Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 23384 words

Chapter 5 - Sirikar Zamani By khadeeja mrs.Bassakwaceya.txt

Ads the beginning of article before Image

04 Jun 2024

315

Ads at the middle of Article

da mutunci tunda satanta haryakai tayi a gidan surukan ta ta zubar mata da mutunci buɗan bakin MAMAH tace,ai bakan ta farau ba,nan ta rinƙa zagin MARYAM tace ta cireta a ƴaƴanta bata-bata harduniya ta naɗe tunda taci mutuncinta dan ta ɗauko bargo haka ko ta ɗau bargon taba MARYAM ta mayar da sharaɗin karta ƙara zuwa inda take daga lokacin ko MARYAM bata ƙara waiwayan MAMAH ba,ta kuma hana ƙannan ta zuwa inda take da yayarta FATEEMAH bayan auran MARYAM sai yayarta FATEEMAH tai aure ta aura wani babban ɗan kasuwa hatsi yake saidawa,sai UMAIMAIH,ita mai aikin banki,sai ZAINAB engineering ne shi ahalin yanzun NAFEESA ce kaɗai bata aure ba,MALAN GARBA DA MALAN HALLIRU sun rasu ne ta hanyar hatsarin motor ahanyar su ta zuwa ɗaura auran ɗan maƙwaftan su suka gamu da ajalinsu hankalin MAMAH da MAMAN GAJE ba ƙaramin tashi yayiba sanda labarin mutwar mazajen su yazo musu,MAMAH ta tsine ma auran nan yafi millions inta tina,gwamma maman gaje tayi ta kaba da idda saɓanin mamah da daƙyar tai idda ta fara biyan bokayenta.








*WANNAN KENAN CIGABAN LBR*






MORE COMMENTS
MORE TTPING🖌️




_typing🖌️_






*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*








NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*








SADAUKARWA GAREKU *LEEMAH PINKY ND REAL AUNTY ZEE MAI HAƘURI*






DEDICATED BY *AUNTY BABYLO,UMMIE HAIRA FATEEMAH SUNUSI,EASHAT,USMAN ANGO*






_GAJERAN LABARI👌_






*PAGE 26&27*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*






___________📖AHMAD bashi yakai NANAH gida ba sai kusan uku,ɗan tsaban mugunta baisaya mata ko ruwa ba haka ya maidata ya aje ya tafi sai lokacin ya kunna waya aiko yana kunnanwa saƙunan nashigowa sai kuma kira na REEDWAAN ɗauka yayi yai shiru yana gimtse dariya don yasan yau tabbas ya taɓo REEDWAAN sai ya zazzage masa buhun masifa da bala'i,aiko REEDWAAN ta inda yake shiga batanan yake fita ba,saida yaji yayi shiru dan kansa yace,"yi haƙuri YAYAH REEDWAAN",yayan ubanwa ƙato dakai wazai iya zama da matanka amatsayin kishiya Allah ya kiyaye in baka RAHMA",murmushi AHMAD yayi yace,"mace mana", dariya REEDWAAN ya kwashe dashi yace,"wai kai gidan ubanwa kake ne ka kashe waya?,saida AHMAD ya sosa lallausan gashin kansa yace,nakai amaryata makaranta najira aka tashi don karta wahala ko rana ban bari tashiga ba tana cikin AC",kai banso maganan banza maganan ƴan shayi","murmushi AHMAD yayi yace,"bari inje gida inyi wanka inzo ko awa uku inɗanyi in duba wasu takkaddu","kam balai kana zuwa sai kayi tsallan kwaɗo",dariya duk suka sa tare da kashe wayan direct gida ya nufa ba kowa a falon bisa dukkan alamu kamar gidan ba kowa .










ɗakin shi yashiga da mamakin sa ya taɓa ƙofar yaji a buɗe dafe kai yayi gaban shi ya buga tabbas ZAINAB tamai ɓanna da sauri ya murɗa ƙofar ya shiga ƙare ma ɗakin kallo tabbas anshigo ɗaki don ba haka ya barshi ba zuwa yayi ya taɓa wardrobe ɗinshi yajita a buɗe kallo ɗaya yayima kayansa yasan an ɗeba duk yawan kayan sa amma saida ya gane a ɗeba gefen da yake aje huluna ya duba yaga an ɗeba gabanshi faɗi yayi da sauri ya nufa waje ɗakin ta yayi yana ƙwala mata kira amma shiru buɗe ƙofan yayi ya shiga bata ba alamanta buɗe bayi yayi ya ga wayam ma nan bata ba alamunta ƙwafa yayi dole ya ɗau mataki akan ZAINAB ya gaji da halinta na ɓeraye komawa ɗaki yayi yai wanka duk ransa a ɓace sababbain ɗinki da yayi aciki ta ɗeba da sababin hulunan shi dabai taɓa sawa ba ,shiryawa yayi ya fito ya shiga motor shi ya fice a gidan kai tsaye gidan su ZAINAB ya nufa abakin lungun gidan yai packing ya fito ya kutsa kai cikin lungun kai tsaye ya shiga gidan saida yazo tsakiyar gidan yayi sallama amma suna can suna shewa ko jiyo shi ba suyi ba sai labarin gidan boka da suke ciro wayar sa yayi a aljihu ya dubo number ta ya latsa kira ƙi ɗagawa tayi iyakan tsaki da tayi harta tsinke MAMAH tace,"waye ne?,"taki taja tace,"jarababben nan ne ƙila yaje gida bai ganni ba nagaji da kullen shiyasa na fito"," aikam ya zai kulleki Kamar daddawa gwamma da kika fito kisha iska abinki".










Duk yana ji abinda suke cewa takowa yayi har inda ƙofar yake yasa hannu ya yaye labulan,da sauri suka kalla ƙofar ZAINAB take cikinta ya bada ƙululu yayinda MAMA batasan sanda taji fitsari ya fara fito mata ba danma tana zaune kan kujera MAMAN GAJE ne ta washe jajayen haurunta tace,"a'a AHMADU ne bako sallama sannu da shigowa lale marhaban shigo mana",cikin kakkausar murya yace,"bazama nazo yi ba don banga wajen zama ba abani kaya na da aka sato ko in tsinke igiyoyin auran ƴarku haɗa zuri'a daku baida amfani na gode ma Allah da ban haihu da ZAINAB ba sannan duk naji magan ganun ku ku riƙe ƴarku tunda kunfi so kuganta a gaban ku sai sanda na nemeta",wani gigitacce kuka ZAINAB ta sake yayin da MAMAH DA MAMAN GAJE,ke jero salati MAMANGAJE tai ƙarfin hali tace,"kai ma Allah AHMADU kayi haƙuri karkace haka", yimin shiru tsofi banza kai kunsan Allah ne kuke shirka da zuwa gidan boka kunsan Allah ne kuke gantali zuwa gidan SURUKAN ku koko kunsan Allah ne baku gode masa ,kusan Allah ne kuke sa ƴaƴan ku sacesace iye?,shiru tayi ta rufe baki tai ɓam MAMA ko ƙarashe sakin fitsarin tayi.










Zainab kuka riris take ,AHMAD ko ajikinsa ya wuce cikin ɗakin ya ɗauko jakan kayan sabida yasan jakan shiya siyo ma ZAINAB ita a dubai taɓa baki yayi yace," SURUKAR ZAMANI kike koh?,tou nima da kike ganina ƙwallon shege ne nima cikakken ɗan iska kuma nima SURUKIN ZAMANINE mai tafiya dai-dai da halin SURUKAR ZAMANI,kuma kar in sake inga ƙafar ku gidana komai aini nasaya badaga gidan nan kukazo dashi ba",yana gama faɗa yasa kai ya fice cike da takaicin halin SURUKAN nasa dana matarshi,MAMA saida yafita tasamu bakin magana tace,"ohhh ni SARATU anyi la'anan nan yaro sam bai ganinada gashi MAMAN GAJE ko sati ba ayiba da naje na lale dubu hamsin don ariƙe min kansu amma kanshi yafi na sauran tauri",ZAINAB cikin kuka tace," MAMAH shikenan AHMAD ya sakeni ki wani abu bansan kwana a gidan nan gidan nan sauro ga kuɗin cizo ga ba wuta",hankalin MAMA ya ƙara ɗagawa tace,"ki kwantar da hankalin ki zaki koma muje na maidaki da kaina ina zan barki a gabana da babban bazawara ai gwara babban budurwa tashi muje kafin ya rigamu zuwa ɗaukan mayafi bata damu da ta sauya kaya ba sabida fitsarin da ta saki ba,ZAINAB tace," MAMAH bakisan halin AHMAD ba zai iya wulaƙanta mu a gaban kowa in muka kai kanmu kikira boka yasa sunan shi a allon ƙarfe dakan shi zaitaho murama duk rashin mutunci da yayi mana",ahhh haka kuma .








TOHHHHHHH FAAAAAAAAAA








MORE COMMENTS
MORE TYPING🖌️




_typing🖌️_






*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*








NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*








SADAUKARWA GAREKU *LEEMAH PINKY ND REAL AUNTY ZEE MAI HAƘURI*






_GAJERAN LABARI👌_






*PAGE 28&29*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*










___________📖ZAINAB tace,"MAMAH bakisan halin AHMAD ba, zai iya wulaƙanta mu a gaban kowa in muka kai kanmu kikira boka yasa sunan shi a allon ƙarfe dakanshi zai taho mu rama duk rashin mutuncin da yayi mana",ahhhh haka kuma",ciro wayarta tayi a lalita ta kwaɗa ma bokanta kira yana ɗauka ya zayyane mata komi akan abinda ya faru tsakanin ta da surukinta yace subashi kwana ɗaya AHMAD dai da wiya ya kamu amma zaiyi iyakan yinsa yanda zuciyar sa zatai sanyi,cike da farin ciki inde ƴarta zata koma ɗakin miji komi ma ayi.








*WAYE AHMAD?*


_NIMA BAN SANI BA🤷‍♀️_






AHMDA BASHEER MAI KAJI shine cikakken sunan AHMAD mahaifin sa asalin sa ɗan gari malumfashi ne ta jahar katsina mahaifiyar HAJIYA AMEENA ƴar ƙanin BABAN KAKAN AHMAD NE a taƙaice dai auran zumuta akai musu kunsan katsinawa da auran zumunci kamar sunfi kowa dangi shi ma haka iyaye da kankanin su sana'an kaji suke har zuwa kan ALHAJI BASHEER kasuwancin kajinsu ya bunƙasa gari-gari ake zuwa malumfashi saran kaji hakan yasa sukai gidan gona ana yankawa a gyara asa a firichi da mai saya yazo in har yanason gyararra gatanan inko wacce ba a yanka bane sum sunanan sun gina gidajen gono a gari daban-daban Allah ya albarkaci dukiyar su sosai AHMAD shine babba a gun mahaifin shi sai ƙanin sa ZAYYID da yake aiki a lokoja barrister ne shi sai NAJA'ATOU da AISHA auta ,NAJAATOU tayi aure a katsina inda take auran yaron matemakin gwamnan katsina AISHA kuma tana nan tana karatu bata gama ba inda take karanta mass com ,mahaifin su AHMAD ya rasu sakamakkon gajeran rashin lafiya na wuni ɗaya mutuwan da ya girgiza al'umma da dama aALHAJI BAAHEER mutumin arziki mai tausayin talakawa hannun shi a buɗe yake kuɗi ko ba nasa bane yaga mai buƙata sai ya ɗauka ya bada in yaso inkazo ya baka haƙuri ,ALHAJI BASHEER lokacin da baida ƴan kuɗi ko kuɗin cefanen gidan sa yana badawa su kwana da yunwa haka ɗan sa AHMAD yaro ne mai ladabi da biyayya ga tausayin na ƙasa dashi duk ranan week end yana kai ziyara gidan gona mahaifin sa yana dudduba abubuwan dake gudana.








Wata rana ranan sunday yakai ziyara ranan ne ZAINAB ta matsa ma saurayinta sai ya sai mata kaji da yake sunayin harda gasassu sunayi tou aranan taga AHMAD hankalinta ya tashi taga komi ya mata nashi number motor sa kaɗai ta ɗauka ta kawo ma MAMA aka kaishi gidan boka aka sa sunan shi a allon ƙarfe baisan ya akai ya aure ta ba aikin boka da ƴan tsubbu da MAMA tasa akai mata wayan gari kawai yayi yaganshi da auranta kullum tun safe mahaifiyarta ta na hanyar gidan ta su kwashe masa hatsi da abinci komi nashi asace yake da hatta kayan sawan shi,mahaifiyar shi itace mutum ta farko da yake gaya ma damuwan shi haka yajeya faɗamata ahibai masan yanda akai ya aure ZAINAB ba itama mahaifiyar shi da suke ce ma MAMY lokacin da yazo da maganan auran ZAINAB batai ammanna ba daga farko saida taga hankalin ɗanta yayi mugun tashi har kuka yake akan ta barshi ya aure ZAINAB yasa ta amince batare da tayi zargin komi ba duk atunanin ta tsananin so ne kawai lokacin da yazo mata s baƙon alamarin baisan ya aure ZAINAB buɗe ido kawai yayi ya gan sa da auranta yasa ta shirya taje wajen mahaifinta a malumfashi da yake malamin tsangaya ne tamai bayanin komi nan yabata addu'o'i da rubuta ta kawo mai a kullum in mahaifiyar shi tatashi sai ta masa addu'a sai ta sama albarka bai wasa da azkhar ɗin safe na rana dana dare hakan yasa ko MAMA taje ta bugo asirinta bai kama shi.


*(ADDUAN MAHAIFIYA YANA DA MATUƘAR TA SIRI GA ƳAƳANTA DON HAKA MU RAGE FUSHI AKAN ƳAƳAN MU BAWAI ƳAƳA DA SUN MANA LAIFI BA LAIFI BA RANMU YA ƁACI MUFARA MUSU MUMMUNAN KALMA,BAKUSAN KO YAYA MUKAI MA ƳAƳAN MU MUGGAN KALMA BA ZAI IYA HAWA KANSU KAMAR SU ƊAN BANZA WAWA ISKAN CIN BANZA DUK BASU DA KYAU IN DANKI YAZAMA ƊAN BANZA KECE DA HAUSHI IN YAZAMA WAWA KIN SHIGA UKU IN YA ZAMA ƊAN ISKA ZAA RINƘA NUNA KI GA UWAR ƊAN ISKA ALLAH YASA MUDACE)*


_WANNAN KENAN CIGABAN LABARI._








"UMMUNA zan wuce", cike da mamaki UMMU take kallon ta NANAH da ba'ason zuwa makaranta yau tun bakwai saura,UMMU shara fa zami ansa sunana a ƴan shara kuma banso inje in samu an gama bulala za'amin",NANAH kiji tsoran Allah ba kuna da NANY ba masu shara a makaranta?,turo baki tayi tace,"UMMU fa duk gwamnati ta kore su", badan UMMU ta yarda ba tai mata adduan a dawo lafiya,UMMU ki rage min tuwo tunda ban karya ba ƙosai da koko zan saya a get ɗin makaranta mu","tou kin maidani hambama kenan",dariya ta ƙyalƙyale dashi ta fita da gudu girgiza kai UMMU tayi tace," NANAH sarkin zolaya,Allah ya shirya min ke".










NANAH koh tafita da wuri don gujin haɗuwarta da AHMAD,shiko AHMAD.............!








MORE COMMENTS
MORE TYPING




_typing🖌️_






*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*




_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*










NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*








SADAUKARWA GA
*RAHMA SADAU,AISHA SADAU,FATEEMAH SADAU ND ABBA SADAU WANNAN SHAFIN NAKUNE ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA KU🥰*






_GAJERAN LABARI👌_














_GAJERAN LABARI👌_






*PAGE 30&31*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*








_________📖NANAH koh tafita da wuri don gudun haɗiwarta da AHMAD,shiko AHMAD lokacin ya tashi a tsanake ya shirya ya nufi kitchen ya dafa indomie da ruwan tea yaci yasha kafin ya fito a gidan kai tsaye unguwansu NANAH ya nufa ko da yaje ya tsaya tura yaro yayi yaje ya kira NANAH inji AHMAD,UMMUH koh dake sharan ɗaki tace,"ace masa aitawuce",dafe kansa yayi cike da takaicin tafiyar NANAH bata jirasa ba.








NANAH sanda ta isa makaranta kasancewar mashin ta hau da wuri ta isa mutane tsiraru ne ajin su ta nufa taje ta zaɓa benci ta aje jakanta mai-makon tai shara ɗaura ƙafafuwan ta tayi kan table tana kallon window tana kallon ɗalibai sunata zuwa wata class mate ɗinta WALEEDAH ce tashigo ajin tana kallon NANAH ta taɓa baki tace," ba saban ba ɗan ƙauye yayi agogo lungu-lungu sai ɗaga hannu",NANAH ko ɗaga kai batayi ba ta dibe inda WALEEDA ke tsaye WALEEDA bata daddara ba taci gaba da faɗin su o'o anyi sammako kamar an kor.......!








Bata ƙarasa ba sai ganin mutum tai a gabanta ta danƙo wiyan hijjab ɗinta tana huci.




WALEEDAH saida hanjin cikin suka motsa don tasan halin NANAH bata barin saita kwana balle tai tsami.








NANAH tace,"ke banza ƙazama in kika ƙara shiga harkata sai nayi ƙuliƙulin kubrah da yarinya kinsan ni niba kanwar lasa bace banza kazan kowa",hankaɗa tayi tayi baya ta buga kaida benci wani ƙara ta saki dai-dai lokacin wani teacher ya zo gittawa ya leƙo yace,"ke KHADEEJA AHMAD MUSA mai tai miki?.






Turo baki tayi tace,"rashin kunya mana uncle HABEEB".








Daidai lokacin ya ƙaraso ya ɗago WALEEDA goshinta ya tasa yayi tsawo yace,"subhanallah KHADEEJA AHMAD MUSA kinga yanda kika canja mata kama kuwa a lokaci kaɗan?.








Haɗe rai tayi tace,"laifin wa UNCLE HABEEB ni banshiga harkan kowa saboda banson raini ina ruwanta da zuwana da wuri da zata zageni wallahi kaja ma yarinya kunne ko inji mata ciwo".








Sake baki yayi yana kallonta ta rufe ido tana magana ba tsoron ido lallai yarinyar nan tana da tsaurin ido dole ya hukunta yarinyar nan anacewa tana da rashin kunya bai taɓa gani tashiga sabgar kowa ba sai yau haɗe rai yayi cikin kakkuasar murya yace,"fita a ajinnan kifita waje kije ki kama min kunne yau zan gyara miki zama".








Murmushi tayi wanda yake ƙara ma fuskarta kyau tace,"dalilinka akan na bige wannan jakar wayace ta zageni ko wa yace tashiga sabgata Allah ko minene bazanyi saide a koreni daga makarantan nan amma ba wanda zan bari ya taɓa ni akan gaskiyata nike bari ma kagani malan" ,zuwa inda jakanta take ta ɗauka ta goya ta juya tafice a ajin ta barshi tsaye ya saki baki.










Bama WALEEDAH haƙuri yayi tasa ido zai ɗau mataki kaita clinic ɗin school ɗin aka ɗan dubata aka bata drugs, a assembly yana ta zuba ido zaiga NANAH amma ba labarinta dole ya haƙura bayan a koma class ƴan aji na ta tambayan WALEEDA mi ya faru saide tace bigewa tayi NANAH na jiyo su dayake ba ruwanta da kowa yasa ta kama bakinta ta tsuke don bata ɗaukan raini.








Wani malami yashigo ajin ya kirata fita tayi tabi bayansa sai office ɗin principal ta iske WAHEEDAH tsaye sai UNCLE HABEEB gaida principal ɗin tayi ta amsa tace,"KHADIJA miya haɗaku dashi da WALEEDA, gyara tsayuwa tayi ba ko tsoro tace,UNCLE HABEEB dai kullum sai yace nazo na same shi yana mugun sha'awata ita kuma WALEEDA ƴar lesbian ce taɓa min ɗuwawu take da nono shiyasa na bigeta".










Gaba ɗayansu gwalalo ido kow yayi UNCLE HABEEB yace................!








MORE COMMENTS
MORE TYPING🖌️




_typing🖌️_






*🔵SURUKAR ZAMANI🔵*




_NA MARUBUCIYAR_
*SAMHA*
*ƳAR MACE*
*KISHIYA CE*
*NOOR JAHAN*
*JAHAN KHATOON*
_ND NOW_
*SURUKAR ZAMANI ND MATAR BAHAUSHE*










NOT EDITING❌




NA *KHADEEJATOU BASAHEER BASAKKWACE(MRS BATURE BASAKKWACE)*








SADAUKARWA GA
*RAHMA SADAU,AISHAv SAUDAU ND FATEEMAH SADAU WANNAN SHAFIN NAKUNE ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA KU🥰*






_GAJERAN LABARI👌_














_GAJERAN LABARI👌_






*PAGE 32&33*






*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI.*








___________📖Gaba ɗayansu suka gwalalo idanuwa jin sharrin da NANAH ke laƙaba musu UNCLE HABEEB yace,"KHAD......,saurin da katar dashi tayi ta hanyar juyowa ta kalle shi ta tsura masa idanuwan ta masu matuƙar kwarjini cikin kakkausar murya tace," ko ba ai haka ba musawa zakayi koko ƙaryatani zakai wannan shine tarbiyan da iayayen mu suka turo mu kuyi mana?taɓa baki tayi kafin tace,"ande ji kunya MALAMI da neman ɗaliban shi da lalata".










PRINCIPAL ƙasa tai da kanta tana nazari magan ganun NANAH tabbas in ba gaskiya bane ba yanda zaai ta haƙiƙance sannan HABEEB da WALEEDA su kasa musawa balle su kare kansu inde hakane HABEEB ya gama bata kunya yana ɗaya daga cikin mallaman da take ganin su da mutunci ashe two face ne.








HABEEB koh kunya kamar ta nitsar dashi ƙasa ya rasa da wani kalma zaice tunda yarinyar bade baki ba yana fara magana zata katse shi ta ƙara da gula zance,lallai yarinyar nan ta fiye tsaurin ido bako tsoro ba shakka ta samu waje ta tsaya ta watso masu sharri ta haɗe rai kamar duk kenan.








WALEEDA yau duk bakinta na rashin kunya yayi shiru ta haɗu da kakar mamanta a harkan.






PRINCIPAL ɗagowa tayi ta kalla NANAH tace,"KHADIJA AHMAD MUSA",juyawa tayi ta zuba mata idanuwanta ba tare da tayi magana ba,PRINCIPAL taci gaba da faɗin, naji daɗi da kika zamto ƴa na gari mai tarbiya da watsats-tsiya ce da tuni kin gama bada kanki garesu Allah ya miki albarka kuma duk wanda ya ƙara miki magana makaman ci haka kizo ki gaya min zan ɗau mataki, ku-kuma ta maida kallon ta kan HABEEB da WALEEDAH taci gaba da haɗin kun ban ma-maki

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads