Showing 15001 words to 18000 words out of 34154 words
Chapter 6 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt
Abba Inason Aysher Abba kataimaka kajemin neman aurenta kafin nadawo karsu bada ita dan Allah Abba mudansir zaiyi excorting dinka gidansu dan Allah Abba I love her very much wallahi idan na rasata bazan iya auren wata ba Abba"
Ahmad yakarasa fada yana ZUBAR HAWAYE
_Hakika Alh.Aliyu yatausayama dan nasa abinda zaisaka Ahmad kuka ba karamin abu bane dan Ahmad jarumine na gaske dawuya kagane yana cikin damuwa but akan Soyayyar Aysher yadawo mace mai rauni dole zanje nagana da Mahaifin yarinyar nan tabbas Ahmad yafara shiryuwa may be ma harda taimakon Aysher dan haka zanje na nemo masa aurenta_
Alh.Aliyu yayi murmushi for the first time tun tasowarsu daga Nigeria yakalli dan nasa yace"Ahmad zanje maka neman auren Aysher In Allah yaso amman sai naga yanayinka kafin ayi auren ina nufin sai bayan shekara daya"
Kai Ahmad ya girgiza tare da cewa nayadda Abba Nagode Allah saka da Alheri zan baka mamaki Abba.
Sallama Alh.Aliyu yayi da Fallata yakarasa gurin mai taxi daya dauko drop dan aranar zai koma cikin mecca dan jirginsu zuwa Nigeria zai tashi da asuba ne.
Ya bude bayan motar zaishiga dasauri Ahmad yakarasa gurin Mahaifin nasa ya tsugunna tare da ajiye kafafunsa a kasa kamo hanun mahaifin nasa yayi yana Mai ZUBAR HAWAYE tare da fadin"Abban kayafeni dan Allah duk laifin danayi maka a baya da bacin ran dana saka ka a ciki kayafemin In sha Allahu saina zamo abin fahari a gareka zan baka mamaki zan zamo fiye da yadda kakeso nadawo Abbana I will missed you kacema Umma tayafemin zankirata na roki gafararta Nasan nasaku bakin ciki amman In Allah yaso daga yau yazama tarihi Abbana.
Alh.Aliyu shima ZUBAR HAWAYEN YAKE cikin ransa kuwa fadi yake *dole ne zaisa nabarka Ahmad inasonka fiye da sauran yarana dole ne zaisa nadauki tsawon shekara batare da nasaka a idona ba*
A fili kuwa cewa yayi"Na yafe maka Ahmad ubangiji ya yafe mana kuskurenmu zan turo maka da kudi idan kana bukata amman na bama fallata wasu kudaden masu dama I love u too my son Allah maka Albarka"
Ahmad cikin jin dadi yadinga cewa Amin Amin Abba inada kudi sosai a account dina ma nagode Dad Allah yasaka maka da Aljanna.
Cikin dariya Alh.Aliyu yace wow naji dadi Ahmad lallai kafara hankali kaine zakace bakason kudi kacemin nabarshi Alhamdulillahi Ahmad lallai kafara nutsuwa Allah maka Albarka Allah kara shiryamin kai.
Dakyar shima Alh.Aliyu yatafi yabar 'Dan nasa suna dagama juna hannu.
Fallata dakin da Ahmad zai zauna ya nuna masa daki dayane da toilet a ciki da katifa a kasa.
Addua Ahmad yayi Allah yasa hakane mafi Alheri a gareshi Amman baisan yazaiyi da rayuwa cikin larabawa da basajin hausa ba sai larabci kadan daga cikinsu ne suka iya turanci....
Wannan kenan
MAMAN HANAN
[10/18, 3:40 PM] Zeetty: [10/18, 3:40 PM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 29-30
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
*Maman hanan lafiya kuwa yau naga typing din naki ba page kuma da alamar kamar badaga inda yakamata kifara ba kenan*
_Nagode da kirana dakukayi kuka ankarar dani kuskurena hakika maman hanan tana jin dadin yadda kukebin wannan novel din nata nagode ayimin hakuri mistake nayi gurin posting zantafi dauko Hanan daga school ina saurine_
Artabu akayi sosai tsakanin yansandan dake gadin gidan Nura tare da wasu mutane guda biyu wanda suka boye fuskokinsu.
Saida sukaga dagaske idan basu gudu ba police din zasu iya kamasu kamin subar gidan dagudu dan kar asirinsu ya tonu.
Bayan komai yalafa a daren yansanda sunyi-sunyi da Nura yafadi wanda yake zargi da aikata masa haka Nura yace bakowa shidai kawai jikinsa ne yabashi wani al'amari zaifaru shisa yace suzo.
Bayanda basuyi da nura ba yafada musu gaskiya amman yaki.
Dan haka suka rabu dashi.
Da asubahin ranar yadauki iyalansa suka kama hanyar zuwa zaria cikin ransa yanata tunanin yadda zaiyi yataimakawa Aysher koda zai iya rasa rayuwarsa tabbas yanzu yatabbatar Hon.Mahmoud bashi da imani kuma zai iya aikata komai saboda Yasamin Aysher.
Ina zanga wannan saurayin nata ko mahaifinta kai dole zuwa yola yakamani.
Tunanin da nura yaketayi kenan har suka karasa anguwar tudun wadan zaria gidan surukansa
Kaiwa yakeyi yana komowa Hon.Mahmoud kenan a kasaitacciyar falonsa yakalli yaran nasa tare da fadin kukace kunje gidan a kulle ko?
Oko ya gyada kansa yakara da cewa eh mai gida harta katanga munhaura amman da alamar babu wani abu mai motsi a gidan.
Gyada kansa yayi cikin gamsuwa kafin yace kutashi kutafi kusa ido akansa sosai duk inda kukagansa kudaukomin shi.
Angama maigida suka fada gaba dayansu.
Kuje nasallameku.
Mikewa sukayi suka fice daga falon.
Nura dani kake magana zansa duk inda kake a bincikominka bazan halaka kaba kodan sanadiyar dakayimin na haduwa da Aysher amma zansa a kullemin kai harsai bayan bikinmu da Aysher kafin a sakoka lokacin munriga munzama daya nida ita badaman rabuwa.
Hon.Mahmaud yafada dakarfi tare da wani irin dariya mai sauti dayayi.
*********
Zaune take a dakin Fatima dan yau gidansu fatima tazo hira.
Aysher takalli fatima tace"kawata nifa duk abinda wannan mutumin ya aiko dashi bana amfani dashi kuma wayar daya aikomin ma na ajiyeta dan ko kallonta banason nayi.
Awayar yadikko yake kirana nan ma harya gama sambatunsa bana cemasa komai"
Fatima tace yauwa haka zakiyi tamasa harya gaji ya hakura maye kawai ni wallahi nafisonki da Ahmad dinnan kunyi matching sosai har kamanni kukeyi dashi.
Cikin bacin rai Aysher tace"Ahmad yau kwana 8 banji daga gareshi ba ina tunanin koma yaudarata yazo yayine"
Kul karki sake fadin haka Ahmad na Allah ne masoyinki ne nagaskiya bazai taba yaudaranki ba kawata kiyimasa uzuri.........
Tsalle Aysher tadaka tare da ihu mara sauti can kuma saita tsaya data tuno wayar dake manne a kugunta wanda fatima tasa matashi a vibrating ne yake vibrate a jikinta dasauri taciro wayar daga jikinta tafara nunawa fatima number da ake kiranta dashi fatima tace Number kasar waje ne Aysher yisauri kidauka karya katse.
Kafin Aysher tadauka kiran yakatse
Aka kara bugowa tadauka cikin sanyin muryansa taji yace"Amincin Allah yatabbata a gareki masoyiyata ma'abociyar nutsuwa da kamala"
Wani murmushi tayi ta dagama Aysher gira kafin tabashi amsa da cewa"Nayi farinciki dajin wannan zazzakar murya taka ya sahibi na amman ina fushin rashin jinka dabanyi ba tsawon kwana takwas.
"kiyi hakuri my love hakan yafarune saboda wasu abubuwan dana tsayayi kece mutum nafarko dana fara kira yanzu na sayi layin dan awayar kasuwa naketa waya da yan Nigeria kwanaki takwas dinnan da banjiki ba jinsa nakeyi kamar shekaru takwas kiyi hakuri natsaya yimana shirin gina rayuwa makyau ni dake da yaran da zamu haifa bari zankiraki da daddare kiyi hakuri ina saudiyya hakan yafaru sakamakon wani laifi danayi Mudansir zaizo yadubaki zaisanar miki da komai dafatan bazaki gujeni ba idankinji ko wanene ni a baya ina sonki Aysher sonki mai zafi ina miki son da bantaba yima wata mace ba a rayuwata,
Cikin sanyin hali Aysher tace" Inasonka dayawa Ahmad ubangiji ya tsaremin kai karikemin amana banda wani miji saikai ina sonka aduk yadda kake muddin kayi tuba dan Allah"
Ajiyar zuciya Ahmad yayi kafin yace Nagode ki kulamin da kanki dan Allah zankiraki da daddare mudansir zaizo mexai kawo miki?.....
Bakomai karka damu saika kiradin bana bukatar komai kahuta.
Ahmad yace'Bye i love u"
I love u too Ayshee tabashi amsa.
Wani ihu fatima tasake kafin tace Aysher Ahmad yamayar min dake mara kunya lallai najinjina masa.
Dariya sukayi gaba dayansu.
[10/18, 3:40 PM] Zeetty: [10/18, 11:12 AM] Zeetty: πππππ
πππππ
Mudansir a daren ranar yazo yakira Aysher tafito tagaisheshi ya amsa cikin fara'a yanata tsokananta tare da tambayarta kawarta fatima tace tana gida.
Mudansir Yace"Abokina yaturoni gurinki domin baiyana miki abinda yafaru dashi abaya hakika abokina yakasance maitaurinkai zaciya gefe guda yanada hakuri da saurin yafe abu.
Abaya Ahmad bayajin magana irin wanda dai kikasan samarin yanzu matasa harma da kadan daga cikin masu aure suna aikatawa amman yanzu cikin ikon Allah yashiryu.
Allah ya taimaka yakintsu dalilin haduwa dake Aysher....
Dasauri Aysher tadago kai takalli mudansir
Yace"kwarai kuwa Aysher Allah yakawoki rayuwar Ahmad domin kizamo tsanin shiryuwansa domin tunda yahadu dake Lokaci daya ya tsunduma cikin kogin kaunarki.
Ya lura dake keba irin wadancan yan matan dayake mu'amala dasu bane dan haka yadinga rage wasu abubuwan ahankali lokacin daya tabbatar sonki yake da gaske saiya hakura da wancan abubuwan dayake aikatawa saboda yasamu amincewarki.
Aysher bana fatan Abokina yarasaki arayuwarsa domin kasancewar hakan yana nufin abubuwa dayawa game da rayuwarsa wanda bana fatan hakan takasance dan Allah karki guje masa natabbata bazaki taba samun masoyinki na gaskiya kamarsa ba.
Dalilin tafiya dashi saudiya kuwa shine wakar dayayi ta Hiphop zakiji ana fadin wakar *A.A HAMEED* ko?
Aysher tace"Eh inajin wakar sosai a radio dakuma gari"
Mudansir yace toh Ahmad dinkine ya rerata abinda ake nufi da A.A Hameed kuwa shine Ahmad Aliyu Hameed shine cikakken sunansa.
Ido Aysher tazaro sosai.
Mudansir baikulataba yaci gaba da cewa"Wannan wakar tunkafin Ahmad yayita nahanashi rerata yakiji batare da saninaba yaje yayita Ahmad yayi wakar nanne kawai dan ra'ayin kansa dankuwa mahaifinsa ya tara kudin da har bayan ransa bazasuyi talauci ba kawai sha'awa abin yabashi Ahmad yanada degree a bangaren hada magunguna (Medicine) wanda yayi a Ghana.
Masters akaturoshi garin nan amman ya buge da hakan dan a guji turashi wata kasar ne saboda gudun haka
Amman yanzu ina mai tabbatar miki Ahmad ya natsu bazan ce komaiba saboda yahanani fada amman Lokaci zai tabbatar da hakan wato nan da wata takwas din da zaidawo saboda haka kicigaba da masa addua mahaifinsane yaturashi kasar saudiyya awani kauye mai suna asir gurin abokinsa akan yaxauna acan amatsayin horo gareshi.
Cikin alamun gamsuwa Aysher tace nagode Mudansir inason Ahmad koda ace abinda ya aikata yafi haka muni tunda ya tuba inasonshi..
Idan kunyi waya kace masa soyayyarsa tananan daram cikin zuciyata babu abinda yaragu bagudu babu ja da baya.
Kace masa ina nan inajiransa har sanda zaidawo.
Inayimasa fatan alheri Allah ya datar dashi.
Cikin murmushi mudansir yadinga amsawa da amin Aysher amin nayima abokina murna gashi wannan yace nasiyo nataho miki dashi.
Aysher tace"Kai yaya mudansir saida yasaka dawai niyya Alhalin baya kasar nikam nayafe"
Bakisan Ahmad bane zaimiki abinda yafi haka wannan bakomai bane indai yanadashi bakudina bane kudinsa yaturomin nadinga kulamasa da iyalinsa a cewarsa baki da wanda zaimiki saishi kofa abude take idan kinada bukatar wani abu kisanar masa zanzo nakawomiki kanwata bazan gajiba"
Godiya sosai Aysher tayi masa bayan takarbi ledojin hanun mudansir sukayi sallama tashige gida shikuma yashige mota yatafi.
MAMAN HANAN
[10/19, 9:07 AM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 31-32
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
*BAYAN WATA 3*
Abubuwa dayawa sun faru abangarori da dama.
Bangaren Aysher Alh.Mahmoud zuwansa yola biyu kuma duk zuwan dayakeyi basu taba haduwa da Baffa Usman ba wato mahaifin Aysher.
Duk zuwan dayakeyi baitaba samun hadin kan Aysher ba saima bakaken maganganu dayake samu daga gurinta,
Gefe guda soyayyarsu Da Ahmad tana kara bunkasa suna manne da junansu a waya koda yaushe kuma haryau yadikko batasan da wayar ba.
Mudansir yana yawan zuwa idan yana gari dan idan yasamu hutu kano yake komawa kuma duk zuwan dazaiyi saiya taho mata da sako inji Ahmad kamaru turere body spray da roll on dasauran kayan kwalliya dai akwai lokacin daya kawoma Aysher wasu dogayen riguna saudi fashions da zobuna na gold guda biyu da sarka da dankunne yace Ahmad ne yaturo mata daga saudiya.
Awannan lokacin dakyar Aysher ta karba tana mamakin yadda Ahmad yasamu kudi masu yawa haka shida akace yatafi kauye kiwo da noma.
Mudansir ne yakwantar mata da hankali cewar Ahmad idan yayi kiwon nan kudi ake biyansa shine yatara yasiyo mata wadan nan kayan.
Itadai bata gamsu da hakan ba ammamdai tabishine kawai a haka.
Nura baisamu zuwa yola amman yabar Abj yakamawa matarsa gida a zaria cikin dare sukaje suka kwashe kayan nan ma saida akayi artabu tsakanin yan ta'adda da yan sandan da Nura yatafi dasu.
Nanma Nura kin fadawa yansandan wani abu yayi dan koba komai Hon.Mahmoud babban mutum ne bazai yiwu ya tozarta shiba amma zaibidashi tabayan gida inyasan wata ai baisan wata ba bazai taba bari duniya tasan matsakar dake tare da Hon.mahmoud ba amman bazai yadda ya cutar da yarinyaba wadanda ya cutar abayama sun isa.
Za6e yafara gabatowa dan haka Hon.Mahmoud yayima yadikko magana a waya cewar yanaso yaturo magabatansa suzo su samu mahaifin Aysher.
Yadikko tace"Alh. Kafara zuwa tukunna kugaisa da mahaifinta kafin manya suzo yanzu hakama yazo daga lagos yana gida"..
Toh inanan zuwa gobe ko jibi.
Shikenan saikazo ranka dade
Kwanaki biyu tsakani Hon.Mahmoud yadira a garin yola.
Bayan sunhadu da mahaifin Aysher Baffa Usman sungaisa Hon.Mahmoud yagabatar masa da kansa a matsayin mai neman auren Aysher tare da cewa sundade tare dan yakwashe watanni biyar yana zuwa.
Cike da mamaki Mahaifin Aysher yakira Aysher tazo tambayarta yafarayi ko tasan da zuwa Hon.Mahmoud
Kai Aysher ta girgiza kafin tace"Baffa bansani ba asalima nadakatar dashi dan banasonshi"
Kaji abinda tace Malam Mamuda.
Cikin kame -kame Hon.Mahmoud yace tasani mana dan har mahaifiyarta tasan da maganar.
_Sai yanzu Baffa Usman yagane karatun wato dai shine mijin da yadikko tace tayiwa Aysher aikuwa bazai yiwu ba dan bai amince da mutumin ba_
Dan haka baffa yace"Toh kayi hakuri kaji abinda yarinya tace dan tunkwanaki danazo yarinyar nan tacemin bata amince dakai ba kuma na fadawa mahaifiyarta bata sanar maka bane kawai kayi hakuri dan Allah.
Allah yazaba maka abinda yafe Alheri.
Kan Hon. Mahmoud a sunkuye yakasa amsawa har baffa yatashi dan yin alwala zaije masallaci.
Aysher tamike zata shige gida Hon.mahmoud yace "Kituromin maman taki muyi sallama"
Dan Allah mama kitaimaka yanzu tsawon wata biyar ina hanya tsakanin Abj da yola dan tsananin soyayyar Aysher na fahimci halinta inasonta da yawa kibama Baba Hakuri Aysher yarinyace haryanzu batasan menene so ba nasan zata soni bayan munyi aure ni mama konawane zan kashe idan zansamu Aysher.
Barwannan maganar Alhaji ai mahaifinta kudi bazai siyeshiba yanada taurinkai kabari kawai zan nemo Yarbingel tarakani gurin wani malami dan ayi masa addua ya amince matsalar kawai kudi malamin yake yankowa dayawa....
Cikin rawan jiki Hon.Mahmoud ya karkace yadauko bandir na yan dubu-dubu yabama yadikko dubu dari biyu yakara da cewa ki kirani a waya idan ana bukatar kari dan Allah yayi aiki mai zafi sonake ayi auren nan da wata biyu lokacin zabe yarage wata daya kenan.
Bayan sunyi sallama yadikko dasauri takoma daki tafara boye kudin kafin takira Yar bingel awaya cewar tazo gobe dan rakata gurin boka Hargitsa'u.......
*Masu karatu yanzu za'afara labarin ku kasance dani*
MAMAN HANAN
[10/19, 9:11 AM] Zeetty: [10/18, 10:00 PM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 33-34
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
*Godiya gadukkan yan group din Hausa novels only group*
*Inajin dadin yadda kukebin wannan labarin nawa dama wanda nayi a baya I love u All*π―
Washe gari su yadikko sukaje gurin boko hargitsa'u gaisheshi suka farayi dayi masa kirari.
Ya amsa da cewar sannunku da zuwa tsinannu la'anannun Allah tsinuwar Allah yatabbata a gareku nasan abinda yake tafe daku amman ina bukatar nasakeji daga bakinku.
Cikin rawar jiki Yadikko tayi masa bayanin komai sunaso a cusa son Alh.Mahmoud a zuciyar Aysher shikuma mahaifinta shima asaka mashi son Mahmoud acikin ransa ya amince da aurensu.
Abu maisauki kenan inji Boka hagitsa'u yafada a baiyane.
Nan ya harhada musu abubuwa yabasu tare da cewa nan da kwanaki uku zasu ga abinda zaibiyo baya.
***********
Ahmad suna manne da Aysher tawaya yana baiyana mata yadda sonta yaketa karuwa cikin ransa itama tana fada masa yadda takeji game dashi.
Yace"Ni babban farin cikina shine saura wata uku nazo naganki awannan lokacin kuwa natabbata Abba bazaiki zuwa neman min aurenkiba saidai jikina yana bani labarin akwai wani babban Al'amari dazai faru bansan ko daga wani bangare bane amman ina addu'ar Allah yasa koma meye yazomana dasauki,
Kuma Allah yasa bake abin zaishafa ba ko auren mu dan Aysher ina miki son da bakina bazai iya furtawa ba zantayi miki addua Allah yakareminke zandinga miki dawafi duk ranar juma'a namiki Alkawari matata"
Aysher tace"Nagode sahibi na in sha Allah ba abinda zaifaru Ni takace bata kowa ba"
Inajin dadin yadda kike karamin karfin gwiwa akan aurenmu nagode.
Hira sukaci gaba dayi cikin so da kaunar junansu.
Cikin kwana 3 komai yakasance wato Baffa Usman dakansa yacema Yadikko taturo masa wannan mutumin dayazo neman auren Aysher yanason ganinsa.
Wohoho kazo kaga murna gurin yadikko dan haka aranar takira Hon. Mahmoud tasanar masa a washegarin ranar yabiyo jirgi zuwa yola.
Zuwan safe yayi shikansa ganin irin tarban daya samu gurin surukin nasa yasan da banbanci da wancan lokacin da suka hadu bayan gaishe-gaishe baffa Usman yace"Kayi hakuri bisa abinda yafaru a baya nazauna nayi nazari kaine kafi dacewa da Aysher tunda bata dawani tsayayye kuma nima aurar da ita nakeso nayi dan haka ina neman Alfarman ko bayan aurenku kabarta tazana jarabawan kammala sakandire.
Cikin jindadi Hon.Mahmoud yace"In sha Allahu Baba nagode!Nagode"
Baffa yamike tare da fadin barin turo maka Aysher.
Aysher tana dakinta ta tattara kayan da Ahmad ya aiko mata dasu harda zobunanta da sarkan zatakai gidansu fatima aboye mata _Dan yawanci kayan da mudansir yake kawo mata gidansu fatima take kaiwa a boye mata tadauki abu guda daya ko biyu dan idan yadikko tagani kwacewa zatayi ta aikama yarta_
_Duk kayan da Hon.mahmoud yake aiko mata dashi bataso yadikko ne take karbewa amman bazata iya nuna mata na Ahmad ba dan tana sonshi_
Tana cikin tura kayan a babban leda taji muryan mahaifinta yana kwala mata kira.
Dasauri tafito dan tana gudun karya leko dakin yaga kayan.
Kije kinada bako awaje yana gama fadin haka yayi wucewarsa yabarta a tsaye.
Komawa daki tayi tadauki hijab tasaka tafita.
Hon.Mahmoud tagani jingine jikin taxi din daya taho dashi daga airport haka kawai taji bazata iya masa rashin da'a ba dan haka tafara gaidashi ya amsa yana washe baki dan tunda yake zuwa shi kadai baitaba ganin ranar da Aysher ta gaisheshi ba sai yau.
Surutu yayita mata itadai bata bashi amsa yayi mata maganar turo manya nanmadai shiru Aysher tayi masa amman takasa bude bakinta tace masa batasonshi.
Ahaka suka gama Hiran sukayi sallama.
Shidai Hankalin Hon.Mahmoud rabi yakwanta rabi kuma yana tunanin inda zaisa a nemo masa Nura yakamashi yaboye bayaso yatona masa asiri dan yadda yake ganin yafara shawo kan Aysher da mahaifinta bazaiso wani abu yazo yagifta tsakani wanda har zaizamo cikan ga lamari aurensu ba.
Kafin Baffa Usman yakoma lagos saida Hon.Mahmoud yaturo magabatansa aka tsayar da maganar aure wata biyu masu zuwa amman amarya bazata tare ba sai bayan tazana jarabawarta ta kammala sakandire da wannan yarjejeniyar aka rabu.
Zuciyar Yadikko fari tasss saboda bakaramin