Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 36590 words

Chapter 12 - A TUNANINA Complete Book Document by Safiyya .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yaji son k'ara kasancewa da ita yak'ara bijiro mishi.


Tagama tsiwanta ta juya zata Shiga wanka, ya shan maceta ya fizgota ta fad'o bisa k'irjinsa ya maidata k'asanshi ya rufemata baki da nashi yayin data bud'e zatayi magana.


Shikansa barr yasan yayi mata mugunta domin saida yayi mata ligis hattashima yagaji.

Yad'agata yashiga wanka yafito yasameta zaune gefen bed ta zuro k'afafunta k'asa ta rufe jikinta da bargo.
Ruwan sumarsa ya yarfa mata a fuska taja ajiyar zuciya tana kallonsa yace "ya dai ruhina koda sauran tsiwanne injiraki kigama nikuma ind'ora daga inda na tsaya? Fuska ta kauda batace dashi komiba yayi murmushi mai sauti yace "uhmm gaskiyane da ake muku kirari dogayen mata nacewa
*doguqar mace ni'imar maza* lallai kuwa ni'imarce domin nashaida hakan akanki my sweet lil sis d'ita.


Yamatso ya shafa face d'inta "ya!! ni kuma dogon namiji alfarmar matan barrister ko? Ta ture hannunsa, cikin sanyi tace nikabani towel in d'aura.
"In ank'ifa? Ta kalleshi idanu cike da tsoro, "kayi hak'uri natuba bazan k'ara yima tsiwaba kuma kafi gaban alfarmar matanka sai dai akiraka gidan dad'inta.
Tafad'i haka ne domin tasan k'aramin aikinsa ne yak'ara turmusheta sabida tafahimci baya gajiya.


yasa dariya har da tafawa, ya d'auko mata towel d'in ta d'aura tashige toilet.








Ana gobe barr zai koma wurin aikinsa, ya d'auki sophy sukaje yayiwa su mamie sallama.


Daf da magriba sukayiwa su mamie sallama, mamie tayi tayi nasu tsaya suyi dinner barr yak'i yace yana da shirye shirye dazaiyi kuma gashi zai wuce da wuri don ko biyowa ta wurinsu bazai yiba.


Mamie da Abba sukayi mishi fatan isa lafiya.


Mamie ta dubi sophy tace "to goben sai kiyo parking kizo sai inyadawo kuma,


tana kallon barr ta amsa "to mamie cike da farin ciki.

Murmushi yayi yana girgiza kai batare da yace komiba.



Suna hawa samar titi ya kallota, tana ta murmushi fuskanta cike da murna.
"Kina murna zantapi ko? Ta juyo tana dubanshi sai kuma ta kauda fuska, ya murd'e kunnenta "ina tambayarki kinyimin shiru salon in d'au mataki kisoma min fushi ko? Tak'i kulashi nanma.


"Zamu had'u dake anjuma at night Ai


Ta juyo tana hararanshi tace "muhad'un mana, banajin tsoro yau ehe, yasaki dariya "wato kinsan kina off shiyasa zakimin tsiwa ko? "Tasa dariya itama "uhmm wallahi inkatapi zanyi kewarka amma kuma pp na zai huta da suburbud'anka kwana biyu.

Ya tallabe mata k'yeya ya amsa "so da k'auna yake kawo haka lil sis, "uhmm tace kawai.




Washe gari da 7:00am dai dai suka isa airport, yakira driver n mamie yazo, bai jimaba ya iso, ya mik'a mishi keys d'in gidansu da ta motarshi yana cewa "ka kaima mamie kace zankirata in mun isa.
Ya amsa "to tare da Barin wurin bayan yayi musu fatan sauka lafiya.


Sophy sai bin barr da Ido takeyi takasa cewa komi sabida mamaki.

Shiko yawani had'e fuska, yakuma k'i kallon gefenta sai dai hannunsa sark'e da nata.


Ahaka aka kirasu, basu jimaba jirgin ya d'aga dasu zuwa birnin ikko.


Tunda suka soma keta hazo barr ya kwanto bisa kafad'anta yana jifanta da murmushi ita kam k'ara had'e fuska tayi tana jinjina wayo irin na barr, Sam jiya bai nuna mata tare zasuba, Sam.
sai yanxu ta gano dalilin hanata shirya mishi kayansa da yayi, ashe yasan bai shirya gaskiya ba.


*ooo*
























*Mrs j moon*
[5/10, 11:05 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*59 to 60*
*©Safiyya*








Sun sauka lafiya.
Wani abokin aikinshi, suka samu a airport d'in, yana jiran isowarsu.


Yana ganinsu yak'araso suka rungume juna da barr.
"Madam barka da zuwa, ya hanya? Yace da ita "Barka kadai, Alhamdulillah.


Daganan ya d'aukeso zuwa gida.
barr deen tare da barr Mahmud sai hiransu sukeyi, ita dai sai kalle kallen gine ginen garin takeyi.
yana saukesu ya juya yace da sophy "sai nakawo madam ta gaisheki tana murmushi ta amsa "to sai tazo, agaidamin da ita da kuma yara,"zataji amma yara suna hanyar zuwa"to Allah ya kawosu lafiya "Amin tayi murmushi tare da shigewa cikin gidan tabarsu suna sallama.


Bayan sunyi wanka, ya fita yasamo musu take away awani restaurant.


Suna gama ci sophy ta mik'e ya yawo hannunta ta koma ta zauna tana kallonshi.
Ya kashe mata Ido d'aya sannan yace "kayan dad'in barr ya kikaga garin ikko? Ta yamutsa fuska tace "garin Kaduna yafishi komi don haka sati d'aya zanyi inkoma wurin mamie, ya shafi fuskanta "inkinga kin koma to kina tafiya da k'yat ne, baki ta bud'e "mikake nufi da haka? Ko so kakeyi inkoma da ciwon k'afafu? Yana dariya ya nunata da yatsa yace"kai lil sis baki da Hausa sosai sabida baki gane zaurance.
"To ina nufin sai kina da ciki tsoho zaki koma,shima sabida nasan mamie zata matsamin kidawo haihuwa ne.


Tasaki murmushi tana kulle idannunta da hannayenta wai taji kunya.


Ta gyara zama tace "amma zumana mi yahanaka fad'amin tare zamu tafi?
"Sabida kada kifad'awa mamie ta hanani tafiya da ke amma Abba yasani sabida ranar dana dawo daga asibitinku wurin neman alfarma su aramin ke na sati biyu, sai na wuce gidan gonar Abba nasanar dashi kuma ya fahimceni, yasamana albarka sannan yace kada infad'a miki da mamie sabida gudun samun matsala.


Kai ta jinjina ta kuma cewa "to amma in satin biyun yayi zaka maidani da gaske? Yayi jim yana tunani zuwa can ya amsa "a,a gaskiya, ni fa inaga kintaho kenan, aikinma kinbarshi, sabida nine cikakken patient dazaki bama kulawa sosai domin wad'an can inbaki wasu zasu maye gurbinki yayin dani kuma bawanda zai maye gurbinki agareni.


Taja numfashi tace "amma gaskiya ina son aikina sosai,, "nasan kina so lil sis, saidai kiyi hak'uri bazan iya jure rashinki kusa daniba.
Tayi murmushin gamsuwa da zancensa tace "nima inkayi nesa dani ina jin kewarka
Ya jantota ta kwanta bisa k'irjinsa cikin farin ciki yace "lil sis Allah yabarmu tare cikin so da k'aunar juna "amin zumana.




Daren ranar suna kwance bayan yagama yamutsata kamar yadda musulunci yakoyar idan mace tana hailah ga yadda mijinta zai bi da ita domin samun nutsuwarshi.


Ya gyara mata kwanciya a k'irjinsa yana shafa sumar kanta yace "lil sis *atunanina* bantaba kawowa zaki zama mallakina abin iko na ba sai gashi Allah ya mallakamin ke batare da nayi zatoba.
Tayi shiru tana saurarensa, yaci gaba "nayi ta mufarkin ina kwance dake kamar haka, wanda yaso yazamamin matsala saida na hana kaina barci da dare, nakwana nafilfili tare da karatun QUR'ANI sanna nasami sauk'i tare da tai makon addu'o'in da imam yabani ya d'ago fuskanta yana kallo tsawon lokaci, itama Ido ta zuba mishi kice da k'auna yaja numfashi ahankali tare da cewa "lil sis na soki da k'aunarki tun ranar da naganki, kuma aranar nayi alk'awarin zamowa yayarki mai baki kulawa na hakik'a, sabida haka ina rok'onki ki rik'eni amana nima zan rik'eki cikin aminci.
Yayi shiru yana wasa da k'irjinta.


Cikin sanyin murya tace "yaya Deen lallai kaid'in masoyina na hakik'a ne, nagode da kulawanka, nagode da so tare da k'aunar dakayimin tun bansan kaina ba, Allah yabiyaka da mafificin sakamako
"Amin ya amsa.


"Lil sis bani labarin yadda kike jina acikin zuciyarki, d'an dariya tayi tare da kaiwa k'ijinsa dukan wasa "muyi addu'ar shiga barci zumana hiran ta isa haka, kasan gobe kana da fita office dai, ya matse hannunta "nak'i wayon naki saikin fad'amin ko d'an mitsitsine.
"To bud'e kunninka kaji yako turo kunninsa bakinta ta sakar mishi kiss mai k'ara da sauri ya janye kunninsa yana sosawa, dariya tayi mishi tace kaji ko? ya tashi zaune itama ya zaunar da ita, "oya fad'amin ko yau in hanaki barci da aikin lada takama baki tanayi masa dariya ya soma balle bottom d'in rigar barcinta yana cewa "bari kiga insoma rage hanya ta kama hannunsa tana girgiza kai tana cewa "zanfad'a maka zumana "ehm ina saurarenki sweetie.


Ta damk'e hannunsa sannan tace "yaya Deen nasoma sonka tun sanda kadawo karatu nikuma lokacin nagama secondary school, alokacin ban d'auka so irin na aure bane, amma ranar da beastie tafad'an kai takeso, ranar har kuka saida nayi, nayi ta istiggifari tare da rok'on Allah yakawomin d'auki bisa wannan bala'i ace yayana uwa daya uba d'aya shinake so.
Da k'yar nasamu narage tunaninka sannan na sama zuciyata son ya saif da k'yar, to yin hakan yasa nasami sauk'i amma lokaci lokaci ina fad'awa kogin begenka, Ashe bansa niba mud'in da aure tsakaninmu.


Sannan ayanzu inajin sonka da k'aunarka har brain d'ina, jini da jijiyana tare da kashi da bargona har zuwa tsokana, nake jinka.


Rungumeta yayi yana kaimata kisses ta ko ina bakinsa nafad'in *"nagode! Nagode!! Ruhina*




Washe gari tare suka had'a break fast, bayan sun kammala karyawa yawuce office.


Gyara gidan tayi yafito tsaf sai k'amshin room fresh keyi.


Gidan d'an madai daici ne mai d'auke da gaton parlour tare da d'akin barci biyu, sai kitchen da toilet acikin kowani bedroom.


K'arfe hud'u dai dai Barr Deen ya iso gida cike da karsashi kamar badaga aiki yataso ba.
Bataji dirin motarsaba sai ganisa tayi tsaye ak'ofar shigowa ya zuba mata idannu fuskansa d'auke da murmushi.


Cikin yanga ta isa wurinshi ta rungumeshi dama yana ganin tasowanta ya bud'e hannayensa.
Sundad'e tsaye rungume da juna sannan ta jashi bedroom ta had'a mishi ruwan wanka.






Yacika cikinsa da girkinta mai dad'i yanata santi.
Yace "lil sis komi naki mai dad'i ne barinma cikin tsakiyar dare ta harareshi tare da murgud'a mishi baki ya kai hannu zai matse bakin ta mik'e taja baya tana dariya.




Rayuwa mai dad'i sophy da barr ke gabatarwa, sosai suke bawa junarsu kulawa.
Fanin kula da buk'atarsa sosai take jurewa, hakan na k'ara mata k'ima a idonshi, domin yasan tana k'ok'ari da buk'atunshi sosai.
shiyasa azumin littani da alhamis baya wuceshi, har yakoya mata, itama tanayi.

Tunda tacika sati biyu mamie takirashi tace yamaido da ita, yace to gasunan ahanya tasa Ido.


mamie har da yi musu abincin tarba na musanman amma har dare yayi bata gansuba kuma wayarsu kashe, sai washe gari tasami wayar sophy tayi ta fad'a sun sata wahala ba su zoba, ita dai sophy dariya abin yabata, ta tabbatarwa mamie da bawani kawotan da zaiyi hasalima yace maganar aiki babu, mamie ta datse kiran tana jinjina rashin ta idon barrister.


Tundaga nan bata k'ara yi musu maganar dawo wantaba, sai dai takan kirasu taji lafiyarsu hakama Abba kullum sai sun gaisa dashi.








*bayan waya shida*


Barr Deen yashigo yana kiran "sweetie! kayan dad'inna!! Ina kike? Albishirinki tafito daga kitchen tana goge hannunta da k'aramin towel, ta amsa "goro kuma fari sol, "meelan umma ta haihu yanzu jameel yakirani yake fad'amin.


Wani ihun murna tasaki tare da rungumeshi sai kuma tasoma rawa tana cewa "gobe zanga mamiena wayyo dad'i.


"Namune ko naku? Yaja hancinta ya amsa "soja akasamu ta mannawa gemunsa kiss tace Allah raya. "Amin.


"Wayyo beastie ansan duniya yanxu, "au da bata san duniya ba? "Eh bata saniba sai yanxu da ta haihu, yayi murmushi to kema sai kin haihu kenan zaki sani? Ta amsa "eh ya dungure mata kai "mara kunya ta amsa "to aikaine malamina, zai kamota ta zille takoma kitchen yabi bayanta yana cewa lil sis kinfayi k'iba tare da k'ara cikowar komi na Jikinta barinma k'irjinki da hips d'in ki ga kuma hasken da kike k'arawa,


shin ko miye sirrin? Tana motsa stew ta amsa "Kaine sirrin daka matsa musu da yamutsa.
Yasa dariya yamatsa ya kashe gas d'in zatayi magana yarigata,
"zo muje incigaba da yamutsa kayana, ta tureshi zata gudu ya cafkota.




Ana saura kwana biyu suna sukayi parking sukayowa garin Kaduna tsinke, Wanda ko mamie basu fad'ama suntasoba domin so suke subata surprice.




















*Mrs j moon*
[5/11, 2:43 PM] Mrs j moon🙂: *ATUNANINA*🤔
*61 to 62*
*©Safiyya*


Gidansu suka fara isah, cike da jin barci sophy ta fad'a bisa bed, tanaji barr yana cewa "a'a lil sis kiyi wanka mutafi gidan mamie zaifi da ki kwanta barcin nan naki nafama wanda narasa gane kanshi sam akwana kin nan.
Ta bud'e idanunta da suka soma yi mata nauyi sabida da jin barci tace "Allah zumana bazan iya xuwa ko ina ba yanzu sai nayi barci ko na 1hr ne.
"OK to bari intafi inzo miki da abinci,


zuwa dare ko gobe kyaje gaidasu, ta gyad'a kai idanunta kulle ta amsa "to kadawo lafiya, ina gaida mamie. Ya fice yana mamakin wannan irin barci dazai hana lil sis zuwa ganin mamie yau.


Sai daf da magrib ta tashi tayi mik'a tare da salati sannan fad'a toilet.


Bayan tafito ta gabatar da sallar tazauna har lokacin isha'i yashiga ta gabatar dashi tayi safa'i da wutri tazauna gaban mirror tayi kyalliya mai sauk'i ta zura wani swiss lace mai manyan flowers mai ruwan goro.
Tayi kyau sosai kuma d'inki yayi mata d'as har ya d'an kamata a k'irji sai alokacin ta fahimci lallai maganar barr gaskiya ne domin ita kanta tafahimci boobs d'inta yak'ara cika kuma tayi 'yar k'iba mai ban sha'awa.
Tana shafa face d'inta ta furta "lallai aure babbar rahama ne.


Parlour tafito hannunta d'auke da gyelanta tare da pox d'inta wanda ta jefa phone d'inta ciki.


Shiru bataji motsin barr ba, ta hango kuloki a jere bisa dinning table ta isa ta bud'e domin ganin mike ciki.


Masar alkhama ce tayi taushi sai miyan ugun wanda yawatatu da naman kaza sai k'amshi ketashi, gefe ga kunun aya mai dad'in anjefa k'ank'ara cikinsa.


Tasaki murmushi tace "Allah sarki mamiena,Allah yarabaki da sharrin duniya da dukkan wani abin k'i "Amin ya rabbi ta tsinkayi muryan barr na amsawa.
Tajuyo tana kallonsa, ya iso yarumgumeta ya manna mata kiss a goshi ya furta "kinyi kyau my beauty ta maida mishi da martani a bisa labbabsa tare da cewa "kaima kayi kyau har kafini, dariya yayi yace "inna fiki kyau ai da sai insoma sa nik'af tana dariya tace "tafd'i jan!! Ai ko da ankai labarinka BBC "yo ayi takaiwa man ba mutuncina nakareba kada mata su kwacewa matata ni, hannunsa ta ciza kad'an yayi k'ara cike da wasa.


Suka zauna cin abinci cike da raha har suka kammala sannan yad'auketa suka tafi gidan mamie.


Mamie tare da aunty Bahijja suka samu suna kallo.
Da sauri ta isa ta rungume Bahijja tana cewa yaushe kika zo? Bayanta tasha ta amsa "d'azun anan nasami bros ta juyo tana kallon barr ta tura baki "shine baka fad'aminba ko? ya kanne mata ido d'aya yace "sanda kike barci nafad'a miki ko kinmanta? Ta kauda fuska "bawani kafad'amin.
Ta kallo mamie taga ta zuba mata idanu murmushi d'auke afuskanta, tamik'e zata isa wurinta bahijja ta janyota ta rad'a mata a kunni "kanwata ko munsami k'aruwa ne? Ta zame tace "namefa? "Baby ta fad'a ahankali itama ahankali tace "a,a yanxu hakama ina period murd'e mata kunni tayi tafurta "Wallahi k'arya kikeyi yarinya, tana liliya kunninta tana dariya ta isa wurin mamie ta zauna gefen k'afafunta ta sunkuyar dakai tace "mamie barka da war haka, "barkanmu yarinyar mamie dafatan bakya zazzabi ko? "Inayi amma da dare shimad'in ba sosaiba "to sannu Allah yaraba lafiya, ta zare Ido tace "Allah mamie bani da komi ni kitambayi yaya Deen kijima.


Barr ya ja gemunsa yace "baruwana nikam, nasan dai bakiga bak'onki ba watan jiya dana yau
Tayi mishi k'uri tana tunano yaushe tayi last period natama. Take ta tuno wata biyu kenan, ita sam ta manta ma da wani mensuration period ma.
Ta soke kanta jikin mamie tace "Allah mamie sharri ya kemin nibanda komi "uhmm yarinyar mamie miyasa kikeson boye mana abin farin cikinmu? Ta kwabe fuska kamar zatayi kuka "Allah mamie ban saniba nima, murmushi mamie tayi tare da cewa "amma ke wata iriyan nurse ce haka mara kula? "Uhmm nifa mamie... Dasauri barr yatareta "sweetie kada kice komi, nadai kusa zama baba kawai, hararansa tayi sai kuma ta cukume mamie tana dariya, duk kansu sukasa dariyan suma cike da farin ciki.


Koda Abba yadawo, Bahijja ta fesa mishi, yayi murna sosai yayi addu'an Allah raba lafiya.
Yayin da sophy tayi ta nok'e kai wai ita kunya.


Adaren taje gidan umma inda beasties nta take.
Sabida tazo gidan umma ciwon nak'uda ya kamata ko kafin a fidda mota faya ta fashe, sai kawai aka kira nurse a kusa dasu takarbi haihuwan.
To shine akabarta tayi wankanta anan.


Sophy tunda ta rik'e baby sai kallonsa takeyi cike da sha'awa.
Inta kalli jamee sai ta kalli baby sai kuma ta kalli jameel wanda suka tarad agidan, zuwacan sai tasa dariya.
Jamee ta dallah mata harara "to uwar sharri mikike tantancewa? Cike da dariya tace "ina duba wa yafi wani son abin lokacin yin cikin, sabida naji ance in yaro yafi kama da d'aya acikin iyayensa to wannan yafi kwazo yayin samuwarshi.


"La'ilaha illallahu!! Jamee taja salati tana kama haba, tace "Beastie yaushe kika zama mara kunya haka? Su jameel suka kwashe da dariya har da sophy, ta kallo barr tace "kinganshi nan shine ya lalatani "baruwan yaya Deen kedai dama can kunyar gulma ke gareki, ta kaimata duka abaya tace "aike kika koyamin "dalla ni baruwana "tasaki dariya tana kallon barr tace "zumana Ai ruwanta na jikinta ko? Ya kauda fuska cike dajin kunya yana jinjina rashin kunya lil sis data koya yanzu.


Jamee da jameel suka soma yi mishi dariya, tana sabe da babyn aka fad'anta ta bi hanyar fita zuwa parlour tana cewa "baby dai yayi kama da babansa, wannan yanuna Beastie bata da k'wazo a tafiya zuwa birnin dad'in.


baki bud'e barr yabi bayanta da kallo, yayin da jameel ya kallo jamee

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads