Showing 24001 words to 27000 words out of 33454 words
Chapter 9 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt
tana yi maka?
Koda jin wannan tambaya sai Shamsal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu, daga can sai ya ɗago da kanshu ya dubi sarkin yaƙi ya ce "ya sarkin yaƙi ka yi sani cewa haƙiƙa ban fahimci wani abu ba game da kallon da khadijat ke yi min ba,
sai dai a lokacin da muka haɗa idanu na ji zuciyata ta buga da ƙarfi".
Da jin wannan batu sai sarkin yaƙi ya yi murmushi ya ce "ai kuwa dukkanin ku kun faɗa tarkon so ne ba ku sani ba, lallai nan da wani lokaci za ku cigaba da kasance a kogin SOYAYYA, amma wani hanzari ba gudu ba kai a yanayin da kake kallon khadijat kana ganin cewa halin talauci ne ya sanya ta yin aikatau a ƙarƙashin sarkin kasuwa Sha'aran?
Jiki na ba ni cewa tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare da ita.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai bawa Shamsal ya yi shiru karo na biyu sannan ya dube shi ya ce "tabbas maganar ka akwai ƙamshin gaskiya a ciki, domin a lokacin da muka sauka a rumfa su muna cin abinci na ga kallon da khadijat ke yiwa yaro Imran ya zarta misali. Bisa nazari da nayi haƙiƙa kallo ne mai ɗauke da tsantsar tausayi irin na 'yan uwa na jini. Amma dai ko ma dai mene ne komai zai bayyana domin masu iya magana na cewa, komai nisan jifa ƙasa zata faɗo, kuma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe.
Sarkin yaƙi ya ce "tabbas zancen ka dutse ya abokina";
Daga wannan furuci ne kowannen su ya yi shiru.
Wannan shi ne abin da ya faru da tsakanin sarkin yaƙi da bawa shamsal a masaukin su.
Al'amrin yarinya Shuraiba kuwa lokacin da gimbiya Lamrat ta ɗauke ta a cikin keken dokin ta suka durfafi hanyar da zata sada su da gidan sarauta, sai ya zamana cewa duk inda suka gifta a cikin birnin Istanbul sai dai ka ga jama'a na faɗuwa ƙasa suna gaisuwa tamkar za su yi mata sujjada.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har aka iso ƙofar gidan sarauta aka kunna kai izuwa ciki.
Bisa wani ƙasaitacce ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa a gidan sarautar, keken dokin ya sauke su gimbiya Lamrat, kai tsaye ta kutsa kai izuwa ciki, hannun riƙe da na yarinya shuraiba dakaru na take mata baya, ɓangaren cike yake da kuyangi, barori, hadimai da bayi suna ta kai komo suna ta hidima.
Nan fa ya zamana cewa yarinya Shuraiba ta zamto cikakkiyar 'yar ƙauye, ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni.
Wata kyakkyawar budurwa daga cikin kuyangin ta rugo izuwa inda suke ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa ga gimbiya sannan ta ɓuɗi baki cikin ladabi da girmama ta ce "ya shugabata shin me kike da bukata?
Gombiya Lamrat ta ce "ya ke Lazura ki yi sani cewa abi nda nake buƙata shi ne ki tafi da wannan yarinya a tsaftace mata jikinta a sanya mata tufafi masu kyawu, sannan a haɗa mana abin kalaci".
Ko da jin wannan umarni daga baƙin Lamrat sai kuyanga Lazura ta risina ta ce "an gama ya shugabata"
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta kama hannun yarinya Shuraiba ta shige da izuwa wani ɓangare na daban.
Sannan gimbiya ta shige izuwa turakarta dakaru masu tsaron lafiyar na biye da ita.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya Shuraiba da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas.
Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da ya isa izuwa masaukin su sai ya shiga kewaye ya watsa ruwa kuma ya ɗaura alwala, sannan ya gabar da Sallar magariba, bayan ya kammala ya yi godiya ga Ubangiji
Koda gama aiwatar da hakan sai ya ji an ƙwanƙwasa Ƙofar dakinshi.
Kawai ya tashi ya je ya buɗe domin ya ga wane ne, sai ya ga a she hadima khadijat ɗauke da abin kalaci da taceccen ruwan inibi bisa kofin azurfa.
Bayan ta ajiye a gaban shi sai ta samu waje ta zauna shi ma ya yi koyi da ita.
Khadijah ta dube shi ta ce "na samu wani labari dake yawo a gari akan abin da yafaru tsakanin ka da matsafi Shamrul, tabbas idan hakan ya tabbata dola ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana domin a kowane lokaci dakarun farmaki zasl su dunga kawo mana ziyara don ganin bayan ka".
Koda jin wannan batu daga bakin khadijat sai yaro Imran ya jinjina al'amarin a cikin ranshi
sannan ya dubi khadijat ya ce 'tabbas maganar ki gaskiya ce ya 'yar uwanta, kuma Ubangiji yana tare da mu a kodayaushe yanzu bari na yi kalaci sai ki dawo mu gabatar da sallar isha'i.
Da jin hakan saikhadijat ta miƙe tsaye ta juya ta fice daga ɗakin tana mai waigen Imran.
Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran lokacin da ya isa masaukin su.
BABI NA SHA HUƊU
Lokacin da dare ya tsala sai sarkin yaƙi Darusu ya ɗauki sarki Lazwar ya gurfanar da shi a gaban mai girma Ladiyas Ladiyas, a lokacin da ya ke zaune a cikin wata ƙasaitacciyar turaka. tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar turakar zai iya zamowa ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai komai ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan dole ne ya zamto bagidaje kuma cikekken ɗan kauye.
Bisa wata ƙasaitacciyar kejera wani mutum zaune a kai.
Mutumin ya kasance mai ƙirar sadaukai ya tara ƙwanji, kyakyawa ne na gaban kwatance kuma ma'abocin kwarjini da haiba, Sanye yake da tufafi riga da wando irin na hamshakan sarakai, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa.
Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Ladiyas ibn Fairuz. A wannan lokaci yana zaune yana hangen wani ɓangare na lambun shaƙatawar daga tagar turakar. Yana cin kayan marmari dake ajiye akan faranti na zinare bisa wani madaidaicin teburi na azurfa.
Koda bayyanar sarkin yaƙi Darusu sai ya ajiye tuffa dake hannunshu ya juya yana mai fuskantar shi. Gami da ƙarewa sarki Lazwar kallo a lokacin da suke durƙushe a ƙasa bisa gwiwoyinsu kuma sun sunkuiyar da kawunansu ƙasa.
Lokacin da sarki Lazwar ya ji shi durƙushe a gaban sarki Ladiyas sai baƙin ciki da takaici suka mamaye zuciyarshi, ya ji kamar ya ƙwalla ihu, wai yau a ce shi ne durƙusawa wani sarki saboda kawai neman biyan bukata, a matsayin shu na hamshaƙin sarki mai cike da taƙama da BAƘAR IZZA.
Tsawon daƙiƙa ana cikin wannan hali, sai daga bisani sarki Ladiyas ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya buɗi baki ya ce "ya kai dirkar birnina alamu sun nuna min baƙom bawan da ka zo da shi zai iya kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar gimbiya, amma sai dai ba zai yiwu na amince da hakan ba face ya shiga izuwa ɗakin duhu kuma ya samu nasarar cin jarabawar FARAUTAR RAI, lallai ne gobe da safe ka gabatar da shi a fada domin yi mashi jarabawar";
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki Ladiyas sai sarkin yaƙi darusi ya risina cikin ladabi ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya tashi tsaye ya juya ya fice daga turakar sarki Lazwar ya yi koyi da shi yana mai bin bayan shi, suka durfafi wani ɓangare daban.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da aka gabar da shi a gaban mai girma Ladiyas.
Al'amarin yarinya Shuraiba kuwa, lokacin da kuyangi suka kammala yai mata wanka da ado kuma suka ciyar da ita daddaɗan abinci, sai barci mai nauyi ya ɗauke ta.
Ba ta farka ba sai da dare ya tsala, a wannan lokaci gimbiya na zaune a kusa da ita bisa kan gadon da take kwance.
Sa'adda ta ga Shuraiba ta farka daga barci sai ta sanya hannayenta biyu tashe ta tsaye ta ja hannun ta izuwa wata ƙasaitacciyar kujera, da a gaban ta aka ajiye wani teburin azurfa mai ɗauke da nau'ikan abinci, bin sha da tanɗe-tanɗe.
Cikin matuƙar farin ciki gimbiya ta shiga ɗibar abinci da abin sha tana bawa Shuraiba a baki.
Nan take Shuraiba ta ji tamkar mahaifiyarta ce ke ciyar da ita, ita kuwa gimbiya farin cikin ta ba zai misaltu ba, bisa ganin cewa yau ita ce ke ciyar da 'yarta da hannunta da ta shafe tsawon shekaru tana kewar ta.
Bayan gimbiya ta kammala bata abincin, ita ma ta kimtsa cikinta, sai Shuraiba ta shiga bawa gimbiya labarin rayuwar ta, tun daga lokacin da sarki Ladiyas ya raba ta da mahaifiyarta ya mayar da ita baiwar shi, har izuwa sa'adda suka koma rayuwa a daji ita da mahaifinta, har kawo lokacin da ta haɗu da su sarki Lazwar, tun daga farko har ƙarshe ta zayyane wa gimbiya.
Sa'adda gimbiya ta ji wannan labari daga bakin yarinya Shuraiba ba ta san sa'adda ta rungume ta ba su duka biyun suna masu fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. sai daga bisa ne gimbiya ta janye jikinta daga na Shuraiba suka fuskantaci juna.
Kawai sai gimbiya ta sanya hannunta ta ya ye mayafin dake kanta fuskarta ta bayyana a fili ƙarara.
Sa'adda Shuraiba ta yi arba da fuskar gimbiya ba ta san sa'adda ta sake rungume ta ba a karo na biyu tana mai fashe da kukan murna.
Ba komai ne ya sanya ta hakan ba sai domin arba da ta yi da fuskar mahaifiyarta Lamrat,
tana mai cewa ashe zan sake ganin ki ya ummina ashe daman kina raye?
Daƙyar gimbiya Lamrat ta lallashe ta tayi shiru ta share mata hawaye, bayan ta samu nutsuwa ne sai ta dube ta cikin annashiwa da farin ciki ta ce "ya 'yata kuma farin zuciyata Haƙiƙa ina raye ban mutuwa, a kowace rana idan dare ya tsala sai nayi kukan baƙin ciki tare da roƙon abin bauta akan ya kare min ke kuma ya kawo min lokacin da zan ɗauki fansa akan BAKIN AZZALUMI da ya lalata rayuwar mu wato sarki Ladiyas. Sai gashi abin bauta ya dawo min dake cikin ƙoshin lafiya, ina so mu ɓoye sirrin dake tsakanin mu har izuwa lokacin da zamu ɗauki fansa.
Saboda hakan ma ya sanya na ɓoye miki fuskata a lokacin da muka haɗu a kasawu, domin matuƙar wani ya gane hakan har sarki ya samu labari tofa dukkan shirin mu ya tarwatse.
Sa'adda gimbiya ta zo dai-dai nan azancenta sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, tana mai cewa tabbas na aminta da ke ummina kuma za mu ɗauki fansa akan sarki Ladiyas.
Wannan shine abin da ya wakana tsananin yarinya Shuraiba da mahaifiyarta gimbiya Ramlat.
Al'amarin yaro Imran kuwa tun sa'adda ya yi bankwana da hadima Khadijat bayan sun sun tattauna akan abin da ya wakana tsakanin shi da matsafi Shamrul a cikin kasuwa, sai ya shiga kimtsa cikin shi bayan ya kammala ne Khadijat ta dawo gare shi suka gabatar da sallar Isha'i
Bayan kammala wa ne ya kwanta domin ya huce gajiyar dake tattare da shi.
Wannan shi ne ya faru da yaro Imran ma'abincin addinin Musulunci.
BABI NA SHA BIYAR
BIRNIN ISTANBUL
Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki Ladiyas ta cika ta batse da jama'a maza, mata yara da manya, duk inda mutun ya duba kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke, tamkar dandazon kiyasai.
Domin a yau ne aka samu labarin cewa za'a gudanar da gasar farautar rai, domin tsallake matakin ƙarshe da zai bawa sarki Lazwar damar kasance ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar gimbiya Lamrat.
Bayan jama'a sun hallara kuma sarki Ladiyas ya hakimce a bisa karagarshi ta mulki, sanye cikin ƙasaitacciyar shiga ta kece raini. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango sarkin yaƙi Darusu ya shigo izuwa fadar tare da dakaru sun tuso ƙeyar sarki Lazwar ɗaure a cikin sarari na baƙin ƙarfe.
Sa'adda jama'a suka yi arba da sarki Lazwar sai fadar ta kaure da shewa, sai da sarkin yaƙi ya ɗaga hannunshi sama sannan fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Sannan ya fuskanci mutane bayan ya yi gyaran murya sai ya buɗi baki ya ce ''ya ku jama'ar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa ba komai ne ya sanya muka tara ku anan ba sai domin a yau ne mai girma Ladiyas ya bayar da umarnin a saka jarumi Lazwar izuwa ɗakin duhu. Domin ya yi gwagwarmaya da miyagun halittun da suke ciki kuma idan ya samu nasarar tsallake matakin zai zamto daya cikin masu tsaron lafiyar mai martaba sarki.
Sa'adda sarkin yaƙi Darusu ya zo dai-dai nan a zancen shi, sai fadar ta sake kaurewa da shewa a karo na biyu, sai daga bisani ne sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru mutum hamsin suka wangame wata makekiyar kofar dake jikin bangon fadar, take wani makeken ɗaki ya bayyana mai ɗauke da waɗansu nau'ikan halittu dangin kuraye da zakuna gami da macizai.
Cikin hanzari waɗansu dakarun na daban suka buɗe ƙofar ɗakin, su ɗauki sarki Lazwar suka jefa shi izuwa ciki, kana suka kwance sarƙoƙin dake riƙe da halittun, suka mayar da ƙofar suka rufe ruf!
Sa'adda gimbiya Mashlira dake sanye cikin tufafin dakaru cikin ɓaddakama, ta ga an sanya masoyinta Lazwar a cikin ɗakin duhu sai takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyartq taji kamar ta ƙwallawa ƙara.
Amma sai ta danne saboda ta san cewa ba don komai masoyin nata ya shiga wannan hali ba sai domin kawai ya sadu da baiwa Sharifa da zata taimaka mashi wajen mallakar abubuwan da zasu warkar da shi daga sihirin da abokin gabar shi ya yi mashi, sai kawai ta shiga yi mashi fatan samun nasara, amma har yanzu hankalin ta a matuƙar tashe ya ke ainun.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Lazwar da halittun, kuraye biyu zakuna biyu sai waɗansu rin mucizai masu kawuna biyar.
Duk da kasancewar sarki Lazwar GWARZON MAYAƘI kuma GWARZON DUNIYA sai da hankalin shi ya dugunzuma ainun, domin iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin halittu masu kwarjini da ban tsoron tamkar su ba.
Tsawon daƙiƙa hamsin halittun na kewaye lazwar suna gurnani gami da hargagi mai matuƙar ban tsoro, sai daga bisani ne suka yi ɗauki kan shi suna kururuwa da ihu mai ɗimauta DANDAZON MAYAƘA suna masu kai mashi cizo da yakushi da faratansu, macizan na kai mashi sara gami da furzar da dafi daga bakunansu cikin wani irin baƙin zafin nama da ya ɗimauta hankali.
Shi kuwa sarki Lazwar ya wanzu ya na zillewa tare da kaucewa hare-haren halittun cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA. Sai da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi ba tare da ɗaya daga cikin su ya samu nasara ba, a dai-dai wannan lokaci ne halittun suka fara galabaitar da Lazwar ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanshi.
Ana cikin artabun ne wani daga cikin zakunan ya yakushe shi a cinyarshi ta hagu take ya yi mashi mugun rauni, sarki Lazwar ya kurma wawan ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da ya ji jini ya kwaranya.
Kafin ya sake yin wani yunƙuri wani maciji ya kafta mashi wawan sara a gadon bayanshi, saboda matuƙar azaba sai da sarki Lazwar ya faɗi a ƙas yana nishin wahala.
Nan fa masoyan sarki Lazwar suka cika da matuƙar baƙin ciki har waɗansu na zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da jarumin su ke ciki.
Shi kuwa Sarki Ladiyas dake hakimce bisa karagar mulkin sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta har da kyakyatawa nan fa sauran 'yan majalisa da fadawa suka yi koyi da shi.
Al'amarin da ya sanya zuciyar gimbiya Mashlira ta karaya kenan har kwalla ta cika mata idanu, bisa ganin halin da masoyinta ke ciki amma saboda tsoron kar wani ya gane halin da take ciki asirinta ya tunu sai ta yi sauri ta goge hawaye dake kan fuskarta, dai-dai lokacin ne ta hango bawa Shamsal da sarkin yaƙi a cikin jama'ar gari suka zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da shugabansu ya tsinci kanshi a ciki, da koyaushe zai iya rasa rayuwar shi.
Lokacin da sarki Lazwar ya tsinci kanshi a tsakanin RAYUWA DA HALAKA, kuma ya tabbatar da cewa haƙiƙa a koda yaushe zai iya sheƙawa barzahu, sai kawai ya fara amfani da zallar ƙarfin