Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 67160 words

Chapter 20 - SIRRI NE BOOK COMPLETE BY AUNTY AISHA J.B.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

611

Ads at the middle of Article

wlh saina miki tsayuwar dare Allah yasa yau zayyad ya danna miki ciki... da sauri Zeey tace.. shegiya beaty da kuwa na ja miki Allah ya isa sai naci bura na koshi kwashe sukayi da dariya hatta su fahad harda kama ciki inda sabo sun saba halin kawayensu rauda tace. shegiya jarababbiya Zeey tace besty zan kawo miki abubufa fahad yace dalla malama tafi bama so karki cuceta gwara ke kina da miji shema'u tace sharesu Rabi'a na zuwa gobe zata fara gyara mana besty sunyi shakiyancin su kala kala kafin suka tafi suka barta dasu fahad suma basu jima ba suka tafi fati tazo ta kawo mata shatara na arziki sosai rauda tayi murna sai dai wannan karon bata zo da litel rauda ba kwanan ta ɗaya ta tafi bayan sun ƙeɓe i'ta da hajiya da umma harda abbu bansan mai suka tattauna ba dai amma ina mamakin yanda suka san juna haka Sayyadi nada wata ɗaya akama sajida aiki domin ta kasa haihuwa da ƙanta sai dai ana gama mata aikin bayan an cire mata yarta mace ko kallon fusƙan yarinyar batayi ba tace ga garinku mutuwarta ya girgiza kowa rauda tayi kuka hakama hajiya (nima haka naji mutumar sosai to ta tabbata hajiya zata goya shege😎) lokacin da labari ya iske anas a firgice yazo amma koran kare hajiya ta masa yayi kuka sosai kuma yayi ladamar abinda ya mata.. tunda na haihu umma da kawaye na suke tsumani sosai da magunguna nidai a ganina bai dace a gyara ni ba tunda ba miji gareni ba kuma babu wanda yafito nimana amma lamarinsu na bani mamaki matuka ganin yanda suke tsumani gashi abubuwa sun min yawa a jikina wani maganinma bana sha sabida wani da nasha in har lna zaune ne sai inji na jiƙe gashi lna bukatar kasancewa da namijj sosai...


*BAYAN SHEKARA ƊAYA*


~Sorry my fan's a gurguje~😉


watan sayyadi takwas yayi tafiya yaro ɗan albarka mai halin Dadynsa bashi da kiriniya sam gashi da hakuri ko irin kuƙansu da damun iyaye irin na wasu ƴaƴan baya yi nono in bani na bashi ba bazai nima ba, kasancewar ya fara cin abinci da huri duk krshen sati hajiya sai ta kawo mana ziyara ga Ummul-aymana ma ta girma yarinyar sajida tana kama da Anas duk da a hoto na taɓa ganinsa shima lokacin sajida ce ta nuna min sosai naƙe son yarinyar. shekaran sayyadi ɗaya na yaye shi inda hajiya ta ɗauƙe shi suka tafi sati biyu da tafiyar su aunty fati tazo i'ta da litel rauda yarinya ta girma sosai naji daɗin zuwansu sosai lokacin da fati tace ta kawota hutu kasancewar an bada hutun makaranta murna a guna kamar na zuba ruwa a kasa insha dan daɗi bata kwana ba ta koma sosai nake kula da baby rauda yarinyar na ɗebe min kewa sosai misalin karfe takwas lna zaune saman bed bayan na gama shirin barci litel ce a cinyata tana shan barcinta umma da abbu ne suka shigo hannunsu sakale da juna murmushi nayi lokacin dana amsa sallamarsu kana na gyarawa litel kwanciyarta himar na saka sannan suka zauna ina tsakiyar su abbu ya rinƙe hannun haguna ummata ta riƙe damata shuru ne ya ziyarci ɗakin na kusan minti goma daga bisa ni umma tace. mamanah yanda ta kirani cikin sanyin murya yasa na ɗago abbu yace. RAUDAH shima kallonsa nayi shuru ne ya kara ratsa ɗakin daga bisa abbu yaci gaba RAUDA menene matsayi na a gurinki? ciƙe da faɗuwar gaba nace "MAHAIFI... kara riƙe hannuna yayin kafin yace masha Allah a matsayi na na mahaifinki ni yadace inzaɓa miki mijin aure ko ba haka ba ? gyaɗa masa kai nayi domin maganarsa ya fara sakani cikin duhu "kuma na zaba miki duk da ba zabin ranki bane amma sai kika min biyayya kika zauna dashi har zuwa yanzun da ubangiji ya ɗauki abinsa.... numfashi yaja kafin yaci gaba. yanzun kina matsayin bazaura kice ya dace ki fiddo da mijin da kike so amma RAUDAH wani hanzari ba gudu ba ina roƙon alfarma a gareki... da sauri na katseshi. haba abbu wacece ni da har zaka nimi alfarma a gareni umurnin kawai zaka bani ya mahaifina... cike da farin ciki da jin daɗin kalamanta yace. nagode Allah ya miki albarka ubangiji yasa ki gama da duniya lafiya cikin zuciyata ,nace amin umma tace nima alfarma nazo nima kallonsu nayi kafin na zame na durkusa bisa gwiwowina. "ku keda iko dani bani dake da iko da kainaba, ku faɗamin bukatarku koma menene nayi muku alkawari zanyi shi" miƙewa abbu yai tare da harɗe hannuwansa a kirjinsa murya a tausashe yace. "RAUDAH tsawon lokacin da kika kwashe banga kin kula kowa ba, kuma kinsan zaman ki a haka bazai yuhu ba, shiyasa a matsayina na mahaifinki na zaba miki miji a karo na biyu na bada ke lsha Allahu nanda sati biyu za'a ɗaura miki aure... da sauri na ɗago kaina dab ban taba tunani za'a kawo min maganar aure a dai dai wannan lokacin ba magana nake son inyi amma sai ya katse ni "alkawari kika ɗauka ƴata karki zama mai sabawa kiyi min biyayya lnsha Allahu zakiji daɗin zaɓin da namiki fiye dana baya..." ba batare da na shirya ba nace . waye mijin wanene shi ? murmushi umma tayi kafin tace *SIRRI NE* ɗan share kwallan daya zubo mata tayi kafin tace. shiƙenan umma abbu zan muku biyayya a karo na biyu..... wani irin kuka ne ya kwace mata lokacin data tuna da uncle ɗinta shiƙenan rumgumeta umma tayi itama tana hawaye nagode sosai mamana yanda kika mana biyayya ubangiji ya azurtaki da ƴaƴa nagari wanda zasu miki biyayya fiye da yanda kika mana ki bar kuka nasan da ciwo amma daurewa zakiyi kinji ƴata ubangiji ya miki albarka nagode nagode... sosai suka tausasa zuciyarta da kalamai masu sanyaya rai kafin suka fita umma ciƙe da tausayinta ta kwanta suna fita rauda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya sai maimaita kallar SIRRI NE take cikin zuciyarta ganin kuka babu maganin da zai mata yasa taje ta ɗauro alwala tayi nafila tama mijinta addu'a sosai sanna tayi lstihara alqur'ani ta buɗe tana karatu har barci ya ɗauketa . washe gari wasai ta tashi bata jin damuwar komai saima nutsuwa data samu ...




*nagode sosai masoyana da masu bibiyar littafina alherin Allah ya kai gareku lna sanku ina kaunarki sosai Allah ya barmu har a aljanna*


*sai mun haɗu a pagen pagen... basai na faɗa ba*


_200 ne cakal mtn ko transfer ta wannan number 08062715485 screen short tanan 07061631956_




*AYSHA J.B*
_Aunty jagab😎_
69_70


Not Editing
Yasin mura nake,


_My Wattpad fan's lna yinku Totally wlh one luv na Baku shafin nan kyauta Nagode sosai da Addu'oinku gareni.._





Tana gudanar da aiyuk'anta cikin sakin jiki sosai take kula da littel rauda tana ma yarinyar wani'irin son da batayiwa Sayyadi, Bayan kwana uku da faruwar Haka rauda ta Kira kawayenta Gabad'aya suka tace suzo harda Fahad da nagari da yamma suka iso gidan bayan ta cikasu da kayan motsa Baki sun Gama ci sun nutsu kana ta numfasa tare da sauk'e ajiyan zuciya, Rabi'a ce ta kalleta tare da fad'in “kawata menene naganki wani i'rin da fatan dai lafiya?” zamewa rauda tayi ta zauna a tsakiyar carpet tare da sakin wani marayan kuka ganin haka yasa Gabad'ayansu Hankalinsu ya tashi zama sukayi Kusa da i'ta Suna tambayarta lafiya? Sai,da tayi kuka mai'sarta sanna ta fad'a musu komai kowa shuru yai Cike da tausayinta domin sun jinjinawa kok'arinta, Suna kuma mamakin biyayyarta , Zeey ce ta numfasa tare da fad'in “gaskiya kinyi kok'ari kuma muna kara Baki kwarin gwiwa da kiyi hakuri kiyi biyayya a karo na biyu, kamar yanda umma tace rauda zakiga riban biyayya kuma inshallah zakiji dad'i fiye da baya fatana Addu'a ta a gareki kawata Allah.." da sauri Rauda ta katseta "Zainab... na sani ba uncle zakice ba?" Gyaɗa mata kai Zeey tayi cikin sanyi murya rauda taci gaba “tun Bayan rasa mijina ba abinda nake marari muradin son gani kamar uncle na sani kun sani lna masa masifar so ina masa son da banyiwa kowa Bayan iyayena lna kaunar Uncle na sosai Amma nasan a yanzun yamini nisa zuciyata tana Cike da haushinsa na rashin min ta'aziyar mijina..."
Nagari ya katseta da sauri "karkice haka Rauda baki san uzirinsa ba kiyi hakuri nasan da ciwo ƙan amma hakuri zakiyi kina ransa kaman yanda yake naki ran kinsan haka kurun bazai banzatar da lamuranki ba" Rabi'a tace "gaskiyarka Allah ya shige mana gaba" da "Ameen" suka amsa sun tausasheta da maganganu masu daɗi kafin suka bar gidan ana biki saura sati ɗaya Aunty Fati ta kawo mata ziyara, suna zaune suna hira fati tace "ƙanwata muyi magana mana" fusƙantanta rauda tayi tare da bata hankalinta kama mata hannunta fati tayi sannna tace "mijina nake so ki Aura" wani irin kallo rauda ta watsa mata kafin tace. "cabɗi mijinki fa Aunty wlh never, bazan iya ba, nida zanyi Aure nanda sati kuma kinsani gaskiya haƙan bazai yuwu ba" ɗan murmushi fati tayi sanna tace "shiƙenan amma fa bazan samu damar zuwa biƙin ki ba, B'cos zanyiwa mijina aure naso da kece sabida lna kaunarki halinki yamin ,amma tunda kince haka shiƙenan" miƙewa tayi tsaye tana shirin fita saga ɗakin da sauri rauda ta karasa gareta "haba Aunty na bikina bazaki zo ba..." cikin wani irin yanayi Fati tace "bazaki gane bane rauda abubuwa sun shamin kai ne amma zanzo fa" cikin jin daɗi rauda ta rumgumeta "nagode sosai aunty na Allah ya barmu" zamewa fati tayi tana murmushin karfin hali domin i'ta kaɗai tasan mai take ji a zuciyarta tasan tana tsananin kaunar Uncle tana kishinsa fiye da tunanin mai'karatu amma haƙan ba yana nufin zata tauyeshi bane, ta kasance mace mai'tsananin kaunar duk abinda mijinta yake so, koda kuwa i'ta cikin zuciyarta sabanin haƙan ne , tana son Uncle tana son farincikin sa, tana fita bayan sunyi sallama da umma ta shiga motarta kasa ja tayi , cikin sanyi jiki ta kifa ƙanta saman styarin motar wani irin kuka ne ya kwace mata,


****
Wayarta ne ya katseta da sauri ta share hawayenta tare da ɗauka murmushi ta sake ganin Uncle ne mai'kiran "Y'ello angon Raudah baban Raudah hope kana kalau?" tayi maganar tana sakin murmushi a nasa ɓangaren ma murmushi yayi sannan yace. "lafiya kalau uwarGida sarautan mata, fatan kin nufo Gida yanzun?" lumshe ido tayi sannan tace "uhm gani ina shirin kenan" iska ya hura mata ta wayan sannan yace "ya Ƙanwar taki?. "tana lafiya sai dai kewar ka. "uhm haka tace miki? "alamu sun nuna Haƙan" cije lips ɗinsa yayi sannan yace "saikin karaso Allah ya kawoki lafiya" da "Ameen" ta amsa sannan ta kashe wayar ajiyan zuciya ta sauke kafin ta tada motar a guje.
lokaci sai tafiya yaƙe yayin da umma take da gyran rauda biki sauran kwana uku yau labara ba Rauda ce kwance sai juyi take tunda tayi sallar la'asar take kwance ƙan sallaya littel Rauda ce ta shigo da gudu tayi ƙanta amma ganin halin da take ciki yasa ta koma tana faɗin. "lah mamy bakida lafiya daman?" tayi maganar tana kwalalo ido waje hannun rauda ta mika mata alamar tazo amma tuni tayi waje Rauda na kiranta amma ina ko saurarenta batayi ba, gurin umma ta nufa tana haki ɗan sunkuyawa tayi saka riƙeta umma tayi tana faɗi. " a a mamana bana hanaki gudu ba ki daina fa" cinno baki tayi gaba sannan tace "to naji kizo muje mamy batada lafiya" da sauri umma ta mike "subahalillah maiya sameta?" kafaɗa ta ɗaga mata "oho nima ban sani ba" ɗakin rauda suka nufa har yanzun tana juye juye riƙe da ƙai kamata umma tayi tana salati "a a meya sameki" da kyar rauda ta iya faɗin "kai kana umma kaman zai fashe Allah" ta karasa maganan hawaye na sauƙo mata "innalillahi bari na kawo miki magani" fita tayi bayan 3mnt sai gata da magani da ruwa da kyar rauda ta haɗiye domin bata son kwaya kwanciya tayi tana juyi sai girzgiza ƙanta take domin wani irin ciwo yake mata umma na zaune da i'ta har magariba zuwa lokacin barci ya ɗauketa littel ma ganin halin da mamynta take ciki yasa ta zauna tayi tagumi momy ce ta shigo ɗakin tana faɗin "harira lafiya kin bar girki sai hajiya na gani a kitchin" miƙewa umma tayi "wallahi na manta rauda ce ba lafiya shine na ɗan tsaya"


Eyya Allah ya sauwake. ameen umma tace sanna suka fita hawa gadon littel tayi tare da kwanciya kusa da Rauda jikin rauda ƙan yaki domi ko runtsawa batayi ba, sosai hankalin umma ya tashi abbu ma hankalinsa ya tashi a ɗakin rauda suka kwana washegari yan biki duk sun cika gida anata hidiman biki amariya babu lafiya umma ce ta sanar da su Rabi'a halin da rauda take ciki daman suna Shema'u suna shirin zuwa Zeey nema suke jira babu bata lokaci i'tama tazo suka nufo Gidan, kwance suka iske rauda tana riƙe da kai yanzun dai taji ɗan dama tana ganinsu tayi murmushi zama sukayi suna mata ya jiki da sauki yanzun nake cewa zankira ku najiku shuru, Shema tace wlh Zainab ta bata mana lokaci sai ga kiran umma wai baki da lafiya Allah ya kara lafiya dan Allah karsu tashi babu Uncle kusa. ta karasa maganar cikin zolaya ta karasa maganar , pillon data ke kwance akai ta jefeta dashi. Wallahi shema baki da kyau dariya shema tayi cab konayi wanka? Rabi'a tace gaskiyar Shema yanzun in suka tashi ai mun shiga ukunmu kai wallahi kun cikani ku daina min maganar uncle zuciyata bugawa yakeyi Zeey tace an gama Amariya tashi ga wani turare na kawo miki na tsuguno yamutsa fuska rauda tayi tare da kawad da ƙanta. ke ni wallahi da kusan halin da nake ciki inna yi amfani da magani Allah dakun barshi abin yamin yawa jiya nan banda lafiya saida umman ta bani wani magani nasha Allah marana ma ciwo yake duk kun addabeni aƙan mutumin da banma sansa ba, dalla malama kije da abinki ban bukata, narantse baki i'sa ba sai kinyi muguwa koma waye gwara yaji ki zam zam yasan namu ba irin nasu bane kin gane ai? dariya suka saka gaba-ɗayan su, rauda tace Allah ya isan kuna barci a ɗakunan ku ni ina can ina a barni na gaji...


wani irin dariya suka saka Shema harda riƙe ciki, rabi'a tace dalla malama an bar wannan kauyancin bayan uncle ya gama ragargaza abin Farouq ya karasa abinsa hum rauda tace wlh ba zaku gane ba ku ni ko ɗan yatsa na saka Allah bazai huce ba kusan Halitta halittace ni da angama sex nake komawa yanda nake shiyasa Allah ban kaunar wannan magungunan wanda nasha ma ya wadatar, aikuwa baki isa ba dan wallahi saikinyi wanan ya banbanta da sauran Allah saikin bani labari kedai ki daure kawai wannan fa haɗin Shuwa ne zaki rikita bawan Allah sosai nidai Allah yasa ma bashi da mata domin wallahi in yanada i'ta sai sorry rabi'a tace inma yanada ita Allah yasa part ɗinsu da nisa ba irin na kurkusa da juna ba, shewa sukayi tsaki rauda taja wallahi zakuji dashi nidai karku lalatamin ƴa, ta faɗi haka tare da jawo littel, Zeey tace Allah sarki ƴarmu mai'kama da uncle ohh ya Allah zainab zanci tsakiyar ki fa haba!! lalala cab Allah Raudah baki isa ki cini ba da dai Zayyan ne to, ta faɗi haka tare da fita daga ɗakin Rauda tace kai Gundura kallon shema tayi. gundura nanan ma kuwa rabona fa da i'ta tun lokacin da muke makaranta (Gundura wata kawarsuce sunanta Fai'za shegen surunta ne ga naciyar tsiya yasa rauda ta saka mata gundura sai dai i'ta bata cika zaman garin ba , sabida mijinta matafiyi ne) rabi'a tace tana nan na faɗa mata ma aurenki tace maybe gobe su shigo da mijinta, Shema tace zamusha ta tunda gundura na zuwa rauda tace aikuwa wallahi nayi kewarta da surutun nan Ahah aikuwa kaman yanzun cewar Zeey dake shigowa da gauwashir huta, sauko malama kiyi kar hutan ya mutu kinsan icen kirya rauda tace uhm ya na i'ya da gundura dole data nace saida akayi kawance da i'ta, Kuma dole a tsuguna a hutar ba in kuma ba haka ba wallahi ki biyani kuɗin dana siyo saukowa rauda tayi tare da ɗaukan zani. to ya zanyi dole nayi shegiya uwar son kuɗi sai kace kin ban ajiyan kuɗin karban turaren tayi tana tsunguno akai tana zuba masifa Zeey tace dole dai sai kinyi muguwa kawai koda rauda ta gama tsaki ta ringa ja wani mugun dariya Zeey ta saka lokacin da take fita da kaskon hutan tsayawa tayi bakin kofa tare da kallon rauda. wallahi zakiyi masa bayani ne yarinya tunda kinyi amfani dashi jikinki saiya faɗa miki hum humm hummm... saukowa rauda tayi daga saman gadon tana faɗin muguwa daman nasan wannan dariyar da kike bana arziki bane Allah ya isan , fita zeey tayi da sauri komawa rauda tayi ta zauna abinci Zeey ta shigo musu dashi sai tsokanar rauda take sai dare kafin mazajensu suka zo suka kwashesu bayan kowa yaba rauda gudumawa mai'tsoka.
ranar asabar da safe aka ɗaura auren wanda tana kwance lokacin bayan tayi wanka jikinta ne yayi wani mugun sanyi ga zazzaɓin da take ji tana daurewa ne kawai bata son ɗagawa umma hankali ganin tana fama da hidimar jama'a rabi'a da suke zaune duk suna kallonta gundunra ce tace kai rauda ki shirya mana kinsan muna ƙan hanya ga motocin ɗaukar amariya rau-rau Rauda tayi tare da riƙe hannun Gundura Allah fai'za bazaki gane bane gabana sai faɗuwa yake yi ina jin zazzaɓi sosai banson barin mamana ni haka Allah ya kaddaromin auren ƙan gari bazan zauna kusa da iyayena ba, Cikin tausayawa fai'za tace hakuri zakiyi rauda sai lallashinta suke aƙan ta shirya amma taki ganin haka yasa shema mikewa ta kira umma.. rabi'a kuma na haɗa kayanta dana littel tare da Abbu suka shigo zama umma tayi tana kama rauda menene kuma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads