Showing 6001 words to 9000 words out of 34154 words
Chapter 3 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt
yana gudun kar yafadawa mahaifinsa dan fuskanci tsananin bacin rai daga gurinsa
Wata kilama dai yahanasa karatun gaba daya.
Abangare guda kuwa yayi-yayi yasamu kebewa da Aysher yarasa hanyar hakan gashi bashi da wani abokin shawara mudansir yafita harkansa kwata-kwata.
Gashi Inna wuro tadauki hutu a gurin aikinta dan haka tasama Aysher ido taki yarda Ahmad yasamu ke6ewa da ita dan bata yadda da take-takensa ba.
Dayaga alamun hakan sai shima yafita harkan Aysher ammanfa a gaban Innawuro
Dan a zuciyarsa bazai ta6a iya cire sha'awarta dayake ba.
Ahankali yasamo mafita wata ranar laraba suntaso daga makaranta kwatsam yataresu ahanyar makarantar Aysher wanda ta zage cikin kawayenta tana hira cikin harshen hausa ita yadinga bi dakallo tare da mamakin karyan data zubo masa cewar batajin hausa.
Dasauri ya isa gurinsu tare dayimusu sallama Aysher ce taganeshi dan haka ta6ata rai.
Daya daga cikin abokan tafiyarta azima ce tayi tsagal tare da cewa"wa'alaikassalam gidan waye kake tambaya"
Ahmad yace"No bagidan kowa nake tambaya ba inason magana ne da wancan yarinyar" _yafada tare da nuna Aysher_
Jin haka yasa Fatima tacema sauran kuzo mujirasu acan dan Allah _Tafadi haka tare da yima aysher alama da ido cewar tasaurari abinda zaifada mata_
Ahmad Aysher yakalla yace"Sannu Aysher sannu da kokari amman nasan malaminku yafada muku karya bakyau ko"?
Aysher cikin kwarin gwiwa tace"yafada mana haka zalika yafadamana cewar abinda kakesha haramun ne"..
Dan gajeran tunani Ahmad yayi kafin yatuna da abinda take nufi wato sigari azuciyarsa yace _Shi kadai tasani batasan inashan iyayensu bama, batasan cewar itama da abinda yasani zuwa gurinta ba_
Azahiri kuwa dariya yayi yace"Ai nikam nadaina tunda nafahimci bakyaso but amman meyasa zakimin karya meye dalilinki da hakan nimafa fulani ne kawaidai dan banajin yaren ne ballantana kimin wariyar launin fata danni ba kad'o bane"
Kara daure fuska Aysher tayi kafin tace"Eh banyi maka karyaba dan hausa ba yarena bane Fulatancine yaren nawa kuma ba karya namaka ba dalilin dayasa nace haka kuwa shine saboda Banason doguwar Alaka dakai zan wuce sai anjima.
Tana gama fadin haka tawuce idanuwansa yabita dashi yana kallonta tare da kara mai-maita abinda Aysher tace *BANASON WATA DOGUWAR ALAKA DAKAI*
Nantake wani bacin rai ya ziyarci cikin zuciyarsa hakika kallamar tayi bala'in bata masa rai _Toh kabarta mana ga mata nan manya masu class sunfita komai_ wata zuciyar ne take basa wannan shawaran dan haka a zahiri yace NO dakarfi dole saina ciki burina akanta sigari yadauko wanda yake aljihusa cikin kwali ya cinna masa wuta yafara zuka ransa yabaci.
[10/12, 7:48 PM] Zeetty: Yarbingel tasauka garin yola lafiya itadasu Honourable kai tsaye gidansu Aysher suka yima tsinke yadikko tayi musu karba maikyau dan tasamu labarin zuwan nasu dakin mijinta tayi musu masauki anan suka kara gaisawa takawo musu abinci wanda akan girkin abincin yau tahana Aysher zuwa gidan aikinta tace zasuyi baki.
Hon.Mahmoud sundan taba girkin dan yayi musu dadi balaifi.
Bayan sungama Nura yabukaci a turo musu Aysher sugaisa nan yar bingel tamike ahanzarce tashige gidan dan ita yadikko wai adole tana kunya anzo maganar auren yarta.
Aysher bata kawo komaiba cikin ranta tasa hijabi tafita zuciyarta fess.
Bayan tagaishesu ne tayunkura zatabar dakin nan Nura yayi saurin tsayar da ita tare da cewa"Aysher bazaki tsaya kugaida da mutumin naki sosai ba (Yafadi hakatare da nuna Hon.mahmoud wanda yakame a kuje cikin mamaki Aysher in-ina Aysher tafara cewa wa....waye...ni....ni ai bansashiba yau nafara ganinsa cikin mamaki Alh.Nura yace "Bangane ba kina nufin bada saninki aka tura mana hotonki abuja ba?
Gyada kanta Aysher tayi _Anan tagano kudin hoton da yadikko tabata ashe tallanta za'akai abj_...
A hanzarce Aysher tabar dakin tana tunanin me yadikko take nufi da haka
Damm kirjinta yabuga da Aure yazo mata cikin ranta a'a bazai yiwu ba dasauri Aysher tadakatar da zuciyarta daga wannan tunanin.
Yadikko tana ganin yadda Aysher tashigo gidan aguje dakuma hanyar dakinta data nufa idanuwanta alamun kuka takeyi dasauri tacema yarbingel yi sauri kije kijiyo mana kodai batayi musu bane ko halin tsiyarta ta shuka musu suka korota keda kikace wata kila tafito da dubu hamsin kyauta.
Ahanzarce yar bingel ta fice zuwa dakin.
Ko sallama babu take tambayar lafiya kuwa.
Hajiya daman baku mata bayani bane kuka tura mana hotonta abj..
Cewar Nura
Cikin Alamun rashin gaskiya Yarbingel tace " Aa....eh bata saniba saboda yarinyar tanada son karatu munbari dai komai yayi dai-dai bazata kiba ai tanada biyayya kuma ai da sanin iyayenta uwa da uba ai kunga irin karban mutumcin da mahaifiyarta tayi maku.
Cikin alamar gamsuwa da bayaninta Nura ya gyada kai tare da cewa bari muje mu kama hotel zamu dawo da daddare.
Cikin motar Hon.Mahmoud yakalli nura dake tuki yace Nifa Nura ko ana ha maza ha mata sai na auri yarinyar nan dan ina bala'in sonta ko Amina banyi mata irin wannan son ba soyayyace mai shiga farat daya ta shigeni ina sonta dayawa dabi'unta sunyimin sanyinta dakomai yazo dai-dai da yadda nakeso matata tazama.
Kallonsa Nura yayi yace"Nikuma Hon. Tausayintane yakamani bata dace da mai irin laluranka ba kamilan yarinya karama da ita inama zaka barmin nayi ta biyu da ita dan gaskiya........wani kallon da Hon. Ya watso mishine yadakatar dashi daga karashen maganar sa
Hon. Mahmoud yace cikin fusata "Baka da hankali nura nace baka da hankali dabadan wani abuba dakuma yadda danayi dakai sosai dasai nace ko yan adawa sun siye kane kariga kasan akan rashin aure zan iya rasa kujerata amman kake fadin haka toh nikam kozan fadi zabe bazan hakura da Aysher ba naganta inasonta dayawa ba kadan ba jina nake kamar saurayi.........
MAMAN HANAN
[10/12, 10:13 PM] Zeetty: [10/12, 9:41 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 14-15
© ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP
Bangaren Ahmad kuwa hankalinsa yakasa kwanciya saboda rashin ganin Aysher a wunin yau kasan cewar asabar ne ba makarantar boko sukeda shiba kuma gashi yau batazo gidan ba _Ashe ganinta dayakeyi kullum rahama ne agareshi kodai son yarinyar nan nakeyi_ bazai yiwu kawai raina ne yabiya akanta inaso namaida mugun yawu
Da daddare Ahmad kasa samun nutsuwa yayi yanaso yaje club amman ya yanke shawarar mai gadi yarakashi gidansu Aysher abokansa sunata kiransa yana cemusu gashinan zuwa akarshe ya kashe wayar dan bayaso ya gayyaci kowa gidansu Aysher sai mudansir toh shima din ransa ya biya akan Aysher haryana kirarin cewa zai aureta tsaki Ahmad yasake dakarfi baba maigadi yakalleshi yace"kaida waye kake tsaki haka"
Ahmad yace" Hmmm natuna wani abu ne"
Suna dosar kofar yasamu yaro ya aika akira masa Aysher yaune zuwansa kofar gidan nafarko yakalli baba maigadi godiya yamasa tare dacewa yatafi kawai.
Cikin gidan kuwa yadikko bata tambayi kowaye mai neman Aysher ba tace aje ace masa tana zuwa a tunaninta su Hon.mahmoud ne dan sunce zasu dawo da dare.
Aysher ta kwalawa kira kafin tace cikin daure fuska mai nuna alamun kada ki kuskura tace"kije kofar gida bakinki sunzo kindaiji gargadin dana miki ki kiyaye"
Cikin sanyin jiki Aysher tafita kofar gidan.
🍒🍒🍒🍒🍒
Wani sanyi taji cikin ranta lokacin data hangoshi a tsaye cikin shiga ta kananan kaya tayi masa kyau kuwa _lallai ashe gwara wani kiyayyar akan wani itakam gwara zuwan wannan fiye da zuwan masu manyan tumbin na_ Aysher tafada aranta cikin kwarin gwiwa tare da sassauta hade fuskar datayi ta karasa gurinshi da sallama ya amsa ta gaisheshi ya amsa yana murmushi rasa abinda zaice mata yayi _Shidai yaganta hankalinsa ya kwanta_
Cikin wata irin murya yace"Maiyahanaki zuwa yau"
Aysher tace"Yadikko ne ta dakatar dani wai zatayi baki but har sunzoma"
Kuramata ido Ahmad yana kallon bakinta yadda take magana abin yabashi sha'awa.
Yace"meye zakiyima bakin kuma mazane ko mata"
Aysher tace"Mazane wai daga abj"
Cikin nuna Alamun kishi Ahmad yace"Girkin naki sukaci harkin iya girkin abincin da wasu zasuci mstwwwww Ahmad yaja doguwar tsaki kafin Aysher tabashi amsa sai sukaji tsayuwar mota.
Waiyagawa Sukayi dan ganin kowaye
Nura ne yafara fitowa dan neman yaro yakira musu Aysher.
Dammm kirjin Aysher yabuga dan ganin Nura datayi tagane sune sukazo da rana
Ahmad yana lura da ita.
Waige-waigen da Nura yakeyine dan neman yaron da zai aika idonshi ya hango masa Aysher
[10/12, 10:12 PM] Zeetty: Dasauri yakarasa gurin dasuke yayi sallama kafin yace"Dan Allah abokina kadan sallameta yanzu maigida yana mota yana jiranta"
Wani matsiyacin kallo Ahmad ya watsa masa tare da cewa"Maigida? Shi maigidan dan gidan uban waye dan iskanci muna tsaye kace wai nasallameta mai gida yana nemanta....ke daman kinsansu ne
Suna zuwa gurinki?
Cikin yanayi na tsoro saboda gaba daya Ahmad ya canja tace"Sune bakin yadikko wanda nayi musu girki dazun sunedai wanda nake fada maka sunzo daga abj"
Wani malalacin kallo Ahmad yabita dashi kafin yace"Saurayinki dai ko kinyi masa girki yaci makaryaciya nizaki yima karya wato har zance kikeyi a mota ko?
Kai Aysher take girgiza masa alamar bahaka bane
Cikin tsawa yace"Kifadamin zance kike dashi a mota yar figigiya dake kin iya jaraba"
Nura daya fuskanci zance Ahmad inda yasa gaba kuma da alamar rashin yarda da ita daya darsu a cikin zuciyarta yanzu yace aransa _Barin wanke yar mutane ni ai tausayima take bani da alamar bata da budewan ido_ dan haka yadafa kafadar Ahmad tare da cewa "Calm down my friend duk karikita yar mutane toh muma yau muka fara zuwa gurinta bata ta6a haduwa damuba sai yau kuma ga menemanta can a mota"
Ture hannunsa Ahmad yayi cikin masifa da hargagi yafara fadin dan iskanci shine zaice taje tasameshi a mota kai kafito kabasu guri wato yayi mata duk abinda yaga dama ko macuta azzalumai toh ni Ahmad nace bazata jeba zanga uban daya isa yasata taje gurinsa kaje kafada masa tunda kaine kanzaginsa idan baija motarsa ba daga gurin nan Narantse da Allah yau koni koshi motarku saita canja kammanni"
Sum!Sum Nura yaja jiki yabar gurin dan ganin yanayin Ahmad duk abinda yace zai aikata zaiyi din daga ganinsa yanada jarumta
Mota da sauri batare dayacema Hon.Mahmoud komai ba yaja motar sukabar gurin.
Ahmad kallon Aysher yayi hakika yanayinta yabashi tausayi amman shikam yafi tausayama kansa a yanzu yakalleta yace"Waye ya hadaki da wadannan"
Aysher tace yadikko ne.
A ina suka ganki?
Tace"Hotona wai ta tura musu abj"
Dafe kai Ahmad yayi tare da fadin Oh my God! Kika dau hotonki kika bata why Aysher why pls....kansa yana sunkuye dan wani irin sarawa dayake masa (yanada ciwon kai na gefe daya magrine)
Aysher tabude baki tace"Wlh....stop Aysher just Go!Go!! I said go yafada da karfi cikin tsawa dagudu Aysher tabar gurinsa dan ta tsorata gida tashiga dasauri.
Ahmad yadade a gurin kafin yaja kafarsa dakyar dan zuwa gida _Maman hanan tace Ahmad kaida kake sha'awarta meye nashiga damuwa dan masoyinta yazo mujedai zuwa_
*************
Kai Nura meye kawani figi mota aguje kabar gurin batare da kayimin dogon wani bayani ba bayan naga kajima a waje har lekowa nayi naganka da My love tare da wani.
Wani kallo Nura yayi masa azuciyarsa yana takaicin hali irin na Hon.Mahmoud dan haka ya shaftaro karya yace masa"wato maigida saurayin daka ganta dashi abuge yake yasha tayi masa karo yayi mankas gefen hagunka kuwa dan baka kallon gurin ne abokanansa ne yan bana bakwai sunyi masa rakiya sunkai su goma danaje gurinsu nima natafine da niyyar hayaniya amman inaji yana kwala musu kira nanemi sulhu daga karshe rantsuwa yayi dacewa idan bamu ja motarmu daga gurin ba zasu cinna mana wuta dukan mu mu kone yakara da cewa akan Aysher zai iya rasa ransa koya hallaka mutum shine naji tsoro nazo naja motar muka tafi dan naga alamarsa babu Allah a ransa wani abin takaicin ma Aysher da alamar tana bala'in sonshi dan yana magana tana cewa nagode nawan kubar kofar gidan kunji abinda masoyina yace muku.
Tsaki Hon.mahmoud yayi kafin yace"Lallai za'ayi mutuwar kasko kuwa dan akan Aysher nima zan iya rasa rayuwata kai zan hallaka mutum akan wannan babyn kaima dai matsoracine amman kuma kanada gaskiya bamusan abinda suka taka ba mubari gobe muzo da rana ido na ganin ido kuma mu fadawa mahaifiyarta cewar arabata da wannan dan iskan yaron kawai may be komawarmu ma sai jibi monday kawai.
_shege kaima saikace wani na Allah ne banda yanzu da duniya takoyama hankali wato bazaka hakura da yarinyar nan ba kenan maye kawai_ Nura ne kefadin haka a zuciyarsa a fili kuwa cewa yayi yadda kace haka za'ayi Honourable.
MAMAN HANAN
[10/13, 3:15 PM] Zeetty: [10/13, 2:45 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 16-17
Wayyo Allah nashiga uku dan Allah yadikko kiyi hakuri wallahi ba dan iska bane a gidansu Alh.lawan yake Allah baitaba zuwaba sai jiya cikin shesshekar kuka Aysher take fadin haka dan hakika tadaku yau kam agurin yadikko.
Barta haka Mama hakika tadaku sosai yau ai zataji maganarki wannan uban duka haka ni wallahi sainajima kamar jikina kike duka kawai dai gidansu yaron zakije aja masa kunne yarabu da ita, ita kuma daga yau nahanata zuwa aiki gidan zandinga biyanki abinda kike samu duk wata har ninkawa zanyi dan yaronnan baida imani daga ganinsa jiya fa dakyar muka sha mama _Hon.mahmoud ne ke wannan bayanin harda karya wai yaga Ahmad kamar dagaske_
Yadikko cikin sauri ta gyada kai kafin tace"Angama Alh. Aiki dagayau ansokeshi kuma In sha Allahu yanzu zanje gidan nasamu maigidan nayi masa bayanin ashiga tsakaninsa da yarinyata zai batamin ita.
Hon.Mahoud yayi murmushi tare da fadin nagode mama ga kudi nan yazaro dubu 20 yace takai Aysher asibiti a duba lafiyarta dan ko tashi takasayi daga inda take.
Kudin yadikko takarba tare da cewa barinje nadawo saina kaita General Hospital adubata da kyau ai maganin mai taurin kai kenan.
Nura dake gefe a tsaye yana kallon duk abinda ke faruwa karasawa yayi gurin Aysher yana yimata sannu kafin yabi bayan Hon.Mahmoud dan zuwa hotel.
Cikin mota Nura yakalli Hon.mahmoud tare da cewa oga dan Allah bakaji tausayin yarinyar nan ba?
Ni zuciyata kokwanto takeyi anya kuwa wannan mahaifiyar Aysher ce idan har ita ta haifeta bazatayi mata irin wannan dukan ba uwa mace mai tausayi bawai namiji ba,
Gaskiya da alamar tambaya yakamata mubincika.
Mubincika uban me Nura kanka daya kuwa ni nalura da take-takenka bakin ciki kake nunamin azahiri.
Nura yace bakin ciki kuma wane irin bakin ciki bayan tun farko ni na baka wannan shawarar.
Ehmana bakin ciki toh idan banda bakin cikin da kakemin ina ruwanka da cewar sai anbinciko mahaifiyar yarinyar nan koda wannan ba ita tahaifeta ba ai itace ke rike da ita kuma duk dan tasoni inace akeyi mata haka amman kai kazo kana wani irin banzan magana mtswwwww yakarasa fada tare da tsaki.
Nura yakalli Hon.mahmoud yace"Da nasan yarinyar dazaka zaba karamace sosai kamar Aysher mai nutsuwa wallahi bazan kawo wannan shawaran ba dan Allah kacanja kanemi yar duniya kamarka wanda matsalarku da ita daya ne karka cuci Aysher"
Saunawa zan fada maka cewar baka isaba narantse da Allah ina komawa abj zan ajiyeka daga ranar kadaina aiki a karkashina muna fiki kawai.
Nura bai kara cewa komaiba yayi shiru amman cikin ransa yayi alkawarin saiya taimakawa Aysher.
[10/13, 3:15 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒
Kwance yake akan gadon dakinsa yanata malelekuwa tare da fadin innalillahi wa'inna ilahi raji'un kansa yana matukar sara masa hakika jiya baiyi bacci ba dan wani bakon Al-amari daya sameshi SOYAYYAR AYSHER yakeyi dagaske bawai sha'awarta ba kamar yadda yafada a baya yanason tazama matarsa uwar 'ya'yansa toh amman yana ganin dakyar zai yiwu dan iyayenta sunyi mata zabi.
Adaren kasa bacci yayi kuma yakishan duk wani kwaya ko syrup dazai sakashi bacci yanaso ya dan-dana zafin soyayya yanaso wannan daren yazamo daya daga cikin dare mai matukar bakin ciki a rayuwarsa sai sigari dayaketa bankawa cikinsa.
Dasafe ko breakfast yakasa shiga gidan yayi yana kwance kamar mara numfashi.
Idi mai wanki Alh.lawan yaturo yakirasa.
Yatarar dashi a kwance yafada masa sakon ubangidansa cikin karfin hali Ahmad yace "yafada yanazuwa"
Yayunkura dakyar yasaka jallabiya yafito harabar gidan yahango baffansa tsaye da wata mata tanata bala'i yakarasa da sallama tare da gaida baffan nasa ya amsa bayabo ba fallasa.
Ahmad yakalli matar _Haka kawai yaji bata kwanta masa araiba_ yagaisheta ta amsa a dake.
Alh.lawan yakalleshi rai abace kafin yace"Yanzu Ahmad abinda kake aikatawa daman baka daina yiba saboda hakan fa aka turoka garin karatu amman bazaka gyara rayuwarka ba yanzu saboda Allah Aysher datake zuwa aiki gidan nan kakeso ka batawa rayuwa haba Ahmad karka jawomin bacin suna a anguwa mana bayan kowa yana ganin girmana toh ga mahaifiyar Aysher dai tazo tana gargadin arabaka da yarta.
Cikin yamutsa fuska Ahmad yace"Baffa Uwar rikonta dai ba mahaifiyarta ba ko"
Cikin hasala Alh.lawan yace"Koma dai yaya take agurinta tadaizo tanajan kunne arabaka da yarta yadikko gashi kiyi masa bayani".
Cikin masifa Yadikko tace"Hmmm ai idan baiyimin hakaba Aradun Allah baicika lalatacce ba dan iska Toh ina gargadinka da kakkausan murya kafita harkan yarinyar gurina kobani na haifeta ba a gurinadai kaganta kake bibiyarta dan iska mara kunya toh dagayau tabar kara zuwa aiki gidan nan kuma wallahi ka kuskura kaje kofar gidanmu gurinta hukumace zata rabani dakai dan aurenta za'ayi kwana kusa lalatacen banza lalatacce wo.....wani tsawa Ahmad yadaka mata jikinsa yana 6ari yace"Ya isheki haka kinci Albarkacin Aysher yau dasai da miki dan banzan duka a gidan nan sannan kitabbatar cewar nidin dan iskane dakike cewa karna sake zuwa gidanki saboda hukuma waye yake tsoronta toh ina gargadinki da ki tsaya akan cewa karna sake zuwa gurin 'yar kishiyarki amman karki sake aibatani nafada miki"..
Baijira abinda zata fada masa ba yasakai yawuce Alh lawan yana kiransa amman bai juyoba balle ya saurareshi.
Daki yashiga yatarar wayarsa tana ringing yakarasa da sauri yadauka sunan Bro daya gani shiya tabbatar masa dacewar Dan uwansa ne yake kiransa awaya.
Dasauri yadauka gaisheshi kanin nasa yafarayi kafin yace"Yaya meyasa zakayi haka, yaya meyasa zakayi waka harta baza duniya haka, yaya why ina tsoron kar Abba yaji dan komai zai iya faruwa ni nasan kaine *A.A.HAMEED*
da wakarsa ta Hiphop tazaga duniya mekarasa kana karatun medicine meya kaika zama mawaki?
Haba yaya Ahmad why....
Ahmad wanda ranar yau tazamo masa ranar bakin ciki a gareshi cewa dan uwansa yayi pls Bro karka damu idan Abba yasani ni badamuwata bace inada damuwar datafi wannan pls kabarni nayi facing dinta" yana gama fadin haka ya katse wayar.
Saddiq bin wayar da yayansa yakatse yayi dakallo tare da mamakin yayansa Ahmad daya kamashi, shin akwai wata damuwa data shige fushin iyaye akan dansu lallai akwai matsala akan yayansa kodai wata kwayar yasha ta taba masa kwanya........
MAMAN HANAN
[10/13, 10:49 PM] Zeetty: [10/13, 7:56 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 18-19
*Wannan page din sadaukarwane sukutum gareki Rukayya Omar Alsaweey maman fatima Allah yarayata da imani nagode da so da kaunarki gareni*
Yadikko dai batakai aysher asibiti ba sai chemist data kaita aka bata magunguna na