Showing 9001 words to 12000 words out of 18811 words
Chapter 4 - Yar Mulki book Complete document by Maryam A. Ahmad .txt
Haneefa ko uhmm batace ba,tayi banxa kamar bata ji,ta mike ta nufi kitchen.
ROYAL BLUE doguwar riga tasa da akayi mata kwalliya da red stone,shape din rigar ya fita,tayiwa haneefa kyau sosai,lallausan gashin kanta a nannade yake,xakayi tunanin acuci tasa,tasa jan dankunne karami a kunnen ta,ta yafa karamin gyale,sannan tasa flat shoe ja.haba ai kyan ba'a magana.
Tana shiga kitchen din ta bude bridge ta dakko ruwa da lemu tasa akan faranti,ta dakko hadadden glass container ta shiga store din dake kitchen din ta xubo danbun nama,tasa a gefen ruwan da lemu,ta kama farantin da hannu biyu sannan ta nufi falon da su Abdul suke xaune.
Tayi sallama,suka ansan idon naseer nakan wayarshi ko kallonta baiyi ba,ta nufi wajen da suke gently takarasa gaban su,tatsugunna ta ajiye farantin a nutse,Naseer na kallon kafar haneefa ya rikice saboda kyan halittar ta,sannan ya kalli xaratan yatsun hannayen ta,in takai ce muku saida naseer ya kalleta from head to toe,ta gama bigeshi,ga saje da ya kwannata yayi luf luf a gaban goshinta da gefen fuskarta ya kara birgeshe,kaiii Allahu Akbar yace aransa,Allah yasa wannan kyan nata ya xama mallakina,haneefa ta katse shi da cewa ina wuni,dakyar naseer ya iya ansawa ji swt voice din da bai taba karo da itaba duk cikin matan da suke masa roushing,ya basar gudun kar a ganoshi,Abdul yace weldone haneefa,Naseer yace wawww nyc Name aransa,gaskiya she must be myn,i lv u hannyfa ya lumshe ido.
Abdul Naseer bismillah,murmushi kawai yake,Abdul yace aboki I can c dat r smile increased,ya basar just lyk that.
Bayan sun gama,suka sha hirar su batare da Naseer ya fadawa Abdul sirrin da ransa ba.
[10/16, 8:00 PM] โช+234 706 370 3994โฌ: ๐บ'YAR MULKI๐บ
2016
51-55
๐โ
Mai martaba da sarki,suma falonsa suka koma,yasa aka kawowa his excellency kayan motsa baki suka sha hira,sannan suka koma gida shi da Naseer.
Haneefa na komawa daki tace,Amal xan fada miki gaskiya yau kam ko xakiji haushina bai kamata kiringa fadawa yaya Abdul haka ba,ko da ba agaban idonsa bane.
Cikin masifa Amal tace hehehehehe,look haneefa karki kara shiga tsakanina da yaya Abdul,kin fini kusanci dashine?? Banda munafurci ina ruwanki?? Dama ke kikayi munafurcin da bama jituwa ni da yaya Abdul,mtshwwww tayi tsaki,so maintain ur self.
Haneefa tace aranta,da ina da freedom a gidannan da saina tsinkawa Amal Mari.hhmm.tace sannan ta ci gaba da harkokinta.
NEXT DAY.....๐
Motoci ne guda biyar Amal tasa aka jerasu,ko wacce bata da number,'yar mulki ne a number motar gabadaya,ansa 'yar mulki-1,2,3,4 up to five.kowacce mota da number da take dauke dashi.
Amal ta fito cikin kasaita,kuyangun ta biyu na daga gefenta,tana wata tafiyar Mulki,ga kuma guards dinta guda biyu,ta shiga motar ta xauna tare da masu yi mata hidima,driver motar 'yar mulki-1 ya fito ya risina agaban Amal yace ran gimbiya ya dade ina xamu?? ko magana Amal batayi ba ta kalli kuyan garta alamar ta bashi answer,jiki na rawa tace,banki gimbiya takeso taje xatayi thumb print.
Haka suka nufi bank din motocin na tafiya serially.
Motacin na tsayawa,guard dinta daya ya shiga bank din da sauri yace,kowa ya fita gimbiya Amal xata shigo,sanin rashin mutuncin Amal yasa kowa baiyi gardama ba ya fito.
Mutane sai kunkuni suke,yadda baxa ta gane ba,kowa yasan halinta agarin,haka kuma kowa ya dauka sarkine yake ya shagwabata shiyasa akarasa mai kai karar Amal wajen maimartaba.
Motar da take ciki mai tudu ce ta xuro kafafuwan a hankali ta fito,sannan tace kuyangun ta da body guards su jirata a kofar bank din.
Amal taga wata kyakykyawar budurwa a tsaye suna hada ido,ta karasa kusa da ita,ta daga hannu da sirfa mata mari,sannan tace banason too much kallo daga yau,take note.yarinyar tasa kuka.kowa na wajen abin ya kona musu rai.
Saida ta gama abinda xatayi ta fito sannan kowa ya koma cikin bank din.
Naseer ya kira Abdul a waya yakai 6missed calls bai daga ba,Naseer yaji kamar ya fasa wayar dake hannunsa.sai ga kiran Abdul yana shigowa wayar sa.
Haske kawai wayar tayi,bai bari ta fara ringing ba caraf yayi picking call din,yace hlo,Abdul yace sorry Naseer bana kusa da wayar ne.
Naseer yace no bad,sannan Naseer yace nifa nayi mata a gidanku,Abdul yasa dariya๐ yace wakenan?? Abdul yace kanwar ka,Abdul yace kannen nawa ai biyune wacce daga ciki?
Naseer yace karamar,yace Amal kenen,Naseer yace nooo haneefa naji ka kirata dashi ranar da mukaxo da his excellency,yace haneefa ce babba sannan Amal ai,sannan yace hahhh no wonder ashe kamuwa kayi shiyasa ranar naga smile yaki karewa,Naseer yayi dariya.๐
Abdul yace congrats aboki,dan kuwa kayi sa'ar mata,nasan dai kyau ne ya rude ka amma ka dace haneefa akwai kyan xuciya dana fili,Naseer yace ka tura min no dinta to yanxu, amma ka fara fada mata kafin na kirata,Abdul yace it's alright.Naseer yace bye sai naji yadda kukayi.
Suna gama waya Abdul ya kira haneefa suka fara tattaunawa kamar haka.
Ya fara lallaba haneefa saboda yasan kokadan bata da rawar kai akan maxa,yace kawanta,haneefa tace na'an yaya Abdul,yace akwai saurayin da kike tare dashine presently?? Tace a'a,baxan iya irga wanda suke sona ba amma nayi decline dinsu,tace,yaya Abdul ko kadan banason yin saurayi.
Abdul yace koda ni na kawo shi? Haneefa tayi shiru kanta a kasa,saboda tanajin nauyin yaya Abdul.
Friend dina da kika same mu a falo yester tym shine yake sonki,haneefa bashi da problem ko kadan.
Yace Naseer mutumin kirkine kanwata kinsan baxan bari ki auri wanda bai kamata ba.pleasee kice kin amince.
Haneefa baxata iya yiwa Abdul musu ba tace shikena ba damuwa.Abdul yace na bashi number ki at any giving tym xai iya kiranki.tace ok.
Aranta take magana tace, bansan iyayena ba meyasa xan yarda nafara maganar auren?asan ko bayanxu ba sai anyimin gorin iyaye,gashi baxan iya embassing yaya Abdul ba.ni maryam (haneefa) inaxan sa kaina.Allah ka bani mafuta.
Abdul kuwa shi mantawa ma yake haneefa ba 'yar gidan bace,saboda tun bata da wayo take gidan amma ita kullum abin yana ranta.tace ya Allah ka kawo sanadi daxan fita daga gidannan naje har wajen da iyayena suke.ta fashe da kuka๐ญ.
2hours later....
Naseer ya kira haneefa a waya,ta daga hlo,muryar haneefa akwai xaki,Naseer ya lumshe ido,yace ya gida,haneefa ta amsa lafiya kalau.
kina magana da Naseer mohd salees,frnd din yayan ki Abbdul,haneefa tace ok,yace naji dadi sosai da Allah ya hadani dake haneefa,i luv u morethan u anticipate.
Salon yadda Naseer yakewa haneefa magana yasa ta gane lallai da alama Naseer ya iya soyayya.
Taji har sonsa ya shigeta,har mamaki take,Naseer yace ina neman ixini bayan sallar isha naxo na ganki mai cikakken iko,haneefa tayi murmushi irin najin dadi๐,jin yadda naseer ya fasa mata kai.
Haneefa tace ai kaine mai cikakken iko,haneefa taji dadin sunan,Naseer ya karya murya cikkn salon soyayya yace baby na are u free?? Tym din yayi miki?
Haneefa ta sake murmushi,tace yayi,Allah ya kawo ka lafiya,Naseer yace,ok bye bye,take a very good care of ur self babynah,.
Ta ansa I will try,bye....
Gaskiya inason Naseer,rana daya kawai ya canja min rayuwa,ji nake kamar ban taba damuwa ba.
A kasan,xuciyar ta tace gara nasakk jiki muyi soyayyar mu,dan bansan lokacin daxan ga iyayena ba,inaji ajikina kamar naseer shine mijina.
Ya Allah ka xabamin abinda yafi Alkhairi.
Ashe Amal na tsaye akan haneefa,kallonta kawai take,ta gama fahimtar cewa haneefa sabon saurayi tayi,aranta tace ki gamashan soyayya ba mai auren shegiya a garinnan.tayi gaba part din mummy ta nufa.
Naseer da haneefa na xaune,sai hira suke kamar ba ranar suka fara haduwa ba,gabadayan su sunyi mummunan falling,Naseer yace yau shine gani na uku danayi miki amma kamar tunda Allah ya haliccemu na sanki haka nake ji,hanny tayi dareeya hmm kamar dagaske, sannan tace kamanta yau shine ganinka na biyu dani.
Naseer yace xaki iya tuna ranar da kika kade wasu a titin bypass,tace eh na tuna,nasan a rikice kike shiyasa baxaki ganeni ba,tundaga ranar naji ina sonki sai gashi Allah ya sake hadani dake.haneefa tayi murmushi.
Tace dama kaine? Kuwa ranar naji haji haushi,naseer ya gwiwar sa akasa yace baby am on ma kneels kiyi hakuri,haneefa tace do u want me to be on ma kneels too?? Yace noooo tace to ka tashi it's over.
I don't wanna miss u Naseer ya fada tare da watsawa haneefa kallo da sleeping eyes dinnan nasa,yace daddy najira na xamuyi wata magana ne.
Hanny tace ok,tarakashi mota sannan ta dagamasa hannu tare da fadin I luv u Yaya Naseer.
1month later....
Shakuwa mai tsanani ta shiga tsakanin naseer da haneefa,basa iya komai idan basuji muryar juna ba,naseer yana yawan xuwa shiyasa sukaji kanar sun shekara dari da fara soyayya,idan kaga yadda suke caring juna abin xai birge mai karatu saboda nasan kowa yasan yadda kulawa,damuwa,da kuma tausayi suke tasiri axuciyar masoya.
AMAL....
Amal batasan wanda yake xuwa wajen haneefa ba,ita dai kawai ta arawa haneefa lokaci,tana ta hada mugunta,wai sai sun gama shakuwa xata tona sirrin haneefa,cewar 'yar cikin shegece,tayi dariyar mugunta,tace soyayya manya๐๐.
Tofah idan Naseer yaji hakan xaisa yafasa auren haneefa??
By
Hauwa s.Ahmad&
Maryam y.Ahmad๐
For comment
08063495753
08033660286
๐๐๐๐๐
[10/16, 8:01 PM] โช+234 706 370 3994โฌ: ๐บ'YAR MULKI๐บ
2016
6โฃ1โฃ
๐โ
Su Amal na fitowa daga lecture,suka nufi wajen da suka saba xama ita da Afrah da mufeeda,guards dinta sukayi yunkurin take mata baya,Amal ta daga musu hannu alamar dakatar wa,tace nooo basai kun bini ba,daya nake so kawai daga cikin ku,akwai aikin daxan sa aimin,kawai ta juya suka cigaba da tafiya,haka daya daga cikin guards din yabi bayansu.
Suna karasawa wajen suka xauna,guard din Amal kuwa na tsaye yana jira abashi umarni,Amal ta dora kafa daya kan daya,tace luqman aikin danake so na saka ba mai wahala bane amma,yace ok ur highness,ta bude jakarta ta dakko number motar mujaheed a takardar datayi writting down dinta ta mika wa lukman,yasa hannu ya karba cikin respect,tace motar da take dauke da wannan number tana cikin tana cikin makarantar nan,kayi going round ka tabbatar ka sameta,sannan inaso ka sace iskar tayoyin motar gaba daya,yadda ba xa'a iya gyarawa ba sai dai a sake tayoyin.
Luqman ya karba yace done.Amal tace bafa naso asami matsala,make sure that u do as I mentioned,tafada cikin mulki da kuma jan kunne.
Cikin girmamawa luqman yace,angama,sannan ya juya ya tafi.
Afrah da mufeedah suka tafa atare,mufeeda ta ce nyc idea 'yar mulki gaskiya kin hadu,Afrah ma tace lallai kam yau ran mujaheed idan yayi dubu sai ya baci,suka kwashe da dareeya,Amal tace hah ai ba ayi masa komai ba yanxu,this is just d begining.
Kamar yadda Amal ta umarci luqman haka yayi gabadaya saida ya sace tayoyin motar mujaheed tasss sannan yabar jikin motar.
Amal tayi sallama da su Afrah,drivers dinta suka jera motoci cikin tsari,kuyangunta kuma suka rakata mota,sannan suka nufi hanyar gida.
Mujaheed ya gama duk wani abinda xaiyi,so yake kawai yaje ya kwanta ya huta dan kuwa ya gaji,gashi har yanajin kansa yana sarawa.
Da sauri mujaheed ya karasa wajen da yayi parking motar shi,ya bude ya shiga,banda kanshi ba abin da motar take,yasa key sannan ya fara kokarin tayar da motar,kawai sai gani yayi wani waje yana bashi signal na red danger ga kuma hoton tayar mota daga gefen da red danger'n ke blinking,yace to meyake faruwa? Ya tambayi kansa.ya fito daga mota dan duba lafiyar tayoyin.yanasa idon shi an tayoyin yagasu a sace gaba daya,ransa yayi bala'in baci.
Shiruuuuu mujaheed yayi yana tunanin barnar da akayi masa,ya ja tsaki sannan yace wanne irin rashin mutunci ne haka? Wannan ai da niyya akayi,ya jingina ajikin motar tare da sakale hannayensa biyu a kirjinsa,ya sake yin shiruuuuu sannan yace duk cikin makarantar nan ba wanda xai min haka sai Amal.amma lallai yarinyar nan ya fada cike da takaici,sai ta gane kuskuren ta.
Mujaheed ya fito da wayar sa,yayi dialing number qualified engineer'n shi,yace inason irin tayoyin motata gaba daya hudun,ka ara kudi ka siyo,kasameni a cikin school,idan kaxo sai mu biya ta ATM na baka kudin,seti yace to ba damuwa yanxu xaka ganni insha Allah.
Haka seti yaxo akasa tayoyin gabadaya,sannan suka wuce ya bashi kudin.
Mujaheed da yakeson fita daga school tun kafin magrib shine sai da ya kai har karfe tara na dare.
Mujaheed ya gama tsara abinda xaiyi wa amal dan kuwa ya rantse sai ta gane kuskurenta.
EMIR'S HOUSE....
Haneefa yau bata je school ba,tun safe tana daki a kwance,ba abinda take sai tunani kala kala,amma tunanin nata yafi rinjaye akan inda xataga iyayenta,aranta tace oh ni haneefa,yanxu idan iyayena xan fara nema ma bansan ta inda xan fara ba,ni dai daxaman gidannan gara naje na sami wani gidan ko shara da wanke-wanke ne na ringa yi,tana cikin wannan tunanin taga kiran Naseer na shigowa wayar ta.
Ta saki wani murmushi,da har saida dimple dinta ya fito,ta daga wayar tare da fadin hello,Naseer yace mai cikakken iko I hope u r ok,wani irin dadi ya kama haneefa jin muryar naseer ya kirata da wannan sunnan,tace am fyn my dear,Naseer yace tun daxu ina office amma na kasa komai saboda rashin jin muryarki,totally banajin dadi idan banji ki ba,haneefa tayi murmushin da har saida ya fito fili tace,kamar yadda nima nakasayin komai kenan?
Naseer yace haneefa kenan kina ganin kamar son danake miki wasa ne ko?,u wil never undrstnd hw am feeling,haneefa am sincerely deeply in luv wit u.
Shiya sa xakiga bana iya komai idan banjiki ba,na riga nasanar da mom da dad dina komai,yanxu kawai jira nake ki bani dama aturo,dan banaso auren mu yakai da nisa.
Gani nake kamar xa'a sami wanda xai kwacemin ke,dan kuwa ba wanda zaiga kyan surarki,da halayyar ki yaji baya son kasancewa tare dake a matsayi mata.
Jikin haneefa yayi sanyi jin yadda taga Naseer yayi xurfi acikin sonta,tsoron ranar daxai san asalinta take,dan kuwa ba lallai ne yayi bearing da stuation din da take ciki ba,ta saki wata irin doguwar ajiyar xuciya,takasa cewa komai dan kuwa gabadaya ruwan kanta ya gama tsotsewa tunda Naseer ya sako maganar aure.
Naseer yace hello,haneefa,tace inajinka yaya Naseer,yace naji kinyi shiru ne,haneefa tace bakomai.sannan tace yaya Naseer da cewa nayi mu bari idan nayi completing level 2 sai a fara maganar aure,kaga daga wannan semester'n mun gama level 1,aganin haneefa kafin nan Allah ya kawo mata solution.
Naseer yace karki damu babynah,ko a gidana ai xakiyi karatu dan har tayaki xan ringa yi.ta dan yi murmushin yake.
Sannan ta mai da numfashi tace to,bari dai mu gama wannan semester'n.Naseer yace no bad babyna.
Suna cikin wayarne Naseer yaji ana knocking kofar office din,yace sorry baby I will call u back,haneefa tace ok bye,stay blessed.
By
Hauwa s.Ahmad
Maryam y.Ahmad๐
๐๐๐๐
[10/16, 8:02 PM] โช+234 706 370 3994โฌ: ๐บ'YAR MULKI๐บ
2016
6โฃ2โฃ
๐โ
EMIR'S PALACE.....
Sarki salahudden Adam na fada a xaune tare da fadawansa,suna tattaunawa kan yadda xai samarwa jama'ar kano jin dadi,dakuma neman shawarar su dan samar da cigaban al'umma.
Abdul na daga gefen mai martaba,ko ina Abdul yana tare da sarki,sai dai idan wani jenue uxuri Abdul yake dashi.