Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 18811 words

Chapter 1 - Yar Mulki book Complete document by Maryam A. Ahmad .txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

381

Ads at the middle of Article

[10/15, 10:26 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺
1⃣ -5⃣


👑👑




Cikin nutswa drivers din suke tukin,gudun kar ran Amal ya baci,motoci ne guda biyar ajere,gabadayansu bakakene,motar tsakiya itace wadda Amal ke ciki,akwai biyu agaba biyu a baya wadanda duk body guards din Amal ne aciki.


Haka suka cigaba da tafiya,tana faman basu umarnin yadda take son tukin yakasance cikin tsiwa,da kuma mulki,suna xuwa kofar gidan,mai gadin yayi xumbur ya mike ya bude gate din tacewa drivern kai tsaya cikin tsiwa,ta xuge glass ta kalli mai gadin a wulakance,tace,banace maka idan na dawo kadaina batamin lokaci wajen bude gate ba?? Ya tsugunna yace kiyi hakuri ranki ya dade,baxan sake ba,Amal tace idan ka bari na kara maka magana a karo na biyu a ranar xakabar gidannan.ta bada umarni drivern yaja motar xuwa harabar gidan.




Motar da Amal ke ciki na tsayawa,bayin ta guda biyu suka fito,kowacce a gefen ta guda daya,suna ta faman gyara mata riga wadda ke jan kasa,suka shiga cikin gida.




Bangaren momy ta nufa,tana shiga momy tace my Amal kindawo?,Amal ta karasa ta kwanta a cinyar momy tace ehh,momy ta shafa kanta,tace Amal meya faru ne? Naga duk ranki a bace,yau kuma waya taba min ke? idon Amal ya ciko da kwalla tace momy nifa vanason mai gadin nan wlh,duk sai ya batawa mutane lokaci kafin ya bude gate,momy tace akan wannan kawai kike nema kiyi kuka? So kike ki tayarmin hankali,kawai dan kuka baya miki wahala? Kinga kiyi shiru xansa mai martaba,ya canja masa aiki acikin gidannan.momy ta kalli jakadiya dake gefenta tace kawowa Amal ice cream,jakadiya tace to rankiya dade,ta fita cikin hanxari,,sannan momy ta mai da idanun ta kan Amal tace,nasa akawo miki abinda kike so,ki daina bata ranki kinji.Amal tayi shiru alamar ta gamsu da rarrashin da momy tayi mata.




Amal kyakykyawace,farace tass, gashinta har gadon baya,hakoranta ajere suke wadanda suma farare tasss,tana da diri mai kyau,Amal akwai mulki dasan nuna ita 'yar sarki ce👑,babu dama mutum yayi wani abu ba dai-dai ba sai ta nuna masa isa,da nuna sai abinda take so,akwai son hutu da kuma shanawa,wannan kadan kenan daga cikin halayyar Amal.


Amal tace momy bari naje na kwanta bacci nake nakeji,ta kaimin ice cream din daki,momy tace to,ki turomin haneefa,Amal tace to.




Amal na shiga daki ta tarar da haneefa a xaune akan sallaya tana karatun Alkur'ani,tacewa haneefa kije inji momy,yadda Amal tayiwa haneefa maganar kamar bataso,haneefa na karasa shafin da take karantawa tasa alamar tsayawa,ta tashi dan xuwa kiran da momy tayi mata,saboda tasan tana kara mintina dayawa xata sha fada awajen momy.




Tana xuwa momy tace da haneefa kije cikin abin kayan wankin dakina ki debo duk ilahirin inner wears din dake ciki maxa-maxa ki wanke min su,wannan kan bashine na farko ba,haneefa ta saba tunda ta taso ita take wa hajiya fateema wankin inner wears,haka ta wuce ta debo kayan.


Tana fitowa falon Abdul ya jijjiga kai aransa yace ina matukar tausayin yarinyar nan,haneefa tace yaya Abdul ina wuni ya ansa,lfy kalau haneefa ya karatu tace lfy kalau,ta wuce toilet don wanke kayan da momy ta bata.


😭😭


By
Maryam y.Ahmad
Hauwa s.Ahmad📚✍




😭😭
[10/16, 7:56 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺 'YAR MULKI🌺
6-10




📚✍✍






Yau kam haneefa da wuri ta shirya,taje bangaren momy ta wanke toilet,ta gyara daki da kuma falon momy, wannan aikin haneefa ne na kullum,dan kuwa uwar gidan maimartaba hajiya fati bata barin kowa ya gyara mata bangarenta sai haneefa,ko jakadiya, bangaren maimartaba ne kawai hajiya fati take gyarawa da kanta,bayan haneefa ta gama tsaf ta koma daki inda ta tarar da Amal a kwance bata da ko niyyar tashi,ta dan taba gefen kafarta,sannan tace Amal-Amal kitashi lokaci xai kure karki makara,Amal tayi wani irin juyi tayi tsaki sannan ta mai dakai tacigaba da bacci abinta,gudun karsu sami matsala a tsakanin su yasa haneefa bata kara tashin Amal ba.


Haneefa ta bude wardrop dinta wadda banda kanshi ba abinda yake tashi aciki,ko wanne jinsin kaya bangarensa daban ne acikin wardrop din,kayan awanke suke a goge,komai na cikin wardrop din tsaf,haneefa tana da tsafta matuka bata taba barin wani abu nata da datti saita tabbatar yayi tassss.wajen tsaftar jiki kuwa tayi fice danni na dade banga mai tsafta irin ta haneefa ba,ta dakko wani pink din gyale,gyalen kam ya hadu,taje gaban mudubi ta gyara fuskarta sannan ta nannade gashin kanta mai tsayin gaske,dakyar ribbon din ya rike gashin haneefa saboda tsananin santsinsa,sannan tayi rolling mayafin dayake bakar doguwar riga tasa,wadda akayi mata kwalliya da pink stones a hannu da kuma wuyan rigar,ta sa pink takalmi da bakar jaka,ta dau key din motarta,tana fita taci karo da yaya Abdul a bolcony ya dora kafa daya kan daya, tace yaya Abdul ashe ka fito?? Da wuri haka?? Yace eh,na gaji da kwanciya shiyasa na fito nan,sannan yace yau morning lectures ne dake kenan?? Haneefa tace eh wlh gashi ma na makara Allah yasa ya barni na shiga,dan lecturer bashi da kirki,yaya Abdul ya ce ahh to kiyi sauri, sai kin dawo amma kiyi tuki fa a nutse,haneefa tace to yaya.




Kuka kwai haneefa take😭😭 rike da stiring mota a hannun ta,xuciyarta sai xugi take,irin kuntatawar da ake mata tayi yawa,dan dai bayyada xatayi ne,amma ji take barin gidan shine kawai xai fi mata sauki,amma sai ta tuna cewar to idan ma tabar gidan ina xataje???.haka dai tayi ta kuka,tana shiga school tun amota ta goge hawayen dake idonta sannan ta wuce hall din daxasuyi lectures din,ta tarar already hidaya ta ajiye mata seat,ta xauna suka gaisa da hidaya,babbar kawar haneefa kenan,baifi minti biyar da shigar haneefa ajin ba lecturer ya shiga aka fara gudanar da lectures.




Amal kuwa na tashi toilet ta fada,tayi wanka ta fito ta shirya tasa kaya,tayi tsananin haduwa,doguwar rigar shadda tasa golden colour anyi mata aiki wanda ya dace da ita sai mayafi data yafa aka,kana ganin shaddar ba sai an fada ba kasan mai tsadace,ta wuce falon momy ta tarar da momy a xaune tana hutawa,tace momy wai ba'a gama breakfast din bane haryanxu? Momy tace xo ki xauna,yanxu xa'a kawo miki,bari naji ko sun gama, Momy ta kwalla kiran jakadiya,da sauri jakadiya ta bayyana a falon,tace ranki ya dade gani,hajiya fatee tace kicewa ladi inason ganinta,nan da nan ta amsa kiran momyn Amal,ta kalle ta tace ladi wai meyasa bakwason gama abinci da wuri a gidannan,?kun sani sarai Amal tana fita makaranta da wuri,ladi tace rankiya dade saura kadan ya karasa,kinsan dankali akwai daukan lokaci,hajiya fatee tace koma dai menene daga yau bana so Amal ta sake kukan ba'a gama abinci da wuriba agidanna,cikin ladabi ladi tace to,angama ranki ya dade,momyn Amal tace ki hanxarta ki kawomata yaxunnan,ladi ta fita cikin sauri,agurguje,nan da nan ta kawo kamar yadda momyn Amal tace,ta jera su akan dining.Haneefa takarasa kan dining din taci abincin sannan tace momy xan wuce school,momyn Amal tace,to sai kindawo,Amal tayi kissing momyn ta,sannan ta fita.


Tana fita,tasa key ta bude motar ta,sannan ta shiga ta xauna,ta bude handbag dinta ta dakko glass ta manna a idonta,ta jefa chewing gum abaki,ta kuma daura agogo a hannun ta,sannan taja mota ta nufi school.



Amal na shiga school ta tarar har an fito daga first lecture amma,bata damu ba ko ajikinta,taje daidai inda su mufeeda da Afrah suke xaune tayi parking,Amal na fitowa daga mota suka taso da sauri tare da fadin oyoyo suka rungume Amal,Afrah tace kai u look gorgiou,Amal tace tnx,sannan ta xauna a tsakiyar su,tace kunyimin attendance? Mufeeda tace kawata idan bamuyi miki ba ashe baxa muyiwa kan mu ba kenan,Amal tayi murmushi tare da gyara glass din dake idon ta,tace kawai tambayar ku nayi,Afrah tace munyi miki mana.Dai dai lokacin da suke wannan maganar Amal ta hango wucewar Haneefa da hidaya,tacewa su Afrah kunga yarinyar can sai na koya mata hankali,bata da aiki sai munafur ci,da asuba haka xata hanani jin dadin bacci,tana karatu bayan ba dan Allah takeyi ba,Afra tace ai fada mata xakiyi idan xatayi ta koma falon ku mana,dole sai tayi a daki?,Amal tace hhmm bakusan abinda yafi damu na akanta ba,cikin yanayin xuga da munafurci mufeeda tace menene? shishahigin da takewa yaya Abdul mana, wallahi ni shi yafi damu na,shima kuma yaya Abdul din yayi ta biye mata,abin yana bani haushi,Afrah tace ai naga yayan naku is simple amma fa akwai sarauta,Amal tace akawai kam,ai bahaye bane gado ne.




Bayan angama lectures haneefa da hidaya sukayi sallama,kowa ya tafi gida.


Haneefa na komawa gida,tayi wanka bayan ta fito taci abinci,dama ko break fast batayi ba haka ta fita school,ta gabatar da sallar la'asar,bayan tayi sallar ne ta nufi wajen baba mareeya.




Baba mareeya tana daya daga cikin masu aikin gidan mai martaba sarkin kano,Alhaji salahudden Adam,tun haneefa tana karama baba mareeya take kula da ita,tana tsananin tausayin haneefa saboda tasan yadda rayuwar ta ta kasance,haneefa ta shaku da baba mareeya sosai, ita take kallo amatsayin mahaifiyar ta a gidan ba momy ba,duk damuwar haneefa baba mareeya kawai take fadawa don ta sami sauki axuciyar ta.




Yauma kamar kullum haneefa da baba mareeya suna tare,baba mareeya tace haneefa kin dawo? Haneefa ta eh baba mareeya,sannan tace naxo ne muyi wata magana,baba mareeya tace to haneefa ina jinki,idon haneefa ya ciko da hawaye😭😭 tace inasone nabar gidannan ba tare da kowa ya sani ba sai ke,nagaji da ganin wasu irin halayen da momy da Amal suke nuna min,gara naje wani wajen daban inda xanfi samun kwanciyar hankali,kullum ina cikin bacin rai,tun bansan komai ba ake nunamin banban ci a gidanna,harna kai lokacin daxan iya sa bacin rai a xuciyata😭😭kuka yaci karfin Haneefa tayi shiru idonta ya kada yayi ja.😭😭




Baba mareeya ta dafa kafadar haneefa tace baxa'ayi haka ba,yanxu idan kika tafi ina kika san xaki fara xuwa??,idan kikayi haka ai ran maimartaba xai baci,ko yananan bai kamata ki tafiba,ballantan yayi tafiya,idan ya dawo yaji cewar bakya gidannan baxaiji dadi ba,haneefa ki kara hakuri komai xai wuce insha Allahu,karki manta fa yau shekarar ki goma sha hudu agidannan kuma na tabbatar baxaki mai-mai taba,don haka kiyi hakuri kinji?? Haneefa ta kafa kai a cinyar baba mareeya sai kuka take,itama kanta baba mareeyan kukan take.😭😭.saboda tausayin haneefa,ganin cewar ta taso a gidan sarauta,kuma acikin daula amma batajin dadin dadin rayuwar ta ko kadan.






Baba mareeya ta cigaba dacewa dan Allah haneefa ki cire wannan kudirin da kika sa aranki,kinga duk abinda da ake miki mai martaba bashi da masaniya,amma a sannu Allah xai fahimtar dashi,ta kara da cewa yanxu magriba tayi kije maxa kiyi sallah,haneefa tace to.






Haneefa na shiga daki ta tarar da Amal nayin sallah,ta fada toilet tayi alola ta gabatar da sallah,bayan ta idar da addu'a,ta dakko handout dinta da sukayi lecture da safe ta fara dubawa,Amal tace haneefa banason irin abin da kike min,cikin masifa Amal takeyin maganar tace karki kara tashina ko xan wuni in kwana ina bacci,ba matsalar ki bace,wannan ai mugunta ce ke baki huta ba shine baxaki barni na huta ba ko?? To wallahi ya isheki,kin gane ai?


Tunda Amal ta fara magana haneefa bata daga kai ta kalleta ba balle ta tanka mata,haka ta gama masifar ta ta hakura,ita dai haneefa karatunta kawai take,amma acikin xuciyar abin ya bala'in kona mata rai,aranta tace ai kuwa kinyi da 'yar halak dan kuwa ko da wasa baxan kara tashinki ba.


😭😭😭


By
Hauwa s.Ahmad
Maryam y.Ahmad📚
[10/16, 7:57 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺
2016


11-15


📚✍✍






Amal da Afrah na tsaye a upstairs din makarantar su,fitowar su kenan daga lecture,suna jiran mufeeda ta karaso su sauka kasa,don suje su sami wajen xama su cigaba da sana'ar tasu ta yiwa mutane rashin mutunci a cikin school,Amal na rike da rubar swan a hannun ta,tasha ta rage ruwan sannan ta leka kasan benen ta kalli Afrah tace leka kiga wannan guy din mai shegen iyayi, yana wani kasaita,sai kace akansa aka fara namiji dan gayu,Afrah na lekawa kafin tayi magana Amal ta saki robar ruwan dake hannunta a dai dai saitin inda mujaheed yake zaune.




Afrah kam batayi mamaki ba,tasan halin kawarta sarai,bata da kirki,ga neman tsokana da kuma nuna ita 'yar sarkice,Afrah tace yesssss 'yar mulki kinmin dai dai,Amal ta gyara glass din dake idon ta cikin wata shegiyar taunar chewing gum tace ai nice dai dai shi acikin makarantar nan.




Mujaheed na jin xubowar ruwa ajikinshi yayi sauri ya kalli saman benen don ganin wanda yayi masa wannan aika aikar,habaaaa yana ganin Amal yace dama sai ita marar kunya,duk makaran tarnan kowa kuka yake da ita,daga yau baxata sake marmarin yiwa wani haka ba,ba tana fariya baban ta sarki ba??, yayi tsaki mtswwww,sannan yatafi fuuuu ya nufi matattakalar benen da xai kaishi wajen da su Amal suke tsaye.




Mufeeda na karasawa wajen dasu Amal suke tace,'yar mulki kuxo mu wuce,nan fa suka nufi hanyar daxata kaisu kasan benan,suna wata tafiya cikin kasaita wadda take indicating su 'yayan wasune.






Mujaheed yana hango sakkowar su ya tsaya a kafar benan dan jiran isowar su.




Suna isowa wajen,mujaheed yasha gaban su dai dai saitin Amal ya tsaya,ya xura hannayensa duka biyu a aljihu ya bata rai sannan ya karkatar da kansan gefe daya.


Ya daga girar sa sama,sannan ya nuna Amal da dan yatsa yace keee baki iya bawa mutane hakuri ba idan kika musu laifi??




Cikin rashin kunya Amal tace hakuri fa kace,Allah ya kiyaye😏 ninasa ka ka xauna a saitin wajen danakeso na jefarda ruwa?? malam kabamu waje mu wuce dan muna da abinyi.




Majaheed yaji haushi sosai ji yake kamar ya tsinkawa Amal mari,yace ki shiga hankalin ki,kuma kisan dawa kike magana,ki bani hakuri idan ba haka na kwasheki da mari,ina ganin a gidan ku ba manya shiyasa kike behaving haka.




Afrah tace dakata mujaheed ya isheka haka,kasan Amal wacece kake mata magana any how???




Mujaheed yasan cewar Amal 'yar sarkice amma sam ya nuna baisan hakan ba,yace koma wacece ita wannan ba damuwata bane,kuma ba abinda naxo na sani acikin makarantar nan ba kenan,kawai ta bani hakuri.




Amal aranta tace amma wannan guy din ya rainamin hankali,yana nufin yace baimasan ko ni wacece ba???


A fusace Amal tace kaga ka matsa mu wuce dan ko mutuwa xakayi wallahi baxan taba baka hakuri ba.




Mujaheed yace kinyi kuskuren shiga gonata,xaki bani hakuri ko ba yauba,put this at the back of ur mind,ya sake mai maitawa,saikin bani hakuri ko ba yauba,kinci sa'ar addinin musulunci wallahi da saina mareki.kawai ya juya ya tafi,kallo daya xakayi masa kasan ransa ya mugun baci.




Amal da friends dinta suka sami waje suka xauna sai tattauna abin da ya faru suke.




Amal tace dama acikin makarantar nan akwai wanda xai iya kallo na yafadamin irin kamalan da guy din can ya fadamin? dole nasa a daure shi,kuma kafin ni na bashi hakuri shi xai fara bani hakuri.xanga wanda yake gadara dashi.




Mufeeda tace 'yar mulki ina ganin kiyi hakuri ki kyaleshi,kina sawa a daure mutane da dama,amma banga alamar xakiyi nasara akan mujaheed ba,Amal ta kalli mufeeda cike da mamaki tace waye shi?? Dabaxan iya sawa a daure shiba.




Mufeeda tace ba dan kowa bane amma,gaskiya ina ganin daure shi xaiyi wuya.




Afrah tace nima dai gani nake ta kyale shi,Amal kinga next week abbanki xai dawo,idan kikasa aka daure shi na tabbata xancen nan sai ya koma kunnen mai martaba,nan danan jikin Amal yayi sanyi saboda tasan totally Sarki Salahuddeen baisan tana wannan iskancin a gari ba,komai takeyi momyn ta ke goya mata baya,batason ganin bacin ran Amal ko kadan.


Afrah ta dafa Amal tace kawata kirama da wani abu,amma karkisa a daure shi,Amal ta dan yatsine fuska,tace ba matsala,amma sai ya gane kuskurensa.




Gobene xa'ayi birthday din Afrah dukkan su sun shirya cewar kowa xai kawo 200,000.Naira contribution,saboda sunaso birthday ya hadu yadda ya kamata.






Amal na shiga dakin momyn ta direct akwatin kudi ta nufa ta xari 250,000Naira,ta fice abinta,ta dauki mota ta nufi wajen birthday din,riga da wando tasa,sun matseta sosai,amma fa tayi kyau to d core,rigar blue ce da kwalliyar baki,sai wando da takalmi bakake,tayi wani hadadden dauri,ta manna na gadon a idonta(glass),kanshin da take kuwa xakayi tunanin companyn turaren ne

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads