Showing 33001 words to 34154 words out of 34154 words
Chapter 12 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt
sosai akan rayuwar da yayi a baya.
Jikin Ahmad duk yayi sanyi kwarai, sai hakuri yake bama mahaifin nasa.
Bayan doguwar tattaunawa da akayi, nan aka tsaida maganar, Aysher bazata tare ba saita k'ara samun lafiya.
Gogan naku yayi mirsisi yace"Shidai abashi matar sa yau ta tare, basai ank'ara d'aukar wani lokaci ba, yakara da cewa ko agidan shima zata warke ballantana ma babu abinda yake damun matar sa yanzu, tunda likitoci suka basu sallama."
Kunyace sosai tarufe Alh.Aliyu yakasa cewa komai, lura da hakan da Baffa Usman yayi sai yace"Me za'ajira daman Alh? Tunda anganta, ai akaita gidan mijin ta Allah basu zaman lafiya, nima yau zan wuce In sha Allahu."
Kowa yayi na'am da haka, dan haka a ranar Baffa Usman yajuya zuwa yola, aran su Aunty Maryam da su Fatima da K'annen mahaifin Aysher suka kaita gidan mijin ta, tare da yi mata sallama kasan cewar sammako zasuyi dan tafiya gida, dakyar suka rabu da Aysher sai kuka takeyi....Hmmm Aure kenan (Maman Hanan)
*******
Da daddare aka rako ango, Mudansir ne kad'ai yazo hannuwansu shak'e da kaya nik'i-nik'i, dan duk abokan sun juya, tsiya kala-kala ya dinga ma Ahmad kafin yayi musu addu'a tare da fatan samun zuri'a nagari, yatashi zai tafi, Ahmad ne yayi masa rakiya zuwa inda ya faka motar sa, kallonsa Mudansir yayi kafin yace"Ayi dai a hankali Dr. She is a patient"
"Dalla malam yimin shiru wai ina ruwan ka da nine, sa ido sana'ar....."
Dariya sukayi gaba d'ayansu tare da tafawa, Mudansir yaja motar sa yafice daga gidan bayan mai gadi ya wangale masa gate d'in gidan.
Ahmad yana dawowa falon ya k'arasa gurin matar sa ya rungumota, kafin yace"Kisa a ranki, gidan Ahmad babu yaji, ballantana saki, ina sonki matana, bazan yafewa Farida ba ta wahalar min dake, ban boyemiki ba, nasanar dake komai game da rayuwata.
"Matso nabaki abinci kici, kafin muje muyi wanka tare da alwala mu mik'a godiyarmu ga Allah (S.W.A)."
Dakyar Aysher ta yadda taci kazar tare da fresh milk Ahmad ya bata a baki.
Bayan sun gama ya nuna ma Aysher 'Dakin ta dan ya lura kunyar sa takeji sosai, yana fita Aysher tashiga tayi wanka, tare da d'auro Alwala, tafito tashirya cikin doguwar riga mara nauyi ta zira hijabin ta duk tagama feshe jikinta da turare.
Tana gamawa Ahmad yashigo, yace mata"My love kingama?"
Kai ta gyad'a masa, batare da tace masa komai ba.
Bayan yajasu sallah sun idar yayima Aysher tambayoyi dangane da addini, tabashi amsa dai-dai gwargwado.
Dafe kanta yayi yayi mata addu'a suka shafa, daga nan nace Asubah tagari.
🍒🍒🍒🍒🍒
Zaman sukeyi mai tsafta a tsakanin su, sun gama fahimtar juna, kowa yana buk'atar yaga ya farantawa d'an uwan shi rai, suna gudun 6acin ran junan su, (Haka zama yake ko anyi aure indai da so da k'auna za'ayi zaman lafiya, duk da cewa tsakanin harshe da hak'ori ana sa6awa).
Wani kulawa suke nunama junan su, Aysher ta zubda makamanta na kunya, kulawa da tsantsar soyayya take nunama mijinta hankali kwance...
Suna waya dasu Fatima sosai har ma da Mahaifiyar ta.
[11/1, 6:25 PM] Zeetty: 🔚🔚🔚🔚🔚
Anyankema Feedo dasu Ladi Reza hukuncin shekara d'aya a gidan yari, da sharad'in ba ita babusu Aysher da Ahmad.
Hutun su Ahmad ya k'are dan haka sunata shirye-shiryen komawa saudi'a,
Sun kira 'yan yola sunyi musu sallama, ana gobe zasu tafi sukaje gidan Umma sukayi mata sallama, tayi musu Nasiha mai ratsa zuciya tare da jama Ahmad kunne sosai.
Washe gari suka d'aga zuwa saudiyya.
*BAYAN SHEKARA UKU*
Ahmad zama babban mutum magidanci, ya kammala karatun sa, ya samu koyarwa a Baze university dake Abj, dan haka a Abj suke zaune da matar sa Aysher yaranta namiji mai suna Aliyu suna kiranshi da Hydar, Aysher ta k'ara kyau da gogewa.
Mudansir shima ya natsu har ya auri Fatima k'awar Aysher, tana d'auke da k'aramin ciki.
Baffa Usman yadawo da mahaifiyar Aysher Halima, harta haifi Namiji shima sunan shi Sulaiman, kuma tana aikin ta a wani asibiti dake garin Yola.
Yadikko ta zubar da makamanta gaba d'aya ta rungumi k'addarar cigaba da zama da kishiya a karo na biyu, dan tanacin arzikin Aysher ita da 'ya'yanta.
Zumunci sosai akeyi da Nura da su Ahmad, abakinsa suka samu labarin rasuwar Honourable Mahmoud a hanyar sa ta dawowa Abj daga yola tun lokacin auren sa da Aysher.
🍒🍒🍒
Aysher suna zaune da d'anta Hydar da Ahmad a falo, Aysher ta kalli d'anta Hydar d'an shekara Uku da watanni tace masa" Hydar yasunan yaran Manzon Allah S.A.W?"
Zaman sa ya gyara akan cinyar Abban sa kafin yace"Momy guda bakwai ne ga sunan su kamar haka;-
*ALKHASEEM*
*ABDULLAHI*
*IBRAHIM*
*FA'DIMA*
*RUKAYYA*
*ZAINAB*
*UMMU KHULSUM*
Kabbara sukayi masa, kafin Aysher ta sake tambayarsa Addu'ar da mutum zaiyi idan yana cikin fushi, Hydar yace " *A'UZUBILLAHI MINASH SHAI 'DANIRRAJIM*
Addu'ar yayin fara alwala,
*BISMILLAH*
Addu'a yayi kammala alwala,
*ASH-HADU ANLA ILA HA ILLALLAH*
*WAHADAHU LA SHARI QALA*
*WA'ASH HADU ANNA MUHAMMADUN WA RASULAHU*
Addu'ar fita daga gida,
*BISMILLAH, TAWAKKALTU ALAL LAH, WALA HAULA-WALA QUWATA ILLA BILLAH*
"Allahu akbar my son lallai siyan sabon keke ya kamani" cewar Ahmad, kafin yakalli Aysher yace"Gaisheki uwa tagari, Allah baki ikon cigaba da bama yarana tarbiya nagari"
Ameen Aysher ta bashi amsa
Suna zaune a falo suna kallo, Hydar yayi bacci, Ahmad yana zaune Aysher tana kwance akan cinyarshi ya kalleta yayi murmushi kafin yace"My love lallai nazamo mai sa'a da samunki a matsayi mata danayi, dan kuwa a baya zamowa nayi mai HANGEN DALA, ina ta yaudarar 'yan mata, wanda hakan yasani kasa fahimtar cewa ashe komai DAGA ALLAH NE, namik'a HANYAR LIBIYA sai da Allah ya had'ani dake kika dawo dani dai-dai, da taimakonki na chanja DABI'A ta, hakika rashin ki zai sani ZUBAR HAWAYE....Dan Allah karki gujeni.
Murmushi Aysher tayi, ta k'ara gyara kwanciyarta akan cinyar mijin ta, kafi tace"Baban Hydar am urs, i will be urs forever, fatana Allah ya k'ara maka budi, ya tsaremin kai daga fad'awa tarkon 'yan matan jami'ar BAZE.
Ameen mata na.
Tammat.
_DARASIN DAKE CIKIN WANNAN LABARIN SHINE_
GAREKU SAMARI MASU YAUDARAN 'YAN MATA, DAN ALLAH KUDAINA KUNGA YADDA AHMAD DAI YA K'ARE DA AMARYAN SA, WATO HUKUNCIN DA FEEDO TA 'DAUKA A KAN MATAR SA, SHARRI 'DAN AIKE NE IDAN KAYI DUK DAREN DADEWA ZAI DAWO KANKA, KO WANI NAKA.
SANNAN WAK'A BAWAI WANI ABU BANE YAKE SAKASHI, KO ACE RASHIN KUDI, AKWAI MASU RA'AYIN HAKAN NE KAWAI, MUSAMMAN A WANNAN ZAMANI.
MASU SOYAYYAR SHAN MINTI DAN ALLAH KUDAINA DAN KUWA BABU KYAU ABIN DA KAYIMA 'DAN WANI, DOLE SAI ANYIMA NAKA.
_DA BAZARKU NAKE RAWA_
*ZAUREN LITATTAFAN HAUSA GROUP*
*DUNIYAR MARUBUTA GROUP*
*INDABAWA HAUSA NOVELS GROUP*
*MACE MUTUM WRITER'S*
_BAZAN MANTA DA KUBA 'YAN QUNGIYAR ZAMANI WRITER'S_(ZWA)
*Nasmat ('yar mutanen Arkillah)*
*Queen Hauwa Hausy*
*Beauty Queen*
*Queen 'yar mama*
*Action baby*
*king boy*
*Shaxee*
*Maman Haneef*
*Roukie baby*
*Maman Nurr*
*Hafsat*
*Layuza*
*Ama Alh.Kabir*
*Biehoh*
*Kamala Minna*
Da duk wanda ban lissafoba ayimin uzuri.
_Ina sonku kamar yadda kuke sona Fan's_
Maman fatima
Maman Afnan
Ahmad serious
Maman ashraf
Moonat
Maryam yahaya (with ur group member)
I love u all.
Maman Hanan takuce gyara ko k'orafi is Allowed.....ana mugun tare
Sai mun Hadu a cigaban Labarin HANYAR LIBIYA PART 2.
MAMAN HANAN