Showing 15001 words to 18000 words out of 36590 words
Chapter 6 - A TUNANINA Complete Book Document by Safiyya .txt
yakuma yi masa gamshasha shiyar bayani.
Matsalarsa da junnu dakuma sa'abu arai yana haifar da mufarkin sex amma mafi inganci zance junnu ke haifar da haka.
Yabashi magani na wanka tare da sha, sannan yarubuta mishi nafilfili masu inganci da kariya daga sharrin shaid'anu, yakuma k'ara jadda mishi duk runtsi kada yayi sakaci da yin arollah kafin ya kwanta.
Yayi ta godiya tare da ajiye mishi sadaka.
***** biki budiri bured'e
Gobe d'aurin aure.
Amare amsha gyara ansha kyau kam ba'a maganarshi.
Sosai kuke haskawa.
'Yan Maiduguri sun iso tun ana saura kwana biyu wato ranar dasu gabatar da lunching.
Yau kuma ranar walima ce.
Don haka awani katafaren gidan Abbansu Safiyya akashirya gabatar da walimar Wanda gaba daya amaren sun had'u agidan.
Jamee,sophy tare da nafee.
Wacce dole ta hak'ura da zama da kishiya.
Sosai walimar ya k'ayatar malama mamie waru ta gabatar da wa'azi mai tatsa jini da jijiya, domin tayi k'ok'arin tabo zancen manzo SAW akan falalar da mace mai biyayyar aure take samu arayuwarta tare da nasarori.
Bayan ta gama malama Hameeda ta d'ora da tata akan tsafta da kula tare da kuma rik'e sirrin miji sai uwa uba hak'uri jigon zaman aure.
Tunda akasoma gabatar da lectures hankalin Sophy yake kan wata matashiyar mata tare da wata budurwa mai tsananin kama da ita sosai.
Suma tafahimci hankalinsu na kanta domin tana hago yadda suke kallonta suna k'usk'us akanta.
Gawani fad'uwa da gabanta keyi akai akai tun jiya.
Agefe d'aya kuma bak'in cikin rashin zuwar barr Deen bikin ke damunta.
Bama tasan anyi addu'ar tashiba sai dai tacinkayi maganar beastynta tana cewa" beasty mamie tana kiranki gatacan tare da k'anwar baban ustax d'inki, zaku gaisa, taja hannunta tana cewa amma beasty kunyi kama da budurwancan mai siffan larabawa.
*Mrs j moon*
[4/20, 1:57 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*29 to 30*
*©Safiyya*
*Page d'in nakine my Sahiba(Aisha' Ashmee) banmanta dakeba,Allah yabarmu tare cikin Aminci Amin.*
Mamie ce ta kamo kafad'anta tana cewa "yarinyar mamie ga surukanki Ku gaisa, k'anwar Abban Saifullah ne.
Cikin jin kunya ta russuna tace "inayini? Lafiya lau Amaryanmu, tana murmushin kunya tafad'a jikin mamie.
Abayanta ta cinkayi maganar budurwan tana cewa "Aunty Allah sai data matso sannan nak'ara ganin kanarta da mum sosai domin hatta kwayar idanunta na mum ce, ta kama haba "kai amma wannar kama harta baci.
Mamie tayi yak'e kawai, batare da tace komiba,domin ita kanta gabanta fad'uwa yakeyi tun sanda tayi arba da photocopy n yarinyarta.
Aunty ta ja ajiyar zuciya tace "kai eshat kinfiye surutu, to Ai kema mumyn ki kika kwaso, tasa dariya eh, hakane aunty amma abin ya jefani cikin matsanancin mamaki, kuma bros kada wasa bai taba cemin matarsa kamatake damuba, ko miya hanashi fad'a oho.
Zuwa lokacin ita kanta mamie ta jinjinawa surutu irin na eshat.
Su dai su Sophy da Jamee Ido suka zuba mata, tana magana tanawani lunshe idanu kamar mai jin barci.
*haka idanun meena yake lol*
Aunty ta kaimata duka kad'an tace kin balle da surutu kamar aku, ko gaisawa da twins sis d'in taki(cewarki) bakiyiba
Aiko da sauri ta rungumeta tsan tsan tana kaiwa wuyanta kiss.
Sophy bugun zuciyarta yak'aru akan nada.
Tasaketa, tanacewa "twins sis d'ita kuma aunty na, ya hidimar biki da hak'uri da my bros? "Domin nasan bros zama dashi sai da hak'uri, sabida yana da saurin fushi amma nada saurin sauka, tajuyo tana duban Nafee wacce ta iso wurin tare da wasu k'awayenta.
Cikin wasa tace "yawwa Amaryan k'auye kema kina hak'uri da Bros ko? Harara tawatsa mata, batare data bi takanta ba, tana fuskantar aunty Fatima tace"aunty kuzo mu wuce kowa ya tafi saura mu kadai yarage, tund'azun muke jiranku.
Aisha ta ja tsaki tare da jan hannun sophy tana duban mamie tace"mamienmu zo mutafi ni gidanku zan kwana tare da twins sis d'ina, aunty kifad'awa mum sai in kunzo d'aukan amarya zata ta ganni, aikomin da kayana gobe da safe.
Batajira ansawar auntyba tawuce rik'e da hannun sophy da jamee tana xuba musu surutu kamar wacce taci duwai d'in kaza sadda take kyarkyaran kwai hhhhh lol.
Aunty takasa rufe baki, don mamakin wannan rawar kai irin na Aisha.
Afili tafurta "ko sai yaushe zata koyi natsuwa ne oho.
Mamie tasa dariya "a,a Hajiya Fatie tana da natsuwanta kawai tafiye son jama,a ne da rashin bak'unta.
Aunty ta jijjiga kai, "tace e dakuma wannan kam, domin duk inda taje sai tabarsu da kewanta.
"Hakan yana da kyau Ai.
Aunty taja su nafisat suka tafi, suma su mamie gida suka wuce tare da eshat.
Kowa yaganta sai yayi maganar kamarsu da juna.
Suna isa room d'in Sophy, eshat tafad'a bisa bed tana cewa "wash!! nagajifa sosai beastynmu, jamee tasa dariya tana girgiza kai, tace eshat hoo, kina da abin dariya itama dariyan tasa, ta dubi sophy wacce ke k'ok'arin tube kayan jikinta domin shiga wanka.
"Twins sis kedai baki da saurin sabo, don Allah jiba tunda muka had'u nake magana amma kedai iyakanki murmushi ko girgiza kai, tak'arasa maganar tare da turbune fuska baki a tsuke, sosai tabawa sophy d jamee dariya.
Ta dafa kafad'anta tace "yi hakuri my sis, nima ina da sabo kamarki, yanzu bari in nafito wanka kibani labarin Maiduguri, duk da muma asalinmu chan ne amma komunje bana fita ko ina sai tare dasu mamie.
"K pito kuwa ki kwashi labari har sai kingaji da sauraro.
Har takama handle zata bud'e toilet taji eshat ta kwalla mata kira, ta juyo.
Waya ta karamata akunni, tana cewa " mum ce kugaisa.
Cikin girmamawa tagaisheta itama cikin kulawa ta amsa, tana mai cewa "saikinyi hak'uri da rawar kan eshat, murmushi tayi batare datace komiba.
Tamik'a mata wayar tare da shigewa toilet.
Tana fitowa tayi Shafa, tana lalabo 9t were tanajin hiran Jamee da Eshat.
Jamee tace "To Ku daza akawo muku amarya, miya kaiku zuwa?
Cikin karad'i eshat ta amsa"dad yace muzo, in and'aura aure mutapi da amaren kawai sabida gudun kada Ammi taja mum fad'a.
Jamee tana k'ok'arin jefa mata wani tambayar sophy tace ya isa zancen hakanan, kuxo muje,muyi dinner domin yunwa nakeji ni, rabona da abinci tun na safe
Suna cin abinci, sai santi eshat keyi wai mamie ta iya girki, ta kalli sophy ta kanne mata Ido d'aya tace " dafatan kin iya irinsa, domin gidanku zankoma da zama, inmiki zaman d'aki, dariya suka kwashe dashi su duka cikin dariya Jamee tace lallai dakuwa kinbada sabon salo k'anwar miji da zaman d'aki, nanma dariyan sukayi.
Suna shirin kwaciya wayar barr yashigo, cikin tura baki ta d'auka tayi shiru, yanajin haka yasan fushi tayi, cikin 'yar dariya yasoma magana,
"Affuwan sweet lil sis yanxu haka ina shirin hawa jirgine, zanzo, aikine yayimin yawa, shiyasa ban halarci programs d'inku ba amma da yardan Allahu dani za'a d'aura aure gobe.
"Nan da lokaci k'ank'ani zan iso, don haka kada kiyi barci, kijirani, kuma kimin girki mai sauk'in nuna kafin in iso, bai jira cewarta ba ya katse kiran yanajin wani nushad'i aransa, mai makon k'uncin dake damunshi duk inyatuna da batun auren.
Eshat sarkin sa ido tanaganin tamik'e zata pita, ta duro itama tabiyota bayanta.
Su biyu a kitchen sai aiki sukeyi, suna hira kad'an kad'an.
Mamie tasamesu, agogo tafara kallo taga k'arfe d'aya saura na dare.
"mikukeyi har yanzu bakuyi barci ba?
Ad'an zabure suka juyo, domin basuji motsinta ba sai dai maganarta sukaji.
"Yaya Deen mukewa abinci, yace yana hanya.
Cike da kakabi mamie tace"Allah ya shiryaku, ace duk abincin dake gidannan arasa wanda zaici inya iso saikin shiga kitchen da uban darennan baku tsoron almatsutsui.
Cike da dariya tace "wallahi mamie munfi k'arfin shaid'anu, "uhmm naji Allah dai yak'ara tsaremu "Amin 'suka amsa.
Coffee ta had'awa Abba tafice tabarsu suna k'ok'arin kammala girkinsu.
2:00am ya iso, suna zaune apalour zaman jiransa.
Eshat charting takeyi da hubbynta yayi da Jamee ke free call da oga jameel, wacce bayan sungama girki ta iso, ita kuwa sophy barci keson d'aukanta, ta kwanta abisa Cushing.
Ahaka yasamesu, alokaci daya ya d'imauce da ganin mai kama da lil sis d'inta, domin eshat duk yadda sophy tayi nasa kaya tare da parking na sumarta shi tayi, 9t were ma irin nata tasa banbancin colour ne kawai.
Ganin yakasa k'arasowa ciki, yasa sophy isa wurinshi tajawo hannunsa zuwa dinning area.
Yanayi mishi sannu dazuwa su Jamee suka k'ataso
Sosai yake duban eshat yana jiran k'arin bayani.
Itako sai murmushi take mishi domin bak'aramin kwar jini yayi mataba.
Tayi saving d'insa.
Ci abinci barrister nmu, sai inyi maka bayani.
Kai ya gyad'a tare dayin bismillah yasoma aikawa da tumbinsa hakkinsa.
Barr yasha mamaki dayaji k'anwar ustax ne, wai babansu d'aya.
Ak'asan zuciyarsa yace anya ba tsintarta suma sukayiba, kamar yadda muka sami lil sis ba? Kai ina da ja akansu kam, amma bari muga zuwa wayewar gari.
Yayi musu sallama tare da godiyan girki yashige room d'insa, suma sama suka yaye agajiye idanuwansu cike dajin barci.
Daf da subahi sophy ta farka agigice saka makon mufarkin da dayi wai ita da mamie tare da barr suna ta kuka anrasa mai rarrashin wani cikinsu.
Tayi addu'an falfawa daga barci sannan ta shiga toilet ta d'auro arollah tasoma nafila har aka kira assalatu, lokacin Jamee da eshat suka tashi.
Tana sallame sallar subahi ta bingire a bisa sallayar, barci mai dad'i ya kwasheta.
*Mrs j moon*
[4/21, 3:58 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*
*31 to 32*
*©Safiyya*
*Gaisuwace agareki my sis Zainab vc, ubangiji Allah yayi Rahama ga Boy Al-Amin Allah yasa majik'an musulmai ne. Allah yabaku dangana da juriyan rashinsa Ya shafe zuciyarku shafan musulunci, Alfarmar Manson Allah SAW Amin*👏🏻
Sophy tasha barci mai yawa sabida ji take kamar barcin dare takeyi, sakamakon dad'in dataji yayin barcin.
Misalin k'arfe sha biyu da minti arba'in wato daya saura, ta tashi.
Koda tabude idanunta bakinta d'auke da addua.
eshat tayi arba da ita zaune agefenta taci uban kyalliya sai k'amshin humra takeyi mai dad'in shak'a.
Saidai kallo d'aya tayi mata tagano yayi kuka domin idanunta sun tasa kad'an kuma sun rage fari ba kamar jiyiba
Murmushi tasakar mata tare da tanbayar ta ina beasty?
Ta kauda kai, idanunta suna shirin zubo da ruwa.
Azabure sophy ta mik'e zaune, takamo hannun eshat tabud'e murya sosai tace "ina beastyna nace!!?
Ahankaki eshat ta amsa "taje gidansu, domin anfiso a d'aurawa mutun aure yana cikin gidansu, sabida da haka tana can, amma nasan tana daf da shigowa yanzu.
Ahankali tasaki ajiyar zuciya tare da sakin hannun eshat.
Tamik'e tashiga bayi tahad'a kayan k'amshin na wanka.
tashiga ruwan tasoma gabatar da wankanta tana lunshe idanu domin k'amshin yayi mata sosai. Had'in k'amshin Aunty Khady k'amshi kenan Wanda ta kawo mata gudun mawa hhh lol.
Ta d'au lokaci mai tsawo sannan tafito.
Eshat ce jingine a allon bed ta runtse idanu hawaye na zurara mata tamkar an bud'e tap.
Asanyaye sophy ta zauna gefanta, tasa hannu tana share mata hawayen, ta bud'e idanu tasa karwa sophy murmushi tana rik'e hannunta.
Sohy ta had'e fuska, tace "kinga sis banson haka, inzaki fad'amin mikefaru kifad'amin bawai kiyi ta kuka ba tam.
Eshat ta jijjiga kai, kamar zatayi magana sai kuma ta rungumeta tsan tsan wanda saida sophy ta saki d'an k'ara tana cewa "ke!! ni sakeni kada ki ballani kiyiwa swt ustax d'ina illah.
Eshat ta saketa, tana goge fuskanta, tanashirin magana barrister ya turo k'ofa.
Eshat ce ta amsa mishi sallama tana dariya k'asa k'asa kuma ahankali ta furta "sannu da zuwa Angonmu.
Cikin murmushin farin ciki ya amsa "yawwa k'anwarmu.
Sophy ta saki baki tana kallobahi, tana kuma tunanin wa yaya Deen ya aura kuma yaushe?
Ta kai dubanta ga reshi.
Yaci uban kyalliya cikin wani tsadadden yadi milk da ratsin golden, anyi mushi d'inki 'yar ciki da babbar riga sai hulansa da ya kafa, bak'a, sajennan da d'an jemunsa sunsha gyara sai kyalli sukeyi.
Ganin ya tsurawa cinyoyinta Ido yasa ta tuna da ba kaya jikinta sai d'an k'aramin towel, wanda iyakacinsa cinyarta.
Ta tura baki ta jawo bargo tana kici kicin rufa.
Barr ya fizge bargon yayi cilli dashi gefe alokaci d'aya ya rungumeta tsan tsan a k'irjinta, yasa hannunsa yana shafa tsakiyan bayanta yana kuma sunsuna sumar kanta zuwa wuyanta, tana ta kici kicin kwace kanta, ta jiyo eshat tana tafi raf! raf!! raf!!! Da kuma k'arfi, tana cewa "soyayyada dad'i wallahi Allah yabarmin Ku cikin kariyansa asha Zuma a more.
Sophy ta zare idanu cikin rawar murya tasoma cewa "yaya Deen karufamin asiri ka sakeni, kada wani yashigo yaganmu haka, kasan bai daceba abinda kakeyi, duk da muna shak'ik'an juna amma hakan haramun ne.
Mai makon yasaketa saima k'ara rungumeta yayi da kyau, tanajin yadda zuciyarsa ke bugawa, ita kam jikinta rawa yakeyi.
Ganin yak'i sakinta kawai sai tasakar mishi kuka mai sauti.
Da sauri yasaketa, ya cire hularsa tare da babbar rigansa, tana son tashi ta gudu amma ya danne mata cinya da gwaiwan hannunsa.
Cikin kuka ta kalli eshat wacce ke zaune bisa stool tana doka murmuahi, tace "keko sis kina kallo ana cimin mutunci kinkasa cewa komi saima murna kikeyi, baki ko kishin d'an uwanki, akema wasa da jiki, taja hanci sannan taci gaba "to wallahi alhaki awuyanki tunda kina kallo kike marawa shaid'anci baya.
Eshat ta saki dariya tanacewa "lallai twins sis manya, yanzu mijin naki kike cewa na shaid'anci'' uhmm to kuwa kiyi gaggawan tubawa Allah ko ki fad'a halaka yanzu yanzu kuwa.
Batasan sadda ta ture barr ba ta isa wurin eshat ta cukumota tana fad'an "kina haukane da zaki ce yayana uwa d'aya uba d'aya kice mijina? Ehye!!!!
Barr ya jawota ya zaunar, cikin sanyin murya yasoma magana "lil sis kiyi hak'uri tare da tawakkali, domin haka k'addaranmu take tun farkon samuwanmu, Allah ya rubuta a lauhun mahfuz cewa sai munzamo mata da miji.
To gashi Allah cikin I...... Azabure ta mik'e batare da tagamajin magar ba.
Tayi hanyar fita, cikin sauri eshat ta tareta"jibi yadda zaki fitafa, tureta tayi tana jifanta da wani mugun kallo.
Batabi takan kowaba acikin parlourn Wanda yakasance shak'e da mutane 'yan biki cikinsu har da doctors tare da nurses mata 'yan asibitinsu, sunzo tayata murna.
Sister Ummu nadrah tare da Aisha (mmn Ramla)
Suna cikinsu hhhhh lol.
'Dakin mamie ta fad'a bako sallama.
Binsu tayi da kallo sanda tashiga, har ta dire kan mamie wacce take cikin farinci.
Ta fad'a jikin mamie tana cewa mamie kina ina kayi wannan kwamacalan.
Tasaketa ta tsura mata idanu bako k'ifrata, tace "mamiena fad'amin gaskiyan zancen, shin wai and'auramin aure da yaya deen?
Jim mamie tayi sannan ta amsa "kiyi hak'uri yarinyar mamie haka Allah yanufa barrister shine zai zamo abokin rayuwarki ma'ana mijinki.
Wani k'ara tasaki mai sauti tare da dafe kanta tace "no!!!! Bazai yuwuba, yayana najini shine mijina! Kai haba awani duniya akeyin haka mamie? Ta zube bisa gwaiwoyinta tana kuka sosai.
Sai kuma ta d'ago tana kallon mutanen cikin d'akin.
Dada fanna ce yayar Abba sai hajiya Fatima k'anwar Abban ustax agefenta wata farar mace ce, mai tsananin kama da eshat, ba tantama mum d'in tace.
Tamik'e tasoma ja dabaya, tana cewa "to afad'amin cikinmu waye d'an cintuwa?
Farar matanta ta amsa "kece baby Zarah.
Idanu waje tace "waye Zarah? Wannan karan dada fanna ta amsa "kece, Nana Safiyya ayanxu amma ada fatimatul zara'u sunarki kafin k'addara ta gifta na bacewarki.
Zuwa lokacin Jan numfashi take dakyat, cikin sark'ewar murya tace"yanxu ni bani da uwa balle uba? nid'in 'yan kwararoce dama? Mara asali!!? Wayyo kaicona!! Ya salamu kakawomin agaji!! Tayi baya zata fad'i sakamakon jirin da ya kwasheta.
Barr dake tsaye abayanta yatareta, yana jijjigata amma ko motsi batayiba.
a gigice eshat tasaki kuka, yayin da su mamie sukayo kanta.
K'awayenta doctor sukayi k'ok'arin bata taimakon gaggawa, kuma cikin ikon Allah numfashin yadawo bugawa normal.
Akayi mata allura, tasami barci.
Kowa yafice domin ba'ason hayaniya ya dameta, barr ne kawai akabari agunta cikin room d'in mamie.
Ya k'ank'ame hannunta yana tunanin ko inta farka zata amshe shi amatsayin miji?
*shin wai ma miya farune da har aka gano ustax babansu d'aya da sophy?*
*kubiyoni zuwa ranar Monday*🙊
*Mrs j moon*
[4/24, 12:06 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*33 to 34*
*©Safiyya*
Hajiya Sadiya ce zaune tare da ustax saif acikin d'akinsa, Wanda aka ware masa cikin gidan uncle d'insa Alhaji Adam kuma surukinka Abban su nafisat.
Wani magana suke tattaunawa mai mahimnanci, sosai suka d'auki lokaci mai tsawo suna nemo mafita.
Hajiyan tamik'e tana dariya ta ware hannunta alamun dak'uwa tare dacewa "Allah my boy bakada kunya, ya sosa sumar kansa ya amsa "Allah mum ina da kunya sosai kamar mace.
Murmushi tayi kawai batare da tace komi tasakai zata fice, ustax yace "yawwa mum ajiyemin wannan emblem d'in, yana magana tare da jawo durowar gefen gadonsa, abin mamaki emblem d'in yace d'auke inka ganni, yayi ta nemarsa baiganiba abinda ya haddasa shi fidda komi na cikin durowar.
Wani photo ne yaja hankalin mum d'in wanda garin binciken da ustax keyi ya watsoshi tare da 'yan uwansa.
Photon take kallo cike da mamiki, taya akayi saifullah ya d'aukeshi batare da tasaniba.
"Yawwa mum gashi nagani, ashe acikin sip nasa shi. Jin tayi shiru yasashi kai dubansa bisa abinda yad'auke mata hankali.
Matsowa yayi sosai domin ganin pic d'in daya had'au hankalinta haka
Dariya yasaki kad'an yana sosa k'yeyarsa, "mum kina kallon surukarki ce sadda take jaririya? Baijira amsawar taba yaci gaba"wallahi inason photon sosai, watarana muna hira nabuk'aci tabani album d'inta amma wanda take baby ingani, to shine na d'au wannan photon sabida yayimin kyau sosai, ganin tayi