Header Ads
Showing 18001 words to 18811 words out of 18811 words

Chapter 7 - Yar Mulki book Complete document by Maryam A. Ahmad .txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

386

Ads at the middle of Article

Amal dake gefe kuwa sai wuri-wuri take da ido irin na rashin gaskiya,saboda tana tsoron mai martaba,dakyar Amal ta iya bude baki dan bawa mai martaba hakuri,tace Abba dan Allah kayi haku-..anan maimartaba ya katseta,cikin tsawa yace dalla rufemin baki mutuniyar banxa! Ko menene bake kika jawo ba?? Amal ta fashe da kuka.




Momy'n Amal tace dan Allah kayi hakuri yarinyar nan fa haryanxu akwai sauran kuruciya atare da ita.


Sarki ya dagawa momy'n Amal hannu da nufin dakatar wa,yace ya isheni haka,nariga nasan cewa dake da Amal kuka takurawa haneefa acikin gidan nan.
Jiya ba abinda ba'a fada min ba akan kuntatawar da kukayi mata,yayi kyau..!!!


Momy'n Amal tace kayi hakuri duk akan rashin sanine,ni dai fatana Allah ya bayyana hanneefa,amma a karkashin xuciyar ta ba hakan take so ba.


Jin addu'ar da tayi yasa mai martaba ya sakko kadan,ta sake cewa yakamata muje kaci abinci,tun jiya rabonka da abinci,mai martaba yace banajin yunwa,idan ina bukatar hakan xan sanar dake.suna cikin haka




Abdul ya shigo cikin falon,mai martaba yayi xumbur ya mike tare da jefawa Abdul tambaya cewar ansameta?? Idon Abdul yayi ja sosai,ya jijjiga kai yace nooo Abba bamu sameta ba,sarki ya saki wata irin doguwar ajiyar xuciya.yace Allah ka bayyana mana haneefa ka kareta daga kowanne irin sharri a duk inda take.Abdul yace Amin ya rabbi.


Sannan yace Abba ni abin ne ma yake bani mamaki,sanarwa ake ba kakkautawa amma shiru kake ji ba wani alamar samunta,ko a dan kawo labari ma ace an ganta a wani waje babu,is unfurtunate.Allah yasa haneefa is safe some where else.




Sarki yace Amin Allah dai ya bayyanata.








GOVERNMENT HOUSE.....🏤




Naseer ne a kwance ya rasa abinda yake masa dadi,banda hawaye ba abinda yake fita daga gefen idonsa masu xafin gaske,yasa hannu ya janyo wayar sa daga gefen bed side drawer,ya fara dialing number'n hanny,amma switched of,yasan cewa number'n akashe take amma ya kasa resisting dole sai yayi dialing sannan yake samun peace of mynd,yanajinta arufe sai ransa ya shiga tafarfasa.juyi kawai yake amma ya kasa jin dadin kwanciyar,yaji wani irin haushi ya kamashi kawai ya kashe wayar gaba daya,dan bayason ganin call din kowa idan ba na haneefa ba.




His excellency yace da momy'n Naseer,let's go and pleaseee Naseer nasan yana cikin damuwa sosai dan na fahimci yana son yarinyannan sosai,Her excellency tace ni kaina abin ya dameni ba yadda banyi da Naseer ba yaci abinci amma totally yaki,let's go and c him,suka dunguma dakin.


Ganin yanayin da naseer yake ciki yayi matukar basu tausayi,suka xauna kowanne daga gefen naseer sai faman bashi baki suke.


Naseer shi kadaine dansu tilo,shiyasa suke bala'in ji dashi,ko kadan basason bacin ransa,haka suka ci gaba da rarrashinsa amma inaaaaaa shidai kawai ganin haneefa shine kwanciyar hankalinsa.






ADNAN.....


Yace haneefa ina ganin kiyi giving up,ki shirya xama dani,dan ko kin gudu daga gidannan sai na dawo dake na fada miki.


Baxan ci gaba da takura miki akan bukatata ba,saboda inason amincewar ki,amma ki xauna kiyi naxari,ni dai baxan taba bari kibar gidan nan ba,ya rage naki,na baki nan da gobe,ina jiran amsarki.




Haneefah ta fashe da wani irin kuka na ban tausayi,jiki ba kwari ta tsugunna,tafi awa hudu a bakin kofar nan amma ba alamar Adnan xaiyi releasing dinta,ganin ba sarki sai Allah ta hakura ta koma dakin da Adnan ya nuna mata a matsayin masaukinta ganin magrib ta yi don tayi sallah,ta jingine akwatin ta gefe daya sannan tayi locking dakin da mukulli gudun kar Adnan ya shigo,ta xauna agefen gado tana ta tunanin yadda xa'ayi ta gudu daga gidan.




Ta nisa aranta tace kaico,ina tausayawa rayuwar Adnan,gashi kyakykyawa ga arxiki Allah ya bashi,kyau kamar shi yayi kansa? Amma halinsa baiyi ba ko kadan,ya Allah ka kare ni daga sharrin Adnan,ta tashi ta shiga toilet dan yin,Alola,tana shiga tace Alhamdulillah ganin ta fara fashin sallah,wani irin dadi taji,ganin ta sami babban uxiri da xata fakewa Adnan dashi,kafin nan kuma sai ta shirya wasu 'yan dabaru don barin gidan,wanka kawai tayi mai makon alolar ta fito ta shirya tsaff,amma har alokacin hankalin ta bai kwanta ba,sanin cewar lallai Adnan shu'umin kansa ne.zai iyayin komai don ganin burin sa ya cika.




Mu kam mukace ai bai fi karfin Allah ba...!




LUV U MORE 'YAN SAUYIE....!






By
Hauwa s.Ahmad
Maryam y.Ahmad





💞💞💞💞

Ads At the End of Article
5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads