Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 33454 words

Chapter 11 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt

Ads the beginning of article before Image

29 May 2024

501

Ads at the middle of Article

yaro imran
Cikin hanzari waɗansu likitoci suka shigo fadar ɗauke da kayan aiki suka shiga duba lafiye yarinya Shuraiba, gimbiya Lamrat,da sarki Lazwar.
Sannan yaro Imran ya ruga izuwa inda hadima Khadijat take suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa sake saduwa da juna da suka tsawon shekaru.
Daga bisani yaro Imran ya janye jikinshi daga na 'yar uwarshi Sharifa.
Ya juya ya fuskanci jama'a sannan ya buɗi baki ya ce "ya ku al'ummar wannan birni mai albarka haƙiƙa na tabbatar da cewa a halin yanzu zukatanku sun gamsu cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah mai kowa mai komai.
Saboda haka yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba yaro Imran ya faɗi kalmar shahada, take ɗaruruwan jama'ar dake fadar suka maimaita.
Sautin muryoyinsu ya cika fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin baki ɗaya.
Bisa mamaki sai Imran da hadima Khadijat suka ji sarki Lazwar da sarkin yaƙinshi haɗe da bawa Shamsal tare gimbiya Mashlira sun amsa kalamar shahadar.
Nan fa suka cika da al'ajabi, sarki Lazwar ya tako da ƙafafuwanshi izuwa inda imran da Khadijat suke ya dubi Khadijat cikin girmamawa ya ce "ya ke Sharifat Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, na zo wannan birni neman ki, ashe kina tare da ni ban sani ba, yanzu ga shi na karɓi addinin Musulunci shin ina makomar tafiya ta izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Durwazu ya yi min, na karɓi Musulunci ne domin yadda a zuciyata, na samu tabbacin ne a lokacin da nake fafata yaƙi da miyagun halittun dake cikin ɗakin duhu, inda dukkan wata dubara ta ƙwace min na nemi taimakon Ubangijin imran".
Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai Sharifa, yaro Imran da sauran jama'a suka cika da matuƙar mamaki.
Sharifat ta ce ''ya kai wannan sarki mai daraja ka yi sani cewa ai shi addinin Musulunci yana shafe duk abin da ya tuve, saboda haka a halin yanzu sihirin da sarki Durwazu ya yi maka ya karye.
Babu buƙatar sai na taimaka maka wajen mallako abubuwan da za su warkar da kai daga sihirin, domin abubuwan da za'a mallako dukkanin su na tsafi ne.
A halin yanzu zaka iya kusantar kowace irin 'ya mace kuma har ka samu haihuwa ka yarda Ubangijin musulunci kawai a koda yaushe";
Koda jin wannan batu daga bakin Sharifa wato sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar farin ciki wanda bai taɓa yin kamar shi ba.
Daga wannan ne aka ɗunguma izuwa gidan sarauta domin kowa ya huce gajiyar dake tattare da shi.
A cikin wannan dare ne hirar soyayya ta ɓarke tsakanin sarki Lazwar da gimbiya Mashlira 'yar shugaban maridai, yaro Imran da yarinya Shuraiba, Sharifat da bawa Shamsal.
Kuma a wannan dare ne akayi shelar naɗin sarautar yaro Imran da wazirinshi Shamsal.
kafin wayewar gari ciki da wajen birnin Istanbul ya cika ya batse da jama'a baƙin sarakuna daga kowa ce nahiya da 'yan kasuwa.
Tun lokacin da alfijir ya keto bayan an gabatar da sallar asuba sai jama'a suka yi tsinke a fadar maza da mata yara da manya.
Sarakuna da manyan baƙi an ware masu wajen zaman su daban, haka ma na talakawa, komai dai an yi shi bisa tsari.
Sarkin fadar birnin Istanbul wani dattijo ya tashi ya gabatar da jawabin maraba ga mahalar ta taro. Sannan ma'ajin sarautar ya gabato da kayan sarauta da suka haɗar da alkyabba, rawani, kwagiri, takalmi da sauaran su.
Sarkin fada Huzaifa ya ɗauki kayan ya shiga sanya wa yaro Imran a jikin shi, bayan ya kammala ne sai ya umarci yaro Imran ya je ya zauna bisa karagar mulki ya hakimce, nan fa tsananin kyawun surar Imran ya fito ƙarara yarinya shuraiba kuwa sai ta dunga satar kallon shi tana yi mashi kallo mai nuna alamun tsantsar so da ƙauna.
Nan take jama'ar fadar suka yi mubaya'a a gare shi, daga bisani kuma sai aka shiga shagalin ɗaurin aure mutum shida sarki Imran da yarinya Shuraiba baiwa Sharifa da bawa Shamsal, sarki Lazwar da gimbiya Mashlira.
A wannan rana anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin kamar shi ba tsawon kafuwar birnin Istanbul.
Bayan an kammala ciye-ciye da tanɗe-tande, kowa ya cika cikinshi sai sarakunan da suka halararci bikin naɗin sarautar suka dunga zuwa, gaban sarki Imran suna karɓar KALMAR SHAHADA tare da jama'arsu, haƙiƙa farin ciki ya cika zuciyar kowa.
Bayan tarewar angwaye uku sarki Imran, shamsal da sarki Lazwar.
Sai sarki Imran ya umarci aljani Hadimul-kahiri ya ɗauki sarki Lazwar da amaryarshi gimbiya Mashlira da sarkin yaƙi haɗe da aljani Za'aratul-layal domin ya kai su izuwa birnin ZAWATUL-IFDAR, amma sai da aka fara zuwa ta birnin su gimbiya Mashlira aka musuluntar da sarkin maridai da mutanenshi kuma aka karya sihirin tsafin da aka yi masu suka dawo ainahin siffar su irin ta bil'adama suka daina cin naman bil'adama bisa taimakon Ubangijin halitta.
An yi shagalin farin cikin dawowar yar sarkin muridai gimbiya mashlira. Sai da aka shafe mako ɗaya sannan aka sake ɗungumawa aka durfafi birnin Zawatul-ifdal, amma sai aka bar sarkin yaƙi imhal domin ya cigaba da bayar da ilimin addini ga jama'ar birnin, kuma sarkin maridai ya naɗashi wazirinshi.
Lokacin da aka isa birnin Zawatul-ifdal sai sarki lazwar ya cika da matuƙar farin ciki, bisa jin labarin abin da ya faru tsakanin magajin gari Yasiran da amarya Munirat wacce a halin yanzu ita ce ke riƙe da karagar mulkin birnin.
Jama'a sunyi farin cikin dawowar sarki Lazwar, ba tare da ɓata lokaci ba aka sake ɗaura auren amarya Nunirat da sarki Lazwar, sakamakon mutuwar angonta, amma da ƙyar da siɗin goshi sarki Lazwar ya shawo kan gimbiya Mashlira ta amince aka ɗaura auren. Sai aljani Za'aratul-layal da Hadimul-kahiri suka koma izuwa birnin Istanbul.
Sannu-sannu bayan mako ashirin sai aka wayi gari matayen sarki Lazwar Munirat da Mashlira suna ɗauke da juna biyu.
Farin ciki a wajen sarki Lazwar kuwa kamar ya zautu, ya dinga rabon dukiya da suturu na alfarma.
Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye duniya baki ɗaya zaman lafiya ya wanzu, zalunci da bautar gumaka suka rushe baki ɗaya.




Ƙarshe


Alhamdulillah


Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.


MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071






FATAUCIN BAYI
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI


Lokacin da su jaruma Nabihat suka iso izuwa bakin tanatin, sai Nabihat ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa cikin tantin, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi.
kawai sai suka cire tufafin dakarun suka maye da na sannan suka rufe fusakunsu da hulunan ƙarfe.
Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe ruf.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso izuwa inda wani sadauki yake.
Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan karen daɗi haka?
Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba.
Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu. Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa.
Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari.
A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata maɓuya a cikin jirgin suka laɓe.
A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa sai ya yi arba da masu dafa abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su.
Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana mai ƙwallawa sauran dakarun kira.
Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin dakawa dakarun tsawa.
A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci.
Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu
Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban al'ajabi.
Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da kururuwar mazaje.
Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA.
Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare.
Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta.
Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu.
Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta girɓawa sharkar naushi a fuska.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa, yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa.
Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa.
A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka hallaka su baki ɗaya.
Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya
Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku, kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu.
Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita".
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma izuwa birnin su.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da Lazimat ta sare mashi na zubar da jini.
Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA.
Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci.
Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi.
Ana cikin wannan hali ne
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa,
Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya, kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici.
Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN ƘARE DANGI.
Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads