Showing 15001 words to 18000 words out of 23384 words
Chapter 6 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt
kai HABEEB da nake kallonka da daraja da kima ashe sumu-mu kasau ne kema WALEEDAH this is the last warning da zan ƙaraji kina neman ɗalibai da lalata ,kuma ga KHADIJA AHMAD MUSA wani abu ya sameta wallahi ko kallon banza kuyi mata ku gani,suna miki kallon banza ko wata baƙar magana ki........ƙaran wayarta ya katse mata maganan da takeyi ganin mai kira yasa ta ɗauka cewa kawai tayi Ina office shigo",ta katse wayar,taci gaba da faɗa kamar zata dake su UNCLE HABEEB suko sunyi tsuru lokacin da baƙon nata ya shigo tayi shiru da rufa musu asiri tace ta sallame su juyawan da NANAH zatai wa zata gani shima wa zai gani tsura ma juna ido sukai suna kallon-kallo tsawan daƙiƙa biyar yace," NANAH", cikin sanyin muryanshi mai daɗi da taushi.
Murguɗa masa baki tayi tare da galla masa hara-ra ta wuce,murmushi yayi .
PRINCIPAL dake kallon su tace," aa ɗana AHMAD kasan tane?,fuskanshi ɗauke da murmushi yace," eh NANAH ba ina sonta amma batasan inayi ba wallahi AUNTY da zaki temaka min wajan faɗa mata",buɗe baki PRINCIPAL tayi tana kallon shi kafinta galla masa harara tace ,"tou ina ruwana kaje YAYAH AMEENAH ta faɗa maka tunda nice marainiyan wayonka ko?
Dariya yayi yana zama yace,"AUNTYNA ta kaina inbaki nema min ba wazata nema min tou",harara ta ƙara galla masa tace," tou wancan sadakar yalla waya nemo ma da ka aura ka rufe idanuwanka bakaji baka gani akanta ka tasamu a gaba kana kuka saika aureta gashinan ai ka aura babu ribar haihuwa saidai suci su sata",dariya yake yi sosai yanda ta dage tana magana.
"Dariya ma na baka ko?, tashi kabar min office ɗina inci gaba da aiki ka ƙi zama naka sannan zaka zo ni kasani a gaba da surutu ka hanani aiki".
Tsagaita dariyan yayi yace,"aunty dama na kwana biyu ban ganki bane shine nazo dubaki,kinsan inaji dake kamar MAMY na","nidai ka rainani kamar abokiyar wasanka zakace".
Danne dariyar dake ƙoƙarin fito masa yayi don yanda take magana dole ya baka dariya yace,"AUNTY na wane ni in maidaki abokiyar wasa bari in gudu tunkafin ki ɗau bulala",ya faɗa yana mai miƙewa.
Murmushi tayi tace,"aiko da kaci gaba da zama hakan zanma tunda bakason zama office yawo yama yawa",AUNTY ni ban ma kai office ba yau ma tashi da ziyara naje gidan su NANAH in ɗaukota in kawota ban sameta ba,daga nan na zarce gidan MAMY na mu nacika ciki da abincinta mai daɗi shine na zarto nan nasan ba zanganki gidaba yanzun ma gidan su BAPPAH zani".
Gwalo ido tayi cike da mamakin halin AHMAD mai wasa da aikin sa tace,"tou duk naji ka tabbata ka wuce office Allah in baka wuce ba zan saɓa ma AHMAD duk laifin YAYAH ne ai da tasan dakwai aiki taganka da safenan bata koreka ba,"tou AUNTY kiyi haƙuri bazan ƙaraba","kama ƙara kasan sauran maza kawuce Allah yayi albarka,"ameen AUNTY na",ficewa yayi yana murmushi duk masifan AUNTU tana da sauƙi.
Ƙarfe biyu daidai tayi mai abakin get ɗin makarantan bai shigaba ya fito ya tsaya ya naɗe hannu a ƙirji ya ƙura ma ƙofar ido ɗalibai na fiffitowa suna kama hanyar gida ƴanmata nata wucewa ta gaban sa suna gyara tafiya da zaman hijjab amma ko kallon su baiyi ya zuba idanuwa yaga ta inda zata fito har ya fara cire rai da fitowar ta ƙilama ta fito ta wuce bai kulaba ya hangota tana tafe goye da jakanta duk tayi laushi kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar da yinwa ya jigatata jakan dake bayanta na rinjayarta da sauri ya kutsa ta cikin ɗalibai bata kula dashiba saiji tayi an riƙe mata jaka ta baya ga wani daddaɗan ƙamshin turare da ta manta a ina ta taɓa jin sa.
juyowa tayi azuciye zata fara masifa tana jujjuya ido sai caraf anasa turo baki tayi cikin tsawa tace,"kai driver miye haka",cakkkk ya tsaya yana kallonta ƴanmatan da suke ta kai mai hari buɗe baki sukai jin tace da wannan handsome guy ɗin driver.
Basar wa yayi tare dayin murmushi cikin kwantaccen murya alaman maganan ya ko ajikin sa yace,"yi haƙuri HAJIYA tuba nike naga jakan na rinjayar kine","yatsina face tayi tace," shine bazaka min magana ba da na juyo da marifa?,murmushi yayi da yake ƙarama fuskan shi kyau yace,"aiba komi tunda ni bawanki ne","tace,"tou sake min jakata",da sauri ya cire hannu,itako zame jakan tayi ta faɗi ƙasa ta yatsine fuska tace,"maza ɗauko ka buɗe min ƙofar motor",dariya taso bashi amma ya danne dariyan ya duƙa ya ɗau jakan yai gaba da ɗan sassarfa ya ƙarasa ya buɗe mata murfin motor ta ƙaraso ta shiga kafin ya kulle ya buɗe gidan baya ya aje jakan kafin ya zagaya yashiga mazaunin shi,ƴammatan wajan kowa baki buɗe ba ƙaramin burgesu AHMAD yayi ba,kowa na cewa azuciyarta dama itace NANAH.
Tafiya suke bawanda yace ma kowa uffan kowa da abinda yake saƙawa aransa har ƙofan gidansu hakimar na zaune har yaje ya buɗe mata ƙofar ta fita kafin ya ɗauko mata jakanta ya buɗe yasa wani abunda nima bansab minene ba ya kulle kafin ya miƙa mata yace,"NANAH dan Allah kimin alƙawarin wani abu ,jin yace,"dan Allah yasa bata tsaya dogon tunani ba tace,"na maka inhar bai saɓa ma addini ba",murmusawa yayi yace,"baima saɓa ba nide abi ɗaya nike roƙo kidena tafiya zanzo in kaiki in ringa ɗauko ki",jim ta ɗanyi kafin tace,"tou shikenan na gode kuɗin UMMU na ya huta ma ƙara jari tana gama faɗa ta faɗa gida da gudu don ta gaji yunwa take ji murmushi yayi ya kira wani yaro ya bashi jakanta ya shigar mata dashi,kafin yashige motor sa yayi gaba.
Tafaɗa gida kenan taci karo da UMMU zata fita,UMMU riƙe baku tayi tace,"keko NANAH na lura baki da ranan girma","murmushi tayi tace,"minayi UMMU,wai inazaki haka naganki da mayafi,"hararan wasa ta galla mata kafin tave,"aike da kika min zantafi","dariya tayi tace,"ai UMMUNA ban aiketa ba kikoma zanje miki innaci abinci","angama mamata" cikin gatse UMMU tai maganan","tou UMMU ta adawo lafiya yunwa nikeji wallahi na kasa sayan komi da kuɗin da naje dashi a break","ainasani shiyasa nace ki karya kin ƙi kifara cin abinci ki sallah kafin wanka bari inshiga gidan MAMAN ZAINAB","tou UMMUNA saikin dawo Allah ya tsare","ameen ƴar albarka zatafita kenan yaro nashigowa da jaka lokacin AHMAD motorshi ke barin ƙofar gidan sai yanzun tagane musabbabin gudun NANAH girgiza kai kawia tayi da taɓa baki tafice.
NANAH saida taci ɗumamen tuwonta da yajin daddawa kafin yamuƙe tai alwala tayi sallah tashi tayi ta jawo jakanta don cire kuɗi ta aje ma UMMU inda ta ɗauka farar................!
MORE COMMENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*
_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*
NOT EDITING❌
NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*
_GAJERAN LABARI👌_
_GAJERAN LABARI👌_
*PAGE 34&35*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*
Cire kuɗi ta aje ma UMMU inda ta ɗauka fafar paper da tagani ne ta zaro ido don asanin ta ba wanda ya taɓa mata jaka waya sa mata paper cirowa tayi ta buɗe taga rubutu kaman haka zaro ido tayi
_Love is like a beautiful garden. It brings zest and enthusiasm into our lives. It fills our lives with bliss. Life without love feels incomplete. I am so lucky to be in love. I love you my sweetheart. To me, you are no less than a dream come true. I love you so much._
Taɓa baki tayi du ƙun-ƙune paper ta wurga cikin jaka tana turo baki.
*****
"MAMAH har yau kwana uku shiru babu aikin boka ba labarinsa haryau AHMAD bai wai wayeni ba MAMAH",ZAINAB ne ke zaune ke zubo zance duk ya sukur kunce.
NAFEESAH taɓa baki tayi tace,"duk wanda baiyi shara masallaci ba zaiyi na kasuwa kasuwar ɓa kasuwar arna,wallahi nide aka kai sunana gidan boka banyafe ba".
"Dalla tafi can mara hankalin wofi,aike bakisan mai duniya yake ciki ba".
Turo baki tayi ta miƙe ta ja hijjab ɗinta tasaka ta fice.
Nan taci gaba da tausan ZAINAB,akan abi komi a hankali.
*******
"Kai banza ni fa na faɗa",AHMAD ke maganan nan,REEDWAAN dake gefe yace,"banson iskanci a rijiya ka faɗa ko ina?," "a'a teku na faɗa ɗan iska kawai","kan fanka neni ba ɗan iska ba".
Dariya suka sheƙe dashi tare da tafa hannu AHMAD yace,"abokina ina son wannan yarinyar NANAH ta wannan ƴar uwan naku".
Harara wasa REEDWAAN ya galla masa yace,"ƴar yarinyar nan mi zatama,baccin kana da taka matan".
"Kai kaga yarinya ni ban gani ba,ba ruwana da wata mata-ta,kuma ahankali zan ringa tura mata sona harta mutu akaina".
"Toh ɗan iska kafito muje musamu mahaifiyarta ai maganan komi bani so a soyi a ƙone ehe salan daga baya aja mata ciwon zuciya".
Taɓe baki yayi yace,"tou BABA REEDWAAN ai yanzun tambaya nizo yi".
Kaikaice kai yayi tare da kanne idanuwa yace," uban Baba ba BABA ba kaji,kamin biyayya ko inje in ɓata ka wallahi kasan halina zan iya".
Dariya suka sheƙe dashi tare da tafa hannu.
_WAI WAYE ADON TAFIYA TUNA BAYA SHINE ROƘO._
*****
Cikakke sunan mahaifin NANAH AHMAD,sunan mahaifin shi MUSA,sunan mahaifiyar shi SADIYA asalin su ƴan garin birnin gwari ne ƙaramar hukumar kaduna sana'an wanki da guga yakeyi a cikin garin kaduna shagari road dake badarawa anan ya haɗu da JIDDAH suka ƙulla soyayya JIDDAH tun tana ƙarama mahaifiyar ta da mahaifinta suka rasu ƙanwar mahaifiyarta dake aure a kaduna taci gaba da kula da ita har ta girma,soyayya mai tsafta sukeyi a tsakanin su har yakai ga aure a gidan shi da yake zaune wanda da kuɗin wanki da gugan ya saya ɗan ƙaramin gida mai ɗaki biyu da kitchen da bayi a nan badarawan shagari closed kusa da primary school na badarawa,alokacin da yana raye yana kyautata ma ƴan uwansa kullum gidan sa zarya ake watan shi bakwai da auran JIDDAH ta samu ciki lokacin cikinta na da wata takwas gabda zata shiga na tara yazo yace,"mata ƙirjin shi na ciwo amma yasai magani yasha tamai sannu ya kwanta.
Daga kwanciyar nan bai ƙara farkwa ba rai yayi halinsa rayuwa kenan shiru-shiru anyi laasar har magariba bai farka ba ta taɓa shi taga mutum jiki ya saki gabanta ya faɗi ta fara girgiza shi amma ina rai yayi halinsa ihu ta kurma kan kace mi makwafta sun shigo ɗaukan shi akai aka garzaya dashi asbiti aka dubashi aka tabbatar rai yayi halinshi faɗi JIDDAH ta rinƙa yi tana suma kiran ƴan uwanshi akai ala sanarda su a daran suka kamo hanya ko kafin suzo a riga an haɗa shi da safe aka kira ta da tamasa addua kasawa tayi illa kukan da take tayi haka aka ɗauke shi aka fita dashi gidan aka masa sallah aka kaishi gidan shi na gaskiya, GWAGGON ta sai tausan ta take da ban baki ahaka har akai kwana bakwai ƴan uwanshi duk suka watse ba tare da sun aje mata komi ba haka suka barta GWAGGONTA ke aiko mata da abinci safe rana dare kuma tana zuwa dubata satin sa huɗu da rasuwa ta taahi da naƙuda inda tasa waya ta kira wata maƙwafciyar ta MAMAN ABDUL ko kafintazo ƴarta tariga tafito tare da mahaifa tana ƙoƙarin yanke cibi MAMAN ABDUL ta shigo ta ansa ta yanke ma ƴar saida ta gyara ƴar kafin ta gyara JIDDAH ta gyara ɗakin gidanta taje ta ɗebo ice kasancewar tana saida ice tazo ta ɗaura ruwan zafi kafin ta tura ɗanta ya gayoma GWAGGO,GWAGGO naji tasaka mayafi tayo gidan cike da fatin ciki da murna,bayan sunyi wanka sun shirya sukaje asbiti aka duba komi lafiya kiran ƴan uwan AHMAD tayi ta sanar dasu sukai mata barka,basu tashi zuwa ba sai ana gobe suna shima ba da abin arziki ba dubu tara kawai suka kawo mata tare da cewa sunsa ma ƴa HALIMATU SAADIYA wato sunan mahaifiyar AHMAD kenan,JIDDA kallonsu tayi ta watsa musu kuɗi tace,"mizatayi dasu ko ɗan shege ta haifa sai haka yau kwana ahidda da haihuwa ba wanda ya waiwayenta sai yau,tinawa tayi sanda mijinta ke a raye da ance matan ɗan uwanshi ta haihu jiki na rawa yake sayan kayan haihuwa da ragonsa na suna ya aika musu amma shi ga yanda nashi iyalan suka wulaƙanta bayan ƙasa ta rufe mai ido share hawayen da ya sakko daga idanuwanta tayi tace,"HALIMA kukasa ma ƴa HALEEMAH ai ba uwata bace kuma bazan sa ba marasa mutunci kunji kunya ni HAUWA'U nasa ma ƴata suna NANAH KHADIJA wato SUNAN GWAGGOTA mariƙiyata nazama mutum har ɗanku ya aura, aini nahaifa ƴata ninai na ƙudanta ba uban wani ba",nan ta musu rashin mutunci suka tafi,tun daga nan basu ƙara wai wayanta ba itama bata ƙara wai wayar suba................!
MORE COMMNENTS
MORE TYPING
_typing🖌️_
_typing🖌️_
*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*
_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*
NOT EDITING❌
NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*
_GAJERAN LABARI👌_
_GAJERAN LABARI👌_
*PAGE 36&37*
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ita ke kula da ƴarta yayinda GWAGGO ke aiko mata da abinci safe rana dare,manema na ta fito mata amma taƙi basu fuska GWAGGO tayi-tayi da ita tai wani aure saide tayi murmushi,don ita ko tunanin aure batayi sabida ƴarta tilo kuma ɗiyar masoyinta AHMAD.
BAYAN SHEKARA GOMA shabiyu tashiga halin damuwa sanadiyar mutuwan da GWAGGO mai temakon ta tayi,ga itama yaran GWAGGON basu da wani ƙarfin da zasu iya temakon ta haka wata ƙawarta DALAH ta bata shawara da taje ta nemi wanke-wanke da shara tarinƙa yi ta samu jari,tunda de ba yanda zatayi,da taso ta koma asalin ƙauyen su ingade sai ta tina inta koma babu makarantu masu in ganci da ƴarta zataci gaba da karatu har itama ta girma ta samu aiki ta ringa tallafa ma alumma yasa taji duk bazata koma shiyasa take zaune a garin kaduna har yanzun.
Shiryawa tayi ta fita bayan NANAH ta wuce makaranta ta tafi GRA neman aiki ko wani gida ta shiga saide suce basu buƙatan mai aiki tayi yawo ta gaji hakan nan ta kamo hanya a ƙofar wani gida ta zauna tana hutawa tsawan lokacin wani motor yazo zai shiga gidan,kanta na duƙe tana hawayen da batasan sanda ya fara zubaba jin tsayuwan motor kusa da ita yasa ta ɗago tana bin motor da kallo bata damu da ta share hawayen dake sauka kan kumatun taba,matashin yaron da alokacin bai wuce shekara ashirin da bakwai da takwas ba ya zuge glass ɗin motor yana dubanta yana nazarinta kafin yace," lafiya kuwa aunty kika zauna anan kina kuka?.
Girgiza kai tayi ba tare da tayi magana ba tace,"ba komi hutawa nake yanzun zan ƙarasa gida".
Zuba mata ido yayi yana na zarinta da nazarin maganan da take ya tabbatar tana ɓoye wani abu akaro na biyu yace,"aunty ko temako kike nema ne?.
Ɗagowa tayi suka haɗa ido tai saurin janye idanuwant daga nashi ba tare da wani tinani ba tace,"eh in zan samu ko wanki da wankewanke in rinƙa ma matan ka koda sharane ma kuna da masu muku wa ƴancan zan ringa yi".
Dafe goshin sa yayi kamar mai nazarin wani abu,buɗe ƙofar yayi ya fito, ya tsaya jikin motor sa ya kalmashe hannu a ƙirjin sa ta zuba mata idanuwanshi yace,"miyasa kina da lafiyan ki da komi kike son cutar zuciya ta same ki,bakisan aikin wanke-wanke,mutuwar zuciya bace,kije kina aiki ƙasar ƴar cikin ki ta nema ta zage ki wata har zagin zatai miki wata har suka musamman ƴaƴan mu na talakawa da suka ga sun aure mai kuɗi burinsu su wulaƙanta talaka baccin suma ba rawa sukai Allah ya basu ɗaukaka ba ɗan kuɗin da zasu baki nawa ne amma akan ɗan kuɗin zakisha wulaƙanci na masifa wanda ko karan gidan su bazasu mai ba".
Jikinta duk yayi sanyi da mangan ganun shi tabbas hakan zai faru,cikin sanyi murya tace," tou bawan Allah dama na wata biyu ko ukku zanyi kuɗin da na ɗan tara sai inje in haɗa jari in fara sana'a in ringa kula da marainiyar ƴata".
Waro ido yayi cike da mamakinta wai wata biyu zuwa uku tou nawa zaa bata da zai isheta sana'an murmushi yayi yace,"tou nawa za'a baki dubu uku ko dubu biyu ashine zaki aje ki sana'a,kinfa ce kina da marainiyar ƴa cinta shanta wankinta tufafinta kuɗin makarantanta inbata da lafiya duk fa acikin kuɗin nan zaki cire ki laru-ro-ri da yawa,tou ina kuɗin sanaan zai rage saide kita tarewa a ƙarƙashin masu kuɗi kina muau bauta mai kuɗi na jin haushin ya temaki talaka,talaka najin haushin mai kuɗi sabida Allah ya ɗaukaka shi fiye dashi".
Sauke ajiyan zuciya tayi tace,"tabbas hakane na gode da tunatar wa bari in lallaɓa gida kar ta dawo makaranta bata iskeni ba".
Yace,"tsaya ki ansa abu buɗe motor shi yayi ya shiga tsawan lokaci sai gashi ya fito da bandir ɗin kuɗi ƴan dubu ɗaya yace,"gashi kije kija jari ki kula da ƴarki sunana REEDWAAN ABUBAKAR nan ne gidan mu inde zakizo nan zaki ganni saide in bana ƙasan".
Girgiza kai tayi tana ɓoye hannunta a baya tana faɗin sunyi yawa tinda nike duniya ban taɓa ganin kuɗi masu yawan wa ƴannan ba balle na riƙesu ace malakina nane".
Dariya taso bashi amma sai ya waske yace,"ai wannan ba komi bane ki ansan ni na mallaka mikisu in kina son ƙari zan ƙara miki,duk sanda kike da wata buƙata kizo nan zaki ganni nayi alƙawarin temakon ki kai da fata".
Shiru tayi tana jinjina karamci da tausasawa irin na wannan bawan ya bata shawara kuma ya temaka mata bata san sanda hawaye ya fara zuba a idanuwanta.
REEDWAAN da aduniya ba abinda ya tsana kamar kukan mace yasa shi jin wani kala duƙawa yayi ya aje kuɗin a gefenta ba tare da yace komi ba ya juya ya shiga motorshi hone yayi mai gadi da kaman jira yake ya wangale get ɗin ya shige ya rufe.
Kasa kukan tai illa mamakin sa da ta koma tanayi,tajima zaune wajen daga nan ta miƙe ta tara abin hawa yakaita gida tana ta tunanin wani sana'a zatayi tunawa tai duk a unguwan ba a saida kayan gwari aiko su ta saro washagari bayan