Showing 15001 words to 18000 words out of 18811 words
Chapter 6 - Yar Mulki book Complete document by Maryam A. Ahmad .txt
suka fasa motsawa ko ina sun dauka labarin inda take aka kawo.
Jakadiya kuwa uwar munafurci har taje ta fesawa Hajiya fati da Amal gawani bako yaxo wai anga haneefa,nan da na suma suka nifi fadar sarki.
An ciki sosai,kowa na gidan ya hallara a fadar.
Malam jibrin yace ina neman gafara awajen sarki,domin laifin danayi muninsa baxai musaltu ba,sharrin shedan ne amma dan Allah kayafemin,sarki yace inajinka ina haneefan? Ko kasheta kayi?
Malam jibrin yazama confused,yace bana na tare da ita,ina kwance naji sanarwa a radio cewar maryam ta bata.
Shiyasa naga gara na bayyana abin da yake gaskiya ne,kafin na koma ga ubangiji na.
Ni ne mutumin dana kawo haneefa wajen ka tun tana karama,nace na tsinceta ,tare da takar da.
Gaskiyar magana maimartaba haneefa 'YAR KACE, kowa sai da xuciyar sa ta buga awajen,dum,dum,dum
,dum.......!!! Malam jibrin yace ina nufin 'yar cikin ka da ka haifa,kamar yadda ka haifi sauran 'ya'yan ka guda biyu.
To fah,sarki kansa ya shiga rudani,saboda a iya sanin sa Abdul ne da Amal kawai 'ya'yansa.amma ya kasa musa abinda malam jibrin ya fada,saboda,yanajin son haneefa a xuciyarsa fiye da sauran 'ya'yansa,yana boyewa ne saboda karya sanya fitina a tsakaninsu.
Sarki yayi kokarin cewa ban fahimce ka ba???
Malam jibrin yace nasan baxaka fahimce niba kamar yadda kowa na wajen nan baxai taba fahimta ba,har sai na baku labarin abin da ya faru.
Ya fara bada labarin kamar haka.
DAN ALLAH KUYI HAKURI BANIDA ENOUGH CHARGE,MU HADU A NEXT PAGE,KUMA KARKUGA PAGES BASA TSAYI SOSAI,MU YIN SUMMARY NE TA YADDA MAI KARATU XAIJI SAUKIN KARANTAWA,MUN GODE SOSAI,FOR LOVE U PEOPLE ARE SHOWING.Thank u once again.
By
Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad📚
08033660286
💞💞💞💞
[10/21, 8:47 PM] +234 814 443 8844: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
6⃣6⃣
📚✍
Malam jibrin ya sake fashewa da kuka,ya gurfana agaban mai martaba,yace dan Allah kayafe min,nasan na tafka babban kuskure.
Duk mutanen dake fadar kowa xuba tagumi yayi suna jira suji yadda malam jibrin xai warware wannan al'amarin.
Malam jibrin yace,ni dan garin gano ne dake karamar hukumar kano,tunda na taso bani da wadata,na shiga kunci mai tsanani,bani da cin yau balle na gobe,lokacin da ya wuce ina daya daga cikin mutanen da suke xuwa gidannan ake bamu sadakar danyen abinci tun lokacin da uwar gidan mai martaba hajiya maryam tana raye.
Ina cikin wannan halin ne wani abokina usman ya shawararce ni da na fara harkar fashi wanda shi dama tuntuni ya dade a cikin harkar,shedan yaci galaba akaina na biye masa nafara fashi.
Ban jima a cikin harkar fashin ba na kware sosai,duk gidan da xamu ina bada gudun muwa,haka kuma muna yin fashi akan titi.
Watarana mun fito fashi,a hanyar kano xuwa yola,dai dai dajin kare kukanka,ranar mun tare motoci da dama,aciki harda wadda uwar gidan ka ke ciki,motar da take ciki tafi duk motocin da muka tare tsada,dan haka muka yashe kudin sauran mutane,ita kuma muka yanke shawarar kwace motar,duk wadanda muka tare suka watse,saura ita da driver'n ta dakuma juna biyu da take dauke dashi.
A take oganmu ya dagargaxa kan driver'n ta da bullet,sakamakon haka uwar gidanka ta tsorata har ya kaita ga haihuwa awajen,naji tausayinta kwarai da gaske,tun daga lokacin imanina ya kara yawaita,dana kare mata kallo sai na gane cewar uwar gidan kace,saboda duk lokacin da ake rabon abinci agidannan tana xama awajen hakan ne ya bani damar ganeta.
Tana haihuwa Allah yayi mata rasuwa,sai ogan mu ya bada umarni muka jefa ta cikin ciyawa,haka shima driver'n,jaririyar sai kuka take akusa da gawarta.
Sai hikima taxomin nace sauran 'yan uwana suyi gaba nixan tafi mana da motar da muka kwace awajensu,gudun kar ayi saurin,gane fashinta mukayi.haka kuwa suka ansa,sukayi gaba da tamu motar cike da dukiyar mutane.
Ni kuma nasanya mahaifyar haneefa da driver'n a mota muka karasa wani kauye dake kusa,nayi wa mutanen garin karya cewar 'yan fashine suka taremu suka kashe matata da driver na,kowa sai da ya nuna tausayawar sa agareni,ganin jariya da kuma gawa biyu dana shiga kauyen dasu,suka tambaya meyasa baxan kaisu gida,sai nace musu nayi waya gida ance nasami gari mafi kusa ayi musu sallah,Allah ya gafarta musu,saboda ganin ni kadaine.
Haka kuwa Suka taimakamin wajen yi musu wanka muka sallace su sannan muka kaisu makabartar kauyen.
Itama kuma haneefa akayi mata wanka,suka taimakamin da kaya aka sa mata.na boye haneefa a gidana wajan matata kuma ban boye mata komai ba,sannan na wuce na kaiwa abokan fashina motar.
Washe gari naji sanarwa cewar an rasa uwar gidan ka da driver'n ta,a hanyar xuwa garin su yola dan yin ta'axiyar kanin mahaifin ta wato galadiman yola.
Harxan kawo haneefa alokacin,sai naga cewar xa'a sa tsaro akaina har agano yadda akayi na tsince ta,sai na yanke shawarar idan ta jima awajena sai na dawo da ita gareka.
Daganan nayi nadama na shiryu na daina fashi,haka kuma nayi alkawarin rike haneefa.
Daga baya kuma danaga xata taso cikin kuncin talauci yasa na yanke shawarar dawo da ita gareka ta yadda baxaka fahimta ba,nayi takardar karya akan tsintar ta nayi.
Lokaci lokaci ina bin diddigin halin da take ciki agidannan,tanan ne na gane tana samun kyakykyawar kulawa daga gareka.
Daga bisani rashin lafiya mai tsanani ta kamani,wadda har yau ban warke ba.
Yau ina kwance naji sanarwa haneefa ta gudu,shiyasa na yanke shawarar xuwa na bayyana abinda yake gaskiya ne,amma dan Allah ka gafartamin.
By
Hauwa s.Ahmad
Maryam y.Ahmad
💞💞💞💞
[10/21, 8:47 PM] +234 814 443 8844: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
6⃣7⃣
📚✍
Sarki salahuddeen yasa wani irin kuka da har sai da sautin sa ya fito,hawayene kawai ke kwarara daga idonsa,ya matso gaban malam jibrin a fusace,ya daga hannu ya kwada masa mari,bai tsaya a daya ba saida yayi masa guda biyar kyawawa.sannan yace ka cuceni da baka sanar dani haneefa 'yata bace tun farko.
Tun batan da maman haneefa tayi mai martaba bai karayin kuka ba kamar yau ba,saboda kullum kukan xuci yake tare da fitar da hawaye,kuma yana jin kamar hajiya maryam ba rasuwa tayi ba,bata tayi,yau kam sosai sautin kukansa yake fita saboda yasan baxai kara ganin maman haneefa ba.
Kowa na wajen saida yayi kwalla banda Amal da momyn ta,ba haka sukaso ba.
Ni kuwa nace to ya xasuyi?
Abdul da naseer ma kukan suke,da sauri Abdul ya karasa kusa da maimartaba ya rike shi,tare da fadin Abba kayi hakuri,yanxu abin da yakamata muyi shine mu nemi haneefa,kar lokaci ya kure.sarki yana kuka yace I can't resist.
Fadawa kuwa basu taba ganin bacin ran mai martaba kamar ranar ba,cewa suke Allah ya huci xuciyar sarki mai adalci contineously....!!!
Lami kuwa(matar jibrin) kuka take haka talle suka xube kasa suna bawa sarki hakuri.
Sarki ya daka musu tsawa tare da fadin ku bace min daga gabana banason ganinku,sannan ya nuna sallama yace ka bisu har kauyen su kasan inda gidan su yake.ya ansa angama ranka ya dade.
Already Abdul da Naseer sun fita duba haneefa cikin gari,duk inda ransu ya raya nan suke bi ko xasu ganta ko kadan inda take banan suka nufa ba,ita tayi gabas su sunyi yamma(hannun riga kenan).
Kafin kace meye wannan har labari ya yadu cikin gari,within a very short period of tym.cewar Haneefa 'yar sarkice.
Nan da nan 'yan jarida suka cika gidan,suka fara suburbudawa mai martaba tambayoyi,wanda suke bukatar amsa daga malam jibrin,hakan ne yasa aka tashi driver da sallama suka dawo da malam jibrin don ansa tambayoyin da suka kamaceshi.
Abin ka da lamarin manya a ranar gabadaya 36 states na Nigeria labari ya yadu,sarkin kano da malam jibrin ake nunawa a kowanne gidan television ga kuma hoton haneefa.
Ummiey matar sarkin yola kenan,na ganin wannan sanar wa ta sanar da mai martaba sarkin yola,nan da nan suma members na family'n kowa ya shiga rudani,basu iya jurewa ba,a lokacin kowa ya shirya suka tafi kano cike da alhinin yadda akayi lamarin ya kasance.
HANEEFAH......
Tunda tayi pillow da akwatin ta ba abinda take sai kuka,mai gadin gidan ne ya fito yace lafiya kike kuka malama,me kike anan da wannan daren haka?tace dashi bakomai amma dan Allah so nake ka taimakamin na shiga gidannan ko xasu bani wajen kwana kafin gobe,mai gadin ya nisa yace masu gidannan basu cika zama ba,yanxu haka da muke magana basanan,jiya jiyan nan suka tafi abuja,acan uban gidana yake aiki,haneefa tace to dan Allah ko a harabar gidannan ne ka tai makamin na kwana,inyaso gobe da wuri sai in wuce,yace to ba damuwa,haka haneefa ta shiga da kayanta tayi shimfida akasa ta kwanta.
Washegari.....
Tayiwa mai gadin godiya tare da yi masa sallama,taja trouly'n ta ta tafi gently,shiruuuu unguwar ba mutane sosai,sai kayi awa bakaga mutum ya wulga ba ko da ranane balle yanxu da sassafe.haka taci gaba da tafiya har ta gaji,taja ta tsaya don jiran abin hawa.
Haneefa tayi xurfi sosai cikin tunanin inda xata,but she did not find out,eyyyahh..!
Kawai sai ji tayi mota ta tsaya a daidai saitin ta,bata ganin fuskar wanda ke cikin motar saboda glass din tinct ne,guy din dake cikin motar ya xuge glass slowly,ya risina kansa kadan ta yadda xai karewa haneefa kallo.
Idon sa na sauka akan haneefa,xuciyar sa tayi shaking aransa yace wawwwww,such beauty,yace amm 'yan mata ina xuwa haka da wuri? Haneefa bata amsa masa ba sanin cewar batasan inda xata ba,ya sake cewa,idan baxaki damu ba muje na rage miki hanya mana,
Haneefa tace nooo,thank u,yace kiyi hakuri mana idan na tafi baxan ji dadin rejecting kyautatawar danakeso nayi miki ba,please let's go
Haneefa ta danyi murmushi kadan da kyanta ya sake bayyana,wanda ba har xuci ba,Adnan ya fito ya karbi akwatin dake hannun haneefa yasa a boot,ya bude mata gidan gaba,ta shiga,ya rufe ta sannan ya koma seat dinshi,ya fara driving slowly.
By
Hauwa s.Ahmad
Maryam y.Ahmad
💞💞💞💞
[10/21, 8:47 PM] +234 814 443 8844: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
6⃣8⃣
📚✍
Adnan ya juya ya kalli haneefa wadda ba karamin birgeshi tayi ba,aransa yace baxan taba bari wannan kyakykyawar yarinyar tayi escaping daga gare ni ba,har sai bukata ta ta biya.ya saki wani shu'umin murmushi,sannan yace amm menene sunan ki? Ta dan basar sannan tace sunana haneefa,Adnan yace,sunan akwai dadi,ni kuma sunana Adnan,amma yanxu dole na koma haneef just because of u haneefa.
Ta danyi murmushin yake,sannan ta kawar da kanta,Adnan yace ina xakije haka da wuri?
Nan da nan idon haneefa ya ciko da kwalla,tace ni kaina bansan inda xani ba,bani da kowa agarinnan dawowata kenan jiya daga makaran na tarar gidan mu ya kone har iyayena gaba daya,gashi bani da relatives.
Adnan yace it's ok please,don't cry,kamar dagaske tausayin haneefa yake,nan kuwa,tsanananin pretending ne,aransa yace yessssss dole ki kasance tare dani.
Yace karki damu haneefa,bari xan kaiki gidanmu,wajen mamana,nasan xakiji dadin kasancewa da ita,haneefa taji wani irin dadi,tace to na gode.
Adnan yayi horn a kofar wani makeken gida,mai gadin yayi sauri ya bude,cikin gidan Adnan yashiga da motar yayi parking a harabar gidan,ya bude boot ya dakko akwatin haneefa,ita kuwa rike take da hand bag dinta,Adnan ne yayi mata jagora xuwa cikin gidan.
Tunda haneefa take bata taba ganin gida mai kyau kamar wannan ba,haka ta wangale ido tana kalle kalle kamar ba a gidan sarki ta taso ba,baxan misalta kyau da kuma tsananin girman gidan ba.
Suka haura saman gidan Adnan yacewa haneefa nan ne dakin ki akwai bandaki a ciki,haneefa tace ok,muje na gai da mama,then sai na dawo,Adnan yace nooo relax,xan je nadan yi wanka,kema nasan kina bukatar haka,idan na shirya xanzo na rakaki har part din mama ku gaisa.haneefa tace alright.
Kowa acikinsu yayi wanka ya shirya,haneefa ash doguwar riga tasa,mai kwalliyar pink amma bai yawaita ba,tayi kyau sosai,ta xauna a gefen gado tana jira Adnan ya xo don rakata wajen maman shi su gaisa.
Sai gashi kuwa yayi knocking,haneefa ta bude ita kanta ya mata kyau,ba karya adnan kyakykyawa ne kam.
Ko ni na shaida...😂 ga kuma ji da Naira.
Yace muje kici abinci kafin mama ta fito tana toilet,haneefa tace ok,dama wata muguwar yunwa take ji,saboda rabonta da abinci tun jiya da yamma.
Haka suka sauka,ta xauna a dining taci abinci tsaf ta kora da ruwa,da lemu sannan ta dau tissue paper ta goge bakin ta.
2hours later.....
Shiru shiru,haneefa bata ga maman Adnan ba balle su gaisa,sai tace amm Adnan ko mu karasa ciki mu gaisa da maman?
Adnan yace bari na fito freely na fada miki gaskiya,ba kowa acikin gidan nan bayan ni sai masu yimin hidima,nan da nan cikin haneefa ya duri ruwa tayi sensing akwai abinda Adnan yake nufi da kaita wannan gidan,yace dan haka ki shirya xama dani,kuma bawai ina nufin xan aureki bane noooo,xaki xama kamar matata dai kuma duk lokacin da bukatata ta taso xaki biya min,danni aure baya gabana ko kadan.
Haneefah tasa kuka tace,please karkamin haka Adnan ni marainiyace bani da kowa na gode da taimakonka,ta nufi saman benen da gudu ta janyo akwatin ta sannan ta nufi kofar fita,shikuwa Adnan tafa hannu ya shiga yi irin na mugayen basawan nan,
Haneefa na murda kofar da nufin xata fita taji is locked,ta juyo cikin yanayin tausayi tace pleasee Adnan this is d first tym na sanka arayuwa ta,dan Allah ina rokon ka kayi hakuri kar ka cutar dani.
Adnan ya ciji lebensa ta gefe daya,tare da yin murmushin mugun ta,yace relax,u can't leave this house haneefa, because every where is locked,so get ready to stay with me okay?.
Cikin fushi,haneefa tace,Never no matter how,no matter what,i can't stay in this house any longer,ta ajiye akwatin ta a gefe daya ta shiga jijjiga kofar da nufin xata balle,Adnan yasa hannu ya riko hannun ta,sannan yace idan xaki shekara kina jijjiga kofarnan baxata taba budewa ba,so ina ganin da kin hakura kawai kinyi abin da nakeso.
Haneefa tace leave my hand,har alokacin Adnan bashi da niyyar sakin ta,ta sake fada cikin tsawa "I said leave my hand"!!! Da taga dai bashi da niyyar sakin ta kawai ta ja hannun ta da kyau ta fisge daga cikin na Adnan.
EMIRS HOUSE....
6:00pm.....
Naseer da Abdul suka dawo sunsha bakar wahala sosai wajen neman haneefa amma Allah baisa sun sameta ba tun safe.Hankalin mai martaba ya tashi sosai ya kasa tsayar da hawayensa.
Haka mutanen yola(Dangin maman haneefa da Abdul) sun karaso,kowa yana cikin damuwa.
Amal da hajiya fati kuwa dan bakin ciki sun rasa inda xasu sa kansu.
Mukace sai dai su mutu....
IT IS MORE APPRECIATED U GUYS FOR UR PRAYER.
THANKS...!
By
Maryam y.Ahmad
Hauwa s.Ahmad
💞💞💞💞
[10/21, 8:47 PM] +234 814 443 8844: 🌺'YAR MULKI🌺
2016
6⃣9⃣
📚✍
Sarki salahuddeen yace wa hajiya fati,kinga irin sakarcin da yarinyar nan Amal tayi ga abinda ya jawo mana,cikin fushi sarkin yake magana.
Hajiya fati ta ririta muryarta tace,Allah ya huci xuciyar mai martaba,sannan tace kasan d'a Amal tasan matsayin haneefa baxa ta taba goranta mata ba,ko ba komai ai itama ai 'yar uwartace.cikin sigar munafurci.
Sarki ya hadiyi yawu irin na bacin rai yace ke kike goya mata baya kenan? Tayi duk abinda take so,ko ma haneefa ba 'yar uwarta bace ai wannan furicin bai kamata ba,akan koma waye.