi ya fito dashi daga cikin masallacin can nesa da masallaci suka tsaya ya haɗe rai yace," REEDWAAN mi kayi kenan?,"auran dole nama koko ince auran bazata tunda kai kaƙi kadawo da matar ka kuma ka ƙi kai hankali ka tura ni sai nai komi,fuska a sake yake maganan,AHMAD ƙwafa yayi tare da jan tsaki yace,"ban wayata tou mallam",sa hannu yayi a aljihu yana danne dariyar sa yaciro ya miƙa masa ba tare da yace komi ba ya amsa wayar shi ya nufi motor shi ya shiga sai kumbura yake,REEDWAAN ko dariya ta ƙwace masa na ganin fushin a AHMAD yake mai makon yai farin ciki,REEDWAAN ko komawa yayi ya rinƙa sallaman baƙin shi.








AHMAD duba wayanshi yayi yaga text ɗin NANAH wani farin ciki ya mamaye masa zuciya da ya tina tazama matar sa yanzun haka fara karanta text ɗin yayi kamar haka
_( A person so upright and ethical like you. A person so dear and near to me like you. I might not say it all the time but all the time I think about is you and you. Good Morning and have a fun day ahead💋💓.)_




Murmushi yayi ya danna kiranta kamar jira take ta ɗaga cikin muryan shagwaɓa da yake ƙara rikita shi tace ,"everlasting ina kashiga ka manta dani?




Waro idanuwa yayi kamar tana ganin sa yayi ƙasa da murya yace,"wane ni my wife".




Murmushi tayi tace,"baby Allah ya gwadamin randa zan zama matarka da nafi kowa jin daɗi".






Cike da mamaki aranshi yace karde NANAH bata san an ɗaura mana aure ba yau da ita tou tana ina ne baride na tambaye ta yace,"baby kina ina haka?.




Uhm har yau ina gidan YAYA REEDWAAN gashi ma mun shirya zamu bikin sister aunty,baby bakaga kyawun da nayiba inkazo gidan aunty kace ta tura ma pics ɗin danayi da wayarta".








Buɗe baki yayi lallai REEDWAAN ɗan iskane ya faɗa a zuciyar shi a zahiri ko murmushi yayi yace,"KHADIJA".






Jin abin tayi banbaraƙwai don bai raɓa kira ba saide yace NANA

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads