Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 173834 words

Chapter 14 - MATAR MUTUM Document Complete by Samira Haroun.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jul 2024

1128

Ads at the middle of Article

kuka mallaka ba, rayuwar da kuke yi ita ke bani sha'awa kuma ita nayi niyyar farawa tare da ke, dan haka duk wata wacce kika san gwana ce ita a harkar tuk'a tuwo to zai fi kyau ki nemi kusanci da ita, dan a kowane dare na rayuwarki gidana shi zaki tuk'a min nayi ta sulmar kayana."


Kecewa tayi da wata siririyar dariya saboda maganarshi ta k'arshe, jinjina kai tayi tace "Ai ni ma na iya, na iya tuwon masara, tuwon hatsi, tuwon dawa dana shinkafa, sannan na iya na garin doya ma da kuma na semovita."


Jinjina kai yayi yace "Yawwa *maah le* ta, haka nake son ji."


Juyawa tayi tana fad'in "Bari na kira mama ku gaisa." Shiga d'aki, tabarmar dake jingine a farkon shiga ta d'auko mama ta kalleta da alamar tambaya, ita ma da ido ta amsa mata da "Shi ya ce na d'auko."


Saida ta juyo zata fito tace "Mama muje ku gaisa."


Sunkuyar da kai tayi ba tace k'ala ba, cikin shagwab'a tace "Mama muje, ko na ce ya shigo ne?"


Da sauri ta kalleta da mamakin wai me yasa wasu lokuta bata gane cewa tana jin nauyinta a matsayinta na babbar 'yarta ne? Girgiza kai tayi ta mik'e ta d'auki d'an gajeran hijabinta ta saka har k'asa, gaba take mama na baya hakan yasa sam bai kula da mutum a bayanta ba, saida ta duk'a dan shinfid'a tabarmar ya ga mama, har ga Allah tunaninshi bai bashi mahaifiyarta ma haka take ba, gashi fuskar maman ba wani tsufa ko dattijantaka, tarrr! Ya kalli fuskar mama da murmushi ya d'an d'ago hannunshi irin yana jiran ta k'araso d'in nan a cabke hannu tunda ga k'anwar matar da zaka aura. Mik'ewar da Mimi tayi ne ta juyo ta nuna mishi Mama tace "Ga mama ku gaisa."


Luuuuuu! Yayi ya sauke hannunshi tare da durk'ushewa yayi tsugunno irin na maza kan shi k'asa, gaba d'aya sai ya rasa bakin magana daya tuna yanda ya dinga kallon fuskarta, har fa yayi shigo dafa kan ta ya bata hannu su gaisa yace mata " *beby ya kike? Ya sunan k'anwar ta mu*?"


Lallai ashe da ya tabka kuskuren da har abada ba zai daina jin kunya ba, ganin ya kasa fad'an komai sai mama ce tace "Ina wuni?"


Da sauri cikin kunya yace "Ina wuninku?"


Da fara'a tace "Lafiya lau, an zo lafiya?"


"Lafiya lau, na sameku lafiya?" Ya fad'a kan shi a k'asa sosai, ita ma kan na ta a k'asa tace "Lafiya lau, ya mutan gida?"


Da fara'a yace "Lafiya lau, sun ce na gaisheku."


Da fara'a ita ma tace "Muna amsawa, a gaishe su sosai."


"Insha'Allahu zasu ji." Juyawa tayi tana fad'in "Allah ya shi albarka, a gaida 'yan gidan."


Saida y'a ji shigewarta ya sake d'ago kai, eh lallai Mimi baiwar Allah ce daya jarabeta ya cirota daga tsatson bayin Allahn nan.


Alama ta mishi da hannu ya zauna, saida ya cire takalminshi a nutse ya zaune tare da jingina a bango, d'aki ta koma ta d'auko duk abinda ta tanada domin shi ta kawo ta aje mi shi, cire takalminta tayi ita ma ta zauna kan tabarmar ta fara tsiyaya masa jus d'in, mik'a masa tayi ya karb'a yana murmushi yace "Nagode gimbiyar mata."


Murmushi tayi ita ma tana k'ara gyara zamanta irin na tsakiyar sallah (zaman tahiya), izinin shi ta nema ta zuba mishi abinci, jinjina kai yayi alamar eh, cikin nutsuwa ta fara zuba mishi farar macca da soyayyan nik'ak'en naman da aka nad'e cikin k'wai, sai soyayyen dankali da ta yi wa jus na mayonnaise da waken gwangwani.


Tura mishi tayi gabanshi ya gyara zamanshi yana fad'in "Da nasan wannan shagalin zan tarar ai da na taho da tsohuwar katifa ta."


Dariya tayi tace "Ka me da ita?"


Cike da zolaya yace "Da na ci nayi kwance mana."


Murmushi tayi ta girgiza kai tace "Gashi gidanmu baya d'aukar bak'on da baisan da zuwanshi ba."


Dariya shi ma yayi yanaa fad'in "Da alama dai baki son bak'o saboda karki raba shinfid'arki da shi, amma karki damu a gidana gadona zan ara miki kina kwana a kai."


Kunya ce ta rufe ta kawai ba tace komai ba, a nutse ya fara aika lomar abincin nan yana lumshe ido, da yatsa ya shiga nunata yana fad'in "Kar ki ce santi ne nake fa, dama ina so na tambayeki kalar kayan da zaki saka a ranar aurenmu?"


Waro ido tayi tana doka murmushi tace "To me kake kenan?"


Girgiza kai yayi yace "Na kare kaina tun kafin na yi magana fa."


Murmushi kawai tayi tace "Ka zab'a mana kawai."


Kallonta yayi yace "Kin yarda dani kenan?"


Lumshe ido tayi tace "D'ari bisa d'ari."


Jinjina kai yayi yace "Insha'Allah gobe zan turo d'an sak'o ya kawo miki wanda na zab'a."


Zaro ido tayi tace "Da wuri haka?"


Hararanta yayi yace "Ban gane da wuri ba? Wata d'aya ne fa, ni fa ranar kawai nake jira ta zo dan na gama komai, Maah kawai nake jira ta sameni gidana."


Sunkuyar da kai tayi cike da kunya, da haka suka ci gaba da hirarsu cikin farin ciki har yayi shirin tafiya, duk mik'ewa sukayi inda ya ce ta kira masa k'annanshi sannan ta fad'awa mama ya wuce, yanda ya buk'ata haka tayi dukansu tare suka isa har k'ofar gidan, saida y'a fara sallama da ita ya nuna mata cikin gidan yace "Koma ciki, nagode da rakiya."


Ba musu ba d'ard'ar tayi abinda ya ce, saida ta shigo kuma saita samu kan ta da tunanin wai ita ce yau namiji ba ubanta ba ya umarta haka, da yatsa fa ya mata wani fit fit koma ciki, murmushi kawai tayi tana fad'in "Allah kar ka kawo ranar da wani zai ramawa yan uwanshi maza abinda na musu, dan ba zan iya d'auka ba gaskiya."


D'aki ta samu mama ta shiga cire kayanta, Mama kam kallonta take har ta cire rigar ta saka riga da wando na bacci, tana idawa su Yaseen suka shigo da sallama da murna, duk gaban mama suka zube suna nuna mata ledar hannunsu, da sauri Mimi ta zauna gabanta ita ma ta jawo ledar ta shiga duba kayan, kayan k'walam ne sai turaruka da kuma kud'in daya zuba a ledar, d'aukar kud'in tayi ta ware jaka bibbiyu har guda goma ta ninkesu tace "Wannan na Abba ne."


Ragowar mama ta mik'awa tace "Mama ga na ki."


Kallonta su Yaseen sukayi suka ce "Mû fa aka ba, shi ne komai ba zaki bamu ba."


Harara ta dalla musu ta nuna Amir da yatsa tace "Daina kumburo min bakin nan kafin ka ji jini a ciki."


Kud'in data d'ora kan cinyar mama ta koma ta d'auka ta zagi jaka bibbiyu ta mik'a musu tace "Ku yi abinda zakuyi."


Farin ciki ne ya lullub'esu wanda ko dala biyar suka samu a hannu murna suke. Mama dai bata tanka musu ba sai al'ajabin lamarin Mimi, ta d'auka zata d'auki wani kaso a cikin kud'in ita ma, amma ba wannan ne gabanta ba mahaifinta ne yafi damunta, dama kuma ko bata cire mishi ba dole ita zata damk'a mishi, kawai ta bar ta tayi yanda take so ne, dan tsabar kawaici ko d'an abun tab'awa wata rana Allah ya hore Abba ya kawo indai Mimi na gidan ita ke rabawa.






*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:50 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����


*NA*




_SAMIRA HAROUNA_




*SADAUKARWA*



_GA DUKA_


*'YAN AMANA TA*




💫� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_�


� *[ T.M.N.A]* � 📖🖊�


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




*15*






"Zamu fita daga nan muje gidan Iya Delu, ke zaki zauna a nan ni kuma saina wuce."


Girgiza kai tayi tace "Mimi kina ganin ba matsala? Ya zakiyi idan Abba ya ganeki? Gaskiya ni dai ina jin tsoro ba za'a yi haka dani ba."


Cike da tabbaci da tsaurin ido tace "Babu abinda zai faru Asma'u, kwantar da hankalinki kawai."


Da alamar jimami sosai a fuskarta tace "Zamu ci amanarsu kenan? Yaudarar Abba zamuyi fa Mimi."


Girgiza kai tayi tace "Ba yaudara bace, Asma'u ki fahimceni mana, kinga yanzu idan..."


D'aga mata hannu tayi tace "Matsalata dake taurin kai, indai kikayi niyyar abu babu mai hanaki."


Mik'ewa tayi ta fara k'ok'arin d'aura zanenta bata sake tankata ba, ita ma mik'ewa tayi ta d'auki hijabinta a hannu ta fito dan tasan sunyi fad'a kenan ko zasu shirya sai sun had'e a islamiyyar yamma, takalminta ta saka a k'ofar d'akin ta wuce tana k'ok'arin saka hijab d'in, da kallo yayan Asma'u ya bi k'ugunta yana murmushi, lura da hakan yasa kishiyar maman Asma'u (mahaifiyarshi) cewa "Kai!"


Wannan tsawar data daka mishi tasa har Mimi juyowa ta kalleta, kallonta shi ma yayi yana zazzare ido, cikin jin haushi tace "Dan ubanka me kake kallo baki sake?"


Yatsina baki Mimi tayi ta juya ta saka hijab d'inta ta wuce ta barsu tana jin yana fad'in "To wai mama bani da ikon kallon abinda na ga dama ni da ido na?"


Ita kuma cikin fad'a take fad'in "Dan ubanka duk zalamarka waccen tafi k'arfinka, na d'aya dai kaga taxi ce ita da kowa ma shigarta yake, na biyu ba kowa take kulawa ba sai wanda taga akwai mamora a jikinsa."


Mimi kam ko fa a kwalar rigarta sai ma fita da tayi daga gidan, ita indai ita zaka tab'a kai tsaye to bata da matsala da kai, ka dai saka iyayenta ne ko da ta hanyar zaginta ne bata lamunta ko kad'an, dan taana da tabbacin ko mijin aurenta zata iya tsinke fuskarshi da mari idan ya nemi fad'a ma iyayenta magana.




*Sheikh*




Cikin nutsuwa ya sake tank'washe k'afafunshi yana had'e tafukan hannayenshi ya ci gaba da fad'in "A duk inda zaku shiga a fad'in duniya, a duk halin da zaku tsinci kanku a ciki yarana kada ku yarda kuyi wasa da addininku, addininku shi ne gatanku, addinin islama shi ne alk'iblarku, addinin nan shi ne madogararku, dan haka duk inda zaku samu kan ku kuyi alfahari da addininku, kada bambamcin yare ko k'abila yasa ku ji kunyar nuna kanku a matsayin musulmi, kada wani rud'i na duniya ko kuma muzgunawa tasa ku wofantar da addinin daya baku madafa a sanda baku da tudun dafawa, addinin musulunci rahama ne a garemu kuma alfarma."


A hankali ya kalli Aisha yace "Aysha, ke ce babba a gidan nan, ina sake gargad'inki da ki kula sosai da yan uwanki ki tayasu rik'e sallarsu ta farilla, kada ki barsu suyi wasa da ita a kowane hali, nasan macece ke kuma a halin yanzu kowane lokaci zaki iya shiga d'akin mijinki, amma hakan ba zai hanani sake jadadda miki rik'o da zumuncinku ba, a duk inda aure ko ratuwarki ta gaba zasu kaiki, zaki iya tsayawa tsayin daka wajen ganin kun rik'e zumuncin nan, ko bayan babu ranmu zaku zama gatan junanku."


Cikin tsareta da ido yace "Kin fahimta?" Jinjina kai tayi alamar eh cikin sanyayyar murya tace "Eh Abie, insha'Allah zamu rik'e zumuncinmu, wannan alk'awari na ne a gareku iyayena."


Jinjina kai yayi yace "Masha'Allah, sai kuma kai *Heezam*." Ya fad'a yana kallon k'annan Aisha mai bi mata, a nutse yace "Bana da d'ar a kan ka dan na saka maka ido sosai ina lura da duk wani tako da motsinka, a tak'aice kuma a yanzu dai banga wani abu daya nuna shagala akan sallahrka ba, haka kuma ban ga alamar wasa a cikin karatunka ba, kamar yanda banga wani b'ataccen aboki da zai iya b'ata tarbiyarka ba, saidai hakan ba shi zai sa na zuba maka ido ina kallonka haka kawai ba, Heezam."


Ya kira sunanshi cikin dakakkiyar murya, amsawa yayi a ladabce yace "Na'am Abie."


D'orawa yayi da "Daga yanzu zamu fara fita tare da kai zaman majlisi, sannan ina so kai ma ka fara wani k'ok'ari akan matasa yan uwanka dan bayar da ta ka gudummuwar."


Da ladabi ya jinjina kai yace "Insha'Allah Abie."


Kallon *Aswane* yayi ya saki murmushi yace "Manya masu gari, macijin k'aik'ayi kenan sari ka nok'e, wato yarona Aswane duk gidan nan babu wanda ya kai ka karatu, haka kuma babu wanda ya kai ka iya shegantaka."


Duk dariya aka d'auka a wajen har Hafsat dake shafar cikinta saboda juyawar da yaron cikin ke yi mata, cikin muryar laushi tace "Akwai son gayu fa kamar ya ga ubanshi Asas, amma kuma yafi kowa tsanar irin shigar da matasa keyi ta k'ananan kaya."


Dariya sheikh yayi sosai yana fad'in "Wannan ikon Allah yana bani mamaki, wai kai ka saka riga da wando na zamani ka d'aure k'ugu da ceinture (belt), amma idan ka fita waje ka ga wani matashi zai wyce da shiga irin ta kai saika gyara tsayuwa ka tsayar ka dinga yanko mishi hadisai da ayoyi harda karatun d'ab'ia na d'an adam ma kana nuna mishi rashin dacewar haka."


A sanyaye ya kalli Aswa'ne daya d'aure fuska tamau yace "Sheikh Aswane ya kake nufi ne to? Shin kana so ka koyar da hallacin shigarka ne ga matasa a aikace? Ko kuma dai kana son su k'yamaci abinda kai suka ga kana yi ne?"


Saida ya sauke ajiyar zuciya ya shafa tarin sumar dake kan shi a gaban yace "Abie, ai ni ba irin waccen shigar nake yi ba da ake zazzago wando ana takawa, kuma nima ina so na daina saidai Allah ne ya saka min soyayyar kayan a raina, kuma sun fi yi min kyau idan na saka."


Girgiza kai yayi yace "Kash! A gaskiya tunani da idonka sun fad'a maka k'arya yarona, taya kake tunanin suturar yahudawa zata fi yi maka kyawu fiye data ka suturar? Wa ya fad'a maka kawai kana son su ne saboda Allah ne ya saka maka soyayyarsu? Aswane magana ta gaskiya sutura ta hausa ita ce cikakkiya kuma kamilalliyar sutura, na yarda idan ka ce sun fi maka kyawu a jikinka, to amma kamala fa? Ita ma suna fito maka da ita ne?"


Shiru yayi kan shi a k'asa hakan yasa shi girgiza kai ya gyara zama tamkar zaiyi magana da d'an shekara ashirin ba wanda shekarunsa duka goma sha biyu bane yace "Aswane, wannan suturar da kake sakawa ta hayudu ce, manufa ce dasu data sa suka k'irk'iri wannan suturar, kuma sun cimma burinsu tunda har suka yi nasarar ribatar ire-irenku, amma ka sani cikar kamala na cikin tufafin hausa, fito da asalin haiba da kwarjinin mutum sai tufafin bahaushe, da wannan nake kira gareka d'ana ka siyawa kanka mutumci ta hanyar yafa shigar mutumci a jikinka."


Jinjina kai Aswane yayi yace "Insha'Allah Abie, zan kiyaye."


Jinjina kai yayi ya kalli d'an k'aramin yace "Wannan shi ne autana kuma ba autana ba, *Munzeer* yaron kirki ne, ba ruwanka da rigima ko fad'a, karatu kawai ka saka a gaba ko yaron kirki?"


Cike da jin dad'i yaron mai shekara biyar ya jinjina kai alamar eh, dafa kanshi yayi yana jinjina kai da murmishi yace "Allah muku albarka, Allah ya k'arawa karatun albarka, Allah ya k'ara had'a kanku, Allah ya wadataku da lafiya mai anfani."


Gyara zama yayi yace "Ku tashi ku tafi." Mik'ewa sukayi bayan sun amsa a ladabce, duk da kallo suka bisu har suka b'ace ma ganinsu, saida suka shige ciki kafin ya mik'e shi ma, hannun Hafsat ya kama yana fad'in "Muje ki kwanta ki huta, dare yayi fa."


Murmushi tayi tana ci gaba da shafa yaron cikinta daya dunk'ule wuri d'aya kamar baya motsi, suna shiga d'akin ta fahimci yau kenan zai kawo mata ziyara, dan baya zaune sai mace ta sameshi d'akinshi, da kanshi yake zuwa inda kike sannan ya lallab'aki ya amshi hakk'inshi, dan haka saita daure sosai ta saki jikinta bata yarda ta nuna bata jin dad'i ba, saida ya tayata yin wanka kafin suka k'arasa gadon girma, duk da tana jin d'an cikinta ya dunk'ule mata a mara haka ta jure bata nuna bata ra'ayi ba, har tambayarta yake ya isa haka saita sunkuyar da kai tace "Sai ka gamsu."


Shi kuma a duniyar Allah yana matuk'ar son mace mai raki, rakin ma irin na tsiyar nan, wallahi a duniya yana son y'a ga mace dake mayar da masassara ciwon kai, wacce zata dinga billi tana kuka akan abinda bai kai bai kawo ba, yana so wata rana Hafsat ta gwada yin haka ko sau d'aya ne, da zai yi zaune ya aje hularsa da babban riga da hirami ya dinga mata hidima yana rarrashinta. Da k'yar ya samu gamsuwa ya taimaka mata ta tsarkake kanta ta dawo ta gyara shinfid'ar ta kwanta a matuk'ar wahale.




*Washe gari*




Tana tsaka da tsantsara kwalliyarta a fuska ta ji wayarta dake cikin k'aramar jakar da zata fita da ita tana vibrations, saida ta d'an d'aga labulen d'akin ta tabbatar suna waje suna harkar gabansu kafin ta ciro wayar, zaro ido tayi ganin lambar sheikh ce wacce tsabar mahimmancin data bata har ta iya hardaceta a kan ta, ita kan ta bata san ta bashi wannan mahimmancin ba. Sam bata son d'aukar wayar a lokacin, amma abun mamaki lambarshi kanta kwarjini take mata ta yanda ba zata iya share kiran ba, hannunta da zuciyarta na kakkarwa ta d'aga kiran tana jan sallama, a sanyaye sosai ya amsa da "Wa'alaiki salam."


Shiru ne ya d'an ratsa na dak'ik'u kafin yace "Ki gafarce ni Ryam na sake kiranki, zuciyata azalzalata take a game da lamarinki, dan Allah ki fad'a min idan Abbanki ya dawo na zo na ganshi."


Wani sanyayyan murmushi ta saki a ranta tana fad'in "Allah mai iko, ni Maryam ba kowa ba kuma ba 'yar kowa ba, yau ni ce har babban malami kamar wannan yake min magiya haka?"


Ajiyar zuciya ta sauke tare da tunanin ai Abba ya karb'i lefenta har da ma kud'in aurenta, dan haka tasan duk girmanshi Abba ba zai yarda yayi magana biyu ba, dan haka ta saki murmushin jin dad'i tare da bud'a bakinta tace "Abba

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads