Showing 3001 words to 6000 words out of 18811 words
Chapter 2 - Yar Mulki book Complete document by Maryam A. Ahmad .txt
ajikin ta.
Tana shiga wajen attention ya dawo kanta frinds an taru,da sauri sukaxo suka rungume Amal,sannan aka cigaba da casu.
Ran momyn Amal ya baci sosai,tace jakadiya kiramin haneefa,cikin girmamawa jakadiya ta risina tace to ranki ya dade,ta fita cikin sauri.
Haneefa na xuwa momy ta dauketa da mari,tace maxa maxa ki wuce ki dakkomin kudina da kika dauka,sata kuma kika koma ??
Hawayene kawai ke xubowa daga idon haneefa😭😭,ta rike kumatunta da hannu daya saitin inda momy ta mare ta,tace wallahi ban daukar miki kudi ba😭😭.
Karya kike,rufemin baki munafuka,to baki isa ba,kudi har two fifty thousand naira?? nafada miki,nabaki nan da 15minutes ki fitomin da kudina,kuma bari mai martaba ya dawo dole kibar gidannan,wannan ai abin kunya ne agaremu ace a gidannan ake sata,
Baba mareeya na dai dai window,a labe tana jin abin dake faruwa,banda kuka ba abin da take.😭
Haneefah tace,dan Allah momy ina rokonki karki bata sunana awajen mai martaba,😭wallahi ban dau kudinki ba,tsawon shekaru muna tare da ina sata da tuni kin dade da sani,momy ban dauka wallahi.😭
Momyn Amal tace na dai fadamiki,kifitomin da kudina, kuma gidannan dolene kibarshi,gobe-goben nan na fadamiki,Allah ya dawo da maimartaba lafiya.
Haneefa kuka kawai take😭😭 aranta kuwa cewa take ya Allah kabani mafuta.
Maryam y.Ahmad
Hauwa s.Ahmad📚
😭😭😭
[10/16, 7:57 PM] +234 706 370 3994: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
16-20
✍✍
Kida ne kawai ke tashi awajen birthday din,Afrah tayi kyau sosai,haka sauran kawayenta,dukkansu english wears sukasa kowacce da irin kalar kyan da tayi,yau itace ranar da Afrah ta cika shekara goma sha bakwai a duniya,kamar yadda aka rubuta ajikin cake din,"SWEET SEVENTEN"
Amal da mufeeda ne suka tsaya ta sides din Afrah sauran friends kuma suka tsaya daga baya suka dau hotuna,kana ganin su kaga manyan yara kuma 'yan gayu,kowacce ji take da kanta saboda naira ta gama ratsa su,haka suka gama budirin su,sannan kowa ya watse.
Amal na kan hanyar komawa gida,tuki take amma kamar bataso saboda ta gaji sosai ji take dama ta fita da drivern ta,haka dai ta karasa gida ba cikakken kuxari.
Tana shiga daki ta yar da jakar ta akan gado,ta juya ta kalli haneefa dake kan gadon ta a kwance sai shashshekar kuka take,Amal tayi tsaki ko ajikin ta kukan da haneefa take bai dameta ba,ta fita ta wuce falo,ta xauna,sannan ta sa bayinta guda biyu suka fara mata tausa.
Tsawa ta daka musu,kaiiii nifa tausa nace kuyimin ba cewa nayi ku karyani ba,nan da nan jikin su ya fara bari saboda duk bayin gidan da masu aikin gidan tsoron Amal suke,atare sukace tuba muke ranki ya dade,nan fa sukaci gaba da lallaba jikin Amal kamar kwan da ba'ason fashewar sa.
Jakadiya na shigowa falon ta gurfana a gaban Amal tace ran gimbiya ya dade hajiya nason ganinki, wanna shine sunan da kowa yake kiran Amal dashi a gidan kawayen ta kuma da 'yar mulki suke kiranta ko Amal,Amal ta dago ido ta kalli jakadiya,ok Amal kawai tace daganan bata sake magana ba,ta tashi ta nufi dakin momyn ta.
Tana shiga dakin kan cinyar momy ta wuce ta kwanta,momy ta shafa kan Amal tace kin dauki kudine a brief case dina?? Amal ta juya kanta idon ta acikin na momynta tace ehhh,dana gama shiryawa na fito sai na tarar kina wanka ni kuma bana so na bata lokaci shiyasa na dauka kawai na tafi,nasan ko kina nan ma cewa xakiyi kawai na dauka,kadan daga cikin aikin Amal kenan,momy tace me xaki siya dasu?? Cikin shagwaba Amal tace kaiii dan Allah momy harsai kin,tambayeni abinda xanyi da kudi?? Sannan tace contribution na bayar na birthday din Afrah,momy kinsan mune manyan friends dole muyi wa Afrah gift mai kyau,ni gani nake ma yayi kadan.
Momy tace ina bude brief case din naga an debi kudi, nasan ba wanda xai dauka sai ke,amma kinsan me nayi??Amal tace a'a,momy tace haneefa na kira nasa ta agaba nace sai ta fito min da kudina,kinga wannan itace hanya mafi sauki da xamu koreta daga gidannan,dankuwa idan mai martaba ya dawo yaji labari baxai yarda taci gaba da xama acikin gidannan ba,saboda ko kadan baya son abinda xai xubar da martabarsa da kuma ta gidannan.
Amal tace yesssss momy kinyimin dai dai,gara ma tayi gaba,dan wallahi na tsani xaman ya rinyarnan agidannan,duk farin cikin danake ciki idan na ganta sai raina ya baci.
Momy tace ai yarinyarce sai kace mai asiri,kowa sonta yake,ba abinda yake bani haushi irin yadda mai martaba yake sawa ku xabi abu tare idan xai sai muku.
Amal tace basai ta xaba ba mugani yanxu,sai dai awani gidan,Allah ya kaimu goben ya dawo.
[10/16, 7:57 PM] +234 706 370 3994: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
21-25
✍✍
Haneefah tayi kukan har ta gaji,bakin cikine kawai yake yawo a ranta,tunanin dawowar mai martaba kawai take,yadda yake ganin hankalinta ace ta saci waddan nan makudan kudin,daga tayi wannan tunanin sai ta fashe da kuka,sannan ta tuna asalin ita wacece nan ma hankalinta ya kara tashi,tun yamma haneefa take kuka har sai da lokacin sallar magrib yayi,dakyar ta tashi da shiga toilet yayi alola bayan ta fito tayi sallah,haneefa bata tashi daga kan sallaya ba ta fara mika kukan ta wajen ubangiji kamar yadda ta saba.
Hannu biyu ta daga sama👏 ta fara addu'a kamar haka a fili.
Ya Allah ina rokonka ka bani ikon cin wannan jarabawar,Allah kai kace mu roke ka bani da wanda xan roka bayan kai,ya Allah ka karamin hakuri da juriya,ka kuma kareni daga sharrin mutum da aljani,da masifar gabas da yamma kudu da arewa,ya Allah ka bani mafita,ka kawomin farin ciki na har abada.
Ya Allah ka kareni daga sharrin dake cikin wannan ranar,nan fa kuka yaci karfin haneefa😭 ta cigaba da cewa Allah ka sadani da alkhairan dake cikin wannan ranar,Allah ka sakawa iyayena da alkhairi,Allah ka sakawa mai martaba da alkhairi.
Banda kuka ba abin da haneefa take😪 ,momy da Amal kuwa suna can sai faman hada wa haneefa tuggu suke.
Haneefah tana idar da addu'a ta wuce wajen baba mareeya,tana xuwa ko magana bata iyayiba ta xauna akusa da baba mareeya,sautin kukane kawai yake fita daga muryar ta,baba mareeya tayi sauri ta dago tare da matsar da kwanon da take kadi daga gabanta,haneefa kiyi hakuri insha Allahu wannan yanayin baxai taba dawwama ba watarana xaki sami canjin rayuwa insha Allah,shi kudi da sarauta da suke ji dashi mai karewa ne,gaskiyar ki kuwa baxa ta taba karewa.
Har alokacin da baba mareeya take magana haneefa kuka kawai take,ta cigaba da cewa nasan cewa baxaki taba iya daukan ko da tsinke na mutum ba,balle makudan kudi haka,haka kuma duk ma'aikatan gidannan kowa yasan baki dauka ba dan dai bamu da iko ne ba yadda xamuyi.
Haneefa tace baba mareeya mai martaba ya rikeni tamkar 'yar da ya haifa komai yana yimin,idan yaji ance na dauki kudi baxai taba jin dadiba ni dai kawai barin gidannan xanyi,baba mareeya tace a'a haneefa idan kika tafi nima ai baxanji dadi ba saboda bansan hannun wanda xaki fada ba kinga ba wanda kika sani,dan haka kiyi hakuri Allah ya kaimu goben muga abinda xai faru idan mai marta ban ya dawo.
Suna cikin wannan tattaunawar ne sukaji ankira sallah,haneefa tace baba mareeya bari na shiga ciki nayi sallah baba mareeya tace to amma dan Allah ki kwantar da hankalinki insha Allahu ba abin da xai faru,haneefa tace toh tare da goge hawayen dake xubowa daga idon ta.
Haneefa tana da hankali sosai gashi ta dace hankalin nata ya hadu da addini,ko kadan bata wasa da sallah,tana ganin girman naga ba da ita komai talaucinsa,bata da yawan magana barkatai sai ta kama,shiyasa ta shiga ran yaya Abdul sosai saboda baya son mutum mai rawar kai da yawa.Allah sarki haneefa baiwar Allah.
Sukayi sallama da baba mareeya,haneefa ta shiga cikin gida,tayi sallar isha,ranar ko karatu bata iyayi ba,gashi da safe tana da test,danma akwai brain ko batayi karatu ba bata tunanin shiga test ko exam,haka ta kwanta dakyar bacci ya sace ta.
Asuba nayi haneefa ta tashi tayi sallah,tana kallon Amal sai sharar baccinta take,har xata tasheta kawai sai ta fasa saboda tasan ba tashi xatayi ba,bayan haka kuma masifa ce kawai xata sha.
Haneefa tayi kyau sosai,amma kana kallon fuskarta kasan akwai damuwa mai tarin yawa,ta nufi sashen momy don ta gyara kamar yadda ta saba.
Tana shiga dakin momy ta daka mata tsawa,what are u doing here?? Muryar haneefa cike da tsoro tace momy dama xan gyara dakin ne,cikin masifa momy tace ok,to banason gyaran,yau kuma idan na barki kika shigomin daki brief case din gabadaya xaki sace ai,haneefa tayi shiruuuuu kamar ruwa ya cinye ta.
Momy tace to bari kiji infada miki daga yau banaso ki kara shigomin daki,keee falo na ma haka,barauniyar banxa barauniyar wofi,ciki shouting tace "oya get out of my room stupid"....
Haneefa kam sai hawaye,jikinta a sanyaye ta bar dakin.
Tana fitowa ta nufi hanyar part dimsu,kanta akasa ta wuce ta gefen yaya Abdul dake kan dining yana break fast,saboda bacin rai bata ma san yanan ba.
Yaya Abdul ya kira sunan ta,haneefa,tajuya slowly ta fara kokarin,seta kanta,gashi ya riga yaga hawayen dake fuskarta.
Yace xo nan,ta karasa kusa dashi,yace haneefa what's wrong?? tayi shiru,ya sake cewa meya faru kike kukane haka?? Still batayi magana ba hasali ma hawane ke kara xubowa daga fuskar ta,cikin yana yin damuwa yaya Abdul yace ehhnn ina jinki,muryar ta na rawa tace ba komai,yaya Abdul yace,no no no no no,banyarda ba,haneefa tace mo"..momy ta katseta,tace dalla can rufawa mutane baki,Abdul yarin yar nan sata ta koma a gidannan,250,000,naira ta dauka jiya a brief case dina,a fili kamar baxata aikata ba.
Abdul yace haba momy,me haneefa xata dau kudi tayi dashi?? Momy tace ok dama ka saba bin bayanta ai,yaya Abdul yace bahaka bane amma dai gaskiya momy kisake duba kudinnan da kyau,ko kinyi misplacing dinsu.
Momy tace ba wani misplacing danayi,gatanan ka tambayeta inda ta kaimin kudina,momy ta juya ta shiga part dinta tare dayin murmushin mugunta aboye...😊😊.
Tausayin haneefa ya kama yaya Abdul,yace take heart haneefa,kije school idan kin dawo sai muyi magana karki makara.
Haneefa tace to ta shiga daki ta tauki jakarta da mayafi tasa takalmi ta wuce school...
Luv yhuuuu ol💞
By
Hauwa s.Ahmad&
Maryam y.Ahmad📚
Luv yhuuu ol..💞
[10/16, 7:58 PM] +234 706 370 3994: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
26-30
✍✍
Tunda haneefa ta fita yaya Abdul yake tunanin ta,yana matukar tausayin ta,yadda momy take treating dinta a cikin gidan,kamar batasan ciwon haihuwa ba.
yana cikin wannan tunanin yaga kiran mai martaba na shigowa wayar shi,yayi picking call din sannan yace Hello Abba,mai martaba yace Abdul ya gida ya su momy?? Abdul yace lafiya kalau Abba,maimartaba yace,yace karfe 4:00pm jirgin mu xaiyi landing,sannan yace,,Abdul na matsu nasaka a kwayar idona,Abdul yace Abba ni kaina ji nake kamar kayi shekara da tafiyar nan,sarki salahuddeen yace wannan ne karo na farko dana farayin tafiya babu kai,haka kuma itace tafiya ta farko da batayi min dadi ba.
Mai marta ya kula cewar jikin abdul a sanyaye yake yace Abdul kodai baka da lafiya ne?? Naji muryar ka sabanin yadda nasabaji.
Abdul yace a'a lafiya kalau Abba,mai martaba yace Abdul karka manta nifa mahaifin kane,nine komai naka arayuwa,dan haka idan kana da damuwa ni yakamata ka fara fadawa.
Abdul yace daddy ba komai,mai martaba yacewa Abdul ka shirya idan na dawo inason nasan menene damuwar ka,Abdul yace to Allah ya dawo dakai lafiya.sukayi sallama.
Yadda marmartaba yaji yanayin Abdul yasan cewa kwarai yana da damuwa,fadamasa ne kawai bayasonyi,yana son Abdul sosai shiyasa komai kankantar damuwa yake fahimtar ta daga gareshi.
Ko kadan mai martaba bayason abin da xai batawa Abdul rai,ya dau son duniya ya dora masa,haryanajin idan Abdul baya tare dashi kamar babu wani babban sashene a jikinsa.Alokacin yaji kamar yayi tsuntsuwa ya dawo dan kasancewa tare da Abdul.
Tuki kawai haneefa take amma hankalinta baya duba yanayin yadda xata seta motar akan titin,bata ankaraba sai gani tayi ta kade wata yarinya da mamanta.
Da sauri haneefa ta fito a gigice,kafin kace meye wannan har mutane sun taru awajen,a rikece haneefa ta durkusa agaban wannan matar tana cewa sannu kinji ciwo?? Haneefa ta daga yarinyar,ganin hankalinta ya tashi sosai maman yarinyar tace yarinya karki damu banji ciwo ba,sai dai ni ta yarinyata nake,kalmar da matar ta fada ta tunawa haneefa inda yake mata ciwo,a ranta tace da ina da mahaifiya nima nasan xataji xafin duk wani abu daxai sameni.
Yarinyar tayi xumbur ta mike tace mama nima fa banji ciwo ba,haneefa taji wani irin dadi ganin yarinyar ta ware,tacewa yarinyar sannu,sannan tace baba ina saurine wallahi ban kula ba,tabasu hakuri sannan ta dakko 5000 a jaka ta basu ganin cewar suna da karamin karfi.
Motar da Naseer yake ciki na karasowa wajen driver'n shi ya yunkurin fita don yayima haneefa magana saboda tayi blocking hanyar,Naseer yace bari na fita da kaina,driver'n yace to.
Naseer ya fito cikin wata bakar suit,ya daura red neck tight ne a wuyanshi,yayi kyau sosai,Naseer kyakykyawan saurayine maiji da kanshi,shine first born wajen mai girma governor'n kano Alhaji muhammad salees.
Ya karasa kusa da haneefa ya nuna ta yace ke wannan wanne irin sakarci haka? Kinxo kinyi blocking hanya,ta sama kike so mutane subi ko yaya??
Haneefa ta watsawa naseer kallo da kyawawan idanun ta,tace malam kayi hakuri bawai nayi hakan intentionally bane,bata sake magana ba ta juya kawai ta shiga motar ta ta nufi makaranta.
Naseer yayi mamakin yadda haneefa ta bashi ansa cikin masalaha,yadda yaga tsananin kyan halittar ta ya dauka xatayi girman kai,gwiwar sa tayi sanyi yaji kawai ta gama birgeshi,yayi wani shegen murmushi ya ciji gefen lebensa kadan ta gefe daya,sannan ya koma cikin mota.
Haneefa na shiga school tayi roushing xuwa class,kowa yayi tsit sun fara test din wasu ma har sunfito,5ive minute ya rage ayi submitting gabadaya,lecturer'n bai hana haneefa shigaba,kawai cemata yayi tym na cika xai karba, he will not wait for her,haneefa ta yarda tayarda akan hakan.
Haka tayi test din cikin minti biyar,kowa yayi sunmitting.
Already hidaya ta fita dama,haneefa na fitowa daga hall din ta wuce wajen da suka saba xama ita da hidaya,tana tuwa ta xauna,hidaya ta jefo mata tambaya kamar haka.
Haneefa ya akayi kika makara sosai haka?? Haneefa tace wallahi na dan bige wasune a hanya shiyasa,sai da na tabbatar da lafiyar su sannan na taho,hidaya tace eyyyahhh Allah ya rufa asiri,haneefa tace amin ya Allah.Daganan haneefa bata sake magana ba,tunani kawai ta tafi wanda har ya kaita ga immagination,harta hasko a idan xuciyarta mai mar taba yace ta kwashe nata ya nata ta bar masa gida,ita kuma sai kuka take.
Ashe har a fili hawane ke xubowa daga idon ta.
Hidaya ta xuba mata ido har tsawon 2minutes abin yana bata mamaki,amma inaaaaa haneefa batasan tanayi ba.
Hidaya tace hanny me yake damunki?? Haneefa tayi firgigit ta dawo daga immagination din da take,tace ba komai.
Hidaya tace haneefa wanne irin tarayya mukeyi?? Ace abu yana damunki amma inaji ina gani bani da matsayin daxaki fadamin,nasha ganin yanayin ki cikin damuwa idan na tambayeki sai ki nuna ba komai.
Ni ina ganin bai kamata ba.
Haneefa tace am