Showing 72001 words to 75000 words out of 173834 words
Chapter 25 - MATAR MUTUM Document Complete by Samira Haroun.txt
tare a gidana kafin mijinta ya sama mata gurin da zata zauna."
Cike da dattako iya tace "Wannan ai ba matsala bane Hajia, tunda dama ai a yau d'in ake da shirin tarewarta."
Da fara'a Hajia tace "To a shirya mana ita zamu d'auki abarmu, dan nan kam naga matsi zata sha."
D'an dungure ma Mimi kai Iya tayi tace "Gwara ta tafi ai ko na huta da jarabar taurin kan ta, dan in nan zata zauna saina fasa mata jikinta da duka."
Da raha Hajia tace "Ai na ga alama ne Iya."
Malam ma cewa yayi "Hajia kin kyauta min da zaki d'aukemin amaryata daga gurin sak'agunan nan, abinda suka iya kenan su sakata gaba suyita narka."
Duk wannan rahar da suke su sheikh na tsaye na saurarensu gaba d'aya jikinshi ya mutu jin hukuncin da Hajia ke ta yankewa a kan shi, haka suka fita Mimi kuma ta sake b'allewa da kuka, Asma'u ma duk da halin da take ciki saida ta taya su Iya rarrashinta, a k'arshe dai wajen kukan nan baccin wahala ya d'auketa dan wajen kukan har jan numfashi take sama sama.
Ai kuwa suna fita a masallacin unguwar sukayi sallah la'asar, ana sallamewa mutanen dake nan aka tattarasu aka d'aura auren Asma'u Bashir da Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif, tuni unguwa aka d'auka kowa ya shiga fadin abinda ya ji ya kuma k'ara da abinda ya fahimta a kai, haka dai gidansu Asma'u ma sai suka fara wani shirin daban suma, inda kishiyoyin mamanta suka shiga bak'in cikin wannan had'i musamman da aka ce sheikh ne yace zai mata lefe bayan ta shiga d'akinta, tunda shi ma Asas ne yayi wa matarshi�, abun bai musu dad'i ba ko kad'an sai ma da aka ce yau ita ma zata tare tunda dai da lallenta da kitsonta, ango kuma ya gyara d'akinshi to babu abinda za'a fasa.
*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:54 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
💫� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_�
� *[ T.M.N.A]* � 📖🖊�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*27*
Sosai dangi suka ci gaba da bikinsu saidai kusan duka angaye da amaren zuciyoyinsu babu dad'i, Sadeeq kan shi yayi wani iri a zuciyarshi da ya ji an d'aura auren Asas da wacce yake da burin aura, amma sai bai nuna ma kowa ba kawai suka ci gaba da shagalinsu, Asas ma sosai yake k'ok'arin nuna dauriya amma abun ya gagara, yayi kuka sosai na rashin Mimi, yana tunanin yanda zai fara rayuwa da wacce sam ba ita ce a tsarinshi ba, sannan ya rayu a kusa da sheikh da matar daya ci burin aura, a wuni d'ayan nan duk sai ya zabge ya fita hayyacinshi, kana kallonshi zaka san yana da damuwa. Haka ta b'angaren Mimi ma ta kafe ta k'i cin duk abinda aka bata ta k'i shan komai ta fad'a ta nanata ita fa asa sheikh ya saketa, tun ana bata maganar har akayi banza da ita aka ci gaba da sabga, labari kuma ya karad'e gari da kewayenshi, sheikh Abdul Waheed yayi aure amarya shakaf, wasu na fad'in dalilin auren wasu kuma a iya auren suke tsayawa. Amma a wajen k'awayen Mimi abun ba haka bane, sosai suke Alhini da kuma son ganin yanda Mimi zata rayu a gidan sheikh, wacce take wanda suka auri tsoho iskanci, ita me fad'in Allah ya rabata da auren sa'an babanta, yau gashi ta samu a b'agas ba fahimtar juna ba soyayya? Abun kam ya jijjigasu inda kowace jiki yayi sanyi tare da komawa gefe dan suga me zai faru.
*D'aukar amarya*
Ta wajen Asma'u kam motoci ne manya da k'anana guda goma sha hid'u suka d'auki dangi da abokan arziki aka nufi da ita gidanta cikin yada magana, kayan jikinta kawai aka d'aukar mata dan dama Asas yace baya buk'atar komai. A wajen uwata Mimi kam saida Abba ya nunata da bakin muciya kafin ta fito a gidan, mota uku Hajia ta turo a d'auketa a had'a da wanda zasu rakata gidanta kafin ranar tarewarta, a mota saida ta cika kunnen shi kan shi dreba dan kuwa kuka take sosai tana kiran "Mama, mama ke, mama, wayyo mama."
Har suka isa gidan Hajia dangi suka tarbeta aka sauketa a d'akin da Hajia ta ware mata wanda aka saka mishi komai na buk'ata, k'arshe dai kowa ya tafi ya barsu ana addu'ar fatan zaman lafiya da zuri'a ta gari. Kusan ba kowa a gidan kafin Hafsat ta zo dan su tarben matar Asas suka tafi, sanda ta samu Mimi aa d'aki kuka take sosai kamar ranta zai bar gangar jikinta, cike da tausaya mata ta zauna gefenta da k'yar tana cije fuska dan sosai ta gaji ga cikinta da take jin bak'in abubuwa da bata saba ba, saida ta dafa kafad'arta cikin taushin murya tace "Mimi."
D'an tsagaitawa tayi amma dai bata yi shiru ba, d'orawa tayi da "Mimi kuka kike dan an aura miki sheikh?"
Shashek'a ta shiga saukewa da sauri sauri, jin batayi magana ba yasa ta sake fad'in "Mimi ki kwantar da hankalinki kin ji ko, nasan waye mijina ba zai tab'a cutar dake ba, ki bani had'in kai mu zauna lafiya dake kinji Mimi?"
D'aga kanta tayi ta kalleta ido sun mata jajir sun kumbura tace "Dan Allah ki sa mijinki ya sakeni, ba zan iya zaman aure da shi ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba."
Wani murmushi tayi mai ciwo tace "Mimi zaki so shi, ni ma da fari haka na d'auka, Mimi ko kinsan ni da sheikh *auren je ka ga d'akin ka* aka mana, ban sani ba shi ma bai sani ba dan a lokacin ma yana madina wajen karatu, mahaifina ya kwanta rashin lafiya kawai aka kira sheikh ya dawo gida, yana zuwa suka taramu suka fad'a mana ai sun d'aura mana aure, gidanmu kawai suka turamu muka fara zama."
Numfashi ta sauke tace "Mimi ke ma idan kika nutsu kika wa iyayenki biyayya zaki ga ribar hakan, ki daina wannan tashin hankalin hakan zai tab'a zuciyoyi da dama wanda ba zasu tab'a mantawa ba har abada, musamman iyayenki da suke ganin sun isa dake, amma a zahiri sai nunawa kike kamar kinfi k'arfinsu ko kuma dai basu isa su umarceki ba, ya kike so mutane su kalleki? A matsayin 'ya wace ta raina iyayenta bata jin maganarsu?"
Jikinta kam yayi sanyi dan haka ta dakata da kukan ta sake kallonta tace "Ban raina iyayena ba, hasalima ina fad'a da duk wanda ya raina min su, indai har abinda nake yi a yanzu yana nuna rashin girmamawa ne ga iyayena, to na daina, zan musu biyayya iya iyawata da yardar Allah."
Murmushi Hafsat tayi tace "Yawwa *yer uwa*, ko ke fa, ki share hawayenki kinji ko."
Jinjina kai tayi tasa hannu tana share hawayen, yunk'urawa Hafsat tayi da k'yar ta tashi tsaye tana fad'in "Wallahi ga gajiya ta baibayeni ga kuma nauyin da cikin nan ya min."
Da kallo kawai Mimi ta bita har tace "Saida safe Mimi, kiyi alk'awarin kin daina kuka."
D'an murmushin yak'e tayi tace "Na daina."
Da kallo ta bita har ta fita tana jin anya kuwa zata iya abinda matar nan tayi? Tab'e baki tayi a ranta tace "Indai kuka na alamu ne na raina iyayena ai na daina har abada, amma wallahi sai mijinki ya shiga *uku* dan zai ga tab'ara."
Cikin shashek'ar kukanta ta d'aga kai ta shiga kallon d'akin, ajiyar zuciya ta sauke da tunanin yau ita ce zata kwana a nan? Wacce take shinfid'a bargo ta kwanta, ba panka sai iskan Allah dake kad'awa, yau gata a d'aki mai ac lak'e ga kuma panka, gyara dararta tayi ta kwanta ta dunk'ule sosai tana ci gaba da sauke ajiyar zuciya. *Asas*! Shi ne sunan daya diro mata a lokacin, da yanzu fa tana d'akinshi a matsayin matarshi, amma shi ne yanzu take zaman matar sheikh k'awarta kuma tana gidan Asas a matsayin mata, lallai inba hukuncin Allah ba me zai juya wannan al'amari haka, ai ko cewa akayi ka tsara dole zaka buk'aci dogon nazarin ta yanda abun zai kasance, amma gashi dake yin Allah komai ya canza kuma da wanda ya so da wanda bai so ba dole an hak'ura da yanda Allah ya tsara.
*Asa-Ma'u*
Tunda ya shigo gidan dare ya tsala sosai ya buga tagumi yana kallon Asma'u dake dunk'ule cikin k'aton hijabi ta had'a kai da gwiwa, baisan ta ina zai fara ba ko kad'an, a yanda ya tsara da Mimi shi ne zai mugun riritata. Ganin zaman shirun ba zai masa ba sai kawai ya sake k'ureta da ido yace "Asma'u."
A hankali ta d'an d'ago kanta tana jan majina da share hawayenta, a sanyaye ya sake fad'in "Muje muyi sallah ko?"
Jinjina kai tayi tare da k'ok'arin sauka a kan gadon, ita ta fara shiga tayi alwala ta fito shi ma ya shiga, sallah sukayi inda ya dafa kanta yayi addu'ar neman alkairin dake tare da ita da kuma neman tsarin dake tare da ita, mik'ewa yayi ya fita hakan yasa ta mik'ewa ita ma ta koma bakin gadon ta zauna tayi tagumi, "Allah sarki Mimi." Shi ne abinda ta fad'a, wa yayi tunanin canzawar abubuwa haka? Sosai take taisaya ma k'awarta musamman data tabbatar ba zatayi saurin duk'awa k'asa ta yarda da zab'in nan ba...Shigowar Asas ta sata saurin juyawa ta kalleshi, d'auke yake da tire da k'aramin faranti a sama, gefenta ya aje tare da fad'in "Bismillah."
Girgiza kai tayi cikin dakusashiyar murya tace "Na k'oshi."
Wani kallo ya mata cike da kawar da komai yace "Kina son d'ure ne?"
Girgiza kai tayi alamar a'a, fuska a had'e yace "To ci."
Jiki a sanyaye ta kai hannu ta d'an tsakuri naman ta kai bakinta tana rarraba ido saboda yanda ya tsaya yana kallonta, murmushi yayi tare da zaunawa kusanta ya saka hannu shi ma ya shiga d'auka yana ci yana saka mata a baki ita ma.
Suna idawa ta koma ban d'akin ta wanke hannaye ta kurkure baki ta fito, ganin baya nan sai kawai ta kwanta a kan gadon da zunbulelen hijabinta, ya d'an jima bai shigo ba har bacci ya d'an fara d'aukarta, kamar daga sama ta ji an bud'e d'akin da sauri ta bud'a ido amma bata juya ba, shi kuma yana ganin haka saiya kwanta gefenta yana karanta addu'a bacci.
*Shei-Haf*
Hannu ya kai zai bud'e k'ofar d'akin amma saiya tsaya cak saboda muryar Aisha da ya ji tana fad'in "Amie wai me yasa Hajia tayi mana haka? Kuna zaman lafiyanku ke da Abie zata had'ashi da wata, me yasa bata hak'ura ba ta sake samun wani saurayin ta aura, Abien mu ba son ta yake ba ita ma haka, idan fa a dalilin auren nan matsololi suka fara faruwa? Ni gaskiya Amie ba zan juri wata yarinya ta raina min uwata ba, kawai ki fad'a ma Abie ya saketa can ta samu wani ta aura."
Bud'e k'ofar yayi sanda Hafsat ke k'ok'arin yi mata tsawa, kallon daya jefi Aisha da shi yasa sunkuyar da kai tana fad'in "Sannu da zuwa Abie."
Cikin yanayi mai rikita bil-adam yace "Sannu da zuwa Kike min Aisha? Ke!"
Yanda ya fad'i ke d'in yasa ta d'aga kai sai kuma ta sake sunkuyar dashi tana d'an wasa da maganin cowon k'afafun data gama shafawa Hafsat, cikin b'acin rai yace "Eesha ke ce da fad'ar wad'annan maganganun a bakinki? Yaushe kikayi girman da har magana mai girma irin wannan zata fita a bakinki? Kina so ki ce min taya uwarki kishi kike kenan?"
Da sauri Hafsat ta kalleshi da mamakin abinda ya fad'a, sai kuma tayi k'asa da kan ta ita ma ba tace komai ba, a tsawace yace "Tashi ki bani wuri, kuma na sake jin bakinki na magana kan abinda bai shafeki ba ki kuka da kanki."
Mik'ewa tayi jiki na b'ari tayi hanyar waje, tana daf da fita yace "Ke!"
Tsayawa tayi ta juyo tana d'an sunkuyawa, cikin murd'add'iyar murya yace "Zan d'aura aurenki da Anas ki fara shiri akan haka dan kowane lokaci zan iya d'aura muku aure."
Da sauri ta kalleshi ido waje baki bud'e, cikin rud'ewa tace "Abie Anas kuma?"
Sama da k'asa ya harereta tare da zaunawa bakin gadon kusa da k'afafun Hafsat da ita dai take jin su da kallonsu, ganin bai kulata ba sauta mik'e tana maimaita Anas a ranta, ta sani bai da wata makusa yaro ne mai k'ok'arin neman ilimi a duk inda yake, d'aya ne a cikin almajiran mahaifinta, yana da ladabi da biyayya sosai suna kallonshi kamar yaya saboda sheikh na d'an sakewa da shi, wasu lokuta ma har karatu yake d'ora mata, to amma ai babu wani tsari na soyayya a gabanta a yanzu, to me ma ya jawo maganar aurenta? Dan kawai ta yi wannan maganar? Ko dai mahaifinta na tsoron kar zamanta a gidan yasa a samu matsala idan amaryarshi ta zo gidan? Babban fargaban shi ne yanda bai saka lokacin ba kawai yace a kowane lokaci, hakan na nufin rana tsaka zata iya jin an d'aura mata aure kenan?
Kallon Hafsat yayi bayan fitar Aisha ya kai hannu kan cikinta yace "Ya kuke?"
D'an murmushin yak'e tayi tace "Lafiya lau, ya hidima?"
Numfashi ya sauke ya gyara zamanshi sosai yace "Manga, kin ga me ya faru a yau ko? Hakan ya sake tabbatar mana ba mu ke da ikon juya rayuwarmu a yanda muke so ba, k'arin aure Allah ne ya halatta mana shi, sai dai a yanda na wa k'arin ya zo a birkice sai naji hankali ya kasa d'auka, tabbas Hajia uwa ce a gaareni data isa zartar da kowane irin hukunci a kaina, saidai a wannan karan qta yanke min hukunci mai tsaurin gaske."
Numfashi ya sauke ya kalleta yana rik'o hannunta yace "Sawwama, na so a ce idan lokacin nan yayi na shawarce, na rarrasheki kamar kowace mace, sannan na miki bajinta kamar yanda ake yi a al'adance ta hanyar kyautatawa, amma duk da haka *Qawwama* ina mai baki hak'uri da yanda abun nan ya zo mana, nasan ke mai hak'uri ce da kawar da kai ga kuma juriya, kiyi hak'uri da hukuncin mahaifiyarmu mu yi mata biyayya, ni dama ke ce k'ashin bayana kuma martabata, dan Allah ki yafe min kinji."
Wani sanyayyen murmushi tayi tace "Hak'uri wai akan me kake bani sheikh nawa? Ni babu abinda ka min wallahi, sheikh karka manta fa na tab'a maka k'orafin k'ara aure amma sai ka ce lokaci ne baiyi ba, to yanzu lokacin ya zo ni kam zai saka ka tsaya kana bani hak'uri?"
Da k'yar ta gyara zama tana fad'in "Idan dai a yanda abun ya zo ne karka damu kan ka, ni Hafsat ina bayanka ba zan tab'a bari a rasa zaman lafiya a gidanka ba insha'Allah."
Murmushi yayi yace "Nagode Hafsy, yanzu fad'a min me kike so?"
Dariyar tsokana tayi tace "Dokin wuya."
Dariya yayi tare da mik'ewa ya durk'usa gabanta yace "Hau muje kinji ta wa."
Dariya tayi sosai tace "Na yafe, wace ni dan zan haye wuyan babban malami a daren nan?"
Wani shu'umin kallo ya mata yace "Ke a mai d'akin shehi mana."
Gyara zama tayi tana yatsina fuska tace "Hakane, amma ai mala'iku ma zasu iya yin hushi dani."
Cike da kulawa ya dafa cikinta yace "Ba kya jin dad'i ne?"
D'an k'aramin tsaki tayi tace "Gaba d'aya cikin nan ya daina min dad'i yanzu, bansan me yasa ba."
Cike da alhini yace "To kinga ki shirya gobe sai muje asibiti ko?"
Jinjina kai tayi dan dama ba musu take mishi ba, ko tana so ko bata so indai yace ayi to yi kawai zatayi.
*Asabar*
Tun asuba da Hajia ta tashi Mimi a bacci ta ji zazzab'in dake jikinta, saida tayi sallah ta kawo mata magani tasha, kallon Hajia tayi da tunanin anya kuwa? Ta ya zata fara shan magani a gabanta? Bata son magani a kai saboda d'aci, karb'a tayi tace "To."
Fita Hajia tayi hakan yasa Mimi d'aukar maganin ta jefa ta windown dake jikin gadon, d'an kurb'a ruwan tayi tare da komawa ta kwanta tana dunk'ulewa, ta d'auka bacci zai d'auke ta saidai sam zafin jikinta da kakkarwar da take ga ciwon kai sai suka hanata samun baccin.
*08:00* Hajia ta turo Salamatu data zo tace ta kira Mimi ta zo tayi kari, tana shigowa d'akin da yatsina fuska ta tunkareta, yanda ta ganta a kwance ta d'auka bacci take har take fad'in "Hmmm! Yar matsiyata kenan an samu wuri, ga lafiyayyen gado ga ac na hura miki iska mai tafe da sanyi, kinga har da wani baccin safe take alhalin iyayenta na can na fama da rana a tsakiyar kansu."
Duk bala'in ciwon da take ji saida ta yaye hijab d'in ta tashi zaune, wani kallon tsana da k'yama ta shiga jefawa Salamatu, ba wai ita mai aiki ba ko Hajia ce ta fad'i haka wallahi saita narka mata magana kafin ta tattara ta bar gidan, kamar yanda ta ji ita ce tasa aka aureta to saidai ta sa a bita da takardarta gida.
Gyara zama tayi sosai cikin muryar wahala da jigatuwa ta kalli idon Salamatu tace "...
_Wannan page gaba d'aya sadaukarwa ce gareki *Bilkissu Kanar*, Allah ya saka miki da alkairi._
*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:54 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_