Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 33454 words

Chapter 10 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt

Ads the beginning of article before Image

29 May 2024

500

Ads at the middle of Article

sihirin tsafinshi, amma sai ya zamana cewa tamkar yana inziga miyagun halittun wajen kai mashi farmaki.
Kwatsam! sai yaro Imran ya faɗo masa a rai zuciyarshi na raya mashi cewa kawai ka nemi taimakon Ubangijin yaro Imran tun da dukkanin wata dubara ta ƙwace maka, domin masu iya magana na cewa da asara gwara gidadanji. Kuma wanda ya faɗa teku ko KAIFIN TAKOBI aka miƙa mashi sai ya kama domin ya tsira.
Tun da a halin yanzu ba wanda zai gane cewa ka nemi taimakon Ubangijin Imran sai kai kaɗai. Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya yi kabbara yana mai ambaton sunan Allah a cikin ranshi yana mai cewa "ya Ubangijin imran ka tseratar da ni daga sharrin miyagun halittun nan".
A dai-dai wannan lokaci ne wani ɗaya daga cikin zakokin ya wangame bakinshi da nufin ya cinye yan yatsun Lazwar na hannu.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Lazwar ya kurma wawan ihu cikin wani zafin nama na ban al'ajabi yana daga kwance ya kama wuyan zakin da hannayen biyu ya murɗe wuyan shi, take ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus! Ƙas ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba, sannan ya miƙe tsaye zumbur aka sake yin wani sabon kallon-kallo tsakanin shi da sauran halittun.
Nan take fadar ta ruɗe da shewa masoyan sarki lazwar suka cika da matuƙar farin cikin bisa ganin gwaninsu ya miƙe tsaye.
Shi kuwa sarki ladiyas fuskarshi a murtuke take babu annuri domin tsawon shekarun da aka shafe ana gwada jarumai, ba a taɓa samun wanda ya kashe dabba ɗaya daga cikin halittun ba.
Daga can sai dukkan halittun suka afkawa Lazwar aka sake ruguntsume wa da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
A wannan karon sai ya zamana cewa duk wanda Lazwar ya gabza wa naushi a cikin halittun sai kaga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗo ƙasa tim.
Amma saboda na ci da zafin nama irin na halittun sai su miƙe tsaye zumbur su sake afka mashi da dukkanin tsagwaron ƙarfin damtsen su.
Kafin cikar rabin sa'a sarki Lazwar ya kashe gaba ɗaya halittun ya jefar da gawarwakin su a ƙas, nan fa fadar ta kaure da shewa da ihu jama'a suna ta mamakin wannan jarumtaka ta sarki Lazwar, domin a tarihin gasar shi ne mutum na farko da ya taɓa kashe miyagun dabbobin baki ɗaya.
Ita kanta gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai bata san sa'adda murmushin farin ciki ya suɓuce mata ba.
Al'amarin da ya sanya zuciyar mai girma Ladiyas ta ci gaban da tafarfasa tamkar zata ƙone kenan.
Kodasamun wannan nasara da sarki Lazwar ya samu sai sarkin yaƙi Darusu ya umurci waɗannan dakaru mutum Hamsin suka je suka buɗe ƙofar ɗakin aka fito da sarki Lazwar, likitoci suka shiga ba shi taimakon gaggawa domin tsayar da jinin dake zuba a jikinshi tare sanya mashi magani akan raunukan shi .
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu dakaru mutum arba'in shirye cikin gagarumar shigar yaƙi sun tuso ƙeyar yaro Imran da hadima Khadijat, ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
A gefe guda kuma matsafi Shamrul ne tare tawagar malaman addininsu sanye da tufafi irin na bauta.
Lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai matsafi shamrul da sauran bokaye suka zube ƙasa bisa gwiwoyin su suka kwashi gaisuwa ga sarki ladiyas. Suna masu sunkuiyar da kawunansu ƙasa.
Sai da suka ɗauki lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani matsafi Shamrul ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi da girmamawa cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya shugabana haƙiƙa abinbauta ya bada umurnin a yanka waɗannan mutane biyu mace da namiji da suka shigo mana da wani sabon addini mai suna musulunci wanda suke jan hankalin mutane wannan birni mai albarka, wanda a dalilin hakan zai janyo mana musiba da annoba da zata haifar da suɓucewar mulkin ka".
Sa'adda da sarki Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin matsafi Shamrul sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinshi ta fito waje, yaji ya tsani hadima Khadijat da yaro Imran.
Kawai sai ya dubi Khadijat da fuskar ta ke rufe da rawani ya ce ''ya ke baiwa Sharifa haƙiƙa kin yaudare ni kin ci amanata da kika zo da wani sabon addini a wannan birni nawa, na aika ki zuwa ga sarkin kasuwa domin ki gane ki zamto 'yan leƙen asiri, domin ki taimaka min na samu nasarar ganin bayanshi, haƙiƙa a yau zan yanke miki hukunci dai-dai da laifin da kika aika ta a gareni";
Sa'adda da mai girma Ladiyas ya zo nan a zancen shi sai sarki Lazwar dake gefe guda likitoci na duba lafiyar shi ya cika da matuƙar al'ajabi da mamaki ainun, bisa jin sarki Ladiyas ya kira hadima Khadijat da suna baiwa Sharifa.
Shin dama Khadijat ita ce baiwa Sharifa da ya fito farautar ta ruwa a jallo?
Tabbas tsugunne bata ƙare ba wai an saci ɗan ɓarawo. Haƙiƙa dole ne ya yi sabon gumurzu domin ceton rayuwar Khadijat.
Sarkin yaƙi, Bawa Shamsal da aljani Za'aratul-layal dake cikin siffar bil'adama tare da gimbiya Mashlira dake sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama, sai suka cika da matuƙar mamaki bisa jin ashe hadima Khadijat ita ce baiwa Sharifa,
wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa "rashin sani kaza ta kwana akan dami".
Ashe sarki Lazwar na tare da abin da yake nema bai sani ba har ya shigar da kanshi cikin uƙubar sarki Ladiyas.
A ɓangaren jama'a kuwa sa'adda ji cewa yaron nan da yiwa matsafi Shamrul tambaya akan addininsu za'a yanke wa hukuncin kisa, sai suka yaɗa labarin izuwa cikin gari, nan fa al'ummar gari suka dinga tuttuɗowa suna cincirindo a fadar domin su ganewa idanuwan su.
Domin a yau ne zasu tantance shin tsakanin Ubangijin wannan yaro Imran da matsafi Shamrul wane ne na abin bauta na gaskiya.
Sarki Ladiyas na kammala wannan batu sai sarki Ladiyas ya koma kan karagar mulkinshi ya hakimce.
Kawai sai wani garjejen ƙato ya ɗauki yaro Imran ya ɗora a jikin wani zagayayyan tudu a fadar sannan ya koma gefe guda ya ja ya tsaya, sarki Ladiyas ya yi wa sarkin yaƙi Darusu inkiya ta wutsiyar idanu dake nuna bashi umarni.
Cikin dakewar zuciya gami da zafin nama sarkin yaƙi ya zare wata sharɓeɓiyar adda a gadon bayanshi ya durfafi inda Imran yake domin ya datse wuyanshi.
Sarki Ladiyas, matsafi Shamrul da sauran bokayen suka bushe da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa.
Jama'a kuwa da yawan su sai suka fara zubar da hawayen takaici da baƙin ciki
Ya yin da sarkin yaƙi ya isa daf da shi sai ya daga addar ya ɗora akan waya yaro Imran.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata kyakkyawar halitta ta keto daga saman fadar ɗauke da waɗansu mutane guda biyu.
Ba wani bane wannan halitta da mutanen biyun ba face aljani Hadimul-khairi ɗauke da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas da 'yarta yarinya Shuraiba.
Kafin addar sarkin yaƙi Darusu ta yanka wuyan Imran aljani Hadimul-khairi ya ɗauko wata farar kwalba mai ɗauke da wani koren ruwa ya watsa inda Imran da baiwa Sharifa suke, take sarƙoƙin dake ɗaure a jikkunansu da addar dake wuyan Imran sun narke suka zama ruwa.
Cikin matuƙar firgici sarkin yaƙi, sarki Ladiyas da sauran jama'ar fada suka ɗaga kawunansu izuwa sama.
Yaro Imran, hadima Khadijat, sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal, kuwa sai suka cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa.
Aljani Hadimul-khairi ya a sauka a turba bisa diga-diganshi.
Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin sarki Ladiyas, da uwar gidanshi gimbiya Lamrat, matsafi Shamrul da yaro Imran da hadima Khadijat wato baiwa Sharifat, sarkin yaƙi Darusu da sarki Lazwar.
Cikin matukar ɓacin rai mai girma Ladiyas ya dubi uwar gidanshi Lamrat ya ce "ya uwar gidana shin ina dalilin wannan zuwa naki a cikin wannan yanayi?
Koda jin wannan tambaya daga bakin Sarki Ladiyas sai gimbiya Lamrat ta tari numfashinshi tana mai daka mashi tsawa, ta dube shi cikin matuƙar fushi ta ce "kai tsohon AZZALUMI kuma la'ananne ka yi sani yanzu kan mage ya waye, a yau ne zan ɗauki fansar jinin mai gidana maƙeri Murrasu daka ni da 'yata Shuraiba, haƙiƙa masu iya magana sun yi magana da suka rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya, ka yi sani cewa tsawon shekarun da ka shuɗe kana azabtar da jama'ar birnin ISTANBUL kana yiwa mutane BAKIN ZALUNCI, to ranar ƙin dillanci ta zo maka.
Shawarar da zan baka ita ce ka yi hanzari ka rubuta wasiyyar da kake son bar wa jama'ar kafin mu zare maka ruhinka daga gangar jikinka. Sannan ina so ka yi sani cewa ni da 'yata Shuraiba tuni mun karɓi addinin yaro Imran.
A halin yanzu ni ba uwar gidanka ba ce face abokiyar gabar ka, dama dai-dai da rana ɗaya ban taɓa ƙaunarka kawai ina yi maka biyayya ne bisa dole don tana din gobe na".
Sa'adda mai girma Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin gimbiya Lamrat sai zuciyarshi takama tafarfasa tamkar zata ƙone ya daka mata tsawa a lokacin da idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur cikin kakkausar murya mai ya ce "kaicon ki yake Lamrat haƙiƙa kin tafka babban kuskure da har kika yi gangancin haɗa kai da maƙiya na domin farautar rai na, a yau ne zan yi maki hukunci mafi muni ke da 'yarki Shuraiba".
Sa'adda sarki Ladiyas ya zo nan azancen shi sai ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar shi ta mulki ya cire alƙyabbarshi, take wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro ta bayyana a jikinshi. Kawai sai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye yana saman ya daga hannunshi sama wata irin sharɓeɓiyar takobin sihiri ta bayyana a gare shi, ya sauka bisa diga-diganshi a daf da inda Lamrat take.
Koda ganin hakan sai yarinya Shuraiba tayi wuf ta zare kwari da bakanta ta yi shirin ko ta kwana.
Sarki Lazwar kuwa duk da cewar jikinshi ya yi tsami akwai manyan raunuka, amma sai ya yi wuf ya kwaci wata takobi a hannun wani badakare ya falfala da azababban gudu izuwa kan sarkin yaƙi Darusu
Baiwa Sharifa da yaro Imran kuwa sai suka yi ɗauki izuwa kan matsafi Shamrul suna masu ƙwala kabbara, bawa Shamsal da sarkin yaƙi kuwa sai suka tari dakarun dake fadar, aljani za'aratul-layal sai ya yi girgiza take surarshi ta canja daga ta bil'adama izuwa ta aljani kawai sai ya rufawa mai gidanshi sarki Lazwar baya,
a lokacin ne gimbiya Mashlira sai cire hular ƙarfen dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili, nan fa kowa ya cika da mamaki ganinta, kawai sai ta yi koyi da aljani Za'aratul-layal ta kaiwa masoyinta sarkin Lazwar ɗauki.
Lokaci guda ɓangarorin biyar suka afkawa juna aka garƙame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
Wohoho! kaico haƙiƙa guguwar annoba idan ta taso babu mai maganin ta face Allah, kuma tabbas in da babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, domin KARON MAZA sai JARUMAN DUNIYA da suka ciri tuta a GUMURZUN SHEKARA DUBU, waɗanda komai TSANANI DA UKUBA a filin DANDAZON MAYAKA baya sa su gudu.
Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya ga yadda fadar ta yamutse da gumurzu dole ne ya ɗimauce ya fita daga hayyacin shi domin dola ne artabun ya zamo tashin hankali.
Nan fa jama'a suka ɗimauce suka kama guje-guje da ifice-ifice domin tsira da rayukansu
Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA tamkar jikkunan su basu kasance na bil'adama mai jini tsoka ba.
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai fita filin yaƙi ba to bai ga ƙarshen tashin hankali ba,
wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi, ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne gimbiya Lamrat, yarinya Shuraiba da Aljani Hadimul- kahiri suka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa tsananin zafin naman sarki ladiyas ya nunka nasu sai arba'in,
Nanfa ya zamana cewa mutum uku sun kasa galaba akan ɗaya ya zame masu alaƙaƙai, duk sa'adda suka kai mashi hari da makaman smmsu idan ya kare da takobinshi, sai kaga makaman sun dakushe kuwa ko gezau bai yi ba.
Idan kuwa Ladiyas ya kai masu harin idan suka goce sai ya zamana cewa duk abin da takobin ta saran sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne.
Matsafi Shamrul, yaro Imran da hadima Khadijat kuwa tuni labari yasha banbam, domin kuwa sun hana tsafi Shamrul rawar gaban hantsi, har sai ya zamana cewa ya daina amfani da makami ya dawo yaƙar su da ƙarfin sihirin tsafi, domin wani lokacin idan Imran da Khadijah suka sare shi ta takubban su sai su ga raunin ya koma ya haɗe sumul, wasu lokutan ma sai ya rikiɗa ya zama haske.
Sarki Lazwar, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal kuwa sun wanzu suna masu kaiwa sarkin yaƙi Darusu hare-hare cikin gwanintar yaƙi tamkar za su cinye shi ɗanye.
Amma bisa mamaki sai ya zame masu ƙadangaren bakin tulu suka kasa samun nasarar koda lakutar jikinshi, duk kuwa da cewar ƙarfin mutum biyu ne da aljani ɗaya akan mutum guda.
A ɓangaren bawa Shamsal da sarkin yaƙi ku wa sun wanzu suna ragargazar dakarun dake fadar duk inda suka sanya gaba sai ka ga dakarun na zubewa ƙasa matattu, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje hade da hargowar aljanu gami da ifice-ificen jama'a ya cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe fadar baki ɗaya tamkar haɗari zai gangamo a kece da ruwan sama.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin manyan sarakuna biyu, aljanu biyu, gami da jarumai shida sai yaƙin ya zamto tashin hankali gami da ban tsoro ga yan kallo.
Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin jaruman ba tare da ɗayan su ya samu nasarar hallaka ɗaya ba.
A bangaren sarki Ladiyas kuwa ya zamewa su gimbiya Lamrat ANNOBA ƊARI domin duk da cewar Hadimul-kahiri na amafni da addu'o'i domin su hallaka sarki Ladiyas amma sai hakan ya gagara domin sai sun datse wuyanshi suna tunanin ya mutu sai kawai su ga wani ruhun ya keto daga cikin ƙarƙashin ƙasa ya sake shiga jikinshi.
Sai kuma a ɗora wani gumurzun, nan fa ya zamana cewa su Hadimul-kahiri sun kashe fiye ruhika arba'in na sarki Ladiyas.
Al'amarin da ya sanya su duka ukun suka samu miyagun raunuka musamman yarinya Shuraiba. Haƙiƙa sarki Ladiyas bakaramin hatsabiba ne domin ya yi nisa a halarar tsafi wanda cimma mashi abu ne mai matuƙar wahala.
A dai-dai wannan lokaci ne yaro Imran da hadima Khadijat suka samu nasarar hallaka matsafi Shamrul, ta hanyar amfani da takubbansu suka soka mashi akan ƙawon zuciyarshi, ya yin da suka hango su yarinya Shuraiba kuma suka ga irin mugun halin da suke ciki sai suka kai masu ɗauki.
Nan fa ya zamana cewa labari ya sha bamban domin a wannan karon sai ya zamana tasirin sihirin dake tare da sarki Ladiyas ya fara karyewa, domin duk sa'adda hadima Khadijat da yaro Imran suka kai mashi hari da makamansu duk inda suka sara sai su ga sun tsarga jikinshi.
Bisa taimakon Ubangijin halitta daƙyar da siɗin goshi suka samu nasarar hallaka sarki ladiyas, ta hanyar sare mashi hannaye da ƙafafuwanshi suka jefar da gawarshu a ƙas.
In da ace mutum ya na wannan waje a lokacin da sarki Ladiyas da matsafi Shamrul suka yi mutuwar wulakanci dole ne ya yi farin ciki maral-musaltuwa. Bisa ganin yadda Allah Ubangijin halitta ya kawo ƙarshen azzalumai.
A dai-dai wannan lokaci ne su gimbiya mashlira, Aljani Za'aratul-layal da sarki Lazwar suka samu nasarar hallaka sarkin yaƙi Darusu.
Sa'adda al'ummar fadar da su bawa Shamsal suka yi arba da gawar sarki Ladiyas, da ta matsafi Shamrul sai dukkanin su suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinsu suka yi mubaya'a, suna masu cewa "haƙiƙa mun bayar da gaskiya ga Ubangijin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads