Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 34154 words

Chapter 4 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

395

Ads at the middle of Article

200 ta soke sauran kudin a aljihu


Da daddare Honourable yazo ganinta toh tadai daure tafito kodan gudun dukan yadikko amman tunda yazo ko uffan batace masa ba shikadai yagama sambatunsa yamike daniyar tafiya yau ko Nura baizo dashiba yace taturo masa mamanta.


Yadikko tazo jiki har rawa yakeyi Hon.Mahmoud yace mata zaitafi amman zai dawo nan da wata daya dan Allah acigaba da kokari ana lallasar masa aysher dan bazai iya hakuri da rashinta ba




Ya ajiye mata bugun abuja dubu dari yace tarike a hanunta kafin yazo.




Yarbingel daman ita tunda tarakosu ta juya bayan itama anyi mata sallama mai tsoka.






********




Kamar saukar aradu haka Mudansir yaga Ahmad yafado masa dakinsa dake Hostel na Apti.


Alokacin Mudansir yadauko wata yarinya dan tayashi kwana suna zaune suna kallo yaga Ahmad yashigo dauke da troly na kayansa.


Ahmad yana kallonsu yasake wani tsaki tare da cewa "Allah dai ya tsinewa Mazinaci" yakalli yarinyar tare da daka mata tsawa "zakizo kifita dan ubanki kosai na lakada miki duka shegiya 'yar iskan banza"
Kallon Mudansir tayi a tsorace kansa ya gyada mata alamar ta tafi kawai dan shima yaga yanayin abokin nasa komai zai iya faruwa.


Dasauri ta dauki jakarta ta arce dagudu dan ganin Ahmad yafara nade hanun rigarsa alamun zai iya kaimata duka a kowane lokaci"




Tsaki Ahmad yasaki tare da cewa shegiya da karki fita mana dakinga hauka.
Mudansir yakalleshi yace"Toh meye hankalinka yakwanta ka korarmin abokiyar taya kwana wai meye yakawoka bayan kashareni nakiraka sau nawa baka dauka saboda kawai nace inason babyn ka....


Ahmad yakalleshi Cikin Alamun nuna mahimmanci akan abinda zaimasa yace"Stop it pls nawan dan Allah kayi aure mana wallahi natuba nadaina tunda nagasgata cewar son Aysher nakeyi da aure kaima nawan pls kadaure kayi aure wannan ba rayuwa bace kana daukar zunubi dayawa"




Kanason Aysher da aure like seriously?


Kai Ahmad ya gyade masa dan bazai iya magana ba.


Wow am very happy nawan nayi murna da faruwan hakan wallahi dan kun dace kaida ita.


Ahmad yace daman basonta kakeyiba dagaske


Eh kawai dai ina tsokanarka ne dan tunfarkon bani labarinta nasan cewar wannan ba sha'awa bace sonta kakeyi dan haka nake tsokanarka da cewa ina sonta kaikuma kanamin hayaniya harka daina daukar wayata but forget about that meyake faruwane naganka a hargitse haka A.A Hameed.




Komai ma yafaru Mudansir komai ya hargitsemin inason Aysher bantaba son wata mace kamar yadda nakesonta ba but ina ganin baxan sameta ba Aysher tayimin nisa nawan.




Kallonsa mudan yayi cikin mamaki kafin yace "Bangane karasata ba cewa tayi bata sonka ko kuma aure aka daura mata da wani"




Batayi aure ba Aysher bata masan ina sonta ba amman Matar babanta tazo hargida tasamu baffa lawan akan yajamin kunne nafita harkar yarinyarta....... _Anan Ahmad yabama Mudansir labarin haduwarsu da aysher da farkon fara maganarsa da ita da kuma yanzu maganar aurenta da akeyi har tura hotonta abj da Akayi.




Cikin nuna Alamar tausayawa Mudansir yace"Natausaya mata wallahi but yanzu yakamata kafara sanar mata cewar kana sonta duk da anhanata zuwa gidan da kake kasamu ko a hanya idan an aiketa kuhadu kafada mata kanasonta nasan idan harta amince toh zata samo maku mafita a gurin mahaifinta ni banga dalilin tahowarka ba ma"


Ahmad yace"Ni kuwa nakeda dalili tunda Ran baffa a bace yake gashi kuma sadiq yakirani yanafadamin cewar wai wakar danayi tabaza gari state-state kowa yasanta wai yana tsoron kar Abbanmu yasamu labari raina zai matukar baci,


Toh ni duk wannan bai dameni bama kamar yadda akeso arabani da Aysher dan sosai nake jinta a nan dina (Yafada yana nuna kirjinsa)


Wani kallo Mudansir yabishi dashi tare da cewar lallai baka da hankali Ahmad har soyayya yafi fushin iyaye ashe?
Banaso kayi wakar nan tun muna Ghana amman saida kayi batare da shawarata ba yanzu gudowa kayi nan kome.


Ahmad yace"Ba gudowa nayi ba nazone nanemi shawara akan soyayyata da Aysher nadan huta kuma kafinnan baffa ya huce.






Allah yakyauta cewar mudan.
[10/13, 8:06 PM] Zeetty: **********
Kaiwa yakeyi yana komowa a tsakiyar hamshakin falonsa dake kasa Alh.Aliyu ne hanunsa rike da waya yana kiran number Ahmad taki shiga alamar ma wayar ankasheta.




Matarsa yakalla yace"Zuwaira wallahi idan har nabincika nagano cewar Ahmad shine yayi wakar nan da gaske inamai tabbatar miki zan daukeshi daga kasar nan naturashi can yankin larabawa a bautar dashi bazan ma barshi a nigeria ba kona kaishi gidan horo anan can kasar larabawa zanturashi aikin bauta tunda yaki karatun kuma zance banda lada karsu biyashi ko naira nagaji da halinsa tunda bazai fasa ba yana gama fadin haka ya haura sama.........






Umma saddiq takalla tace"kai ka tabbata shine yayi wakar nan?
Saddiq ahankali yace wallahi umma shine ainakira wayarsa jiya nake masa magana yace waishi yanada damuwar datafi wannan barima dai nasake kunna miki kiji har raping din turancin Yaya Ahmad ne....
Yadanna Alamar zaikunna wakar Umma tayi saurin dakatar dashi tana fadin"Kaci gidan ku karka kunna nidama yakunna wayar tasane ma sainayi masa magana amman barin kira yaya lawan naji........






MAMAN HANAN
[10/14, 1:47 PM] Zeetty: [10/14, 1:21 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
20-21


*TASHIN HANKALI*




Hankalin Umma yatashi lokacin data kira wayar Alh.lawan yake mayar mata da maganar karar Ahmad da aka kawo shekaran jiya dakuma nemansa dayayi a gidan yarasa a tun shekaran jiyan hankalin Umma yatashi dajin cewa ba'aga Ahmad ba dan haka ta katse wayar cikin sauri tare da haurawa sama gurin maigidanta.
Tasameshi tace"Alh. Kasassautama yaron nan kaga tun shekaran jiya yaya lawan yace yanemeshi baisan inda yatafi ba.


Cikin bacin rai yace"Meya shafeni duk inda zaitafi yatafi mana aiba yaro bane ace shine babba a gidan nan yakasa yima kansa future mai kyau toh duk inda zaije a fadin kasar nan yatafi zansa a nemoshi muddin abinda nake zargi akansa hakane narantse da Allah saina turasa can kasar saudiyya nasamu kauyen da zan kaisa har mungama magana da mutanen da zanturashi gurinsu bautar dashi zasuyi sosai nafada masu.


************




Adaren wannan ranar Ahmad yatakurama Mudansir dole yarakashi yaga Aysher yaga halin datake ciki.


Mudansir yace kabari mana sai gobe tunda yau takabaro anguwar kayi hakuri abokina...


Dakyar Ahmad yahakura amman washe gari da sassafe Ahmad yatashi mudansir yace masa tashi mutafi mu risketa a hanyar school mana


Cikin magagin Bacci Mudansir yace"Pls nawan kabari sai sun tashi daga school din zamu samu lokaci sosai muyi mata magana"


Nan madai shiru Ahmad yayi yana jiran lokaci yayi sunatafi.


12:30pm suka yima anguwar damare tsinke a hanyar makarantar su Aysher suka zauna a cikin mota suna hango makarantar karfe 1:00pm aka tashi 'yan makaranta suka fara fitowa idanun Ahmad yana hanyar da dalibai suke bulbulowa yakafesu da ido yanaso yahango ta inda Hasken idaniyar zata baiyana.


Can yahangota ita da kawarta fatima wani sanyi yaji cikin zuciyarsa dan ganinta su biyu kawai.


Dasauri yatabo Mudansir yana nuna masa ita mudan dariya yayi tare da cewa "kabari sudanyi nisa sai mubisu a baya saboda idanun malamansu kar yajawo mata matsala"


Kai Ahmad ya gyada dan baya bukatara abinda xaitaba lafiyar Aysher ayanzu.




Saida sukayi Nisa da makarantar yadda ba'a hango makarantar ma gaba daya kafin Mudansir yaja motarsa yabisu a baya,




Horn yadinga masu kafin fatima tacema Aysher su tsaya kamar dasu akeyin horn din.


Dakyar Aysher ta tsaya a lokacin Mudansir yasamu guri yayi parking Ahmad ne yafara fitowa dan haka hankalinsa yanakan Aysher.


Ganin Fitowar Ahmad ne yasa Aysher rikicewa tana girgiza kai tare da fadin Fatima zomutafi Yadikko tarabamu dashi kar aje a fada mata ta dakeni.




Rike Hanun Aysher fatima tayi tare da cewar ki nutsu ki saurareshi kiduba dakyau suma sunyi aiki da hankali babu munafikin dazaije yafadawa yadikko idan bani kuma kike zargi ba,


Jin haka yasa jikin aysher sanyi a lokacin Ahmad yakarasa karasowa gurinsu.


Sallama yafara musu suka amsa a tare gami da gaisheshi Ahmad yakalli Fatima yace"Kawarmu kitaimaka kifahimtar da kawarki abinda nakeji araina game da ita nasan kinfita wayewa dai-dai gwargwado nasan kin fahimceni tun randa nafara tareku a hanyar makaranta.........
Haba malam kabari mana nazo natayaka fighting din nagabatar da kaina agurinta da bukatarmu gareta mudansir ne yake fadin haka a lokacin daya karaso.




Sallama yayi musu shima suka amsa tare da gaidashi Aysher dai kanta yana sunkuye dan wani iri takeji a jikinta.




Sunana Mudansir Mustapha ni abokin Ahmad ne na hannun dama garinmu daya kuma tare muke karatu amman kowa abinda yake karanta daban.




Munzo da kokon bararmu gareki Aysher abokina yagani yanaso duk da anyimasa tsakani da gidanku wannan shine dalilin dayasa muka tareku a hanyar dawowarku daga makaranta dafatan zakuyi mana gafara wannan ce kadai muke ganin damar da xamuyi magana dake dan muji tabakinki dakuma inda zaku dinga haduwa kafin komai yazama normal.






Aysher takasa cewa komai sai wasa takeyi da hannun jakar makarantar ta.




Fatima ce takalleshi tace dan Allah kubamu lokaci nan da kwana uku zatayi shawara sai mu hadu anan wato nan da juma'a kenan.


Girgizakai Ahmad yafarayi dan yakasa magana mudansir ne yace"Kawar mu duk da bansan sunanki ba kwana 3 yayi mana nisa dan abokina yanada matsala cikin kwana ukun nan komai zai iya faruwa dashi akwai matsalar datake fuskantarshi bayan amincewa da soyayyarsa agurin Aysher"




Jin haka yasa fatima tadubi Ahmad _Hakika kana kallonsa da yadda yaxubama kawarta ido zakasan dagaske sonta yakeyi bana wasa ba kuma gashi very handsome dashi da'alama yana tattare da nutsuwa a tare dashi_


Fatima tagirmi Aysher da shekara biyu kawai dai kawance ne dakuma yanayin girman jikin Aysher kuma fatima tafi Aysher wayewa dan tana zuwa garuruwa dayawa gurin danginta idan anyi musu hutu har zance tanayi dan haka takalli Mudansir tace"sunana fatima gobe idan antashi kamar lokacin da kukaxo yau goben ma haka zakuzo muhadu a gurinnan zakuji amsar kawata"




Hamdala Mudansir yayi tare da yimata godiya Aysher dai takasa magana shikuwa gogan naku ya zuba mata tsumammun idanuwansa kamar yacinyeta danye.


Fatima tace zamu wuce sai goben.


Ahmad yace'Aysher bawani dan sweet word ne?


Murmushi tayi masa bayan tadago takalleshi kafin taja hanun fatima suka fara tafiya tace sai gobe.


A mota mudansir dariya yaketayima Ahmad dariyar shakiyanci tare da cewa Allah abin godiya gaskiya true love daban yake yau anyi maka kamun kazar kuku sakayyar babies din daka dinga kwasar rabar jikinsu ne yakamaka one time Hakki aiba wasa bane wow thank God yau ina class din naka ka kare a under 18 hahahaha.






Ahmad daya gama fusata tsaki ya saki dakarfi kafin yace gwara ni rabarsu nake kwasa kaida kake keta gona da iri fa zina kakeyi gwarani under 18 nakeso aurenta zanyi wallahi kai idan baka tuba ba kamar yadda natuba idan Allah yatashi kamaka saika rasa na aure ko ka auri bazawara idan Allah bai hadaka cutar tsida ba.




Shiru mudansir yayi dan yasan abokinsa yafishi gaskiya
[10/14, 1:47 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒








Kayi hakuri Alh.Aliyu kuskurene Ahmad yariga ya aikata amman karkayi fushi dashi dan Allah kabari muje abuja wannan taron idan mungama nan da kwana biyu ko uku sai muwuce yolan muji dalilinsa nayin wakar Hiphop CI yarasa ko SUTURA dazaisaka wanda harzai kaishi zuwa studio yin waka idan suna yakeso yayi a duniya ai ko a karatunsa yatsaya zaiyi suna ta bangaren wannan kuma za'ayi alfahari dashi a kasarnan basaita hanyar waka ba idan kuma sha'awa yabashi toh yayi na farko karya sake aikata na biyunsa" wannan bayanine daga bakin Alh.Labaran aminin Alh.Aliyu mahaifin Ahmad.








Bawani sauraransa da zanyi Alh.Aliyu turasa zanyi yaje can yayi hankali idan ba haka nayi masa ba inamai tabbatar maka Ahmad bazai taba kintsuwa ba ko aure nayi masa ba nutsuwa zaiyi ba zai hadu dani taso karakani naje nayi masa visa dan randa naganshi bazai kara kwana daya a Nigeria ba.




A'a kasassauta wannan fushin naka dan Allah ai wakar ba laifi bane yaran manya sunayi sosai suma sunfi yi a kasashen waje kadaiyi hakuri.


Nafariga nagama magana zoka rakani imigration office.


Wannan shine tattaunawa tsakanin Alh.Aliyu da amininsa Alh.labaran a cikin office din Alh.Aliyu.




*YOLA*


Aysher dai ta amince da soyayyar Ahmad da taimakon shawarar da Fatima tabata tare da kara mata karfin gwiwar cewa wannan ne kawai mafitar da zata samu idan Babanta yazo tasanarma Ahmad yaturo manyansa gudun auren Hon.mahmoud jin hakan yasa Aysher amincewa da soyayyar Ahmad acewarta *Dawani gwara wani*


Ranar juma'a 16-March ranace da tana daya daga cikin ranakun da Ahmad bazai manta dashi ba dan a wannan ranar Aysher ta amince da soyayyarsa duk da bata fada masa baki da baki ba saboda kunya amman fatima ta ari bakinta taci mata albasa.



Kudi Ahmad yaciro a accont dinsa masu dama awannan ranar ya dinga rabawa sadaka.


Gidan radio yola kuwa sunata kiranshi akan yazo ayi hira dashi dan masoya wakarsa sunason sanin wanene shi.


Yace musu ayi masa hakuri bashi da wannan lokaci a yanzu.......




MAMAN HANAN
[10/14, 7:12 PM] Zeetty: [10/14, 6:53 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE
Page 23-24









*Nasadaudar da wannan page din ga duk masoya wanda suke kaunar junansu dan Allah ko kuna tare ko kuma wata kaddarar ta rabaku toh wannan page din IS DIDECTED TO YOU GUYS*


Soyayya ta kankama tsakanin Ahmad da Aysher a kwanaki 2 kacal Ahmad wani mahaukacin so yakema Aysher wanda ya makantar dashi matsalar dake fuskantarsa


Da daddare yadamu mudansir da cewa shidai bazai iya bacci mai dadi ba saiyaga Aysher yau da daren nan duk abinda zaifaru saidai yafaru.




Mudansir yace"Haba nawan kar idonka ya rufe mana kaje kajawoma yarinyar mutane tashin hankali mana pls kayi hakuri gobe muje musameta ahanyar makaranta koda da safen ne ma kafin ta shiga class"


No Mudansir i can't wait idan bazaka rakani ba just give me ur key zantafi da kaina.


Mudansir dayaga dagaske yakeyi yamike a hanzarce tare da cewa Mayen Aysher zomuje ko gidansu ka hango hankalinka ya kwanta Romio"


Akofar gidansu Aysher sukayi parking Kafin su sami yaro yashiga dankira masa Aysher.


Wani yaro suka hango ya siyo pure water guda biyu a hanunsa Mudansir yakirashi ya nuna masa gidansu Aysher yace yayi masa sallama da ita.


Can jimawa saiga yaron yafito tare da cewa wai ga babanta nan zuwa.


Kallon juna suka shiga yi tsakanin Ahmad da Mudansir kafin mudansir yace"My man saika shirya Allah yaso manyan kaya muka sako yau zaka gaisa da mahaifin aysher"


Wani farin ciki Ahmad yaji a ransa sanda yahango mahaifin Aysher ya nufo inda suke _Sabanin Da idan sukaje zance mahaifin budurwa yazo daniyyar cewa sufito sai suji wani kunci da bacin rai_




Tsugunnawa sukayi cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa fuska asake tare da fadin _Bismillah kushigo daga ciki_


Dakinsa ya shigar dasu tare da mikewa tsaye yashiga gida yafito musu da lemon gwangwani da ruwa su Ahmad suka kara gaishe shi ya amsa a mutunce.


Mudansir ne yafara gabadatar dakansu a gurin mahaifin Aysher tare da cewa su suna zaune a kano state ne amman suna karatu a yola kuma Alh.Lawan yayan mahaifiyar Ahmad dinne.




Baffa Usman ya yaba da nutsuwar su Ahmad dan haka yace"Na yaba da nutsuwarku Allah tabbatar da Alheri Aysher dai karatu takeyi nan da wata 8 zata kammala kuma bani da burin tayi ilimi mai zurfi a gaba na wannan ma data samu Alhamdulillahi idan har mijinta yayarda takarasa a dakinta barin turo muku ita"




Yamike yashige cikin gidan yatarar yadikko tanata zazzaga masa bala'in cewar tariga tabada Aysher ma wani dan haka bazata fita ba,..




Bai saurareta ba yace Aysher tawuce taje gurin masu kiranta yadikko bata isa tayi iko akanki ba.




Dasauri Aysher takarasa dakin da sallama suka amsa kamshin turaren Ahmad gaba daya ya gaureye dakin tashaka tare da lumshe idanuwanta ta nemi guri nesa dasu kadan tazauna a kan carpet tare da gaishesu suka amsa Ahmad sai washe baki yakeyi kamar gonar auduga.


Ganin Aysher taki sakewa dashi suyi hira yasa Mudansir mikewa dan yabasu guri ko Aysher zata rage kunyar datake yima Ahmad.




Ahmad yana ganin mudansir yafita yamike ya karasa kusa da Aysher durkusawa yayi a gabanta tare da cewa"My baby kunyarki tayi yawa a fulanin kekam dabance pls yau kadai ki kalleni kice kina sona idan ba hakaba zan shiga wani hali"


Kara sunkuyar da kanta tayi takasa dago kanta takalleshi tana wasa da yatsun hanunta.


Ahmad yakalleta yana murmushi gami da fadin " Aysher dan Allah karki gujeni duk wuya duk tsanani pls be with me zan zamo jarumi indai akan soyayyarki ne zan iya komai koda ace shadi za'ayi bisa al'adar garinku zanyadda inasonki ne tsakani da Allah,




Allah ya doramin sonki kuma jikina yana bani kece matata shisa nazo garinnan da niyyar karatu Kinsan ance matar mutum kabarinsa Ina sonki ina matukar kaunarki Fatana Allah ya nunamin ranar da zanganki a dakina amatsayin matata uwar 'ya'yana.




Hakan daya furta yasa Aysher rufe fuskanta da tafukan hannayenta.




Yakara da cewa"Aysher kece muradin raina abin fahari na kinzamo fitila mai haske "yan mata na nad'aki sarauniyyar birnin zuciyata I love u so much my wife"


Dariya Aysher tafara harda kyakyatawa kafin tace"Ya labarin gurinsu mom dafatan suna lafiya kagaisheta idan kunyi waya pls"


Dariya Ahmad yayi yace"So kike kiyimin wayau bakyaso kifurtamin cewar kina sona ko badamuwa su mom lafiya kalau mun kwana biyu bamuyi waya ba cos i switch off all my phones but nakunna yanz......




Wayarsa ce tafata ringin yaduba sunan mai kiran my Bro yagani a rubuce dan haka yadauka da sauri gaisheshi saddiq yafarayi kafin yace"Yaya meyasa ka kashe wayarka tun last 3 days toh akwai problem dad yagano komai cewar kaine kayi wakar nan so yanzu haka yatafi abj jiya zaka iya ganinsa ako da yaushe ma'ana yau ko gobe ko jibi a garin yola yarantse kabar sake karatu a garin yola difffff wayar saddiq ta dauke Ahmad yakira yaji it's not reachable dan haka dole ya hakura ya kalli Aysher tare da mikewa yana fadin Swthrt barin tafi zandawo gobe in sha Allah tunda munsamu babanmu yadawo nasan bamu da matsala zanzo gobe da daddare.




Aysher tace Allah yakaimu kahuta gajiya kacema Yaya mudansir sai da safe.......
[10/14, 7:11 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒


Lokacin da aka aika dasu Ahmad suka aika ayi masu sallama da aysher baffa Usman yana zaune a tsakar gidan wanda ya sauka garin yola da safe.




Abin yabashi mamaki dayaji yadikko tana fadin aje ace musu anyima Aysher mijin aure.


Dakatar da dan aiken yayi ya dubeta tare da cewa "yau she nace miki nayi mata miji bayan asalima bansan wani da yake zuwa gurintaba dan bata fita zance sai yau amman kina cewa kinyi mata miji"


Cikin dakewa yadikko tace"Nayi mata mana mallam lokacin kana lagos kuma kaga yau kadawo bamu samu wani dogon zamaba sosai nidakai shiyasa banyi maka bayani ba.


Kai Baffa Usman ya girgiza tare da cewa mata!Mata!!mata!!!
Sai abarku kunada wuyar sha'ani Aysher

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads