Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 33454 words

Chapter 4 - Sarautar Mutuwa by Mansur Usman Sufi complete .txt

Ads the beginning of article before Image

29 May 2024

495

Ads at the middle of Article

da matuƙar al'ajabi.
Cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karen daɗi tamkar ana busa sarewa, gimbiya Mashlira ta dube su su duka huɗun ta ce "yanzu ba mu da lokaci da zamu tattauna domin a kodayaushe mahaifina zai iya biyo sahun mu, matsawar ya riske mu ɗayan mu ba zai tsira da rayuwar shi ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin Mushlaira sai sarki lazwar ya umarci aljani Za'aratun-layal ya ɗebe su baki ɗaya, zuciyarsu cike da matuƙar farin ciki bisa ganin cewa yarinya shuraiba ta na raye cikin koshin lafiya, kuma gimbiya Mashlira ta ce ci rayuwar su.
A dai-dai wannan lokaci ne sarki Zammar da tawagarshi suka bayyana a wajen, koda ya ga dakarun kurku kwance suna sharar barci kuma babu su Lazwar da 'yarshi Mashlira, sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu, ihun shi ya haddasa wata girgizar ƙasa da ta sanya gine-gine suka dunga rushewa, nan fa birnin ya kaure da gujegujen jama'a domin TSIRA DA RAYUKA.
Sai da sarki ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai ta gidaje suka dai na rushewa mutane suka daina hallaka.
Kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu, yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi hoton aljani Za'aratun-layal ya bayyana a kai, yana tsala azababban gudu ɗauke da su sarki Lazwar da 'yarshi Mashlira.
Koda ganin hakan sai takaici ya ƙara turnuƙe zuciyarshi har ƙwallar baƙin ciki ta zubo mashi, kawai sai ya runtse idanuwanshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafin na daban, koda kammala hakan sai ga wata irin halitta ta ketowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa.
Halittar ta nunka aljani Za'aratun-layal a girma, muni, da kwarjini gami da cika idanu.
Ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar,
Durusul-fannar ya faɗi ƙasa ya yi sujjada ga sarki zammar,
Zammar ya du be shi fuska a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta kan ta.
Cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce "ya kai uban hatsabibai kuma kakan kangararru na duniya ka yi sani cewa, fiye da shekaru dubu ɗaya da ɗoriya rabon da na kira ka domin aiwatar da wani aiki sai yau, to ina so ka yi sani cewa na kirowa ka ne domin ka bi sahun su 'yata Mashlira da ta ci amana ta ta kuɓutar da waɗansu bil'adama da muka farauto.
Ina so ka kawo min su a raye cikin ƙoshin lafiya domin ni da kai na zanyi hukunci,
Koda sarki Zammar ya zo nan zancen shi, sai Durusul-fannar ya sake yin sujjada karo na biyu ga sarki Zammar cikin wata irin murya mai kama da saukar aradu ya ce "an gama ya sarkin sarakai, yin biyayya a gare ka shi ne ibada ta".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya ya yunƙura izuwa sama domin ya bi sahun su aljani Za'aratun-layal, take ya shiga keta gajimare cikin wani irin masifaffan gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Wannan shi ne abin da ya faru a acan birnin muridai.




BABI NA BIYAR




Al'amarin su sarki Lazwar kuwa lokacin da suka ci gaba da gudu a bisa kan aljani Za'aratun-layal, bayan gimbiya Mashlira ta ceci rayuwar su daga hannun mahaifinta, sai suka ci gaba da tafiya a sararin samaniya cikin hanzari.
Ana fara wannan tafiya ne sarki Lazwar ya matsa kusa da Mashlira ya ce" ya ke wannan 'yar sarki ma'abociyar tausayi da jin ƙai, haƙiƙa ba mu san da wane irin baki zamu gode miki ba bisa ceton rayuwar mu da kika yi.
Sai dai abin da muka kasa fahimta ni da abokan tafiya ta shi ne, mene ne dalilin da ya sanya kika biyo mu bayan cewa baki san daga wata duniya muke ba, kuma baki san ina zamuje ba.
Ko da jin wannan batu sai Mashlira ta yi wani ƙayataccen murmushi da ya kara tona asirin tsantsar kyawun surar ta har fararen haƙoranta suka bayyana farare ƙal! Cikin daddaɗar murya ta ce "ya kai wannan sarki ka yi sani cewa kafin na fito daga cikin gidan sarautar birnin mu sai da na gudanar da bincike bisa halarar tsafina, na gano dukkan labarin ku da duk abin da ya baro da ku daga biranan ku, na nemo abubuwan da su warkar da kai daga sihirin da abokin gabar ka sarki Darwazu ya yi maka.
Bakomai ne ya sanya na biyo ku domin gudanar da wannan tafiya ba, duk kuwa da irin haɗurran dake tattare da ita sai domin mahaifina ya gano cewa nan gaba zan samu ɗaukaka mai yawa wacce sai labari na ya yaɗu a duniya, bisa binciken da na gudanar a yau na gano cewa ta silar ku zan samu wannan ɗaukaka.
Sannan kuma zan cika burina na samowa jama'ar birninmu maganin da zai warkar da su, su dawo ainahin surar su ta bil'adama. Da yake duk wannan tattaunawa da ake yi tsakanin sarki Lazwar da Mashlira kowa yana saurare, ya yin da aka ji abin da Mashlira ta furta sai kowa ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi.
Sarki Lazwar ya dube ta cike da matuƙar mamaki ya ce "ya sarauniyar kyawawa shin dama jama'ar birninku bil'adama ne kamar mu ba muridai ba?
Ko da jin wannan tambaya sai idanun Mashlira suka ciko da kwalla, fuskarta cike da matuƙar damuwa ta ce "Bbsa labarin da mahaifina ya ba ni ya tabbatar min da hakan, kuma ya sanar dani maganin da zai warkar da su daga wannan annoba, akwai buƙatar na sanar da ku labarina a taƙaice.


BABI NA SHIDA




A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe lokacin da jahilci ya yi katutu a zukatan bil'adama, ƙarfi da jarumtaka suka zamto jari, kuma ake yin gashin dankali wato babba a sama ƙarami a ƙasa
A wannan lokaci anyi wata nahiya mai ɗauke da manyan birane guda biyar,
biranen na ƙarƙashin mulkin wani gawurtaccen azzalumin matsafi da ake yiwa laƙabi da Sahibul-ukub
Matsafi Sahibul-ukub yakasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa, domin an ce a filin yaƙi yana iya shafe tsawon kwanaki biyu yana yaƙi ba tare da ya ci ko ya sha ba.
Idan ya je farauta daji kuwa yana iya saɓo giwa a kafaɗarshi, ya yi gudun sa'a ɗaya da ita ba tare da ya gaji ba, komai girman bishiya idan ya naushe ta da hannunshi sai ta jijjigo har saiwarta sannan ta faɗi ƙasa,
Kai wasu lokutan ma idan zai kai farmaki wani birni ko alkarya, shi kaɗai yake fita ya yaƙi birnin a dare ɗaya ya farauto bayi, da dukiya mai da ganima mai tarin yawa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya duk biranen da suka ji labarin matsafi Sahibul-ukub zai kawo farmaki, ko da dai su fita su tafi izuwa gare shi su yi MUBAYA'A kafin ya zo, ko kuma su tattare ina-su-ina-su su fice daga birnin su yi hijira izuwa wata nahiyar daban.
Batun ƙarfin sihirin tsafi kuwa, masu bincike da hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu babu matsafi kamarshi, zaluncin shi kuwa ya huce yadda muke tsammani domin saboda matuƙar zaluncin shi yasa aka gina mashi kurkukun ƙarƙashin ƙasa da ake bautar da mutane da aljanu.
A rayuwar matsafi Sahibul-ukub bai taɓa yin aure ba ballantana a ce yana da magaji da zai maye gurbin karagarshi.
wata rana yana zaune a turakar shi sai kawai a ka ji ya taƙarƙare ya ƙwala ihu sannan daga bisani ya bushe da dariya mugunta, bakomai ne ya sanya matsafi sahibul-ukub ihu da dariyar ba face wani labari da sarki yaƙin sa ya kawo mashi, na wani ɓoyayyen birni mai tarin arzikin noma kiwo, da ma'adanan ƙarƙashin kasa.
Birnin Madinatul-Adfal na yamma maso arewacin birnin Sin.
Sarkin da ke mulkin birnin yakasance GWARZON DUNIYA mai karfi na Allah ya isa, yana shugabantar jama'ar shi bisa adalci da matuƙar tausaya wa, bisa wannan dalili ne ya sanya kullum tattalin arzikin birnin yake ƙara haɓaka.
Wani abu da matsafi Sahibul-ukub ya gani bisa halarar tsafinshi shi ne, matuƙar ya mallaki birnin zai zamo mashahurin attajirin da babu kamarshi a faɗin duniya, kuma a wannan birni zai gina fadar da take babu kamar ta a duniya baki ɗaya.
Kasancewar birnin yana ɗauke da dukkanin wani yanayi mai daɗi da bil'adama ke bukata.
Bayan Sahibul-ukub ya kammala dariyar mugunta, sai ya juya ya dubi sarkin yaƙin da ke durƙushe a gaban shi tamkar zai yi mashi sujjada, cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da taƙama gami da BAKAR IZZA ya ce ''ya kai dirkar birnin Jauraful-harbat, haƙiƙa ba ka taɓa zuwa mii da labari mai daɗi kamar wannan ba, Amma lamarin ɓoyayyen birnin ya ba ni mamaki, da har na gasa gano shu bisa halarar tsafi na, amma ba abin mamaki bane domin masu iya magana na cewa shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka ba za ka iya ɗebe abin da ke cikin shi ba sai dai ka ɗebi iya gwargwadon ka.
Yanzu abin da nake so shine a tanadar min dakarun yaƙi guda dubu hamsin, tare da magina dubu goma da kuyangi dubu, bayi da barori, a daren yau ina so alfijir ɗin a subahin gobe ya keto min a birnin madinatul-Adfal, domin wannan yaƙi na musamman ne a gare ni, ko da jin wannan batu sai sarkin yaƙi Shamsal ya risina ga matsafi Sahibul-ukub ya ce "an gama ya shugaba na".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga turakar, domin aiwatar da umarnin da akayi mashi.
A can birnin Madinatul-Adfal kuwa jama'a na gudanar da ayyukan su cikin lumana, masu saye da siyarwa na yi masu noma da kiwo na yi, sauran yara kuwa na wasanni a tsakanin su cikin nishaɗi, hakan kuwa ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya kamar da bakin ƙwarya ƙasa ta kwanta kuma gari ya yi daɗi korayen tsirrai sunyi luɓ-luɓ gwanin ban sha'awa,
A na cikin wannan hali ne sai ka ga gari ya yi duhu dumɗum! Tamakar dare biyu ya haɗu waje guda, kai ka ce hadari ne ya gangamo zaa ɓarke da da ruwan sama, nan fa gari ya kaure da gujegujen jama'a gami da ifice-ifice yara da manya mata da maza.
Ba wani abu ba ne ya haddasa wannan duhu ba face bayyanar rundunar matsafi Sahibul-ukub da ta iso birnin
Sa'adda gimbiya Mashlira yar sarkin muridai Zammar ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta yi shiru, bakomai ne yasanya ta yi hakan ba, sai bisa ganin wata mummunar halitta da ta bayyana a gaban su, ba wani ba ne wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar da mahaifinta ya turo domin ya farauto su.
Ko da bayyanar aljani Durusul-fannar sai cikin kowa ya ɗuru ruwa, hatta shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani.
Wannan fa shine masu iya magana ke cewa GABA DA GABANTA wai aljani ya taka wuta, kafin ɗaya daga cikin su ya yi wani yunƙuri aljani Durusul-fannar ya buda wata irin iska daga bakinshi, nan take su sarki Lazwar suka kama barci mai nauyi, kawai sai ya damƙe su ya makale su ajikin fuka-fukanshi tamkar ya ɗauko 'yan tsaki, ya juya izuwa hanyar da za ta mayar da shi izuwa birnin muridai.
Tofa ana dara ga dare ya yi.
Lokacin da aljani Durusul-fannar ya tsala da azababban gudu, ɗauke da su gimbiya Mashlira, sai ya ci gaba da keta gajimare cikin gudun huce sa'a domin ya isa ga sarki Zammar,
yana cikin wannan gudu ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya yi kiciɓus da wani aljani agaban shi, Aljanin ya kasance ma'abincin kyawun sura fari sol.
Zaune a bisa kanshi wani kyakkyawan yaro ne mai kimanin shekaru goma sha shida, wanda da kaɗan ya ɗara yarinya Shuraiba.
Yaron yana sanye cikin fararen tufafi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayanshi yana rataye da wata sharbebiyar takobi.
Kallo ɗaya zaka yiwa yaron ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na gaban kwatance domin inda za'a ajiye shi daf da gimbiya Mashlira ba za ka iya tantance wane ne yafi kyawu a tsakanin su ba.
Sa'adda Durusul-fannar ya yi arba da su yaji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya ɗarsu a cikin ta.
A karo na farko a rayuwar shi ya ji wata halitta ta razana shi, nan fa ya cika da matuƙar mamaki ainun.
Abu na farko da ya bashi mamaki shine duka aljanin bai kama ƙafarshi a girman jiki da surar jarumtaka ba, kuma wanda ke zaune a kanshi bil'adama ne yaro matashi.
Kawai sai ya yi ƙarfin hali ya dakawa masu tsawon cikin matuƙar fushi ya dube su ya ce ''ya ku waɗannan ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin tunani ya sanya za ku tare min hanya? Ba ku da labarin cewa nine GOBARAR ANNOBA mai tada hankalin duniya, ANNOBA ƊARI mai shayar da jarumai TASKAR AZABA?
Kafin aljani Durusul-fannar ya gama rufe bakinshi kyakkyawan yaron ya tari numfashin sa yana mai cewa ''kaicon ka ya kai tsohon mushriki, ka yi sani cewa yau ƙarshen ka ya zo, kai maza ka miƙo min su sarki Lazwar da ka ɗauko su domin ka kaiwa sarki Zammar ya hallaka su.
Sannan kuma ina kira a gare ka ka bayar da gaskiya da Ubangijin da ya halicci duniya da abin da ke cikin ta";
Ko da jin wannan batu sai zuciyar aljani Durusul-fannar ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ya sake dakawa yaron tsawa a karo na biyu, tabbas yaro man kaza, bai san wuta ba sai ta narka shi, kuma haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka, tsautsayin akuya gai da kura, rabon da wata halitta da ɓata min rai yau shekara dubu hamsin, lallai daga kan ku hakan ba zai sake faruwa ba, domin zan koyar da duniya darasi akan ku".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya yi ɗauki kan su yana ihu da kururuwa mai firgitarwa, tamkar zai tashi duniya baki ɗaya,
Ko da ganin hakan sai kyakyawan yaron ya buɗe bakinshi yana mai karanta waɗansu kalmomi, sannan ya zare takobinshi a gadon bayanshi ya tunkari Durusul-fannar suka yi KARON BATTA.
Kaico! Haƙiƙa KARON MAZA babu daɗi, kuma tashin hankali ba a sa ka mai rana, nan fa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro gami da ban al'ajabi, nan fa yazamana cewa, abin nan da masu iya magana ke faɗi ya fara tabbata, wato ɗan hakin da ka raina shi ne ke tsoka ne maka idanu.
Sai ga shi yaron ya zamto wa Durusul-fannar ƙadangaren bakin tulu kuma alaƙaƙai,
Duka sa'adda da ya kai mashi duka da hannayenshi sai yaron ya zille gami mayar da martani cikin zafin nama, idan takobinshi ta taɓa jikin Durusu sai ka ji ya kurma wawan ihu.
Bakomai ne ya sanya shi ihun ba face tsananin zafi da raɗaɗin da yake ji tamkar ana ƙona shi da wuta.
Abin da Durusul-fannar bai sani ba shi ne takobin yaron na ɗauke da sirri na musamman, ana cikin wannan artabu ne yaron ya kaiwa Durusul-fannar wawan sara a kafaɗarshi, cikin sa'a ya yanke shi, take jikinshi ya kama da wuta, nan fa aljani Durusul-fannar ya kama ihu da kururuwar neman taimako.
Indai ace mutum ya na tsaye a wannan waje yana kallon abinda ke faruwa, dola ne ya yi wa Allah godiya bisa ganin cewa mushriki maƙiyin Allah zai yi mutuwar wulakanci.
Koda kyakyawan yaron ya fahimci cewa wutar zata iya kona su sarki Lazwar da har yanzu su ke cikin halin barci.
Sai kawai ya ya yiwa hadimin shi umarni da ya kai masu ɗauki.
Cikin zafin nama aljani ya miƙa hannayenshi biyu ya ɗauko sarki Lazwar, Mashlira, shuraiba, aljani Za'aratun-layal, sarkin yaƙi da bawa Shamsal, ya ajiye su bisa gadon bayanshi, sannan ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luu!. Ya sauka a turba a dai-dai lokacin da aljani Durusul-fannar ya ƙone kurmus tokar gawarshi ta sheƙe cikin iska.
Ya yin da ya sauka a turba sai ya sauke su sarki Lazwar a ƙasa.
Yaron ya koma gefe guda ya share ƙasa yana mai fuskantar alƙibila ya fara gudanar da ibadar shi irin ta ma'abota addinin Musulunci, kawai sai aljanin ya tsaya a gefen shi a yana mai koyi da shi, Sarki Lazwar ne ya fara farkawa daga barcin, sannan gimbiya Mashlira, bawa Shamsal, sarkin yaƙi, yarinya Shuraiba aljani Za'aratun-layal a ƙarshe.
Lokacin da kowa ya wartsake ya dawo cikin hayyacin shi, suka arba da wannan kyakkyawan yaro da hadimin shi suna gudanar da Sallah,
sai kowa ya yi turus! Cike da matuƙar mamaki gami da al'ajabi.
Abu na farko daya bawa ko mamaki shi ne yadda yaron ke gudanar da ibadar cikin tsafta da tsari mai ban sha'awa, sannan ya aka yi su ka tsira da rayuwar su? Kuma ina aljani Durusul-fannar ya ke?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenen, kawai sai suka zuba idanu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads