Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 33454 words

Chapter 3 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt

Ads the beginning of article before Image

29 May 2024

493

Ads at the middle of Article

su.
Kawai sai ta ci gaba da ta harbin muridan a idanun su cikin matuƙar ƙware wa da zafin nama.
Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce kyan ɗa ya gaji ubanshi, kuma ita sadaukantaka gadon a ke yi ba wai a kasuwa ake siyarwa ba.
Haƙiƙa babu wadda zai yi arba da yarinya Shuraiba a cikin wannan hali face ya jinjina mata.
A ɓangaren sarki Lazwar, sarkin yaƙi da su bawa Kuwait kuwa, sa'adda suka ga yadda yarinya Shuraiba ta gano lagon muridan har ta na samun nasarar hallaka su sai suka yi koyi da ita.
Ya zamana cewa suna daka tsalle sama suna hawa kan muridan suna amfani da takubban su suna soke masu idanu.
Aljani Za'aratun-layal kuwa hannunshi ya dunƙule ya shiga naushin muridan a idanuwansu. Duk wanda ya gabza wa naushin sai dai ka ga ya faɗi kasa matacce.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canja dole ne rawa ta canza. Nan fa muridan suka fara gane kuren su suna yin muguwar hallaka a banza, komai hassadar mutum idan ya ga yadda sarki Lazwar ke ragargazar muridan dole ne ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa tabbas Lazwar ya cika GWARZON DUNIYA kuma SARKIN SADAUKAI.
Saboda yadda yake kashe muridan tamkar yana sassabe a gonar auduga.
Lokacin da aka shafe sa'a ana wannan arbu sai ya zamana cewa duhun dare ya fara kawo kai, nan take tsananin sanyin dake dajin ya daɗa ƙaruwa.
Nan fa su sarki lazwar suka shiga cikin wani tashin hankali, kuma tsawon lokacin da aka shafe ana wannan gumurzu bai huce muridan guda ɗari kacal ba aka hallaka ba.
Koda ganin halin da ake ciki sai sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi domin samun mafita.
Kaico! Hakikya rashin sani yafi dare duhu, inda a ce sarki Lazwar ya san abin da zai biyo baya da bai yi gangancin karanta dalasiman tsafi ba, domin kuwa faruwar keda wuya sai wata irin iska ta musamman ta mamaye dajin baki ɗaya wacce ta sanya sanyin ya kara tsanan ta. kawai sai ya ga jama'ar ya yanke jiki suna faɗuwa ƙasa sumammu.
Ko da ya waiga bayan shi domin ya ga a wane hali
yarinya Shuraiba ke ciki.
Kawai sai ya ga wayam babu ita babu alamar ta, kafin ya mayar da duban shi zuwa ga su sarkin yaƙi sai kawai ji ya yi an gabza mashi wani wawan naushi a fuska take hankalin shi ya gushe ya dai na gane kanshi.
Su sarki Lazwar ba su tsinci kansu a ko ina ba sai a cikin wani ɗakin duhu, wanda saboda matuƙar duhun shi mutum ko tafin hannayenshi ba ya iya gani, a bisa cikin wani irin ƙaton keji da aka yi shi da zallar waɗansu irin itace masu ƙwarin gaske.
Jim kaɗan da farkawar su sai kawai su ka ga ɗakin ya gauraye da wani irin haske mai ban mamaki.
Sai a sannanne sarki Lazwar ya gane cewa kowannen su an sanya shi a keji na daban ba tare da an gama shi da ɗan uwanshi ba, hatta aljani Za'aratun-layal na shi kejin daban, amma duk an daɗɗaure shi da waɗansu irin sarƙoƙi na baƙin ƙarfe.
Sa'adda kowannen su ya sake buɗe idanuwan shi tarwai ya ga babu yarinya Shuraiba da gaba ɗaya sauran tawaga, sai hankulan su suka dugunzuma ainun, kuma aka shiga firgici, aka fara tunanin shin ko yarinya Shuraiba da tawaga sun rasa rayukansu ne.
Shi kanshi aljani Za'aratun-layal da bai kasance bil'adama ba sai ya ji a ran shi yana matuƙar kewar Shuraiba tamkar da ma sun daɗe da shaƙuwa da juna.
Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sai su kaji karar buɗe sakatun kofar ɗakin.
Jim kaɗan sai Kofar ta buɗe sai ga waɗansu irin zaratan dakarun muridan su bakwai sun shigo cikin ɗakin.
Kallo ɗaya su sarki Lazwar su ka yiwa dakarun suka sunƙuiyar da kawunan su ƙasa, saboda matukar kwarjinin da munin siffar su.
Dakarun su ka durfafi inda su sarki lazwar suke, su na isa gare su suka ɗauki kejin da suke ciki su ka ɗora a bisa kafaɗunsu, wanda aljani Za'aratun-layal ke ciki kuwa dakaru biyu suka ɗauka, kawai sai su ka fice daga cikin ɗakin, suka durfafi wata hanya ta musamman su ka shiga izuwa cikin gari.
Nan fa su sarki lazwar suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi suka kama kalle-kalle da dube dube-dube, tamkar ɗan ƙauye ya shiga birni, shi dai gaba ɗaya birnin muridan an gina gidajen shi da waɗansu irin manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, masu matukar tsawo da faɗi.
Ko da jama'ar birnin su ka yi arba da su Lazwar sai suka cika da matuƙar murna, su ka suka shiga tanɗe bakunansu gami dalalar da yawu, saboda matuƙar kwadayin yau za su kalaci da naman bil'adama.
Tafiyar daƙiƙa talatin kacal! aka yi aka iso fadar birnin.
Fadar ta kasance tanƙamemiya mai matuƙar tsawo da faɗi, kuma gininta anyi shi ne da irin waɗannan duwatsu masu ƙyalli, sannan an ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har dama abin da idanu ba su taɓa gani ba.
A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza da mata yara da manya, babu masaka tsinke, bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar ƙarfen jauhari, aka yi mata feshi da koren ruwan yaƙut.
Wani irin shirgegen mutum ne wanda yafi gaba ɗaya muridan girma kwarjini da cika idanu zaune bisa wata ƙasaitacciyar karaga. yana sanye cikin wata irin ƙasaitacciyar shiga irin ta su ta manyan sarakai, sanye da wata alƙyabba da aka yi mata ado da gashin ɗawisu kanshu sanye da wani KAMBUN SARAUTA na zinare.
Zaune a gefen hannunshi na dama, wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance.
Budurwar tana da dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu, ɗigon cikin su ya kasance siɗik mai kwarjini, girar saman su baƙa ce siɗik tayi luf-luf, hancinta dogo ne mai ban sha'awa, a ƙasan shi an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da labbanshi suka kasance jajur, wuyanta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa ya yi tudu a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta daga gaba ya tsuke daga baya kuma ya yi tudu tamkar idan aka ɗora tuffa za ta zauna, 'yan yatsun hannayenta da kafafuwanta sun kasance zara-zara masu ɗaukar hankali.
Wohoho haƙiƙa Allah wannan budurwa ta cika kyakkyawa ta kece raini, babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar halitta face ya ɗimauce, kuma ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyarshi.
Ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarki muridan Kushuful-mannar
Sarki Kushuful-mannar ya auri mahaifiyarta ne a cikin waɗansu a yarin larabawa da aka riba to a matsayin fursunonin yaƙi, bisa binciken da sarki Kushuful-mannar ya yi bisa halarar tsafin shi ya gano cewa 'yar shi Mashlira ce silar dauƙaƙar shi a duniya da ci-gaban zuri'arshi a doran ƙasa, bisa wannan dalili ne ya sanya ya ke matuƙar kaunar ta fiye da komai a rayuwarshi.
Tun kafin dakarun da suke ɗauke da su sarki Lazwar su iso inda karagar mulki take gimbiya Mashlira ta ƙurawa Lazwar idanu ko ƙiftawa ba ta yi, a karon farko a rayuwar ta ta ji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta.
Shi kuwa sarki Lazwar koda ya ga irin kallon da budurwar ke yi mashi sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kama shi jikin shi ya kama ƙyarma, abu na farko da jefa shi cikin wannan hali shi ne, a iya tsawon rayuwarshi tun da yake bai taɓa gani ko jin labarin 'ya mace mai matuƙar kyawun ta ba.
Abu na biyu kuwa shine lokacin da da ya haɗa idanu da ita sai ya ji cewa a duk faɗin duniya babu wata budurwa da yake ƙauna tamkar ta.
Yanzu ta ya ya zuciyarshi za ta kamu da soyayyar wata 'ya mace bayan cewa ba zai taɓa kusantar mace ba da niyar aure ba face ya karya sihirin dake jikinshi.
Wai shin wane tabbaci ya ke da shi cewa waɗannan muridan za su bar shi a raye,
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai hankalinshi ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe.
Lokacin da ya rage sauran kamar taku goma tsakanin su da karagar mulki sai dakarun su ka zube ƙasa, su ka kwashi gaisuwa cikin girmamawa bayan sun ajiye kejin da su Lazwar ke ciki.
Sarki kushuful-mannar ya shin-shina su sarki Lazwar yana mai tanɗe baki tamkar wadda zai ci naman ɗawisu.
Sannan ya busar da iskar dake hancinshi wani irin tiririn baƙin hayaƙi ya fita daga ƙofofin hancinshi.
Kawai sai ya yi wa ɗaya daga cikin dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu. kawai sai badakaren ya buɗe kejin da bawa zailan ke ciki ya ɗauko shi ya kwantar da shi akan wani zagayayyen tudu, sannan ya ɗauko wata zabgegiyar takobi ya ɗaga sama ya datse wuyan bawa Zailan kuma ya shiga daddatsa naman shi.
Koda ganin yadda aka yiwa bawa Zailan sai su sarki Lazwar su ka kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika masu idanu.
Badakaren na kammala daddatsa naman sai ya watsawa jama'ar dake fadar.
Tun kafin ya kai ƙasa jama'a sun wawashe sun cinye suna ihun murna da kururuwa mai tayar da hankali.
Badakaren ya sake sanya hannuwanshi a kan kejin da sarki Lazwar ke ciki ya buɗe sakatun, ya zira hannun sa ya ɗauko shi ya ɗora shi a bisa wannan tudu, a karo na biyu ya sake ɗaga takobin domin ya datse wuyan sarki lazwar.
Kafin takobin ta datse wuyan Lazwar sai gimbiya Mashlira ta dakawa badakaren tsawa sannan ta dubi mahaifinta ta ce "ya abbana ina neman wata alfarma a gare ka da abar mani waɗanan fursunoni zuwa gobe, domin nima ina so na ga na hallaka su da hannaye na domin ɗaukar fansar kisan da su ka yiwa dakarun mu shin ko ka manta ne cewa fiye da shekaru ashirin hakan bai taɓa faruwa ba.
Koda jin wannan batu sai sarki zammar ya yi murmushi mai taushi ga 'yarshi Mashlira ya ce "nayi miki wannan alfarma ya muradin zuciyata ai girma da matsayin ki ya huce haka, gaba ɗaya jama'ar wannan birni da abin da ke cikinsu mallakin ki ne".
Ko da gama faɗin hakan sai ya yi wa badakaren inkiya a karo na biyu kawai sai badakaren ya mayar da takobinshi cikin kuben ta.
Sannan ya ɗauki sarki Lazwar da hannunshi ɗaya tamkar ya ɗauki takarda ya sake jefa shi cikin kejin ya mayar da kofar ya rufe, sannan ya sake umartar waɗannan dakaru suka sake ɗaukar kejinan, har suka fice da fadar gimbiya Mashlira bata daina satar kallon sarki Lazwar ba tana yi mashi murmushi mai ɗauke da alamar tambaya.
Al'amarin yarinya Shuraiba da damisar ta kuwa, a she lokacin da waɗannan samudawan muridai suka samu nasarar kama abokan tafiyarta ta rugawa ne izuwa wani ɓangare a dajin ta laɓe domin ta ga abin da muridan za su aikata
Sa'adda ta ga muridan sun ɗauke su a cikin kejunan sun kunna kai izuwa cikin dajin, sai ta ci gaba da bin sahun su sannu a hankali, har sai da ta shige izuwa cikin birnin su ba tare da wani ya gan ta ba, da yake lokacin dare ya fara duhu sai Shuraiba ta maƙale a dai-dai ƙofar gidan da aka ajiye su sarki Lazwar, tana zuba idanu domin ta ga wanda zai fito daga cikin,
tana nan tsaye sai kawai ta hango waɗansu dakaru su bakwai sun durfafo Ƙofar gidan har dakarun sun zarce gaba, sai kawai ɗaya daga cikin su ya dubi sauran 'yan uwanshi ya ce "haƙiƙa ni fa ina jin ƙamshin bil'adama.
Sauran suka dube shi suka ce "kwarai tabbas zancen ka dutse, muma muna jin hakan kawai dai shiru mu kayi".
Ko da jin abin da dakarun ke tattaunawa sai shuraiba ta yi wuf ta shiga cikin wani kwandon shara tare da damisarta, nan fa wari da ɗoyin dake ciki ya fara galabaitar da ita ga yunwa da addabe ta, take numfashin ta ya ɗauke, ta sulale ƙasa sumammiya, a dai-dai lokacinne badakaren ya haska gwandon sharar da wata fitar ice, dake hannunshi domin ya ga menene a cikin.
Ko da haskawar ta shi sai ya ga babu komai a cikin shawara. cike da mamaki da al'ajabi ya sake shaƙar iska dake wajen amma a wannan karon sai ya ji ba ya jin ƙamshin bil'adama.
Kawai sai ya juya izuwa inda yan uwanshi suke tsaye ya tarar da su ya dube su ya ce "babu komai a wajen tamkar yadda muke tunani, take sauran dakarun su ka cika da matuƙar mamaki, ɗaya daga cikin su ya yi gyaran murya ya ce cikin wata irin kakkausar murya "amma kamar yau na samu labarin cewa dakarun mai girma Zammar masu FARAUTAR MAZAJE sun samu nasarar kamo waɗansu fursunonin bil'adama,'.
Wata ƙila wannan kamashi da muke ji yana da alaƙa da bil'adaman dake cikin wannan birni namu".
Ko da gama faɗin hakan sai dakarun su ka juya suka ci gaba da tafiya.
Kaico! Haƙiƙa yarinya Shuraiba da damisar baƙaramin tsallake rijiya da baya suka yi ba.
Abin da dakarun ba su sani ba shi ne tabbas akwai bil'adama a cikin sharar, kawai dai saboda Shuraiba da damisar ta sun sume ne babu rai a tare da su shine ya sanya ba su ji ƙamshin su ba.
Kuma bisa halayyar muridan matuƙar babu rai a jikin bil'adama ba za su ji kamshin shi ba. Tsananin sanyin da ya mamaye birnin bisa ketowar alfijir, shine abin da ya farkar da yarinya Shuraiba da damisar ta, koda farkawar ta su sai suka yunƙura suka fito sharar, nan take damisar ta fahimci cewa Shuraiba ta galabaita ainun da alamu ƙishi ruwa ce ta addabe ta, koda fahimtar sai kawai ta shiga tona ƙasa da ƙafarta ɗaya jim kaɗan sai ga shi ta tarar da ruwa.
Kawai sai Shuraiba ta sunkuiya ƙasa bisa gwiwoyinta ta sanya hannayenta biyu, tana kamfatar ruwan ta na sha, duk da cewar ruwan yana da sanyi ƙarara har yana kama mata hakuri, amma haka ta cigaba da kwankwaɗar shi har sai da ta ƙoshi.
A sannanne Shuraiba ta ji ƙarfi a jikinta, kawai sai ta yunƙura ta haye bisa gadon bayan damisar.
Sannan ta cigaba da tafiya a cikin birnin, sai dai a wannan karon ba su haɗu da komai ba, haka dai su ka cigaba da tafiya a sannu-sannu, tana cikin tafiyar ne ta hango wani katafaren gida waɗansu irin dakaru tsaye a wajen, kuma shirye cikin gagarumar shigar yaƙi rike da miyagun makamai.
Nan take Shuraiba ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai zurfafa cikin kogin tunani.
Daga can sai kawai ta durfafi ƙofar gidan, kafin ta isa sai ta hango waɗansu dakaru na daban ɗauke da waɗansu kejunan ƙarfe, kawai sai ta rakaɓe a wani waje tana hangen abin da ke faru, ba wasu ba ne a cikin kejin ba face su sarki Lazwar
Ko da ta ƙwarewa kejin kallo sai ta lura cewa ƙofofin kejin suna ɗauke da waɗansu irin kwaɗuna, waɗanda ke nuna cewa akwai mabudin su, wani tunani da ya faɗo wa yarinya Shuraiba shi ne.
Yanzu idan har ta ƙyale aka shige da su sarki Lazwar cikin gidan ba lallai ne suka kasance a raye ba, lallai dole ta yi dukkanin ƙoƙarin da ya dace don ceto rayuwar su kafin gari ya waye.
Gama tunanin hakan keda wuya sai Shuraiba ta hangi wani tsuntsu a saman ta yana yana wani irin kuka da ta ga ya durfafi wani ɓangare na musamman a wannan gida da za shige da su sarki Lazwar, cikin matuƙar farin ciki ta dunga bin bayan tsuntsun, ba tare da waɗannan dakaru sun ganta ba.
Koda isowar ta kusa da saitin inda dakarun suke a dai-dai lokacinne aka iso da su sarki Lazwar za a shiga da su cikin.
Sai kawai ta ga wannan tsuntsu ya buɗe bakinshi ya busa wa gaba ɗaya dakarun wani irin koren haske, kafin ka ce me sun ɓingire ƙasa suna sharar barci har da munshari, kuma koren hasken ya shiga cikin kejunan su sarki Lazwar, take suka narke suka zama ruwa, sarƙoƙi da aka ɗaure aljani Za'aratun-layal suka ɓace ɓat!.
Daga can sai tsuntsun ya rikiɗa izuwa wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarkin murida Zammar.
Nan fa sarki Lazwar, Shuraiba, sarkin yaƙi da bawa Shaiban suka cika

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads