Showing 114001 words to 117000 words out of 173834 words
Chapter 39 - MATAR MUTUM Document Complete by Samira Haroun.txt
yaga wannan dare haka ya wayi gari, rarrashin duniya ba wanda bai mata ba amma ina ta k'i ji, kuma gashu ba lokacin jawo aya ko hadisi bane bare ya tab'osu ko ta saurara, a daddafe yayi sallah ya dawo kan ta ya zauna yana kallonta, idonta sun kumbura sunyi ja har fuskarta ta canza.
Wani dogon numfashi ya sauke yana jin tausayinta na k'ara tsumashi, kukan da take sam bai d'aukeshi na tab'ara ba saina hak'ik'anin gaskiya, kukan shagwab'ar ya mishi yanda yake buk'ata, ya so a ce iya su kad'ai ne a gidan nan da sai ya nuna mata k'arshen zalamarta, zai biye mata ya riritata ya goyata a bayanshi ya mata dokin wuya yanda dole tayi shiru, da zai aje komai na shi ne ya shiga faranta mata rai har sai yaga hak'orinta sun bayyana da sunan dariya.
Tsaf take k'are masa kallo daga rufe fuskarta daa tayi da hannaye tana murzawa wai ita me kuka, sai yanzu ne ta kula ashe fa ustazun nan d'an gaye ne, askin fa kad'an ne ya banbantashi da irin na yan zamani, kawai dai shi ya aske duguzar ne sosai yanda ba'a barta a doron kan ba, amma har wani gyaran fuska yanda gemun ya masa sai ta ga ya birgeta yau kam, ga jallabiyar data fito da surarshi sosai.
Hannayen na ta daya kamo yasa ta rintse ido tana shashek'a, cikin sanyin murya yace "Ryam, zaki sha chocolat?"
Girgiza kai tayi alamar a'a, d'an jim yayi yana kallon gefe alamar tunani sai kuma yace "Zaki sha madara?"
Sake girgiza kai tayi alamar a'a, da sauri yace "Zaki sha ice cream?"
Girgiza kai ta sake yi alamar a'a, d'orawa yayi da "To fad'a min me kike so?"
K'ura masa ido tayi da k'yar ta bud'i bakinta murya can k'asa tace "Gidanmu nake so."
Tsura mata ido shi ma yayi, a take a shiga tunanin ta ya zai kaita gidansu a halin da take cikin nan? Kowa yasan ya zo wa wannan yar yarinyar? A gaskiya yana jin kunya kula ba zai iya ba, shi fa Hafsat ma baya so ta samesu a halin nan, gashi kuma ba zai iya kaita wajen Hajia ba dan kamar akwai cin fuska ma, duk da uwa take gareshi amma ai 'yarta yake aure, haihuwa kuma ba wasa bace, tun suna kawaici suna kawar da kai wata rana shaid'an da zai fara zugasu da saka musu tunani marar kyau.
Rik'o hannayenta yayi da kyau yana kallon fuskarta yace "Ryam, ba zamu je gidanku ba gaskiya, amma idan kina so zamu je wani wuri, na tabbata zai k'ayatar dake, kina so?"
Zuba mishi ido tayi kamar bata gane yarenshi, lumshe ido yayi alamar rok'o yace "Dan Allah Ryam."
Rufe idonta tayi alamar ba ma zata kula shi ba kenan, mik'ewa yayi tsaye ya daddage ya daka mata tsawar data saka ta zabura ta bud'a ido sanda yake fad'in "Dake nake magana malama kina min shiru."
Kyab'e baki tayi zata fashe da kuka ya nunota da yatsa ya sunkuyo daf da ita yace "Kika min kukan nan saina kuma zazzabga miki bulalar da zata fahimtar dake me nake nufi."
Tsaf ta had'e kuka tayi k'asa da kanta, nuna mata k'ofar ban d'aki yayi yace "Maza je kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah."
Jiki na kakkarwa ta shiga saukowa daga kan gadon, saidai allurar da har yanzu bata gama sakin jikinta yasa k'afafunta kasa d'aukarta, shirin fad'uwar da tayi yasa shi azamar tallabota jikinshi, cak ya d'auketa ya nufi ban d'akin da ita yana kallon fuskarta fuskarshi a had'e yace "Yarinya sai taurin kai, bakya gane magana cikin sauk'i."
Tsayar da ita yayi ya shiga cire mata kayan jikinta, nok'ewa ta shiga yi ita ma hakan yasa shi d'aga kai ya kalleta yace "Miye na kunyar kuma? Ba mun zama d'aya ba?"
D'auke kanta tayi tana kumburo baki, murmushi yayi yace "Shikenan bari ki gani, aidai zakiyi k'orafin na kalleki babu kayana ne ko? To bari muyi wankan a tare."
Kar-kar-kar! Jikinta ya fara ta shiga taka k'afafunta zata fita a ban d'akin, rik'ota yayi ya had'ata da k'irjinshi yana kallon fuskarta yace "To miye a ciki? Ni ba naki bane?"
Ko kallonshi ba tayi ba ta shiga sinne kan ta k'asa, b'alle botir d'in rigar yayi tare da tattarota daga k'asa yayi sama da ita, yanda ta ganta kwance a k'irjinshi da babu riga sai kwantaccen bak'in gashin daya kusa mamaye knirjin mai sulb'in gaske kamar na kan shi yasa ta saurin juya baya, hakan ya bashi damar k'arasa cire...� ya jawota ya had'a da jikinshi, yanda yaji jikinta ya fara d'aukar zafi da gaske ga rawar da yake mata yasa shi sakin murmushi ya d'ora hab'arshi a kafad'arta cikin kunne ya rad'a mata "Ryam ga ki da tsoro amma kuma ke ma kina bada tsoro."
Kakkaucewa ta shiga yi saboda kayan jikinta daya fara shirin cire mata, bai bata damar matsawa nesa da shi ba saida ya rabata da kayanta, yanda jikinsu ke gugar na juna tana jin duk wata hallita ta bawan Allahn nan a fatar jikinta sai ta nemi numfashi ta rasa, gaba d'aya ta sarewa lamarin mutumin ko ta ce lamarin maza.
Duk girmanshi, duk shekarunshi, duk matsayinshi yanzu nan ya aje su gefe har ya tsaya gabanta babu kaya zasuyi wanka? Tunda taja numfashinta sama bata maido shi ba ita dai ta k'ame wuri d'aya ta rintse idonta dan bâ zata iya kallonshi ba. Sheikh ko a jikinshi, wanka yake musu sosai cikin nutsuwa tare da wasa da ita, Mimi dai abun jin shi take wani iri, ita dake burin d'an k'aramin mijinta suyi wanka tare sai gashi yau old man ne ke mata wanka kamar baby.
Tana jin sanda ya kashe panpon ruwan suka tsaya, jim kad'an taji yana saka mata rigar wanka, kamo hannunta yayi suka fara takawa tana jin k'asanta na d'an mata zuzar zaren d'inkin nan hakan kuma na k'ara mata rad'ad'i.
Kan kujera ya zzunar da ita gaban madubi, mai ya d'auka ya durk'usa ya fara shafa mata man, kallonshi take yanda har yanzu towel ne a k'ugunshi, sam sai yake mata kamar ba tsoho ba, yanda yake d'aukarta da yanda yake sarrafa jikinshi ba alamar manyanta irin ta tsofaffin da zaka ga suna fama da ciwon baya k'afafu da sauransu. Yanda take kallonshi idonta bud'e yasa shi sakin murmushi yace "Inna Issa har yanzu ba zaki min magana ba."
K'in d'auke idonta tayi a kan shi, d'an murmushi kawai ya sake saki ya ci gaba da murza mata mai, yana gamawa doguwar riga abaya ya d'auko a cikin kayan daya k'ara zuba mata na ban mamaki, pant ya d'auko da bras ya sake durk'usawa ya zura mata k'afafun, kamata yayi ta mik'e zai k'arasa saka mata sai kuma ya kalleta, d'an sosa kai yayi da irin alamar jin kunya yace "Yan matan tsohonta, anya kuwa wannan zai isheki? Ni fa kallon baby nake miki."
D'auke idonta tayi daga kan shi ta k'arasa saka wandon, tam ya mata alamun dai ya matseta sosai, d'aukar bras d'in tayi ta saka ita ma haka ta mata kip, d'aukar rigar tayi ta saka da sauri ya zaunar da ita kan kujerar, macaji ya d'auka ya fara caje mata gashinta, tsaf ya d'aure mata shi da mad'auri sannan ya d'auki kallabin rigar ya fara yane mata kan cike da k'warewa, yana gama mata ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta sannan ya nuna mata sallaya yace "Kiyi sallah, zan je na saka kaya nima."
Takawa tayi ta k'arasa gaban sallayar, tana ganin fitarshi a d'akin tayi saurin cire pant d'in nan dan yana tab'ata a jikinta sosai tana jin zafi saboda d'inkin da aka mata, sallah ta kabbara shi kuma ya shiga d'akinshi dake nan b'angarenta dan shiryawa.
*Asa-Ma'u*
Tunda Asma'u ta zauna jiran Mimi ta ga ba alamarta sai kawai ta ma Hafsat sallama suka taf tare da Kabiru, ita ma suna zuwa gidan suka had'e da Asas, ita kanta sai ta ji kunya da suka had'u da shi ba'a gida ba, a d'arare ta bishi suka nufi na su gidan suma.
A daren kam tasha abubuwa da dama, kunya, fad'uwar gaba, farin ciki da kuma bak'ar wahala, dan kuwa Asas ya nuna mata ya samu lafiya, sun sha amarci sosai da kuma soyayya har garin Allah ya waye, daga wajen Hajia kawai yasa aka kawo musu abinci suna ci ya dunk'ule matarshi a bargo suka shiga ramuwar bacci.
Sake matseta yayi a jikinshi yace "Husna."
A hankali ta amsa da "Na'am."
Cikin taushin murya yace "Kina so na?"
Sinne kanta tayi a k'irjinshi tana d'an shafa cikinshi da hannunta ke kai tana murmushi, cikin shafa bayanta yace "Ina jinki mana, ko ba kya so na?"
Girgiza kai tayi a hankali tace "Ni ban ce ba."
"To me kika ce kenan?" Ya fad'a kai tsaye, cike da jin kunya tana b'oye fuskarta a jikinshi tace "Taya zan ce bana son mijina wanda a yanzu ya zama sirrina, a yanzu fa babu wani abu daya mana shamaki ni da kai, ko na so ka ko na k'i ka ka riga daka zama wani b'angare na jikina."
Matseta yayi sosai ya sumbaci kanta cikin dadad'an murya yace "Ina sonki *Asmy* na, ina sonki sosai, Allah barmu tare."
Cike da jin ya k'arawa kanta girma da farin ciki ta matseshi ita ma cike da jin kunya murya k'asa k'asa tace "Ni ma haka."
D'an tsakulkuli ya mata yana dariya yace "Ke ma me? Sai kin fad'a fa malama ko nima na dawo da kayata na rik'e."
Cikin bille bille ta shiga k'yalk'yala dariya tana fad'in "Nima haka, na fad'a to na fad'a."
Dakatawa yayi yace "Me kika fad'a to? Fad'i ko kuma na sake juyewa a kan ki yanzun nan, dama ba isata kikayi ba dan naji kin k'ara wani irin dad'i."
Dukanshi tayi a k'irji cike da kunya tace "Kai wallahi, haba dai."
Cikin dariya yace "Gaskiya na fad'a ai, na tabbata shirya min kanki kikayi kafin dawowata."
Girgiza kai tayi tace "Ni ba abinda nayi."
"Kin tabbata?" Ya tambaya yana lek'an fuskarta, jinjina kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "To yanzu fad'a min na ji, ke ma kina so na?"
Turo baki tayi tace "To wai me yasa ka damu da sai na fad'a maka nima? Ka yarda da abinda na fad'a maka mana."
Mak'ale kafad'a yayi yace "Um um! Kawai ki fad'a min Husna ko nayi kuka."
Waro ido tayi ta kalleshi da mamaki yanda kam duk ya kyab'e fuska shi shagwab'abb'e, kunya tasa ta rufe fuska tace "To ni ma ina sonka."
Sake k'amk'ameta yayi yana murmushi yace "Ko ke fa, har na ji dad'i."
Cikin farin ciki suka samu baccinsu a nutse suna k'amk'ame da juna kamar dama can asali masoya ne.
*Mim-Sheikh*
Cikin wata dakakkiyar shadda ya shigo d'akin wacce ta sa shi bayyana sak a angonshi, fara ce shaddar ga rigar daya d'ora irin ta malamai ga hula da takalmi k'afa ciki, shagala tayi da kallonshi dan gaskiya da zata iya bud'a baki a wannan lokacin tayi magana to zata ce "Kayi kyau." Ne, amma data ga yana mata murmushi saita d'aure fuska har saida ya tsaya gabanta yace "Zamu iya tafiya?"
Mik'ewa kawai tayi ta nufi hanyar fita, rik'e hannunta yayi suka kalli juna, ba alamar sakin fuska yace "Bana son jin shirun nan idan muka fita, zan d'auki wannan shirun ne kawai saboda ni na ja, amma iyalina ki girmama min su ta hanyar bud'a baki kiyi magana idan sun miki, Hafsat a gaba take da ke, karki jira sai ta gaisheki kafin ki gaisheta."
Shafa kumatunta yayi yace "Kin gane?"
Sunkuyar da idonta tayi saboda k'wallar da taji sun cika mata ido, tallabo fuskarta ya sake yi cikin sanyin murya yace "Kiyi hak'uri kinji, nayi alk'awari na yau kawai zan baki lokaci na gaba d'aya, zan sa ki fara tunanin tsohonki a zuciyarki, sannan nayi alk'awarin saka murmushi a fuskarki yau d'in nan."
Kama hannunta yayi suka shiga takawa a nutse, ta k'ofar waje suka fita kafin ya zagaya ta k'ofar shiga falon Hafsat, saida ya d'an k'wank'wasa sau uku kafin ya shiga da sallama a bakinshi yana sakin hannun Mimi, yaran dake zaune dukansu falo suna karatu ne suka juya suna kallonshi da amsa sallamarshi, da k'yar da lahaula ta cira labb'anta ta furta "Assalama alaikum."
Ido suka fara zuba mata da d'an mamakin nan ta kwana ko me? Sai kuma suka amsa mata sallamar suna gaishe da mahaifinsu a ladabce, cikin k'arfin hali Mimi ta kallesu da fara'a tace "Karatu ake."
Kallonta suka sake yi dukansu sai Munzeer dake k'arami daya washe mata baki yace "E aunty."
Sheikh ne ya kalleshi yace "Ina mamanku?"
Nuna d'akinta yayi yace "Tana ciki."
Hanyar nufa d'akin Hafsat yayi sai kuma ya kula da wani kallo da Aisha da Heezam suka rakashi kallo ne mai tattare da "Abienmu me kake nufi? Yarinyar nan anan ta kwana? D'aki guda kai da ita?"
Sai kawai ya ji ya tsargi kansa, saidai baiji kunya ba dan ita ma matarsa ce, halalinsa ce ba kuma haramun ya aikata da ita ba. Tsaye yayi dan sai yake ganin kamar zasu iya dakuwa da ita idan ya matsa, Mimi kuma da tsayuwar ta gundureta zaune tayi a kan kujera tana kallonsu ita ma.
Zai sake nufa d'akin Hafsat sai gata ta fito da hijab d'inta a jikinta, duk zuba mata ido sukayi har ta k'araso da sakin fuska tana kawar da komai daga ranta tana fad'in "Mimi da safe haka aka taso ki? Amma dai sheikh ka shiga lokacinta."
Duk murmushi sukayi sai Mimi data sunkuyar da kai tace "Ina kwana aunty."
Da fara'a tace "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?"
Da kunya ta amsa da "Lafiya lau."
D'orawa tayi da "Ya kwanan bak'unta kuma?"
D'an murmushin yak'e kawai tayi sai muryar Munzeer da suka ji yace "Amie gidanmu aunty ta kwana?"
Da fara'a Hafsat ta kalkeshi tace "E."
Aswan kam kamar da gangan kamar sub'utar baki sai cewa yayi "A b'angaren Abie ta kwana?"
Kallonshi duk sukayi sai Mimi da taji kamar ta k'urma ihu, a tsawace Hafsat ta kalleshi tace "Aswan wace maganar banza ce wannan? Ina ruwanka to?"
A tsorace ya kalli Hafsat yace "Amie kiyi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba."
D'auke kanta tayi ta kalli sheikh daya tsurawa Aswan ido yana tunanin dole yayi wani abu gaskiya, Aisha dake mace zai matsar da ita dan za'a fi samun matsala da ita saboda mace ce, mazan kuma dama dai lokacin karatunsu yafi yawa akan lokacinsu na zama gida, dan haka zaiyi k'ok'ari yaga raini bai shiga tsakaninsu da matarshi ba.
Kallonta sheikh yayi yana k'ak'aro murmushi yace "Manga kin tashi lafiya?"
Da fara'a tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"
Da fara'a shi ma ya amsa da "Lafiya lau."
A ladabce tace "Ya gajiya kuma?"
Kashe mata ido yayi yana murmushi amma bai ce komai ba, girgiza kai tayi tana murmushi ita ma ta d'auke idonta daga kanshi, d'orawa yayi da fad'in "Manga zamu fita da yarinyar nan mu dawo, ba wara matsala?"
Murmushi ta fad'ad'a tace "Ba matsalar komai sheikh, Allah ya tsare hanya, sai kun dawo."
Mik'ewa Mimi tayi tana d'an cije baki, kallonta Hafsat tayi tana sakin murmishi tace "A dawo lafiya?"
Da murmushi ita ma ta amsa da "Allah yasa, mun gode."
Gaba Mimi tayi sheikh ya ma yaran addu'a kamar yanda ya saba kafin ya bi bayanta yana duba agogon hannunshi ta azurfa data nuna k'arfe *06:20* na safe, da kanshi ya bud'e mata gaban motar ta zauna ya rufe kafin ya zagaya ya shiga suka bar gidan.
*Sorry mutane na, wlh gaba d'aya ne aka d'auke mana network.*
*Alhamdulillah*
7/22/21, 9:00 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
💫� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_�
� *[ T.M.N.A]* � 📖🖊�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*42*
Bud'e bakinta tayi da iya k'arfinta ta fashe da kuka, hankali tashe ya aje kofin hannunshi ya tallabo fuskarta yana fad'in "" A'a Mimi, me na miki kuma daga magana? Kinga idan ba zaki sha ba to shikenan, amma daina kukan kinji."
Hannaye duka biyu ta rattab'a a fuska tana murzar ido tana ci gaba da kukanta, zaune yayi da kyau kusanta ya jawota ya d'ora kanta a k'irjinshi yana shafa kanta yana fad'in "Shikenan to, haba yan matan tsohonta, so kike ace raguwa ce ke a miki dariya?"
Wata irin shashek'a ta shiga yi da gangan kamar zata had'e zuciya, sake tallabo fuskarta yayi ya marairaice yace "Haba Ryam, so kike sai kin nunawa duniya yau sheikh Abdul Waheed ya zo gareki? Ki daina mana kinji, ya isa haka kar kanki yayi ciwo fa."
A tak'aice dai yanda sheikh yaga wannan dare haka ya wayi gari, rarrashin duniya ba wanda bai mata ba amma ina ta k'i ji, kuma gashu ba lokacin jawo aya ko hadisi bane bare ya tab'osu ko ta saurara, a daddafe yayi sallah ya dawo kan ta ya zauna yana kallonta, idonta sun kumbura sunyi ja har fuskarta ta canza.
Wani dogon numfashi ya sauke yana jin tausayinta na k'ara tsumashi, kukan da take sam bai d'aukeshi na tab'ara ba saina hak'ik'anin gaskiya, kukan shagwab'ar ya mishi yanda yake buk'ata, ya so a ce iya su kad'ai ne a gidan nan da sai ya nuna mata k'arshen zalamarta, zai biye mata ya riritata ya goyata a bayanshi ya mata dokin wuya yanda dole tayi shiru, da zai aje komai na shi ne ya shiga faranta mata rai har sai yaga hak'orinta sun bayyana da sunan dariya.
Tsaf take k'are masa kallo daga rufe fuskarta daa tayi da hannaye tana murzawa wai ita me kuka, sai yanzu ne ta kula ashe fa ustazun nan d'an gaye ne, askin fa kad'an ne ya banbantashi da irin na yan zamani, kawai dai shi ya