Showing 3001 words to 6000 words out of 23384 words
Chapter 2 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt
*_Z• W• F•🏝
*NA MARUBUCIYAR*
*SAMHA*
*KISHIYACE*
*ƳARMACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND KNOW*
*SURUKAR ZAMANI*
WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD MRS BASAKKWACE*
FACEBOOK
MAMY BASAKKWACE
GMAIL'S
KHADEE241@GMAIL.COM
OR
MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
GAJEREN LABARI👌
*SHAFI NA SHIDDA6*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI*
Nafeesa ɗagowa tayi cike da mamakin ta duk da tasan Mama zata iya fiye da haka kaɗan daga cikin ƙananan halinta ta buɗe baki tace,"haba Mama wanda yace yana son naka masoyin kane ba maƙiyi k........!,hannunta har rawa yake ta wani buge bakin Nafeesa,hakan yasa tayi shiru haɗa yatsun ta tayi kafin ta sauke mata a fuska alaman daƙuwa,tsuru-tsuru Nafeesa tayi da idanuwa ji take kamar ƙasa ta buɗe ta shige sabida tsananin abin kunyar da Mamah ta ja mata.
Shiko saurayin kanshi ɗaurew yayi da mamakin wannan dattijuwa da take kyarar sa,yasan de duk ta laucin shi gidan su ya fi wannan kangon gidan nata kyan gani da kyan duba,gida kamar bola tunda ta matso take tashi wani wari take kamar mai kiwon kajin turawa daurewa kawai yake yana zuƙunne a gaban ta.
Mama juyowa tayi kansa a hasale maganan ta ya ya dawo dashi daga duniyar tinanin da ya lula,tace,"kai faƙiri kai maza ka bar nan tun kafin na yaga ma rigan rashin mutunci, inci uwar ka,mu tsiya kai tsiya wa zai temaka ma wani kenan,nina ma figanin saide mu taimaka maka,daga ganinka harka mutu bazakai arziki ba alaman ƙarfi ai yana ga mai ƙiba dan haka inuwar ka banson gani kafin in rufe ........" , bata rufe baki ba ya miƙe ba tare da yace ƙala ba ko kallon Nafeesa bai yiba ya raɓa ya wuce ta gefan Mama,dogon tsaki taja tabi gefan rigar shi da harara,baiwar Allah koh Nafeesa da ido tabishi har ya fice daga kwar-kwaɗan lungun tasu.
Mama tsaki taja kamar halshen ta zai tsinke tace,"to munafuka tashi ki ɓace min daga gani kar ki yarda ki shigar min ɗaka da kayan da kika raɓe wancan faƙirin kiyi tsirara ki sa su a igiya naga da alamun ruwan sama zaizo ya bugesu ko dauɗan talaucin nan zai fice,Nafeesa bata iya cewa komi ba ta miƙe zata raɓa ta gefen ta tashiga gida don tagama tsinkewa da al'amuran mahaifiyar ta,da sauri Mamah tawani ja baya ta manne da bango kamar wata ƙadangare tana zaro ido tace,"shegiya munafukar banza so kike ki raɓeni in kwashe tsiya?,bata ce komi ba tashige gida ranta duk a dagule,Mamah bin bayanta tayi sai mitan zancen take,kamfato ruwa tayi a randa ta ɗauko tsintsiya da omo ta dawo ƙofar gidan ta wanke da kalin da suka zauna har ƙasa daya duƙa ta wanke gun tassaa kafin ta shige gida.
a tsakar gida ta iske Nafeesa zaune ta rafka ta gumi hawaye na dirara daga idanuwan ta,tsaki taja ta wuce ɗakin ta tana ta masifa,ɗaukan ƴar wayan ta tayi da Umaimah ta saya mata ta danna kiran number Zainab bugu ɗaya ta ɗaga,ba sallama ba komi tace,"Mamana ɗazun kikazo Ahmad ya hanaki shigowa ban tabbatar da mara mutunci bane shi sai yau".
Mamah taja tsaki tace,"kidena tina min Zainabu da wannan tsinan nan mijin naki mara mutunci".
Zainab taja ƙwafa tace," Mamah bakisan iskancin da yazo min dashi ba ɗazun,ace kamar ni a wannan babban gida da babban motor ga babban falo amma ya ɗauko dankali ya kawo min da su masara,take yanke na gurza masa rashin mutun ci nace ya kai ma dabbobi donni ba akuya bace,tun ɗazun ya fita dasu har yanzun bai dawo ba,nasan babu inda zaije ya kaisu sai gidan muna fukar uwar nan tasa,mai murya sumimi-sumimi".
Mama tawani katse ta cikin tsawan da bata taɓa mata ba tace,"dan ubanki ainice babbar dabban akuyan da ya kawo mawa".
Waro manyan idanuwan ta Zainab tayi tare da lailayo ƙaton ashar ta watsa tace,"wallahi Ahmad ka ɗebo ruwan dafa kanka nizaka raina ma uwa itace akuya kenan?,Mama ta katseta da faɗin," wallahi Zainab inke ƴar halak ce ni Jummai na haife ki ki tabbatar a wannan daran kin karta ma Ahmad rashin mutunci inyaso ya sakoki,ni kasuwa tane zata ƙara buɗewa duk cikin ƴaƴana kinfi su ƙashin arziki".
Zainab tace,saki ko ai ya zama dole Mama yau zan masa ruwan balain da ba..........!
Ahmad dake tsaye tun ɗazun akanta sabida zuciyar ta tana ci da ruwan fitina bata ko lura dashi ba ya katse ta cikin tsawa idanuwan shi har sun canja launi sunyi jaa yace,"Zainab inkin isa in sakeki Allah ya tsine min albarka,ki duk abinda zaki,kuma ɓacin mahaifiyata da kikai akwai lokacin maida martani.
"Mtsuuuh aikin banza aikin wofi,tsoran ka nikeji akace ma mu zuba shege ka fasa",yana jiyo ta baice uffan ba ya shige ɗakin sa yasa key gado ya faɗa zuciyar sa na masa ƙuna ya akai Zainab ta raina sa haka bai gaza a komi ba dole ya nemo mafita,ahaka ba tare da yayi wanka ba balle cire kaya bacci ya kwashe shi.
****
"Ummah ni wallahi na gaji da zuwa makaranta nan ba na gaji da zuwa ace kullum boko da sassafe kin tashe ni wallahi Ummah banson boko sam aje tun safe sai two zaa dawo,uhm,da kadawo sai kuma wannan islamiyan shima kullum",wata yarinya ƴar kimanin shekara sha takwas ke maganan wankan tarwaɗa ce mai matsaikai cin tsayi bata da ƙiba amma tana da shape mai kyau dai dai jikin ta kanta tana da yalwan gashi inda akai mata kitson kalaba ƙanana sai turo baki take,wanta ƴar dattijuwa da bazata wuce shekara arba'in ba ta wani galla mata harara tace,"tou Nanah in bazaki bokon ba mi kikeso kiyi waike kullum akan zuwa boko sai kin rinƙa ɓata ranki ne Nanah toh in bakison boko in miki aure kenan toh wazai temaka mana wajen aurar dake dangin ubanki duk sun guje mu sabida talakawa ne mu bamu da komi sai gidan nan ko shi zamu sayar in miki aure?,ƙara turo baki tayi tace,"Ummah sam ba haka nake nufi ba aure ni ko auran ban isa ba wallahi ƙarama dani ko shatakwas yaushe na cika nide banson makaranta sabida farin cikin ki kawai Ummah nake zuwa", murmushi matan tayi tace,"tou Nanah ta inkina son farin cikina ki dena ɓata rai akan karatu,yanzun a zamanin nan da masu ilimi ake damawa gaba gaba ƙilan ko wanke wanke da shara zaa ɗauke ka sai kana da ilimi kuma kisani ilimi yafi mahimmanci acikin alumma ba kuɗi ba,mussaman ilimin ƴaƴa mata ,kinganni nan Nanah da nayi karatun boko da bakiganni haka ba muna cikin ƙuncin rayuwa da bazamu ƙulla daddawa da barkono da kuka ba muna saidawa",murmushi budurwan yarinyar tayi tace,tou Ummah bari in tashi inyi wanka in shirya,bata jira mai mahaifiyar ta zata ƙara faɗi ba ta dira akan gadon nasu mai rumfa ta ɗau hijjab ta saka ta tafice da gudu kafin ta shiga bayin nasu saida tayi addu'a ta faɗa da ido Ummah ta tabita tana murmushi,bata jima ba tafito ta tarar Ummu harta zuba mata koko a kofi da ƙosai zama tayi ta fara sha tace,"Ummuh" cike da shagwaɓa,Ummuh tace,"lafiya kuma?,tai murmushi tace,"Ummu gobe ki mana shayi kinji please na gaji da koko nan fitsari yake sani sosai inna sha na tafi school harda wani bacci-bacci Ummuh gaskiya inkinaso in rinƙa fahimta Ummu daga monday zuwa friday shayi da ƙwai basai kin sa madaraba banson bread shi zaki rinƙa min sai saturday sunday kirinƙa koko kinsan ranakun ba inda zani sai islamiya da yamma",murmushi Ummu tayi tace,"kide ce Nanah jarin daddawa zan kwashe incinye miki a cikin ki",tace,"a'afa Ummu ba haka nake nufi ba so uku tou asati Ummu"," Uhmmm kide yi kici kishirya bari inje insa ɗumammen tuwo",tace,"tou Ummuh na",.
Agurgujr tagama ci tafito sanye da uniform ɗinta farar riga tass da wandon green sai ɗan ƙaramin hijjab ɗin ta goye take da jakarta ta baya,ƙafanta sanye da takalmi sawunciki ta dubi Ummu dake bakin murhu tace ,Ummuh zan wuce na ɗauka hamsin yau bazan hau abin hawa ba naga bami ciniki sosai ba,hamsin ɗinma na ɗauka ne don in kashe inna gadama,Ummu tai murmushi tace," tou baki abin magana,ya zaai kije makarantan ku a ƙafa dakwai tafiya fa kuma naga bakwai da rabi",turo baki tayi tace Ummu ki banni zanje haka kafin takwas da rabi na isa makaranta,nama je da wuri wasu har tara suke zuwa",murmushi Ummuh ta kuma akaro ba adadi tace toh adawo lafiya Allah ya tsare Allah ya miki albarka",tace ameen Ummuh na kafin tafice a gidan da gudu ,Ummu murmushi tayi da girgiza kai,tace,Nanah an girma ba wayo",taci gaba da fiffita wutan da take ɗumame.
Nanah ko saida tayi tafiya sosai kusan tara saura ta isa get ɗin makaran tan su adaidai get ta iske ana taran latti tawani waro ido,tana haɗa da malamin ta wani galla masa hara tai kaman zata juya sai ta dawo tace,"malan kabarni in wuce in an duke ni mutuwa nike".
Gwalo ido yayi yace,"mutuwa kuma?
tace ,"ƙwarai kuwa ".
yace," aiko yau saide ki mutu amma sai na duke ki".
murguɗa baki tayi tace,"malan niko zanga yanda zaayi ka dukeni,kuma ina gadama sai nashiga,amma yau ban gadama ba doja zan gwada inji da daɗi",tana hama faɗa bata jira jin ta bakin shiba ta juya tashiga GRA ta zauna nan ta tashi can ta tsinka mangwaro ta tsinka fruit duk wanda zai wuce saiya kalle ta har lokacin tashi yayi kafin ta ɗau jakan ta ta goya ta nufo hanyar gida a hanya taji ta gaji ga rana tayi yawa bacci takeji wata motor ta gani anyi parking ba kowa a layin kuma wajen inuwa yazo kawai ta cire jakan ta ta jefa saman motor ta hau bayan motor ta zauna tana sauke ajiyan zuciya tayi ciye-ciye amma ƙishi takeji sabida bata sha ruwa ba kallo ɗaya zaai mata agane tayi laushi da yawa.
Get ɗin wani gida aka buɗe aka fito wasu maza suna tafiya suna magana har suka iso gaban motor basu kula da itaba,saɓanin itako tunda suka fito take kallon su ganin sun doso motor yasa ta ƙara ware ido tana kallon su kartaji saukan mari,tarin da ya sarƙeta tafarayi yasa suka kula da ita duk suka zuba mata ido tsawan minti biyu tarin ya lafa,ɗayan farin mutumin yace,"ke mai kike akan motor nan?, harara tayi masa tare da muguɗa baki sannan tace,"hutawa ko taka ce in ma takace bani sauka sai na gama hutawa ni kaje gidan da kake gadi ka roƙo min ruwa"..................!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
SHARED PLS
typing🖌️
*🟣SURUKAR ZAMANI🟣*
*NA MARUBUCIYAR*
*SAMHA*
*KISHIYACE*
*ƳARMACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND NOW*
*SURUKAR ZAMANI*
WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD MRS BASAKKWACE*
FACEBOOK
MAMY BASAKKWACE
GMAIL'S
KHADEE241@GMAIL.COM
OR
MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
GAJERAN LABARI👌
*SHAFI NA 7&8*
Harara ta galla masa tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tace,"hutawa,kafin taci gaba da faɗin ko taka ce?,in ma takacr bani sauka sai na gama hutawa ni kaje gidan da kake gadi ka roƙon min ruwa wallahi nai tafiya na gaji hamsin ɗin da na ansa gun Ummuh na ban kashe ba ni ban ma iya kashe kuɗi ba rasa mai zansiya nake".
Mamaki fallllll ya cika cikinsu ga rashin kunya ga surutun tsiya kamar taci aku duk cikin su ba wanda bai kafeta da kyawawan idanuwan shiba.
Lura da tayi sun kafe ta da ido yasa tai shiru tana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya,ɗayan dogone baƙi yana da ɗan ƙiba kuma baza'a kirashi ramamme ba yanada da ƴar doguwan fuska da ƴar ƙaramin baki daidai fuskan yana da hanci da baza'a kirashi dogo ba sannan bazaa sashi jerin gajeru ba,saɓanin ɗayan da farine dogo shima kakkaura yana da tarin suma bisa kanshi yana da kyawawan idanuwa masu matuƙar rikita mace in tai tozali dashi yana da dogon hanci da gashin gira masu matuƙar yawa,gashin idon shi masu sheƙi da tsayi kamar an masa ƙari.
acikin mintinan da basufi biyu ba taga ma ƙare musu kallo tare da taɓa baki tace,"ashe ma duk munana ne na tsaya ina ta zuba uhm bari inkama hanya in wuce gida kar Ummuna hankalinta ya tashi na tsaya biye yaran nan", dira tayi daga inda take zaune ta ɗau jakan ta zata goya taji an finciko ta wani tsoro taji yashigeta da gigita tunda tagama rashin kunya batai tunanin zasu iya mata komi ba tunda taga sunyi shiru sun zuba mata ido.
Runtsa ido tayi tare da marai-raice fuska tana faɗin,dan Allah kuyi haƙuri ka sake ni Ummu tace,"innamiji ya taɓa mace ciki takeyi wayyooo nashiga ukuna Ummu zata yankani ta koreni gashi bani da kowa sai ita".
Ɗayan baƙin mizaiyi inba dariya ba duk ƙoƙarin sa da ya danne dariyan amma ina saida ya suɓuce masa,farinko shan toka yayi cikin tsawa yace,"keeeeeee buɗe idanuwanki ki ganni nine mummunan ko kuma nine yaro,abinda yasa nai miki cikin sabida kince min yaro ki tabbatar ni ba yaro bane na isa taɓa mace tai ciki don haka ke kika sani kije can ta kashe ki kuma aka zubar min da ciki nida kune saina kulle Ummun taki kizama almajira ƴar aikin gidana da kin haihu in ɗauke ƴata ko ɗana inaba sabibata wato matata".
buɗe idanuwan ta tayi a tsorace ta sauke kanshi tawani fashe da kuka cikin kuka tace,"wallahi sai na zubar saide ka kashe mu daɗin ma bakasan gidan muba mugu kawai ɗan isk..........!
Da sauri ya kai hannun shi kan bakinta ya buge dole ta haɗiye maganan tata taci gaba da kuka mai kama dana shagwaɓa.
Ɗayan ya haɗiye darinyan shi yace,"Ahmad kar mu bari ta wuce muje muga gidan su don karta zubar ma da ciki tunda kaga Zainab har yanzun batai cikin ba",Ahmad ya kashe mai ido ɗaya yace,"tou kakawo shawara mai kyau Ridwaan".
Ƙara fashewa tayi da kuka tana bubbuga ƙafa a ƙasa tana haɗa hannu alaman ban haƙuri gashi tana so ta gudu ya riƙe mata haɓa gam ko motsin kirki batayi dabadin haka ba da ta kwasa da gudu.
Ahmad cikin tsawa yace,mutafi kishiga motor,ƙin motsawa tayi kamar da dutse ye ma tsawan.
RIDWAN buɗe gidan baya yayi yace,"ɗauke kasata ƙila inka ɗauketa ta haifo ƴan uku ko ƴan huɗu kasan Mom tace riƙe hannun mace ƴan ɗaya ake samu".
AHMAD ya amsa da tou abokina haka zaai don in buƙatan ƴaƴa".
Hankalinta ƙara tashi yayi tana ƴar ƙarama da haihuwar ƴaƴa uku sannan ma bada aure ba da cikin shege,bata ankara ba taji an wani sungume ta ana ƙoƙarin sata a motor ta rasa yanda zatayi ga layin shiru bako tsuntsun dake gittawa intayi ihu ihunta banza tun da yariga ya cuceta ya mata ciki,turata ye a motor ya kulle yanda baza ta buɗe ba ya juyo ya kalle RINDWAAN sukai murmushi yace,"muje ka rakani don kar in manta gidan su".
RIDWAAN yace,"ai dole muje gidan uwar ƴaƴan mu",sheƙewa sukai da dariya tare da tafa hannu kafin suka shiga motor RIDWAAN a mazaunin driver yayi da AHMAD ke gefe ya saita mirrow yana hango NANAH da ba'abin dake fita a idon ta sai hawayen baƙin ciki ita saida tace ma UMMUH batasan boko gashi sanadin boko ta haɗu da wa ƴanda zasuyi mata ciki a hanya.
AHMAD sa hannu yayi ya jawo hannun ta ya haɗe tai yace,"mai ciki ina mukai?
Ƙara ta ƙara ƙwallawa tace,"YAYA dan Allah ku rifa min asiri muje a cire,UMMUNA zata yankani banso in mutu sainayi aure nahaifa ɗan insa masa sunan mahaifina".
Duk ƙoƙarin RIDWAAN ya gintse dariyar ya kasa saida tafito.
AHMAD ya gwalalo ido yace,"cikin wa zaa zubar Allah sai kin haife shi,muje gidan UMMUN taki kuma kina min ƙaryan gida dana kalla idonki zan gane kuma kina ƙara magana sai na ƙara miki ciki donki haifar ƴan goma,kuma kidena min kuka karki kashemin dodon kunni inko kin ƙi kiss zan miki kuma in tattaɓa min breast".
Shiru tayi ta haɗiye kukan,da hannu take gwada masu hanya harsukazo ƙoafar gidan su yace,"fita kikira min UMMUH taki in kafa mata sharɗa,ta haka zan gane gidanku ne koh".
Dagu ta fice a motor ko ta jakan ta batayi ba ta faɗa ɗan ƙaramin gidan su.
REEDWAAN ya dubi AHMAD ya sheƙe da dariya yace,"mai gadi je gidan da kake gadi ka kawo min ruwa",ƙara kwashewa da dariya yayi.
AHMAD murmushi yayi da ya ƙara bayyana tsantsar kyawun sa.
REEDWAAN ya ƙarace wa," ka ɗurar musu da cikin ƴa gaskiya AHMAD baka da kirki duk taban tausayi wallahi,mu gudu kar mamanta tafito da taɓarya".
AHMAD yace,aiko ta daka mu
NANAH ,koh da ihu tashiga gida tana faɗin UMMUH na bani ya min...............!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
typing🖌️
*🟣SURUKAR ZAMANI🟣*
*NA MARUBUCIYAR*
*SAMHA*
*KISHIYACE*
*ƳARMACE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND NOW*
*SURUKAR ZAMANI*
WRITTEN BY *KHADEEJATOU MUHAMMAD MRS BASAKKWACE*
FACEBOOK
MAMY BASAKWACE
GMAIL'S
KHADEE241@GMAIL.COM
OR
MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM
GAJERAN LABARI👌
*SHAFI NA 9&10*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI*
NANA,koh da ihu ta shiga gida tana faɗin," UMMUH na yamin ciki na shiga ukuna,kuma na ƴan goma yace yamin dan Allah kije waje ki roƙe shi a zubar yace in aka zubar ɗaure mu zaiyi".
UMMUH dake zaune tanacin abinci batasan sanda ta tashiba ta jawo ta ta kulle mata baki da hannu tana ƙasa da murya tana faɗin," NANAH maƙwafta mun shiga uku maza kika kai ma kanki?,tarbiyan da na miki kenan NANAH? duk waazin da nake miki da nasiha akan maza bakiji ba NANAH",ta ƙarashe maganan da fashewa da kuka.
Hankalin NANAH ƙara tashi yayi ta ƙara fashewa da kuka tace,"UMMUH na ban kai kaina wajen su ba su suka taɓa min hannu,kuma in ƙarya nayi suna waje kije ki tambaye su".
UMMU saɓan hijjabin ta tayi da yake kan igiya ta zura ta fice koh takalmi bata tsaya sawa ba ,NANAH bin bayanta tayi tana kuka UMMU ta dubeta tace,"toh ina suke?,nuna mata motor su tai da hannu tana sharan hawayen da yaƙi tsayawa.
Tun fitowan su AHMAD ya hango su don hankalinshi na kan ƙofar gidan dama buɗe murfin motor yayi ya fito shima haka REEDWAAN rissinawa sukai gaban UMMU suna gaidata,ko ansawa batayi ba tace,waya ma NANAH ta ciki acik.....,maganan ta maƙalewa yayi sanadiyan haɗa ido da tayi da REEDWAAN.
REEDWAAN ma ita yake kallo tsawan da ƙiƙa kafi tace,"REEDWAAN",kaine yau a ƙofar gidan mu?,ashe rai kan ga rai nasha zuwa wajen da muka haɗu ko zan kuma ganin ka ban ƙara ganin ka ba,Allah sarki na cire tsammani da ƙara haɗa ido da mutumin arziki kamar ka".
AHMAD,sakan baki da ido da hanci yayi yana kallon su,itama NANAH da take kuka take kukan ya tsaya tana kallon REEDWAAN ta kalle mahaifiyar ta.
UMMUH ta dubi NANAH tace,maza jeki shimfiɗa min tabarma manyan baƙi ne nayi su shigo,juyawa tayi ta shiga gida don