Showing 102001 words to 105000 words out of 173834 words
Chapter 35 - MATAR MUTUM Document Complete by Samira Haroun.txt
yarda, ya za'a had'aki da tsohon gwangwani wanda ya kusa ritaya a duniya ma ba'a aiki ba, ke kika yarda? Lallai da ni ce ke saina nunashi da bakin wuk'a nace ya sakeni."
Dariya wasu sukayi sai Hafsat da tace "Ke dai kina jin haushin rasa mijinmu da kikayi."
Kallon Mimi tayi tace "Kinga Mimi kafin tayi aure ba irin asirin da batayi ba dan mijinmu ya aureta, da k'yar ta shafa masa lafiya har kotu aka shiga tsakaninsu."
Dariya aka yi sai Hajia da tace "Yanzu *Karima* d'an nawa ne ma gwangwani? Kinsan fa da a gabansa kike ba zaki iya furta a ba."
Cikin d'aga murya Karima tace "Hajia ai gaskiya na fad'a, shi ma tunda ya zama malamin duba ne ya asircemu indai muna gabansa bama iya d'aga kawunanmu mu kalleshi saboda cuta."
Kallon Mimi tayi tace "Ke k'anwata bari in fad'a miki, yana dawo ki ce ya maida ke gidanku kinji, daga shi har Asas d'in banga wanda ya dace dake bâ tubarkallah dake, idan kuma kikayi wasa yana dawowa nan da wata tara bikin sunan d'anki ko d'iyarki zamu zo, kinga kenan dai kin tabbata a *matar tsoho*."
Sunkuyar da kai ta sake yi inda Hafsat tayi murmushin yak'e sakamakon tunawa yanzu fa duk yanda suke da sheikh ko dan sauke hakk'in yarinyar nan sai yaje mata, sanyayyan numfashi kawai ta sauke aka ci gaba da hira ta raha da nishad'i har su Aisha suka zo ganin k'anwarsu bayan dawowarsu daga makaranta.
Bayan sallah la'asar Rakiya data kula da Hafsat ta shigo tana fad'in "Hajia zaku iya tafiya gida, ba wani abun yanzu insha'Allah."
Take idon Hafsat suka kawo ruwa da tunanin tafiya da zatayi ta bar yarta anan, kallonta likitar tayi tace "Ayya madame! Kiyi hak'uri karki damu, ko ba yarinyarki bace ai zamu kula da ita saboda abinda sheikh ya d'aukemu muyi kenan, bare kuma 'yar sheikh guda?"
Murya a raunane tace "Dan Allah yaushe zan iya zuwa ganinta to?"
Shiru ta d'anyi dan gaskiya ba dan tana ita ba a tsari da dokar asibitin nan da wata biyu da yarinyar zatayi ba zai wuce ta zo ta ganta sau uku ko kad'an da haka ba, amma dake ita ce sai tace "Madame zamu iya yi miki alfarmar zuwa ganinta sau uku a kowane wata."
Da sauri Hafsat ta kalli su Hajia ta kalli Rakiya tace "Sau uku kawai? Amma kuma taya zan rayu nesa da 'yata."
Murmushi tayi tace "Karki damu madame, zata kasance cikin kulawarmu."
Kamar zata fashe da kuka tace "To amma Rakiya ina so 'yata tasha nono ko kad'an ne."
Da fara'a tace "Wannan ba matsala bane madame, duk sanda kika zo ma idan kina so za'a iya tatsa mata nonon na ki sai a bata."
D'an murmushi tayi ta jinjina kai alamar to, da haka ta mik'a musu katin maganin da za'a siya kafin ta fita, haka suma suka mik'e suna shirin tafiya, Hajia ce ta fara kallon Mimi tace "Mimi ku zaku wuce gida ke da Asma'u, idan kunje saiku d'ora abinda zaku ci ko? Zuwa dare zan dawo nima."
Jinjina kai sukayi a tare kafin suka fita dukansu kowa yayi hanyar da zata sadashi da inda ya nufa.
Suna zuwa gida madafa suka shiga suka d'ora lafiyayyen girki da miyar hanta, Asma'u ma na taimaka mata saidai tana koya daga haka, suna kammalawa daf da magriba suka nufi d'akinsu dan yin alwala, wayarta ce tayi k'ara ta duba dan ganin mai kira, lambar sheikh ce ta bayyana hakan yasa gabanta fad'uwa, gyara tsayuwa tayi ta dafe k'ugu tace "Wai me tsohon nan yake nufi dani ne?"
D'auka tayi ta kara a kunne tace "Hello."
Sautin muryarshi ta ji yana murmushi kafin yace "Assalama alaiki yan matan tsohonta?"
Numfashi ta sauke ta dafe k'ugu tace " Ustaz, wai me yasa kake kirana yan matanka ne? Hakan fa da kake ba kyau ko kad'an, kaga dai ni yarinya ce har yanzu, idan kana min irin haka kunya nake ji wallahi."
Yar dariya yayi ya gyara zamanshi sosai yana lumshe ido yana sauraren tab'ara yace "Allah ne ya wankeki ya bani duk da tsufana, kinga dole na kiraki yan matan tsoho, batun kunya kuma da kike fad'a wannan ki aje gefe, dan ina dawowa da kaina zai d'aukeki zuwa gidanki."
Bud'e baki tayi tace "Lahhhh! To ni ai na fad'a maka bana son zama da kai ko, ya kake so na zauna da kai ne a takure?"
Numfashi ya sauke yace "Ba a takure zaki zauna ba, na miki alk'awarin zaki ji dad'in zama dani har ma ki so ni a zuciyarki."
Kyab'e fuska tayi baki tab'e tace "Tabd'ijam, a hamsin ba biyu d'in?"
Shafa sumar kan shi yayi yana lumshe ido sosai yace "Ba hamsin ba biyu bane, nan da d'an lokaci da mun zama d'aya ni dake zai zama 48+17 kinga zasu zama 65, ni dake zamu zama yan shekaru d'aya."
Shiru tayi dan kanta ya kulle da wannan lissafin daya mata, d'an sosa k'eya ta shiga yi na tunanin ya ne abun yake? Muryarshi ta ji yace "Yan matan tsoho, zan turo miki da lambar bud'ewa na asusun nan, na rok'eki Ryma ki ciri duk abinda kika da buk'ata amma karki rok'i wani kinji, kinga fa yanzu ke matata ce ko?"
K'yabta idonta tayi kafin tace "Me yasa kake tunanin zan rok'i wani to idan ka yarda ni matarka ce?"
Ajiyar zuciya ya sauke yayi shiru, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya bud'i baki da k'yar yace " *A tsorace nake Ryam, tsoro nake ji*."
Da rashin bawa abun mahimmanci tace "Tsoron me?"
Murya k'asan mak'oshi yace "Tsoron kar wani ya sake shiga *gonata, hurumi na*."
Gyara tsayuwarta tayi cike da k'uruciya da rashin hankali ta bud'e baki ta fashe da kuka tace "...
*Alhamdulillah*
7/22/21, 8:59 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
💫� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_�
� *[ T.M.N.A]* � 📖🖊�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*38*
Gyara tsayuwa tayi cike da k'uruciya da rashin hankali ta bud'e baki ta fashe da kuka tace "Ni d'in dama taxi ko wata katifa ka mayar dani, Allah zan fad'awa Abba na ce kawai kallon taxi kake min."
A rikice kuma a rud'e ya mik'e tsaye daga zaunen da yake yana fad'in "Ba fa haka nace ba Ryam, nufi na ta wa gonar, ni kad'ai."
Dakatawa tayi dan dama kukan ba hawaye ne da shi ta shiga sharewa tana turo baki tana fad'in "To naji, kuma ai kai ma nasan ba zaka maidani gonarka ba ko? Tunda ai kaga ni kamar y'arka ce bani da wayo."
Wani murmushi ya saki mai sauti yana girgiza kai ya koma ya zauna a k'asan mak'oshi yace "Um."
Cikin shagwab'a tace "To zanyi sallah."
A ladabce yace "Ki min addu'a kinji yan matana."
Kamar wata sakarya sai kuwa tace "Me zan rok'a maka?"
Cike da jin dad'i yace "Na dawo lafiya na sameku cikin k'oshin lafiya, sannan ki rok'a min Allah ya bani nasara a kan ki."
Bud'e baki tayi tace "Kai! So kake ka cuceni?"
Murmushi yayi yana jin a ran shi "Oh Allah." Kafin a zahiri yace "Ba zan cutar dake ba."
"To me zaka min." Ta fad'a tana turo baki, cikin raha yace "Kawai ina so ne idan kin tare gidana na mayar dake yar lelena, autar gidana, shagwab'ab'iyata, rigimammiyata, rikicina kuma sarauniyar kukana."
Kyab'e fuska tayi tana d'an zama bakin gadon tace "Duk ni ce ma mai wannan halin? Shikenan Allah dai yana gani."
Cikin rarrashi yace "Oh ba haka nake nufi ba, ina so ne na mayar dake kamar wata sarauniya, na dinga miki wanka ina baki abinci sannan kiyi bacci idan kin gama kukan jin dad'i."
Rufe fuska tayi saboda jin kunya tace "Da gaske?"
Cikin gasgata yarintarta tace "Da gaske." Jinjina kai tayi tace "To amma ai ba'a wanka sai an cire kaya, kana nufin saina tsaya a gabanka babu kaya?"
Me sheikh zai yi sai ya tintsire da dariya yana dafe goshi, jin yana dariya sai kawai ta murgud'a baki ta daste kiran ta aje wayar ta mik'e, jin ta kashe yasa shi kallon wayar da mamakin wai kashe mishi waya tayi? Girgiza kai yayi yana sakin wani murmushin.
Har suka ci abinci wajen k'arfe 09:00 na dare sannan Hajia ta dawo, sannu suka mata kafin Mimi tace "Hajia a kawo miki abinci ne?"
Cike da gajiya tace "A'a Mimi barshi, mun ci abinci a can, wanka zanyi yanzu na samu kwanta."
D'an murmushi tayi kafin ta mik'e tana d'aukar jakarta da hijab zata shiga d'aki tace "Idan kunyi waya daa sheikh ki nemi izininshi gobe sai kuje can ku wuni ko?"
Cike da kunya ta jinjina kan ta alamar to, suna kallo ta shige kafin Mimi ta gyara zama daga d'an durk'usawar da tayi tana kallon Salamatu, yanda ita ma take kallonta yasa Mimi had'e fuska tace "Na zubo miki tuwon ne?"
Tab'e baki tayi ta wuce na ta d'akin ita ma dan a nan take kwana, tsaki Mimi tayi tana binta da harara, dariya Asma'u tayi tace "Ke kuma me ya had'aki da tsohuwar mutane?"
Tab'e baki tayi tace "Hum! Bata da kirki da kike ganinta." Nan ta kwashe komai ta fad'a mata daya faru wanda ya jawo silar rashin shirinsu, Asma'u dai dariya take sosai.
*00:10*
Mimi na bacci ta ji wayarta na vibration, daddab'ata Asma'u tayi ta farka tana d'aukar wayar, kallon Asma'u tayi da ita ma wayarta mak'ale a kunne da alama da na ta mijin take waya, sake kallon wayar tayi tana danna ok tana fad'in "A wannan lokacin kike wani waya da miji ke jarababbiya, mtsss!"
Tsakin da tayi yasa shi lumshe ido can k'asan mak'oshi yace "Shiyasa nake son ki yan matana, ke ba jarababbiya bace, ko?"
Yanda ya tambayeta yasa saurin cewa "E mana." Ta k'arashe tana hararen Asma'u, kamar wata mai iskokai sai cewa tayi "Yawwa sheikh, Hajia tace gobe zamu je gidanka wajen aunty Hafsat."
Jim yayi yana d'orawa da tantancewa hak'ik'anin me yake ji a kan yarinyar, shirme dai take tabka mishi na gaske, amma sai ya ji ranshi bai b'ace ba, idan kuma ya b'ace na wucen gadi ne komai zai wuce. Asma'u ma kallonta tayi dan wallahi ita tasan da gangan Mimi ta maida kanta kamar wata sakara idan tana gaban sheikh, ai ba haka take ba a da, yarinyar mai ajin tsiya wani zubin ma har da d'aukar kai, amma yanzu ta zama wata mai ido a tsakar ka.
A saanyaye sheikh yace "To fitar d'azu da kukayi da izinin wa aka yi?"
Kan ta tsaye tace "Ai Hajia ce tace muje."
A hankali yace "Kenan Hajia tana bada izini ne?"
A sangarce tace "To kayi hak'uri dai yanzu amma ka barmu mu tafi gobe."
Cike da baccin dake idonshi yace "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya."
Kamar wacce aka kad'awa da hanji sai kawai tace "To saida safe."
Da sauri yace "Baki ji ba." Dakatawa tayi tace "Uhum." Kamar zaiyi bacci yace "Bacci nake ji, dan Allah ki min addu'a."
Da mamaki murya a sanyaye tace "Addu'a kuma? Kamar ya?"
Saida ya sauke numfashi yace "Na saba idan ina cikin iyalina na kanyi musu addu'a idan sunyi bacci, yau kuma da bana tare dasu sai naji ina sha'awar nima a yi min, Hafsana ta jima da yin bacci bare tayi min."
Maganarshi ta k'arshe ce tasa ta jin wani irin duka da k'arfin gaske a zuciyarta, shirun da dukansu sukayi yasa ta jin idonta taf da hawaye, lumshe ido tayi murya na rawa tace "Abdul zuciyata rawa take, bana jin dad'i kaji, ban da lafiya yanzu bacci zanyi."
Shiru yayi yana saurare da karantar yanayin muryarta, a sauk'ak'e yace "Shikenan rik'e waya zan tofa miki addu'a."
Wayar na kunnenta ta ji yana karanta mata addu'ar bacci, yana kammalawa cikin muryar rad'a yace "Saida safe yan matan tsohonta, kiyi bacci lafiya, ina k'aunarki."
K'it! Ya kashe kiran yana k'urawa wayar ido, maganarshi ta k'arshe da maganarta ta k'arshe ya shiga d'orawa a mizani yana san yasan me ya jawo mata rashin lafiyar data fad'a a nan take? Da wannan har ya yi addu'ar bacci ya gyara kwanciyar kafin ya tashi anjima ya gana da mahaliccinsa.
*03:00* daidai goshinsa na k'asa yayi sujada ga ubangiji yana fad'a masa buk'atunsa idonshi na zubar da ruwa, cikin k'ank'anr da kai da kadnaita Allah da mayar da kai ba kowa ba yake kuka yana fad'in "Ya Allah ka gafarta min zunubaina, ni mai laifi ne a gareka Allah ina tuba a duka kurakuraina dana sani da wanda ban sani ba, Allah ka yafe min zunubaina, Allah nagode abisa ni'imominka gareni, Allah nagode da ni'imarka gareni, buwayarka mafi d'aukaka, izzar mulkinka mafi guda, tsarkakar mulkinka wanzanjiya, kyautarka mafi anfanuwa, Allah ina k'ara gode maka. Allah ka shirya min yarana shiri irin na addinin musulunci, Allah ka shirya min kan iyalina su zama mafiya kyawan alak'ar zumunci, Allah ka raya min *Khadija* ka inganta lafiyarta, Allah ka bawa mahaifiyarta lafiyar shayar da ita, Allah ka bata juriya da ikon tarbiyar yaran. Ryam! Allah ka fini sanin sirrin dake cikin tarayyata da ita, bansan komai ba Allah face ilimin daka yarje min na sani a bayyane, ina k'ara neman zab'inka akan lamarina da ita, idan har alkairi ce a gareni Allah ya ka dawwamar da alak'armu tare da saka mana fahimtar junanmu, idan kuma akasin hakane Allah ka gaggauta yin nesa da ita dani da kuma ahalina, Allah na rok'eka da zuciya d'aya inhar Ryam ba alkairina bace duk son da nake mata Allah ka cire min ita a zuciya sannan ka nesanta ta dani da iyalina na har abada. Idan kuma aurena da ita yana nufin koya min darasi akan kalamaina da suke nuna k'yamar mace mai biyar maza ne, Allah gani a gabanka kaina k'asa, ka fini sanin abinda ke cikin zuciyata, idan har tubana na gaskiya ne Allah ka shirya min yarinyar nan ka d'auke idonta da hankalinta daga kowane namiji bayan ni mijinta, Allah na rok'eka inhar tubana na gaskiya Allah ka saka farin ciki a rayuwata data iyalina, astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah-alzeem, astagfirullah wa'atubu ilaikh."
D'agowa yayi hawaye na ci gaba da zarya a fuskarshi, sunkuyar da kai yayi tsabar k'ask'antar da kai yana tahiya kafin ya yi add'u'oin bayan tahiya ya sallame, jim ya d'anyi kafin ya d'aga kanshi ya kalli gabanshi, wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke, cikin muryar data sha kuka a shak'e yace "Nayi alk'awari tsakani na da ubangijina, Allah kaine shaidata kan alk'awarin nan da zan d'auka a yanzu, *Ryam ta riga da ta zama matata, nayi alk'awarin tsare mutumcinta da k'arfina, sannan nayi alk'awarin rik'eta abisa gaskiya da amana, nayi alk'awari ba zan tab'a k'yamarta ba saboda laifin data aikata a baya, nayi alk'awarin ba zan gujeta ba haka kuma ba zan tab'a fallasa sirrinta*, Allah na rok'eka idan har wannan nayi shi ne saboda kai ina fatan zan samu sakamako na a wajenka kamar yanda kayi alk'awarin kyakyawan biya ga ma'abota kyauta da kyautatawa."
Wata ajiyar zuciyar ya sake sauke yana jin wata nutsuwa na ratsashi a sanyaye, gyara zama yayi ya tokare k'afarshi d'aya ya fara zikhri da hannayenshi, bai gushe a wurin ba saida wayarshi ta alamta mishi k'arfe 05:00 kafin ya mik'e ya kabbara sallah subh dan a nan ba masallaci zai ji ba.
*Niger*
Masha'Allah kam Mimi dake akwai wayewa da kuma kunya, tuni ta sake a cikin gidan dan kuwa ita da Asma'u da Fanna cousine d'in su Hafsat sukayi girki na rana dana dare, sosai ta saki jikinta saidai bai hanata kama jikinta ba, dan ko abun dariya akayi zata murmusa, aiki dai nai zata mik'e ta taimaka ko ba'a nemeta ba, yamma nayi ita da Asma'u suka gyara falon tsaf sukayi turaren wuta dana tsintsiya dan sun fahimci a fannin tsafta dai kam Hafsat bata da tsara, dan in maganar gaskiya za'ayi to Mimi zata iya cewa gabanta ya girgiza sanda ta shiga d'akinta ta samu ko ina k'al-k'al kamar ba mutum ke rayuwa a nan ba, amma dake ita d'in yar sa kai uku ce sai ta yatsina fuska ta nuna inhar zasu zauna a matsayin kishiyoyi to zata zauna da ita kuma zata iya ita ma.
Sun idar da sallah magriba tana zaune a falon tare da Munzeer da Aswan kasancewar akwai d'akin da aka ware ana shiga ayi sallah, Hafsat ne gefe zaune akan katifa tana waya k'asa k'asa tana murmushi da alama da sheikh suke magana, Mimi kam da bata damu ba ma remonte ne a hannunta tana ta canza tasha (🤣Baiwar Allah mbc take nema), kallon Munzeer tayi dake kan k'afarta tana murmushi tace "D'an tanti, wai ku baku da wasu tasha ne bayan wannan?"
Cikin maganarshi ta yara yace "E aunty, duka wannan ne kawai."
Aswan dake jinsu ne yace "Auntynmu ai idan nishad'i kike so saidai in kin fita mak'wabta."
Harara Hafsat ta cilla mishi daga nesa hakan shi mik'ewa ya fita waje, Mimi kam aje remonte d'in tana ji a ranta ai ba nishad'i babu mbc, fitowar Asma'u yasa ta fad'in "Asma'u mu wuce gida ko?"
Hafsat dake jinsu d'an d'auke wayar tayi a kunne tace "Ku tafi kamar ya? Tun yanzu?"
Cikin jin kunya tace "E aunty, naga dare ya fara ai."
Girgiza kai tayi tace "Ba yanzu ba gaskiya, to ke Mimi me zai hana kiyi zamanki ma kawai tunda gidanki ne?"
Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta, murmushi Hafsat tayi ta d'ora wayar a kunne, duk da ya ji me take fad'a kuma yaji kamar yace "E hakane Manga, ki matsa mata ta zauna dana dawo ba sai na wahala d'aukota ba."
Amma kuma sai ya nuna kamar ma bai ji ba suka d'ora a inda suka tsaya, fitowar