Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 41234 words

Chapter 3 - ALIYU HAIDAR Book Complete by kausar.txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

473

Ads at the middle of Article

hajiya salma.


"Ke mai ya kawoki gidana"
Cikin muryan tausayi ta hau yin magana
"Alhj nasamu labarin yau aliyu zai tafie makaranta shine nazo in ganshi muyi sallama"


Da gudu aliyu yay inda mame, ma'aikatan gidan kuwa har zuwa ummi sunji dad'in wannan gamuwa tasu.
Rungumeshi tai sosai tana hawaye
"Aliyu Allah yay maka albarka, kayi karatu banda wasa kaji ko"?
Murmushi yay ya k'ara laqamie mame, mame kada ki barni dan Allah"
"Ina tare dakai d'ana a koda yaushe, bazan tab'a barinka ba"


Zubairu!!! Alhj ya hau kiranshi
"Na'am alhj"
Yi maza ka karbomin aliyu saboda zamuyi late idan muka tsaya nan
Da hanzari zubairu ya matsa kusa dasu
"Aliyu alhj na kiranka"
Kara shigewa jikin mame yay.
Yayinda zubairu ya kasance baida zabie illah yayi kaman yanda alhj yace
Hannu yasa ya fara jan aliyu dga jikin mame


Kuka aliyu ya hau yi tare da kiran sunanta
"Mame! Mame dan Allah kice ya kyaleni, bana son tafiya ni gurinki nakeson zama"
Kuka aliyu ya hauyi har idanunshi sun kada sunyi jajir


"Mame! Dan Allah"
Ga aliyu a hannun zubairu ya rikeshi, yana kucce2 a hannunshi, iya karfinshi ya dage yana kiran sunan mame


"Mame kuka takeyi sosai sboda tausayin d'anta
"Aliyu!!!""
Ta kira sunanshi ta fashe da kuka.
Da karfi ya su6uce ga rikon da zubairu yay masa ya qara rugawa da gudu yay gurin mame ya rungumeta
"Mame! Pls ki daukeni mu tafie, mame pls"😭
Kanshi ta shafa itama din kukan takeyi..
Ganin hakan yasa alhj ya tako da kanshi ya rika hannun aliyu tare da janshi, ga kasa . Aliyu y fara bubbuga kafafunshi a k'asa yana kiran mame
"Mame!!!😭
kuka aliyu keyi sosai, har sun kai kopar fita falon ya kara ruguwa da gudu ya k'ara kankamie mame yana kuka yana kiran sunanta..
A falon bbu wnda bai zubar da hawaye ba saboda tsabar tausayin aliyu, illah nana data kasance tsaye ta dora hannayenta akan matar takalar stage din.


Abbi hasala yay da zuciya ya dirkako kan aliyu yaja hannunshi, ya dga hannu ya wanka masa mari mai kyau, wanda yasa aliyu natuswa lokacin da bai zta ba.
Hannu mutanen falon suka saa suka rike baki, ganin abbi bai tab'a daukar hannu ya dorawa aliyu ba sea yau.


B'acin rana kenan😕


Nikam ido na zaro ina mamakin wannan al'amari wea meye dalilin yin hakan na raba uwa da danta da kuma wannan tsanar data shiga tskanin alhj shuraihu da kuma hajiya salma...
Uwar d'ansa tilo namiji wadda kuma a cikin so ya aureta, tabbas akuy wata a qasa😱...
[8/1, 8:14 AM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((15))


©Kausar M Hassan


Idanu Aliyu ya d'ago sukai ido 2 da abbi, abbi yaja hannunshi suka kama hanyar fitah dga gidan, suna tafiya aliyu na waigen baya yana kallon mame tana hawaye tanai masa bye2, yyinda nana keta faman yin dariar jin dad'i, haka har suka bar gidan suka shiga motah.
Kawu musa ganin yanda fuskokinsu sukai yasa bayyi magana ba, kawea yaja motan sea airport.
Suna isa kuwah, yaron abokin abbi na zuwah, aliyu shiru yay baice da kowa komai ba, abbi na kallonshi ya bashi tausayi yama rasa da wanne baki zayyi rarrashin shi, hakan yasa ya barshi yayta huci


Abbi ka taba mana lion fa


Haka aka kirasu suka tashi kowa yaja jakarshi, da kuma jakar goyanshi suka shigah jirgi suka zazzaunah, aliyu da zayyanu guri d'aya suka zaunah. Zaiyyanu yay ta magana, aliyu yay banza dashi haka har jirginsu ya tashi dga Nigeria zuwa saudi Arabia...


Wani irin abu aliyu ke ji a cikin ranshi, baqin cikin dake ranshi yay masa yawa fiye da tsammani, har ynxn fuskan abbi yake kallo ynda ya rabashi da mame, mahaifiyanshi, sanyin idaniyarshi, gatanshi, nisful hayat dinshi...
Allah sarki Aliyu haydar😭😭


®Kausar Luv💞
[11/15, 5:20 PM] Kausar~Luv: [8/1, 8:38 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((16))


©Kausar M Hassan


Rayuwa tafiya takeyi, lokaci gudu yakeyi a gogo, shekara ta koma kmn wata, wata ya koma kamn sati, sati ya koma kaman kwana d'ayah, a kwana a tashi kuma babu wuya ga Allah mai dukkan komai..


Haka aliyu ya wuce makaranta a kasar madinah, iyakarshi da gidah bayan duk shekara d'ayah, idan ya dawo kuma abbi baya barinshi fitah koda wajen gidan, kudurin nana yana nan a cikin rantah, yayinda mame ta kuma chaan wani kauye kusa da garin sokoto wnda ba zea daukeka awa d'aya ba kapin ka isa..


19years later!
A kan matattakarlar shiga da saukowa daga jirgi na hangeshi, kafafunshi sanye da cover shoes brown in colour, sanye da wando shima hka irin mai laushi din nan, da riga fara mai ratsin brown kadan a tsakiyanta, ya rataya jaka a hannunshi tre da riko irinta jaa din nan a kasa (trolley) idanunshi a lumshe kaman wnda ya rufesu ruf, sajen dake fuskanshi ya k'ara masa kyau, dan madaidaicin bakinshi ya kara tsukewa a cikin kyakyawar fuskarshi, d'an jikinshi bul2 dashi, gwanin ban sha'awa.
Murmushi yay shaqar iskar da yayi, ya cigaba da sako kafafunshi zuwa kasa a hka har ya sauko dga kan abun hawa jirgin.
Lion kenan👍🏼👌🏽


"Aliyu"
A hnkli ya bud'e idonshi yagan wake kiranshi.


"Shafi'u"
y furta cikin siriryan muryanshi.
Da sauri shafi'u ya isa gareshi suka rungume juna


Shafi'u ya dubie aliyu
"Kai kaganka kuwa, kayi wani extraordinary fresh sea wani kyau kake karawa alhj"
Kai aliyu y d'aga masa tare da furta
"Ya batun aikin nan anyi kuwa"
Murmushi shafi'u yay
"Aiki an gama lion, ynxn dea muje gidah ummi na chan na jiranka tun d'azun"
Juyawa yay sukyai sallama da zayyanu dake kusa dashi, shafi'u ya daukar masa jakar shi, suka kama hanya zuwa gidah...
[8/1, 8:45 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((17))


©Kausar M Hassan


A cikin mota shafi'u keta faman zuba masa surutu, iyakacin aliyu dea "eh, a'a em......."
A haka har suka k'arasa gida, koda suka isa ummi ce zaune kan kujeran main falo na gidan, ma'aikatan gidan na kai da kawowa.
A hnkli ya cire takalminshi ya nunawa ma'ikatan gidan suyi shiru kada suyi maganar da zata gane cewan ya shigo gidan. Ta baya ya lalla6a ya rufe mata ido, ummi hannu tasa ta saukar da hannunshi ta rike tare da cewan
"D'ana aliyu kenan kana zaton bazan ganeka ba, kamshin turarenka ma yasa naganeka da wad'an nan tafukan naka"


Narai2 da ido yay
"Kai ummi, nikam wata rana sea nasa kin kasa ganeni"
Ummi daria tai
"Mu zuba mu gani to"
Daria sukai dukansu dea2 lokacin abbi ke fitowa dga d'akinshi, aliyu y k'arasa kusa dashi suka karaso tare.
Masu aikin gidan suka fara zuwa ban gajiyah.
Suna zaunawa shafi'u ya dubie aliyu
"D'an balarabe ni zan koma sea munyi waya ko"?
Ummi dake zaune ta juya ta dubieshi
"Haba shaf'u kai kaman wani bako kumah, ka hana aje a daukoshi gashi ya dawo kuma sea ka tafie ka barshi ana hka"?
Murmushi yay
"Ummi inada d'an uzuri ne amma zan dawo in shaa Allah"


Aliyu tashi yay ya taka masa har kopan gidan sukai sallama ya dawo, kusa da ummi ya zaunah, ga kugunshi ga nata, sea faman murmushi sukeyi ita da d'anta aliyu haydar (the lion🦁).


Chaan aliyu ya dudduba, baiga nafisah ba, ummi ta d'aga masa kai
"Wa kake nema ne eyye"?
Dan murmushi yay kad'an
"Ummi ina nafisa kuwa"???
Rufe bakin da zayyi ya hangota tana zuwa, cikin shadda mai kyau taji aiki, rike da yaro a hannunta, daka ganshi ka ganta, a falon ta zauna ko kallon inda aliyu yake batai ba.
Kai y girgiza shima yasan laipienshi ai, a hnkli ya tashi ya matsa kusa da ita kan kujerar ya zauna
"Kanwata fushe kike da yayanki ko"?
Juya masa fuska tai ta bashi bayah, aliyu ya rike hannun yaronta wanda baisan sunanshi ba.
"Ya sunanka little kid"?
Cikin yar muryar su ta yara y amsa da
"Muhammad amin"
Aliyu y rike hannun Muhammad
"Kaga mamanka na fushi da yayanta, idan bata min magana ba ni zan koma inda na fitoh, tashi yay zai wuce, har yayi taku 3 ta tashi tasha gabanshi ta fara bubbuga kafanta a kasa
"Ni Allah yaya aliyu ka dawo"
Daria duk mutanen falon suka saah, ganin yanda tai, ita d'in kanta ta baiwa kanta daria.
Takun sawo sukajie a falon wnda yasasu duba dga ina yake.
Wnda wannan ba kowa bace face nana, murmushi aliyu yay y cigaba da abunda yakeyi.
Kan kujera taja ta zaunah, tana yiwa aliyu wani kallo na rashin so, abunci ummi ta dauko ta bashi
"A'a ummi ina buqatar inyi wnka b4 inci abunci ko b hka abbina"?
Abbi murmushi yay
"Haka take d'ana tashi maza"
Aliyu tashi yay ya dauki bags dinshi yay daki dasu, wanka yay ya fito ya chnza kayan jikinshi zuwa na shan iska, farare tas dasu da fararen takalmi, ya feso turare ya fitoh d'akin zuwa kasah.
Ummi da kanta ta bashi abunci yana ci suna fira wasa da dariah, nana batace dashi komai ba hka shima baice da itah komai ba duk da yaganta kuma itama tasan yagantah.
[8/1, 8:51 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((18))


©Kausar M Hassan


A wannan rana dea haka suka wuni har dare a gidan, cikin farin ciki mara misaltuwa. Sai karfe 9pm mijin nafisa yazo ya dauketa mai suna jafar, haka sukai sallama da nafisa ta tafi gidan mijinta dake wurno road.
Nikam cewa nai ita nana bazata tafie gidan mijinta bane ko yaya🤔 ko ita batayi auren bane.
Ganinta da nai ta shiga d'aki yasa na tabbatar da har ynxn batayi aure ba, ko mai take jirane oho? Kodayake aure kuma lokacine dashi.
Muma Allah ya kaimu lokacin namu, amin.. Duk wadda/wanda batace amin ba to banda ita. lol😜


Aliyu d'akinshi ya nufa wanda aka chnzawa tsari da komai, ga babban photonshi yana yaro da kuma wanda yake yanxn duk da pic din ya shekara 3, dan lokacin daya kammala degree dinshi in computer ya dawo gida yin service yayi shi, to bayan y gama service din ya koma yay masters dinshi duk dai a 6angaren na'ura mai kwakwalwa.
Kwance yay kan gado chan kuma ya tashi ya shiga toilet y watsa ruwa tare dayin alwala, ya chnza kayan jikinshi zuwa wando 3 quarter, ya maida gabanshi gabas yay sallolin dare, har kusan 11pm tukkuna ya kammala yay addu'ah sosai, ya tashi ya hau gado tare dayin addu'an bacci ya kwanta ruf abunshi.
Nima d'in 😲hamma nai na fita dga dkin na koma tsohon d'akin nafisa na kwanta abina saboda tsaro😉...


Washe garin ranar, aliyu bayan ya tashi shida abbi suka tafie masallaci sukai sallah, suka koma kai tsaye d'akin ummi y nufah ya gaisheta, ya d'an zauna suka tab'a firan yaushe gamo tukkuna yay nashi d'akin, yana shiga ya dauki wayanshi ya kira waya wnda wannan ba kowa bane y kira face shafi'u
"Ka shirya kazo muje xuwa 10am"
Shine kawea abunda ya fadamsa yayinda shafi'uh ya amsa da to
"zakin duniyah"


Aliyu ya maida wayan ya kashe, ya juya kenan xai kwanta sea ga nana ta shigo a d'akin, kallonta yay tukkuna ya basar ya juya, cike da izzah da gadara ta fara masa magana
"Kai kana ganina bazaka gaisheni ba, kasan bana wasa dakai dea ko".
Aliyu tashi yay ya sakko dga kan gadon ya tsaya dea2 inda take tsaye
"Nana"
Aliyu y kira sunanta, cikin kakkausar murya ya fara yimata magana, irinta mazan da basa tsoro
"Daa ba ynxn bace, idan kinmin chaan daa na d'auka to kisani ynxn bazan d'auka ba, kada ki kuskura kice zaki shiga gabana, get out of my sight".
Ido nana ta zaro ta kalleshi
"Aliyu ne ke fadamata irin wad'an nan maganganun, lallai tana buqatar tashi tsaye gamedashi"
Fuu ta wuce ta bar d'akin yayinda aliyu ya koma ya kwanta, kusan karfe 9am ya tashi, a gurgujie yay wanka y chnza kayah zuwa kana nan kaya, ya daukie wayanshi yay kasah tare da saka brown din glass, breakfast ummi ta hada mashi da kanta, kad'an yaci tukkuna yasha ruwah....
®Kausar Luv💞
[11/15, 5:20 PM] Kausar~Luv: [8/1, 9:02 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((19))


©Kausar M Hassan


Ba'a dau wani lokaci mai tsawo ba sea ga shafi'u yay sallama, amsawa sukai a gurgujie suka fitah gidan, tare dayiwa abbi da ummi sallama.
Suna fita kai tsaye wata hanya suka mik'a, sun jima akan titi tukkuna suka yanka ta wata hanyar suka isa a wani d'an kauye, gidajen kauyen duk aksarinsu ginin bulun kasa ne, gidan cement bai wuce 5 zuwa 6 ba. Kopan wani gidah shafi'u yay parking, gidan matsakaicine mai kyau da haske a wajenshi.
Bayan shaf'u yayi parking duk suka bud'e motan suka fitah, dea2 kopan gidan suka same yaro, aliyu yace
"Kajie kace wea ana kiran mame"
Yaron dayake bazai wuce shekara 10 ba, ya kuwa dushie kopan gidan ya shiga tare da sallamanshi.
Mame dake zaune kan tabarma ta amsa masa sallaman.
"Wea ance ana kiran mame"
Jin sunan da aka ambata yasa mame hawaye take, ciki da zumud'ie ta amsa masa da
"Kace nace ya shigo"
Yaron fita yay ya koma inda su aliyu, ya fadamasu sakon mame tukkuna ya wuce abinshi.
Glass din dake fuskanshi ya cire ya maida aljihu, tukkuna ya d'ago idanunshi ya dubie shafi'u
"Shafi'u ka bari in shiga in fito"
Shafi'u kai y d'aga masa alamar "to".
Taku y fara kaman wnda babu laka a jikinshi tare da goge hawayen da keta faman yimai zarya dga ido zuwa fuska...
A hka ya shiga gidan dauke da sallama, mame ta amsa, dukansu suka kasa magana, sea chaan ya rage tsayenshi
"Mame I miss you su much"
Mame rungumo d'anta tai da duk idanunsu sun cika da kwallah.
Kusan minti 3 suka d'auka a hka tukkuna aliyu ya zaunah kan tabarmar da mame take zaune akai, ya kama hannunta ya rike gam.
Cikin muryan kuka aliyu y fara magana
"Mame shekara nawa rabona dake, har ynxn idanuna na kallon rabani dake da abbi yay, wannan abun yana cikin zuciyata mame, shine mummunan abu da bazan ta6a mantawa dashi ba a rayuwana, ina ganin hawayenki akaina mame".
Hawayenta ta share tukkuna ta fara magana
"Allah yayi dare aliyu gari ya waye, komai lokacine d'ana! Nayi bakin cikin rabuwa dakai da nai aliyu, tun bayan rabuwana dakai rayuwata take cikin kunci da tashin hankli, bansan yaya kake ba a wanne hali kake ba, ni har na yanke kauna da ganinka aliyu"
Aliyu yay murmushin takaici
"Mame kinsan kuwa ko bayan na kammala degree dina lokacin ina service nata nemanki ban sameki ba, haka har na kare na koma nayou masters dinah, na dawo gidah na koma, sea a wannan karon abokina Shafi'u ya gano inda kike mame, mame mai yasa baki neman ba".


Mame tai shiru na d'an lokaci tukunna ta kalleshi
"Aliyu y zanyi da rayuwar dana tsinci kaina a ciki kuwa, abbinka yace kada in koma shigar masa gida shiyasa"
Aliyu y nisa ya dubieta
"Mame kinyi aure ne"?
Kai ta girgizah mashi alaman a'a, hannunta y qara rikewa
"Mame mai yasa"?
Kallonshi tai duba na tausayi
"Aliyu bbu komai , kaga bani labarin ka, kukan nan ya isa hka kaji ko"? Tasa hannu ta share masa hawayen.
Murmushi yay tukkuna ya kara duban mame😊😄...
Humm Life is some how *KABHI KUSH KABHI GHAM*😉...
sun dea jima tana jin labarin rayuwanshi da yanda yay karatu, wani lokacin tai daria wani lokacin ta girgiza kai, haka sukai sallama tare da bata tabbacin zea rika zuwa akai2, kaman kada su rabu da juna..


😭soyayyan uwa da "ya "ya kenan... Ya Allah ka sakawa iyayenmu da alkhairi, wad'anda suka rigamu gidan gskya a cikinsu ya Allah kai masu gafara, ka yafemasu, ka sasu a aljanna firdaus... Aminnnnnnnnnnnnnnn👏🏽


Fitowa yay ya tarar da shafi'u zaune a cikin mota har y fara gyangyadie.
Hannu yasa y fara bubbuga kafanshi, firgigit yay ya tashi, basu tsaya dogon zance ba suka karasa gidah, kai tsaye aliyu ya nupie d'akinshi, a kopar d'akin yaci karo da nana😚
Kallonshi tai, zatai wata magana, aliyu ya dga mata hannu tare da cewa
"Shhhh! Y isa hka nana, bana tsoronki dama chaan bana tsoronki kada ki kuskura ki shiga harkata, kingane ko? Matsa ki bani hanya in wuce".
Ido ta bishi dashi yyinda yake shirin bankad'arta ya fice, a cikin zuciyanta take cewa
"Ina buqatar in chnza taku"
Ta kama hanya tai d'akinta.


"Oh su nana anki aure dai🤔


Washe garin ranar aliyu ya tashi da safe ya shirya yay wnka kai tsaye ya fitoh, yana fitowa kasa ya tarar da ummi, ummi da murna ta tarbieshi
"D'ana sauko ga abunci na dafa maka"
Da sauri y karasa ya zauna kan dinning d'in ta zuba masa soyayyen kwai da farfesun naman rago, sunan Allah y ambata tukkuna ya fara cin abuncin, kad'an y tsakura, ya yunkura zai tashi sea ga abbi.
Aliyu y koma ya zauna, suka kara gaisawa da abbi, abbi y ciro key a aljihunshi ya mikawa aliyu, aliyu y kar6a ya jujjya key din
"Abbi wannan ai key din motane ko"?
"Eh shine aliyu, motan na nan waje farace, anyi mata duk abunda take buqata, sbd hka na baka wannan mota d'ana".
Gdya Aliyu yay wa abbi tukkuna ya maida dubanshi ga ummi
"Ummi kimin gdya ni zan tafie gidansu shafi'u sea na dawo"
Fita yay dga gidan dea2 lokacin misalin karfe 9am.
Kai tsaye gidan mame ya nupah.
[8/1, 9:08 PM] Kausar Luv💞: *ALIYU_HAYDAR*
Page ((20))


©Kausar M Hassan


Dea2 kopan gidan yay parking motanshi ya fito ya shiga, koda y shiga ya tarar da ita tana sharah, tsintsiyar hannunta y kar6a ya karasa sharan tukkuna suka koma d'aki, kan kafafun mame y d'ora kanshi sunata fira abunsu bayan d'an lokaci aliyu yay mata sallama dga nan ya zarce gidansu shafi'uh.

Bayan kwana 2!
Aliyu ne ya fito dga motanshi dauke da ledojie guda hudu, ya shiga dasu, ya baiwa mame.
Amsa tai tare dayimasa addu'ah, shikuma yay mata sallama y kama hanyar fitah.
Akan hanyarshi ta fitah, ya hangi wata kyakyawar halittan Allah, tana tafiya sanye cikin hijab iya guiwantah, yarinyr black beauty ce, gata da tsayi dea2 misali, ga tsinin hanci, son kowa kin wanda ya rasah, shekarunta bazasu zarce 14 ba.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads