Showing 144001 words to 147000 words out of 173834 words
Chapter 49 - MATAR MUTUM Document Complete by Samira Haroun.txt
tantak'washi da kifi d'anye, sannan yanzun nan Asma'u ta fad'a min wani abu da ake sha ana zama mowa a wurin miji, shine fa zan je na siyo."
Hararanta ta dinga yi amma ba tayi magana ba, sun jima suna kallon juna kafin Iya ta sassauta murya tace "Shikenan na yarda ki je, amma Mimi kar kiyi abinda zaki sa a zageni dan Allah."
Shafa kuncinta Mimi tayi tana mik'ewa tace "Yawwa Kakata, shiyasa nake son ki."
Girgiza kai tayi tace "Kiyi sauri dan Allah kinji, ni ma zan je wajen malam Hadi na sa ya maki rubutu na bakali a wurin miji."
Wata lalatacciyar dariya Mimi tayi ta jinjina kai dan tuni ta hango yanda zatayi ta tsokano sheikh kafin ta fice a gidan.
Ta d'aya hanyar ta bi ta kusa da makarantarsu anan ta samu taxi ta wuce, tana ciki Salma ma ta kirata bayan sun gaisa take sanar mata jibi fa zata shiga lalle, da rawar kai da zumud'i Mimi take ta fad'in Allah kai su ranar su sha biki.
Gurin masu siyar da litattafan hausa ta fara zuwa ta siyo na girki da kuma wasu na ki gyara da kan ki da saurarensu, daga nan gurin masu kayan marmari ta nufa ta shiga had'owa kala kala, ta gama siya ta juya zata nufi Inda zata samu dabino da cukui suka had'e da yayar Asma'u Rayya, gaisawa sukayi saidai jikinta har rawa yake tsabar ta kwab'ar da zance tace "Mimi ke ce kasuwa a lokacin nan? Dama malamai na barin matansu fita haka?"
D'an murmushi tayi dake tana kallonta kamar yar uwa sai tace "Ni ma na je gidan Iya ne shine na biyo siyan wannan."
Murmushi tayi ita ma tace "Lallai fa su Mimi an shiga sahun manyan mata, kin ga yanda kikayi wani fresh dake wallahi kamar na saki a jakata."
Dariya Mimi tayi ba tace komai ba, kama hannunta tayi tace "Zo muje ki gani, ni ma nan ga ne zan je neman d'anyen madarar rak'umi."
Mimi dai bin ta kawai tayi suna tafe take fad'in "Kina ji ko k'anwata, wani sirri ne zan baki ni ma wata malamata ta bani shi, amma fa karki fad'a ma kowa kinji?"
Jinjina kai tayi suka ci gaba da tafiya tana fad'a mata abubuwan buk'ata, hakan yasa Mimi kallonta galala dan duk kayan data fad'a ita ma sune a ledarta, hatta da nonon rak'umin a wata alimentation ta sameshi nan bakin kasuwar, amma sai ta bita da to kawai har saida ta rakata ta siyo na ta kayan ita ma.
Duk da haka ta k'aru da zamansu a d'an lokacin sanda take fad'a mata "Kinga kishiya gareki, karki yarda abokiyar zamanki ta dinga fahimtar halin da kuke ciki ke da mijinki, idan ya b'ata miki karki bari ta sani, idan duka ya miki a d'aki ki fito kina dariya, karki bari ta san k'uncinki ko kukanki bare damuwarki, dinga sakin fuskarki kina nuna farin ciki kawai. Haka kuma dan kina yarinya ba mahaukaciya bace ke, ke ma ki ja d'amara sosai ki k'waci wani kaso a zuciyar mijinki."
Kallonta tayi ta rik'o hannunta sanda suka tsaya bakin titi zasu tafi tace "Mimi ki kula sosai, kishiyarki ta girmeki nesa ba kusa ba tunda ta haifi kamarki a yanda na ji, kinga kenan ta fiki sanin wanene mijinku, kuma kinsan an ce wanda ya rigaka kwana to fa tabbas zai rigaka tashi, zata iya biyo mikita wata sigar da ba lallai ki fahimta ba, zata iya nuna miki ta fiki wayo dan haka ta dinga miki siyasa tana mikina babba da yaro, to fa idan ba nutsuwa kikayi ba a wannan lokacin zata iya rubtawa da ke."
Galala Mimi ta kalleta tace "Kamar ya kenan Aunty Rayya?"
Murmushi tayi ta dafa kafad'arta tace "Misali ko a wajen kula da mijinku, zata iya nuna miki yafi son abu kaza alhalin ba gaskiya ba ne, ko kuma ta nuna miki baya son abu kaza alhalin yana son wannan abu, ke ko a wurin girki idan kika samu makira zata iya saka ki zuba awon da ba zai ishi fad'in gidanku ba, k'arshe da an tambayi ba'asi zamewa zatayi ta barki a ciki."
Shiru Mimi tayi saidai inzata fad'i gaskiya tasan Hafsat tsakani da Allah take fad'a mata wasu abubuwan, tunda wani abu bai tab'a faruwa ba dalilin taimaka mata da tayi, to amma ai ba'a k'in ta mutane tunda shawara ce ta bata.
Daidai lokacin da Rayya ta tsayar da taxi a lokacin Mimi tace "To ya zanyi kenan aunty?"
Kallonta tayi a gaggauce tace "Nutsuwa zakiyi da kyau kisan me mijinki yafi so me ye baya so, sannan ki kwantar da kanki ki girmama duk wanda kika ga yana girmamawa, hakan ba fad'uwa bane ke siyawa girma da soyayyarsa."
Murmushi tayi sosai tace "Nagode aunty Rayya."
Ita ma murmushi tayi tace "Ba komai, kamar Asma'u na d'aukeki."
Mik'o mata wayarta tayi tace "Aunty saka min lambarki mana."
Karb'a tayi tana saka mata tana fad'awa taxin inda zai kaita, mik'o mata tayi kafin ta shiga suna sake sallama, ita ma taxin ta samu ta d'auki hanyar komawa gida abin ta zuciyarta fes bata jin wani k'unci.
*Sheikh*
Lallai idan har bak'on yanayin da baka saba dashi ba ya riskeka dole ko da a yanayi na gangar jikinka ne zai nuna, yau sheikh Abdul Waheed bai iya jira gari ya waye mishi ba a masallaci ya taho gida, kai tsaye kula bayan gidan ya nufa ya tsaya ya zubawa tsintsayen dake shawagi ido, shi ba salatin Annabi ba, shi ba hailala ko istigfari ba, haka kawai yake tunanin yanda 'yarcikin ke neman zama silar tarwatsewar gidanshi da kuma jefashi damuwar da bai san ya zaiyi ya fito da kan shi ba, yarinyar daya rena da hannunshi ya tarbiyanceta, yarinyar da har a cikin gidan nan idan mahaifiyarta bata samu dama ba ita ke karantar da matan auren unguwar nan, amma ita ce yau take neman canzawa gaba d'aya har take iya shiga hurumin da sam bâ na ta bane.
Babban abun damuwar shi ne yanda daga jiya zuwa yanzu da gari ke wayewa yake sake jin wata kewa da muguwar k'aunar Mimi na sake baibayeshi ta yanda har yake jin idan yaje gidansu ko k'asa ne zai durk'usa ya ce tayi hak'uri ta dawo gareshi, uwa uba matsananciyar kunyar had'uwa da iyayenta da yake ji, baisan ya zai ce musu ba, ya fad'a musu 'yar shi ta fi k'arfinshi ne ko kuma dai yace yaro ne na yanzu ka haifa baka haifi halinshi ba?
Wata ajiyar zuciya ya sauke ya na ci gaba da kallon yanda tamtabaru ke tsatsagar k'asa suna d'aukar abincin da ake watsa musu, yana wannan yanayin ne kiran Abban Mimi ya shigo wayarshi, wani mummunan fad'uwar gaba ya ji kamar wanda aka daka da k'atuwar gudumar bak'in k'arfe, har tsigar jikinshi ne ya ji ta tashi saboda rud'anin daya shiga, da k'yar ya d'aga kira ya d'ora a kunne jikinshi har wata makyarkyata yake, a daddafe suka gaisa har ya fad'a mishi zai zo anjima, suna sallama ya sake maida wayar aljihunshi yana tunanin dole ya kira Alhaji Ibrahim tunda uba ne gareshi ya rakashi wajen iyayen Mimi. Rintse idon shi yayi sosai dan har ga Allah wani kuka kuka yake jin yana taho mishi sakamakon abinda yake ji a zuciyarshi, shi da Hafsat ko da wasa basu tab'a musayar yawu ba ta fad'a ya fad'a bare ta kai ta ga yaji, amma yau ga shi wai zai je bikon macen daya tabbata idan bai je ba rayuwarshi ma zata shiga garari.
Wasa wasa sai gashi lokaci ya wuce mishi a wurin nan bai tsinana komai ba. Hafsat ma da taga shiru kuma ta duba d'akinshi baya nan ta tambayi su Heezam sun ce ya jima da dawo gidan sai ta d'auki waya ta kirashi, lalubo wayar yayi ya k'urawa lambarta ido, saida kiran yayi kamar zai tsinke ya d'aga amma kuma sai yayi shiru alamar yana saurare.
Hafsat kuma sai ta d'auka ko har yanzu hushi yake da ita, a sanyaye tace "Ranka shi dad'e, barka da safiya."
A yanayin da zaka san mutum baya cikin walwala ya amsa da "Barka, antashi lafiya?"
"Lafiya lau." Ta fad'a a ladabce kafin ta d'ora da "Dama na ga shiru baka dawo ba tun asuba, ko ka wuce wurin aiki ne?"
Wata zabura yayi yana waro idonshi akan tsintsayen, dafe gaban goshinshi yayi yace "Subhanallah! Na manta wallahi, ina zuwa."
Da sauri ya kashe wayar ya nufo hanyar sashen shi, Hafsat kam da mamaki ta bi wayar da kallo tana fad'in "Mantawa kuma? Aikin da babu abinda ka d'auka da mahimmanci bayanshi sama da mu?"
Tana nan tsaye a falon na ta ta ji k'arar k'ofar b'angarenshi alamar ta k'ofar baya ya shiga, takawa tayi ta shiga falon na shi, a gaggauce ta sameshi yana cire kaya zai shiga ban d'aki, d'an murmushi tayi tace "Yallab'ai garin ya ya ka manta da aikin jama'a haka?"
Kallonta yayi yace "Kuyi hak'uri dan Allah, wallahi na..."
Sai kuma yayi shiru ya sauke numfashi, ban d'akin ya shige da sauri inda ta rakashi da ido, d'an murmushi tayi dan ita dai wani abu ta hango a tare da shi, juyawa tayi da sauri ta je ta had'o masa abun kari a babban faranti ta dawo, tan a shigowa shi ma ya fito alamar bai yarda ya d'auki lokaci ba, cikin sauri yake goge ruwan jikinshi yana fad'in "Manga kiyi hak'uri ba zan tsaya cin abincin nan ba na sake b'ata lokaci, idan na je can na ci idan na shiga hutu."
Kallonshi tayi jikinta a mace tace "Amma ko ya ya ka ci mana, jiya ma fa baka ci abinci ba."
Girgiza kai yayi yace "Ba zan k'ara b'ata lokaci ba Manga, aikin nan na jama'a ne ba nawa ba, hakk'in mutane dayawa ne a kai na, bana so Allah ya tambayeni ko da da lattin minti d'aya ne."
A ladabce tace "To ko na juye maka shi sai ka tafi da shi?"
Da sauri ya kalleta tarrr a fuska dan Mimi ta tuna masa sanda take magiyar ta dinga aika masa abinci, k'arasa d'aure zariyar wandonshi yayi ya girgiza mata kai, bata k'ara magana ba har ya gama saka kayan ya d'auki jakar na'urarshi ya nufota, sumbatar goshinta yayi yace "Sai na dawo."
A sanyaye ta bishi da kallo dan har ya nufi fita tace "A dawo lafiya." Saida ya bud'e k'ofa zai fita yace "Allah yasa."
Yana fita bai ga ko d'aya daga cikin yaran ba alamar duk sun taafi makaranta su ma, da sauri ya shiga motar da jami'in ya bud'e mishi k'ofa suka tayar da jiniya suka d'auki hanya.
*08:30 na dare*
Tun yamma da malam ya dawo yace mata mijinta zai zo anjima ta shirya dan tare zasu koma ta fara fad'awa Iya "Ni wallahi kai na ma ke ciwo."
Iya kam da bata san manufarta ba sai ta d'auki jibda ta bata tace ta shafa dan ta santa ba magani take so ba, ana magriba ta sake kallon Iya tace "Iya kai na fa bai daina ba, kuma ma amai nake ji yana taso min."
Kallonta Iya tayi ta rufe baki sai kuma ta kawar da kai, murmushi ta saki tana girgiza kai tace "To Allah ya sawake ya raba lafiya, bari a yi sallah sai na baki garin hatsin nan kisha aman zai kwanta."
Zuwa 08:30 ta rikita Iya da tsarabe tsaraben kaza ke mata ciwo kaza ta jin na mata ciwo, Abba ne suka shigo tare da malam dake kallon Iya yana fad'in "Mik'o mana tabarma ga mai gidan na ta nan su zo."
Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "Sannunku da zuwa, bari na d'auko."
Tabarma ta d'auko ta shinfid'a musu a kusa da d'akin malam d'in tana kallon malam tace "Amaryar ta ka ma fa bata da lafiya."
A tare suka kalleta da Abba suka ce "Bata da lafiya kuma?"
Kallonsu tayi ita ma tace "E wallahi, tunda yamma daka fita tace kanta na ciwo, yanzu haka dai amai ne tace ya fi damunta da tashin zuciya."
_🤣 Uwata sha'ani_
A rikice malam ya nufi d'akin yana fad'in "Subahanllah! Amma kuma baki aika a fad'a min ba, ina bakin masallaci ai da ba an kaita asibiti ba."
Wani galala Abba ya kallesu dan shi yanzu lamarin Mimi ya daina bashi al'ajabi ma, tab'e baki yayi yace "Malam karku wahalar da kanku, iskanci ne wallahi yarinyar nan zata mana."
Shigewa malam yayi bai ce komai ba sai Abba daya fita dan shigo da su sheikh, jim kad'an suka shigo suna ta gaisawa da Iya a mutumce shi da Alhaji Ibrahim, zaune sukayi inda Iya ke sake fad'a musu "Ai ja'irar ma tana ciki duk ta rikice ba lafiya."
Da wani sauri ya kalli Iya yana d'an jimk'e hannunshi akan gwiwarshi sai kuma ya kalli k'asa ya huro iska bai ce komai ba dan baya so yayi magana ya kwafsa a fahimci rauninshi akan yarinyar, Alhaji Ibrahim ne yace "Assha kuwa, an tafi asibiti kuwa?"
Fitowar malam yasa Iya bata bashi amsa ba dan yana fad'in "Jikin na ta dai babu zafi, aman ne kawai tace yake damunta da ciwon kai, sai k'afafunta da tace suna tauna mata."
Wani kallo Abba ya masa sai yaga ai fa yarinyar nan ma ta rainasu wallahi, to me take nufi? Sheikh kuma sake sunkuyar da kai yayi bakinshi na son furta "Ku min izini na shiga na ganta dan Allah."
Amma kunya da kawaici yasa shi had'ewa ya shanye, Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh d'in yace "To me zai hana ka kaita asibiti?"
Iya ce tayi saurin cewa "Wacece? Mimin? Tabb'!"
Malam ne yace "Ai bata san zuwa asibiti saboda magani da allura."
Abba ne ya gyara zamanshi kan tabarmar yace "Allah gafarta malam bari na fito maka da ita ku wuce gida, ba wani ciwo dake damunta iskanci ne."
Mik'ewa yayi zai shiga d'akin malam yace "A'a fa Adamu, kiyaye ni wallahi akan amaryata."
Sunkuyar da kai Abba yayi yace "Kuyi hak'uri malam dan Allah ku barni da yarinyar nan."
A tausashe kuma a sanyaye sheikh yace "Ku barta."
Shiru sukayi suka zuba masa ido shi kuma yana kallon k'asa, d'orawa yayi da "Ina me baku hak'uri dan Allah da gaba d'aya zuciyata, abinda ya faru sabo ne a gari hakan yasa na rasa hanyar da zan dakatar da abun, amma insha'Allah na tsawatar ta yanda bana tunanin hakan zai sake faruwa nan gaba, kuyi hak'uri dan Allah ita ma ku bata hak'uri, nasan an shiga hakk'inta dayawa amma muna neman afuwarta ni da iyalina."
Cike da girmamawa da ganin dattakonshi Malam ya zauna yace "Ba komai sheikh, komai ya wuce ai insha'Allah, Allah ya yafe mana baki d'aya ya kuma baku zaman lafiya."
Da "Ameen." Duk suka amsa kafin Iya tace "To ya za'ayi da ita yanzu? Zaku tafi tare ne?"
Sheikh ne yace "Tunda bata jin dad'i kawai ku barta, amma dai ya dace a tafi asibiti."
Da murmushi Iya tace "Insha'Allahu zamu k'ok'arta mu gani, indai bata yarda ba ka sani ni zaneta zanyi sannan ta bar min gida."
Murmushi yayi ba tare da sanin bakinshi ya furta ba yace "Kiyi hak'uri Iya karki tab'a ma..."
Sai kuma yayi shiru sanda sukayi ido hud'u da Abba, mik'ewa malam yayi da Abba tare da Alhaji Ibrahim, a sanyaye sheikh ya mik'e sai malam daya kalli Iya yace "Ki mata magana ta fito ko gaisawa suyi."
Iya ce ta mik'e tace "Ko kuma dai ya wuce ba, ciwo ne fa ya zo ga uwayen mita da raki, ko ruwa bata tashi zaune tasha."
Dariya sukayi inda Iya ta gyaraw sheikh tace "Wuce ciki."
Jim yayi a tsaye yana sussunkuyar da kai sai kuma ya shiga takawa babu takalmi a k'afarshi ya nufi d'akin, yana d'aga labulen da sallama Mimi ta sauko daga kan gadon da sauri ta shige k'ark'ashin gadon da babu komai a k'asa sai buhuna.
Baki ya saki yana kallon sarautar Allah matarshi a k'ark'ashin gado, takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsugono irin na maza yana lek'awa k'asa yace "...
_Masha'Allah, hak'ik'a aka ce yaba kyauta tukuici, bamu rok'a ba, bamu shawarci wani ba, haka kawai kuka ga cancanta ta isa ta sa kuyi mana kyautar kud'inku, lallai kun cika mutanen kirki masu daraja a garemu da karamci, kayi a yaba ma kad'ai babban arzik'i ne, sai gashi a wasu grps d'in har da ware mu mu biyu kawai ni da kuma k'awata aminiyata *Sajida* kuka ce zaku mana kyauta saboda k'ok'arin da muke, tabbas zan iya kiran labarin *matar mutum* da gawurtaccen labarina kuma bakandamiyata, dan Allah ya k'ara d'aukaka ni ta dalilinshi, Allah nagode maka ina k'ara godiya a gareka, ba dubarata bace ba kuma wayona bace._
Yan *Nigeria* da kuka kawo wannan shawara ta yi mana kyauta, da kuma yan *Niger* da kuka goya musu baya Allah ubangiji ya saka muku da alkairi, duk da mun dakatar daku mun ce ku bari muyi littafi na kud'i ku siya, amma gaba da gaba kuka nuna mana kunyi niyya kuma ba zaku fasa ba, Allah ya saka muku da alkairinsa, Allah ya biyaku da aljanna ya yafe mana kurakurenmu.
*Sajida* & *Samira*
_(Kwate da Kwate)_�
*Allamdulillah*
7/28/21, 1:54 PM - Ummi Tandama😇: 👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩����👨👩�����
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
💫� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_�
� *[ T.M.N.A]* � 📖🖊�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*52*
Takawa ya shiga yi a sanyaye saida ya tsaya kusa da gadon yayi tsuguno irin na maza yana lek'awa k'asa yace "Ryam."
Yanda ya kira sunan na ta a tausashe yasa ta yin shiru