Showing 3001 words to 6000 words out of 33454 words
Chapter 2 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt
ki na saduwa da mahaifiyarki da kuma ɗaukar fansa a kan sarki Ladiyas".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka kafa sansani,nan fa kuyangi suka shiga aikin dafa abin kalaci, bayan an kammala ne kowa ya kimtsa cikinshi aka huta sai aka sake ɗunguma wa aka hau bisa kan aljani Za'aratun-layal aka cigaba da tafiya tare da yarinya Shuraiba tare da damisar ta.
Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai sai a ka ga waɗansu zaratan dakarun aljanu ɗauke da waɗansu miyagun makamai da idanu basu taɓa ganin irin su ba, gaba ɗayan su suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya.
Nan fa tawagar sarki Lazwar suka firgice, wasu daga cikin su har suna sakin fitsari a wando saboda firgici, sarki Lazwar ne kaɗai bai razana ba shi ma a matuƙar firgice ya ke, kawai dai ƙarfin hali ne da ƙi faɗi irin ta hamshaƙan sarakai.
Shi kan shi Za'aratun-layal duk da kasancewar aljani sai da ya ɗimauce, domin iya tsawon rayuwarshi ko a labari bai taɓa ganin aljanu masu kwarjini da ban tsoro tamkar su ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na tsawon daƙiƙa latalin, sai daga can wani mummuna daga cikin aljanun wanda da alama shi ne shugaban su ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai ban tsoro yace "ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa ban zo gare ku tare da rundunar mayaƙa na ba domin na yaƙe ku ba sai don ku ba ni yarinya Shuraiba, mu kai ta ga sarkin mu mai girma Zammar, domin ya yanka ta ya sana'anta jininta don ya yi wa matayen mu maganin cutar da ke damun su ta makanta fiye da shekaru hamsin.
Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa matsawar ku ka yi taurin kai wajen damƙa Shuraiba a gare mu, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai ƙetare daƙiƙa goma a raye ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun aljanun sai sarki Lazwar ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce " ya ke wannan ƙaramin ƙwaro tabbas ƙaryar ka ta sha ƙarya, kuma ka yi ɓatan basira da ka ke tunanin cewa za ka iya raba mu da Shuraiba.
Ina mai umartar ka da ka janye waɗannan rafkanannun mayaƙan na ka ka koma izuwa ga matsoracin sarkin ku ga faɗa mashi cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne".
Kafin sarki Lazwar ya gama rufe bakinshi jikin aljanun ya kama tsuma yana kyarma tamkar za su ci babu.
Kawai sai su ka yi wani irin ihu da kururuwa mai firgitarwa suka ɗauki kan su.
Ko da ganin hakan sai su sarki suka zare makaman su, ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro da tashin hankali.
Kaico! haƙiƙa tashin hankali ba'a sa ma sa rana, kuma duk wanda ya taɓa fita filin yaƙi shi ne ya gama ganin tashin hankali.
Nan fa karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar dakarun aljanu da bil'adama ta cika dodon kunne, duk sa'adda makaman yaƙin ɓangarorin biyu suka haɗu sai ka ga walƙiya gami da tsawa tamkar za a ke ce da ruwan sama.
Ana fara wannan arbu ne sai wani abin mamaki ya faru domin kuwa yarinya shuraiba ta zame wa dakarun aljanun alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu, ya zamana cewa duk wajen da ta sanya a gaba sai ka ga aljanun na zubewa ƙasa matattu.
Duk wannan artabu da ake yi tsakanin su sarki Lazwar da dakarun aljanun sarki Zammar ya gani a cikin madubin tsafin shi, a lokacin da yake zaune a fadar koda yaga cewa an kashe gaba ɗaya tawagar shi sai ya cika da matuƙar baƙin cikin maral musaltuwa kuma ya takarkare ya kurma ihu.
A ɓangaren su sarki Lazwar kuwa bayan sun samu nasarar hallaka dakarun aljanun sarki Zammar, sai kowa ya shiga sanya magani a raunukan shi, amma aƙalla anyi asarar dakarun yaƙi mutum ɗari biyu da ashirin.
Bayan komai ya samu dai-daituwa ne ba tare da wani ɓata lokaci ba sai aka sake ɗunguma aka ci gaba da tafiya.
Ana fara wannan tafiya ne sai fira ta ɓarke tsakanin yarinya Shuraiba da aljani Za'aratun-layal,
A inda Shuraiba ta dubi Za'aratun-layal tayi gyaran murya ta ce " ya kai wannan dattijon aljani wai kuwa idan ba za ka damu ba nayi maka wata tambaya mana.
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya ce " faɗi tambayar ki ya ke Shuraiba
Shuraiba ta ce "wai kuwa a yanzu a cikin jinsin ku na aljanu akwai wanda yafi ka yawan shekaru?
Koda jin wannan tambaya sai Za'aratun-layal ya bushe da dariya har da kyakyatawa ya ce "a halin yanzu ni ne ɗan auta a cikin jinsin mu na aljanu a ƙalla zan kai shekaru dubu ɗari uku da haihuwa'' .
Cikin matuƙar mamaki shuraiba ta ce "ai kuwa in dai haka ne jinsin aljanu sun fi kowa daɗewa a duniya.
Za'aratun-layal ya ce "kwarai kuwa zancen ki dutse".
Shuraiba ta ce "amma kuwa mai yasa kuke yiwa bil'adama bauta alhalin kunfi su sanin halin da duniya ke ciki
Za'aratun-layal ya ce "Tabbas ke yarinya ce ba ki san komai game da halin duniya ba amma bari na ba ki hikayar sarauniya ABIDAT ta birnin Sin wata ƙila ki shaida batu na.
Za'aratun-layal ya yi gyaran murya sannan ya fara da cewa
BABI NA UKU
Wata mace 'yar kimanin shekaru ashirin da uku ɗauke tsohon ciki a jikinta sanye da tufafi na fatun dabbobi riga da wando.
Zaune take a bisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya take a cikin wani irin daji mai tattare da sarƙaƙiya, kwazazzabai gami da duwatsu.
Kallo ɗaya za ka yiwa mata ka fahimci cewa tana cikin mawuyacin hali.
Kaico! Tana cikin wannan hali ne sai ta ji alamun naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak sannan ta kama ta sauko ƙasa kawai sai ta taka da ƙyar ta durfafi kofar wani kogon dutse.
Kafin ta isa sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, a cikin wannan hali ta haife abin da ke cikin ta.
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance,
duk da cewar tana cikin halin laulayi, ba ta san sa'adda hawayen farin ciki suka kwaranyo daga idanuwanta ba, a dai-dai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki ɗaya, cikin hanzari ta ɗauki wani ice mai kaifi ta yanke cibiyar jaririyar.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ta hango waɗansu dakaru sun durfafo inda take a bisa dawakai.
Kafin tayi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame kibiyarshi ya harbe ta a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da raɗaɗin da ta ji bata san sa'adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta shiga tsala kuka.
Har badakaren ya sake yin shiri a karo na biyu da nufin ya sake harbin ta.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata murgujejiyar zakanya ta yi fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta daki badakaren a kirji.
Saboda matuƙar ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokin shi su ka yi sama tamkar an janye su da ƙungiya, sannan daga bisani suka faɗo ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin zakanyar da mayaƙan.
daga can sai zakanyar ta yi gurnani gami da hargagi sannan ta dako wawan tsalle izuwa kan mayaƙan.
Ko da ganin hakan sai dakarun su ka ɗaga makamansu suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa suka yi ɗauki kanta aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni, ban tsoro da ban al'ajabi.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi shi ne matattarar dukkan bala'i da musiba, kuma idan gwani ya haɗu da gwani JURIYA DA BAJINTA suka game waje guda, dole ne artabu ya zamo abin tsoro.
Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun, ya zamana cewa duk inda ta sanya gaba sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu, a inda za ka ga ta mako badakare faga kan dokinshi ta bishi ta turmushe.
A duk sa'adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙila haɗe da zame wa ta kaucewa saran, kafin badakare ya sake daga takobinshi zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya faratanta ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye, take zai sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu.
Kai wasu lokutan idan ta daki badakare a wuya sai ka ji wuyanshi ya ƙara ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba. Domin kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar ƙasa.
Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce wuya ko da magani babu daɗi, kuma wuya mai sa dole.
Hakan ce ta faru ga sauran dakarun, domin koda su ka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska domin GUDUN TSIRA da rayuka,
sai zakanyar ta dunga ƙure masu gudu tana make su suna faɗuwa ƙasa matattu. Kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakin su a ƙasa.
Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke kwance a ƙasa tana fitar da wani irin gurnani.
BABI NA HUƊU
Lokacin da aljani da aljani Za'aratun-layal ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin sai ya ja bakinshi ya yi shiru.
Cikin alamun matuƙar damuwa Shuraiba ta dube shi ta ce "haba ya masanin HIKAYAR DUNIYA mene ne ya sanya za ka yanke ba ni wannan labari mai matuƙar daɗi gami tsantsar tausayi, haƙiƙa na matsu naji a wane hali wannan mata da jaririyarta su ke ciki?
Kuma wace ce wannan zakanya da ta ceci rayuwar su? Shin mahaifiyar jaririyar ta na raye ko kuwa ta mutu sakamakon harbin kibiya da wannan badakare ya yi mata a gadon baya".
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya cewa da Shuraiba ''shin baki lura da inda muka iso ba ne? Leka izuwa kasa ki gani".
Da jin hakan sai ta sunkuya da kanta ƙasa aikuwa sai ta hangi wani irin baƙin daji mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Sarki Lazwar ya dubi aljani Za'aratun-layal ya ce ''shin me ka fahimta da wannan daji dake gaban mu?
Za'aratun-layal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ya ce " ya shugabana wannan daji dake gaban mu yana ɗauke da tsananin sanyi don haka dole ne kowannen ku ya sanya suturun kariya, sannan kuma dukkanin daji da ya kasance yana tattare da irin yanayin to dole ne a samu miyagun halittu masu shan jinin bil'adama da cin naman su, sai inda kizo ke saƙar shi ne bani da tabbacin waɗanne irin halittu ne.
Ko da jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai kowa yasha jinin jikinshi.
Cikin hanzari sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi ya ɗauko madubin tsafin shi da nufin gudanar da bincike, amma sai aljani Za'aratun-layal ya yi wuf da dakatar da shi ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa amfani da sihirin tsafi a irin wannan tafiya abu ne mai matuƙar haɗarin gaske domin baka da tabbacin cewa wanda za ka yi binciken bai fi ka karfin sihiri ba. Sannan shin ka manta cewa kowa a gidanshi sarki ne,
mafita ɗaya ce a gare mu kowanne ku yakasance cikin shiri tun da gashi yanzu la'asar ta riske mu, ba zamu ɗauki wani tsawon lokaci ba duhun magariba zai gaba ce a dajin kenan dole yaɗa zango cikin dajin dole ne domin mu kwana mu huce gajiyar dake tare da mu.
Da jin wannan batu sai kowa ya shiga sanyawa kanshi rigunan sanyi tun daga ƙasa har sama kuma kowa ya gyara riƙon makamin shi.
Za'aratun-layal ya yi ƙasa-ƙasa ta fuka-fukanshi sannu a hankali har aka sauka a bisa turba .
Sa'adda kowa ya yi arba da dajin sai tsoro ya kara kama shi.
Shi dai wannan daji yakasance gaba ɗayan shi yana ɗauke da waɗansu irin dogayen bishiyu masu rassa masu matuƙar kaifin tsiya masu tattare da sarƙaƙiya, babu wani waje da mutum zai ajiye kafarshi face ya taka dusar ƙanƙara ce, Babu abin da zai ƙara firgita mutum kuma ya jefa tsoro a zuciyarshi sai jin shiru da ya wanzu a dajin tamkar babu wani abu mai rai a cikin shi, kai hatta irin tsuntsaye haka a saman bishiyoyin babu su.
Nan fa aka fara tafiya a cikin ɗar ɗar domin shirin ko ta kwana, amma bisa mamaki sai ga shi an shafe tsawon rabin sa'a ba tare da an jiyo motsin wani abu mai cutarwa ba.
Al'amarin da ya sanya kowa ya fara sakin jikinshi kenan, ana cikin wannan tafiya ne tsinin reshen wata bishiya ya yanki bawa zafiyar a cinyarshi jini ya zuba a ƙasa.
Kawai sai a ka ji gaba ɗaya dajin ya kaure da wani irin gurnani mai ban tsoro ba shiri kowa ya tushe kunnuwanshi domin ƙarar na iya kurumtar da mutum.
Abin da su sarki Lazwar ba su sani ba shi ne zubar jini a dajin shine alamun da halittun ke gane cewa bil'adama ya shigo dajin.
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin zaratan muradai na fitowa daga kowacce kusurwa a dajin.
Muridan sun kasance masu matuƙar tsawo tamkar bishiyar kuka. Jikkunansu a mummurɗe suke tamkar duwatsu suna da rafkeken kai mai ɗauke da idanu ƙwaya ɗaya jal! Wanda ya kasance jajur tamkar garwashin wuta, fuskokin su munana ne babu kyawun gani, duk sa'adda su ka wangame bakunansu sai ka ga cewa wani irin yawun mai yauƙi na dalala, a hannayen su kuwa suna ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai na yaƙi da idanu basu taɓa gani ba, a ƙalla adadin muridan ya kai dubu uku da ɗoriya.
Lokacin da muridan suka kammala yiwa su sarki Lazwar ƙawanya, sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu,tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne muridan su ka yi wata kururuwa mai firgita dandazon mayaƙa a filin daga, su ka yi ɗauki izuwa kan su,
Koda ganin hakan sai su sarki Lazwar su ka yi kururuwa suka ruga izuwa kan muridan.
Ana haɗuwa aka yi muguwar KARON BATTA.
Wohoho! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sa mai rana, kuma ita wutar bala'i kafin ta zo ne ake guje mata, amma idan tazo kawai miƙa wuya ake yi a tare ta ko dai a mutu ko a yi rai.
Kaico! ana fara wannan arbu ne su sarki Lazwar suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin muridan sun zame masu tamkar GOBARAR ANNOBA.
Duk sa'adda ɗaya daga cikin ya kai wa su sarki Lazwar hari da makaminshi, idan su ka goce saran ya sauka akan bishiya sai ka ga ta rabe gida biyu ta faɗi ƙasa rikica za ta danne su.
Kafin ka ce me tuni muridan sun hallaka fiye da dakaru gami da kuyangi fiye da guda dubu.
Al'amarin da ya yi matuƙar figita su sarki Lazwar kenen, babban abin da ya fi dugunzuma hankalin su shi ne yadda muridan suka kasance masu matukar zafin nama, tamkar jikkunan su na amfani da wata na'ura dake sarrafa su.
Shi kan shi aljani Za'aratun-layal duk irin matuƙar karfin damtsen shi sai da ya zamana muridan sun zamto mashi ciwon idanu.
A ɓangaren yarinya shuraiba kuwa ana cikin wannan yaƙi ne wani daga cikin muridan ya kawo mata wani wawan sara da gatarinshi da nufin tsinke mata wuya,
Cikin wani irin baƙin zafin nama ta zille wa saran gatarin muridan ya shige cikin ƙarƙashin ƙasa.
Kafin muridin ya zare gatarin na shi Shuraiba ta ɗame bakanta ta harbe shi da kibiya a idon shi guda, take ya fashe jini ya dunga kwarara tamkar an buɗe kan fanfo, nan fa muridin ya faɗi kasa yana mai kwarara ihu yana birgima zuwa wani lokaci ya sheƙa barzahu komai na jikin shi ya dai na motsi.
Ko da yarinya Shuraiba ta ga wannan nasara da ta samu sai ta cika da matuƙar farin ciki, kuma a sannanne ta fahimci cewa ruhikan muridan suna cikin wannan idanu na su guda ɗaya dake tsakiyar goshin