Showing 6001 words to 9000 words out of 23384 words
Chapter 3 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt
bata wasa da umurnin mahaifiyar ta,kuma tanaso tasan waye wannan REEDWAAN ɗin a wajen mahaifiyar ta.
UMMUH tace,"ku mushiga kusha ruwa",bin bayanta sukai har ɗan tsukukun gidan nata lokacin NANAH har ta shimfiɗa tabarma ta ɗebo ruwa ta aje ta koma gefe ta raɓe kamar munafuka,waje Ummu ta gwada musu suka zauna,"tace,ga ruwa REEDWAANU duk da nasan ƙila bazaku iya shan kalan namu ba".
Murmushi REEDWAAN yayi yace,"haba dai mun isa ai daga ganin shi ruwan randa ne mai sanyi da daɗi".
NANAH turo baki tayi ta fara shashsheƙan kuka,gaba ɗayan su hankalin su yakoma gareta,UMMUH tace,"lafiyanki zaki tasa mu a gaba kina kuka shagwaɓan har a gaban baƙin ido sai kin nuna ".
Zumɓuro baki tayi tace,"UMMUH na ciki fa wancan yamin tare da gwada AHMAD da yatsa taci gaba da faɗin amma harda basu tabarma da ruwa kuna ta fira da wancan baƙin" ,ta ƙarashe maganan cikin muryan kuka.
UMMUH harara ta galla mata tare dacewa kimin shiru anan,kallon ta ta maida ga REEDWAAN don ita har ga Allah ta manta da batun NANAH anmata ciki tunda tai ido biyu da REEDWAAN da ya temaketa tafita daga ƙuncin rayuwa,cikin sanyi murya tace,"REEDWAAN ya akai haka ta faru?,kallon kallo suka fara shida AHMAD yana gimtse dariyan shi da ido yai ma AHMAD alama ya faɗa mata don shi yasa in zai faɗa mata dariya ce rabin maganan.
AHMAD ranƙwafar da kai yayi yace,"ina wuni aunty",cikin daddaɗan muryan shi yake magana.
Ansawa tayi ba fuska ba yabo ba fallasa yayida ƙirjinta ke tsanan ta bugun akan mummunan alamarin da zataji.
AHMAD,ye gyaran murya tare da cewa ,Aunty ita taja ita ta toneni shiyasa,nan ya kwashe miya faru daga farko har ƙarshe ya faɗa mata UMMUH ,UMMUH sauke ajiyan zuciya tayi ,yayinda NANAH sai galla masa harara take in ya ɗago sun haɗa ido,shiko murmushi yake ƙasa-ƙasa,acikin ransa ko yana faɗin mara kunyar ƙarya kawai magana ɗaya ta rikitata.
UMMUH ajiyan zuciya ta sauke tace,"alhamdulillah Allah ya ƙara tsare gaba".
"Ameen" suka amsa dashi.
REEDWAAN har ya buɗe baki zaiyi magana ƙaran wayar sa ta katse shi da sauri yasa hannu a aljihu ya fiddo wayan ganin mai kiran shi yasa shi saurin miƙewa yace,"AHMAD muje oga yayi kira,AUNTY zamu dawo wani lokacin musha hira".
Tace,"tou REEDWAAN Allag yasa da gaske kake ba ka ƙara guduwa bane sai taka ta kawo ka ",murmuahi yayi yace," AUNTY ai da zamu rinƙa zuwa muga mai ciki da yanda lafiyan ƴaƴan mu suke har ta haihu mu ƙwace abin mu".
Murmushi UMMUH tayi tace,"REEDWAAN kenan saina ganka kawai".
Sallama sukai mata suka fice a gidan.
Yayinda NANAH ta haɗa kai da guywa kuka kawai take wai itace yau da ciki cikin ma na shege har ƴan goma zata haifa kuka kawai take.
UMMUH fita batun ta tayi tai kamar batasan tanayi ba yau ta tabbatar NANAH yarinya ce har yau da sauranta,da UMMUH taga bazata bar kukan ba yasa ta zare mata idanuwa dole yasa tayi shiru taje ta cire uniform wanka kawai tayi ta hau gado ta kwanta sai ajiyan zuciya take,tare da tinanin UMMUH ashe ba son ta take ba tuda har zaai mata ciki bata ɗau ƙwaƙƙwaran mataki kan ƴan iskan sa suka lalatata ba harda sata ta shimfiɗa musu tabarma da kawo ruwa,tou wai mai miye tsakanin UMMUH da wannan ɗan baƙin ne? tambayan da ba wanda zai amsa mata shi sai UMMUH,gashi UMMUH duk ta tsane ta tunda taƙi ɗaukan mataki akan ƴan iskan can tsaki taja ƙasa-ƙasa don kar UMMUH taji ta bige mata baki don ta hanata yin tsaki.
*****
"NAFEESAH!NAFEESA!!MAFEESAH wai ke wata iriyan ƴar iskan yarinya ce kina kwance kina jina iye ina ƙwala miki kira".
NAFISA,uhm tace,"wai tou ke MAMA ina zaki tunda naga ki wanke ƙafa ki ɗau hijjab nasan ficewa gidan ƴaƴan naki ya tashi".
"Toh dun ubanki in banje ya zaai na samu na ɓatar wa iye kema ki samu nima na samu yanda nake bin gidan kowa haka kema zan zo gidan ki,ke nafi dogon buri akan ki ma".
Taɓa baki tayi tace,"kikazo ko wallahi MAMA zakiga mizan miki hakanan kawai ki hana ƴaƴan ki rawan gaban hantsi a gidajen auran su" .
Saƙeƙe MAMA tayi da baki tare dayin ƙwafa ta juya tace,"nide na tafi sai na dawo".
NAFISA tace,"gidan boka ko gidan ƴaƴanki?.
"Ko gidan ubanki ne ba ruwanki mara mutunci kawai",sakai tayi ta fice tana ta bam-bami.
Kai tsaye gidan MAMAN GAJE ta nufa bako sallama ta faɗa gidan tana faɗin," ƙawar arziki fito mu lula" .
MAMAN GAJE tace,"aa SARATU dama ke nake jira,ban wani abu inbar ma su HAFSATOU".
Juya ido MAMA tayi tace,"kefa MAMAN GAJE tsiyata dake mayyar roƙo ne wallahi,ke kullum abaki abaki kin yarda da bani bani,kuɗin motor zuwa kwanan fariƙwai ɗinan ni zan miki kuma inba ƴarki na kashewa".
MAMAN GAJE ta washe haƙora tace,"tou ƙawalliya ya zami dola ce tasa haka ƴata kuma ai ƴarki ce inda mutun ci".
Washe haƙora tayi tace,"hakane fa aminiya ciro ɗari biyar tayi ta miƙa mata ɗan HAFSATOU tace,miƙa ma uwarka mu muntafi"..............!
*TOH FA WAI MIYE NENE HAƊIN REEDWAAN DA MAHAIFIYAR NANAH WATOH UMMUH,*
*MAMA DA MAMAN GAJE SUN FITA INA SUKAYI NE HAKA*
*AMSOSHIN KU SUNA GABA*👉
_MORE COMMENTS_
_MORE TYPING_
_typing🖌️_
*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*
NOT EDITING❌
NA *khadeejatou muhammad(MRS BASAKKWACE)*
SADAUKARWA GAREKU *LEEMAH PINKY ND REAL AUNTY ZEE MAI HAƘURI*
*WANNAN SHAFIN NAKU NE ABEEDATOU,MY FATEEMA LADAN,MOM ABDULJALAL,HAFSAT UMMIE,SAKINA ƳAR MUTAN GUSAU,BASHEERU SARDAUNA(MAISUNAN UBANA) ,INAYINKU IRIN TOTTALY*
*JINJINA TA MUSSAMAN GAREKU,FATEEƊEEMATOU MUSƊAPHA(AUNTY BABYLO🤪),GWAGGO UMMIE HAIRAN😜FATEEMAH SUNUSI,ESHAT,USMAN ANGO ƊAN ANACIN MARUBUTA🤗*
*BAN MANSHEKI BA MASOYIYA ABIN ALFAHARI JINI ƊAYA JIKOKIN SHEHU USMAN ƊAN FODIO SAKKWATAWAN SHEHU MASU MAYAR DA BAƘO YA ZAMA ƊAN GARI YA MANTA GARINSU(KHADEEJATOU S DOGARAI MY LIPTON GIRL☕)*
_GAJEREN LABARI👌_
*SHAFI NA 11&12*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI*
________📖Su MAMA tunda aka fita aka rankaya kamar ƴan matan amarya aka nufi baki hanya suka ɗane machine 2in1sukai basu tsaya ko ina ba sai kawo pack pack,inda ake hawan motor kwanan fari ƙwai suka nufa ba kowa cikin motor haka suka shiga suka zauna,suna ta zuba hira a haka motor tacika kusan awa ɗaya suna zaune kafi suka kama hanyar kwanan fari ƙwai basukai good 30minutes ba suka isa da yake sun sami motor mai kyau kuma hanyar ba cinkoson ababen hawa,abaki hanya suka sauka suka ƙara taran mashin ɗaya zasu hau mai machine ɗin yace sai dubu biyu da ɗari biyar zuwa kawai banda dawo wa don dajin da nisa da kunyan shuka akebi don ba hanya kwata-kwata,dole yasa suka ɗau ɗaɗ-ɗaya a ɗari bakwai-bakwai da ƙyar suka yarda suka ɗauke su a haka.
_NIKO NACE WAI INA MAMAH DA MAMAN GAJE ZASUJE HAKA DA SUKA MATSA MA KANSU🤔BARI DE INCI GABA DA BIYAN SU INGA INA SUKA DOSA,TUNI NASAMA MACHINE NIMA NA ƊANE NABI BAYAN SU DUK DA MUNA TARE DA AUNTY BABY WAJEN ƊAU KAN RAHOTO AMMA TINI NA BARTA NAI GABA DON IDONA YUNWA YAKEJI YANA BUƘATAR ABINCI._
Tafiya mai matuƙar tsawo sukai ta kunyar shukar rake kafin suka kawo wajen wani bukka,sallaman masu machine ɗin MAMAH tayi duk da zasu jiresu don ko sun tafi bawanda zasu haɗu dashi su ɗauka,suma in sun tashi fitowa babu abin hawa.
_NIKO SAKAN BAKI NAYI GANIN NISAN TAFIYAR DA SUKAI KO TSORON HAƊUWA DA ƳAN KIDNAPPING BASUYI BA,KUMA GIDAN BOKA CI KAJI SUKA NUFA LALLAƁAWA NAYI NABI TA BAYA NA LAƁE A BAYAN BUKKAN DON JIN WATA MASAR ZAA TOYA TA BAUCHI KO TA SOKOTO._
Suna ƙarasawa suka fara masa kirari" gafara dai boka mai bamu atake babu wani jinkiri ba jeka kadawo sai boka ɗan duƙununu mai aiki kamar yankan wuƙa".
Tawani ɗan kafa na hango wani mummunan mutum ga baƙi ga muni ga wani ƙaton ciki da yake zaman kansa kamar maishan giya idanuwan nan jajaye wulik gasu ƴan fici-fici ga wani wargaje-jen baki,washe hauren sa shiyi jajayene futuk harda wani gansa kuka kamar tunda aka haife shi bai taɓa wanke su ba kannan cuku-cuku kamar rabon shi da aski tun na suna.
Yace,"barkan ku da isowa asararru haihuwan asara kunzo a banza zaku koma abanza SARAU mutuwanki sai an kulle ɗaki,kindawo a ƙara haɗo miki kan suranki sabida sun ɗan fara dawowa hayyacin su,gwamma da kikai sauri dabaki sauri ba ana gabda sako miki ƴaƴanki duka,kuma ba wacce zata ƙara auruwa mussamman ƙaraman".
Waro idanuwa MAMAH tayi tace,"boka dana shiga uku a cigaba da ɗaura aiki aci gaba da bab-baka min zuciyar su a'allon ƙarfe,musamman shegen yaron nan AHMADU,harda wani hanani shiga gidan sa".
Hahahahahaha,cewar boka ɗan duƙunana yaci gaba da faɗi,"ai wannan karan komi zami bazai kama yaron nan ba uwar shi tana masa addu'a fiye da yanda baki tsammani,kuma babu makawa a wannan karan kunkai shi bango sai ya ƙara aure".
Da sauri MAMAH ta dake ƙirjinta tana waro ido tace,"aure kuma boka,yanafa aure zai sakar min ƴa na tabbata,ayi duk yanda za'ayi a hana auran ni boka karaba shi da kowacce mace hatta uwar tasa inda take yadena bi,nasan itace munafukar da zata sa shi ya ƙara aure,ni tsofaitsofai dani har ubansu ya mutu baimin kishiya ba sai ƴata wallahi bazai yuwuba,ka haɗa harda kishiyar FATEEMAH ka aikata waje".
"Hahahahahah,SARATU imanin ki kaɗan ne",bubbuga ƙasa yayi da wasu zane-zane da surkulle,kafin ya ɗago yacigaba da faɗin,buƙatan ki zaibiya ne kawai akan mazajen ƴaƴanki shima bazai jima ba sabida suna alwala,alwala kuma na tasiri wajen karya mana aiki,ki aje kuɗi ninasan abin yi.
MAMAN GAJE koh tana gefe tayi tsumu-tsumu kamar wacce tai ƙarya ashe duk yanda take tunani SARATU tafi gaban haka,lallaikam SARATU mutuwanta sai ankulle ɗaki.
BOKA ƊAN DUƘUNUNU ya dubi MAMANGAJE yace,kekuma kije gida kafin ku isa zakiga aikinki ya ci,ku aje kuɗi na aika aljanu yanzun zasu fara aiki.
Baki MAMANGAJE ta buɗe jin abinda ya faɗa ,tunkafin tamai bayani.
"Hahahaha tunkafin kuzo ai aljani ɗan agadez yamin bayanin komi".
MAMAH ko irga kuɗi tai ta aje masa suka mai sallama da irin kirarin su na aheɗanu suka fice gun masu machine suka ƙarasa suka ɗane machine don fitowa bakin hanya.............!
_TOH FA BUƘATAN MAMAH DA MAMAN GAJE KO ZAI BIYA??????_
MORE COMMENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
*°•🔵•°SURUKAR ZAMANI🔵°•*
_NA MARUBUCIYAR._
*SAMHA*
*ƳARMACE*
*KISHIYA CE*
*JAHAN KHATOON*
*NOOR JAHAN*
*ND NOW*
*SURUKAR ZAMANI*
NOT EDITING❌
NA *KHADEEJATOU BASHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE).*
SADAUKARWA GAREKU *LEEMAH PINKY ND REAL AUNTY ZEE MAI HAƘURI.*
*WANNAN SHAFIN NAKU NE,WALEEDATION S MAPI,JEEDAH S MAPI,TEEMAH LUV (MOM FARHAN)AMMYN KHAIRAT,AUNTY LEEMAH,AUNTY HAUWA SALIS,PRINCESS AISHA,UMMU NASMAT,SUMY NAIGGE ƳATA DA DAI SAURANKU INNACE ZAN LISSAFO KU SAI IN CIKA SHAFI BIYU BAN ƘARE BA.*
_GAJERAN LABARI👌_
*SHAFI NA 13&14*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI.*
___________📖Suna fitowa hanya suka sami abin hawa sai kaduna,sunzo rigacikum suka iske ruwa ake sosai kamar da bakin ƙwarya,har sukazo kawo ruwan bai tsagaita ba haka suka sauka motor suka hau kekenapep suka masa kwatance inda zai kaisu duk sun jiƙe,ciki minti ƙalilan suka iso unguwan su MAMAH aka fara saukewa ta tatattara zani ta falfalada gudu ɗan lungunsu kafin aka sauke MAMAN GAJE.
_MASU IYA MAGANA SUKACE TSAFI GASKIYAN MAI SHI,AIKO HAKA TA FARU DA MAMAN GAJE._
Aiko mai napep na sauketa ya juyowan da zatayi tai katari da SANI mijin HAFSA tsaye cikin ruwa na dukan shi bai ko damu ba ya kafa ma ƙofar gidan ido,ba ƙaramin tsorata tayi ba,amma ta dake zuciyar ta tacika da farin ciki gaskiyan SARATU ne aikin malamin nan kamar yankan wuƙa yake tace,"a'a SANI lafiya kake tsaye cikin ruwa miyasa baka shiga ba sai ciwon sanyi ya kama ka?.
Ƙasa yayi da kansa yana mai matsan ƙwalla take ya zube a ƙasa ya haɗa hannayen sa biyu yace,"dan Allah MAMA kiyi haƙuri ki yafe min ki ba HAFSATOU haƙuri wallahi sharrin sheɗan ne,ina ga hannu aka samin bansan na koreta ba wallahi".
Daɗi ya mamaye zuciyar MAMAN GAJE don rabon SANI ya duƙa gabanta ya mata magana a ladafce tunkafin ya aure HAFSATOU,bayan aura shi da HAFSATOU ba irin rashin kunyar da bata gani ba gaskiya baabin da zata ce da SARATOU,sai fata alkhairi tagama biyanta.
Dafa kafaɗan shi tayi tare da miƙar dashi tace," SANI mushiga mi magana kaga ruwa na dukanmu ",haka suka rankaya har cikin gidan a ɗan rufar ƙofar ɗakin ya tsaya yayinda ita MAMANGAJE tashiga ɗaki tare da buga tsalle ta dubi HAFSA dake kwance ta wage baki tana bacci ta ɗaka mata duka a cinya,firgi-git ta miƙe tana soshe-soshe tare da hamma bako rufe baki.
MAMAN GAJE taja tsaki tace,"dalla kaima SANI tabarma yana faranda bari in sauya kaya,ki natsu karki nuna masa rawan kan ganin shi don kar ya raina ki ko nan gaba" .
Waro ido tayi da sakin baki jin SANI ya kawo kansa fara murza ido tayi taji da gaske ne ko mafarki ne,ƙara ɗaka mata bugu MAMANGAJE tayi tayi firgi-git tana sosai wajen tace,"dalla tashi kije kibashi ruwan ɗumi kuma sabida yasha dukan ruwan sama".
"Tou",ta amsa dashi tare da ɗaukan tabarma tana yin waje.
Zaune yake tsuru ya zuba ma ƙofar ɗakin su ido yaga ta inda zata ɓullo don zuciyar shi a zazzala take ji yake in baiga HAFSATOU ba ayau zai iya rasa ransa yana ganin ta fito ya miƙe jikin sa har rawa yake tare da cin tuntuɓe amma baiko damu ba burin shi ya jita a jikin shi.
HAFSATOU ko jada baya tayi cike da tsoro,lura dayayi ta tsorata yasa ya tsaya ya kafeta da idanuwan shi yana lashe laɓɓa.
Take taji gabanta ya faɗi da ta tina in ya riƙeta a gado bai mata da wasa,raɓawa tayi ta gefenshi ta shimfiɗa tabarma tace,bissimillah ga waje,nufan tabarman yayi ya zauna yana binta da ido kamar ya cinye ta,madafa ta nufa ta ɗibo masa ruwan tea mai citta a kofin silver ta dire a gabansa kafin ta koma gefe ta xuƙunna tace,"ina wuni"?,batare da ya amsa ba yace,"HAFSATOU nazo neman gafaran ki kiyi haƙuri kibini mu koma gida jinake in narasa ki kamar zan rasa raina,kuma inshaAllahu wani abu bazai ƙara faruwa ba da zai kawo rabuwan mu har abada".
Murmushi tayi tace,"tou shikenan SANI,Allah yayafe mana baki ɗaya".
_OHHHHHHHHH ALLAH SU HAFSATOU NO CLASS DAGA ZUWA BIKO HAR TA BADA KAI BORI YA HAU🤔._
MAMAN GAJE dake laɓe bayan labule dan taji mai zaa toya bata san sanda ta buga tsalle ba tana tiƙa rawa.
HAFSATOU ko da SANI tuni hira ya ɓalle tsakanin su har MAMAN GAJE tafice cike da farin ciki ta nufi gidan aminiyar ta SARATU dan tai mata albishi aiki yaci.
SANI koh da yaga MAMAN GAJE ta fice ya nemi ta bashi haɗin kai take taje ta kullo gida suka shige ɗaki suka kullo don itama buƙata take.
*******
Su NANAH wuni akai ana fushi da UMMUNTA,don ko islamiya taƙi zuwa,UMMUH tayi maganan harta gaji ta ƙyaleta,daƙyar taci abinci.
AHMAD koh tunda ya aje REEDWAAN ya nufi gida ,bakowa a falon gashi kaca-kaca ,girgiza kai kawai yayi ya nufi ɗakinsa rage kaya yayi ya faɗa toilet ya watso ruwa ya dawo yasa jallabiya ya hau gado ya ɗanyi bacci kafin la'asar bacci ya ɗebe shi acikin baccin harda mafarkin NANAH yayi gata tazo tana masa tsiwa shiko sai murmushi yake don ba ƙaramin burge shi tsiwan ta yake ba,bashi ya farka ba sai biyar saura miƙewa yayi a gaggauce yashiga bayan gida yayo wanka tare da ɗauro alwala yafito ya gabatar da sallah la'asar,abinda ke bashi mamaki ko wani bugun numfashin sa da zuciyar shi keyi da tunanin NANAH take yi.
_😲AHMADU BADAI SON NANA KAKE BA,DON BAMU SHIRYA AURAR DA NANA BA DON YARINYA CE IN HWAƊIMA,SANNAN BATA IYA KISHI DA ƳAƳAN MAMAH._
*******
"Waike FATEEMAH uwarki batajin kunyar zuwa gidan nan ne wai?,cewar AMEENAH yar mijinta.
FATEEMAH jitayi kamar ƙasa ta tsage tashige sabida kunya,ga kishiyar ta da ƴaƴan mijinta duk a zaune.
RUFAIDAH,babba ɗiyar mijin FATEEMAH,tace,aunty kenan ga wa ƴanda sukasan kunyar ba".
Wacce aka kira da aunty tace,"aiko wannan ɗabi'ar batayi ba nide adena kwashe min abincin ɗan uwa ana kaima tsofi marasa godiyan Allah"..................!
MORE COMMENTS MORE TYPING🖌️
_typing🖌️_
*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*
NOT EDITING❌
NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*
SADAUKARWA GAREKU *LEEMAH PINKY ND REAL AUNTY ZEE MAI HAƘURI*
_GAJERAN LABARI👌_
*SHAFI NA SHA BIYAR SHA SHIDDA15&16*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.*
_________📖Cikin tsawa Fateemah tace,"keeeee aunty MAMI dakata cin fuskar yayi yawa uwa-uwace,koda ɓarauniyar kaji ce,na gode Allah tawa uwa yawo gidan ƴaƴan ta kawai tasa gaba,wasu ko uwar tasu bin mazaje a waje ta......!
"Kutumar uba Fateemah rashin kunya zaki ma yayata wacce take a matsayin uwa gareni ta ɗauki gurbin uwata tou wallahi kinji kaɗan ba a gidan nan ba maza ki duƙa ki bata haƙuri",cewar USMAN mijin FATEEMA,da yanzun ya shigo ya tsinkaye hirar,AUNTY MAMI ko tana jin muryanshi ta fara matsan ƙwalla irin na munafinci,RUFAIDAH da duk yaran suka fara kukan munafinci kowa na matsan ƙwalla saɓanin mahaifiyar su RUFAIDA da ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta turo ɗankwali gaban kai ɗaurin ture kaga tsiya sai jij-jige-jij-jige take tana karkaɗa ƙafa tana danna wayarta kamar bata wajen,saɓanin su waleedah ƴaƴanta dasukai tsuru-tsuru sun rafka ta gumi.
"Haba Dadyn su WALEEDA,katsaya kaji farkon magana kafin kayanke hukunci daga shigowan ka,cewa fa tayi uwata na bin gidan ƴaƴanta tana roƙon abinci",cewar FATEEMA.
Ƙara haɗe rai yayi yace,"ke FATEEMAH banson jayayya bata haƙuri,ƙarya tayi,ai gaskiya ta faɗa duk surukan ƴaƴan ta sun gaji da ita aciki harda ni ,inko kina son cigaba zama dani ki zuƙunna kibata haƙuri sannan kiba duk yaron dake kuka a ɗakinan haƙuri,nabaki second biyar".
Batare da tayi wani dogon nazari da tinani ba ta duƙa ta fans hannayen ta tace,"AUNTY MAMI kiyi haƙuri dan Allah".
Saida ta muli ta mulmule ta gama hura hanci tsawan minti uku kafin tace,"shikenan a tare gaba,kuma adena kwashe mana abincin ɗan uwa,inda san samune ki hana uwarki zuwa gidan nan kwata-kwata ke kyaje".
FATEEMA,sunkuyar da kanta tayi zuciyar ta na mata wani zafi sabida baƙin cikin a dakeka a hanaka kuka dakewa tayi tace,"inshaAllah yanda kukace haka zaai".
Saida taƙara shan ƙamshin ta kafin tace,"tou bama yaran haƙuri,don suma kin so cin mutuncin kakan su ta hanyar yi mata ƙazafi".
Haƙuri taba yaran kafin ta miƙe ta kalla yaran ta da sukai tsuru-tsuru da ido tai musu alaman su tashi suma ɗakin ta ta nufa cike da takaicin halin mahaifiyar ta.
Shiko USMAN zama yayi yana ba Yayar sa haƙuri,nan fa suka fara karanta masa ƙarya da gaskiya.
*********
Tafe take da ƙatoton ciki da ƙyar dake iya ɗaga ƙafa,duk tawani kumbura tayi ƙatuwa sosai duk inda ta wuce mutane binta suke da ido suna nuna ta itace wacce tai cikin shege,tana biyo kwanan unguwan su yara na ganin ta suka fara mata