Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 34154 words

Chapter 10 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

398

Ads at the middle of Article

cewa k'awata kin samu labarin bikin A.A Hameed kuwa dan har an daura auren a yola biki za'ayi amaryan ta tare a nan kai kawata munada chasu fa biki ne na manya"


Kee 'yar auta kinci kaza-kazar ki na rantse da sarkin dake busan numfashi duk wanda ya halarci gurin nan indai yaje sunan sa k'o nanne ni Ahmad zaiyima haka ni zai yaudara na rantse da Allah daga shi har Amaryan tashi da duk wanda zai halarci gurin bikin sunan sa k'onanne......






MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/26, 5:25 PM] Zeetty: [10/26, 5:17 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






_Ina jindadin zama tare daku, ina matuk'ar kaunar ku, 'yan Group din Zauren littattafan Hausa_








*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*










Page 53-54






Ranar laraba mutanen kano suka sauka a garin yola domin juyawa da Amarya washegari, kar6a na mutum ci sosai suka samu daga gurin dangin Aysher da na mahaifin ta.




Sun taho da kayan aure akwati biyar da d'an kit cikon na shidan, masha Allah komai yaji dan Yadikko a ranar sai yanke jiki tayi a gurin ta fad'i daga an kira ta tazo taga kaya, kayane sun ninka na Honourable sau uku a tsada da kuma yawa.




Cicci6ar Yadikko akayi aka kaita d'akin ta tare da d'ebo ruwa aka yayyafa mata, ajiyar numfashi tayi gami da bud'e idonta tana k'arema d'akin kallo da jama'ar d'akin kafin daga bisani ta lumshe idanuwan ta.




Washe gari Alhamis da wuri aka shirya Aysher dan tafiya kano, motoci guda 5 aka turo daga kano dan haka sunyi komi nasu cikin shiri da tsari suka shirya kowane mota mutum 4 za'a dauka baya mutum uku gaba kuma mutum d'aya, wani abin burgewa shine garar da Baffa Usman yayiwa 'yarsa dan kuwa yayi k'ok'ari ba kad'an ba.




Motar da Aysher take ciki ita da Fatima ne da k'anwar mahaifin Aysher Adda Kubura, Sai gaba aka saka mutum d'aya, Ahmad yanata kiran wayar Aysher yaji muryan ta amman kunya ya hanata d'auka tanajin ringing d'in wayar a cikin jakarta.


Dan haka Ahmad yakira Mudansir dan yazo d'aukar Amarya a cikin motar sa ma aka saka Amarya, dan Ahmad yace bai yadda kowa ya d'auko masa matar sa ba sai Mudansir saboda tuk'in sa kawai ya yadda dashi.


Cikin salon tsokana Mudansir ya d'auki wayar tare da fad'in"Ango kasha kamshi munzo ance anfasa bamu amarya sai gobe juma'a"


"Dan girman Allah Mudansir dagaske?"


"Kwarai kuwa gamu dai anata fafatawa munce yau ango yakeson matar sa a kano"


Cikin muryan lallashi Ahmad yace"Abokina kataima ka a bada ita yau tunda har na wakilta ka kazo kayimin iyaka k'kokarin ka pls kamar ina gurin, ni yanzu je ka nemo min ita ka had'ani da ita a waya yau kwata-kwata banji muryan ta ba wani iri nake jina."




"Sannu rasa kunya idan baka da kunya, ni inada ita, bazan iya zuwa neman Aysher ba ka kwantar da hankalin ka tana mota na yanzu zamu taso da yadda Allah amman magana awaya kam ha hali saboda sai anyi siyan baki a Al'adance" Mudansir ya bama Ahmad amsa da hakan.


Tsaki Ahmad yayi kafin yace"Wannan al'ada yakamata a dainata tunda ba addini bane Allah ya kawoku lafiya" yana gama fadin haka ya katse wayar da alama ransa ya 6aci.








Sun sauka a kano da wuri dan haka bayan ankai Aysher da danginta masauki sunci abinci Umma ta aiko da wata Alkyabba, tace Aysher ta shirya a cikin ta dan za'ayi walima karfe 4.


Aysher tayi kyau cikin shigar kamar balarabiya kwaliyan da Fatima tayi mata mai sauki ne amman ta had'u.
Malama Jamila sulaiman (Ammi) ita aka dauko dan fad'a karwa. Tafara bud'e taro da addu'a kamar haka:- *INALHAMDULILLAH,NAHAMADAHU WANASTA'INUHU,WANASTAGFIRUHU,WANA'UZU BILLAHI MIN SHARRI ANFUSUNA,WAMAN SAI'ATU,A'AMALUNA,MANYAHADIHLAHU FALA MUDLIL LAHU WAMAN YADLIL FALA HADIYA LAHU,WA ASH HADU ANLA'ILA HA'ILLALLAH WAHADAHULA SHARIKALAHU WA ASH HADU ANNA MUHAMMADU ABDUHU WARASULUHU,SALLALLAHU WA ALAIHI WA'ALA ALIHI WA ASHABIHI WASALLAMAN TASLIMAN KHASIRAH*




YAN UWANA ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI TA'ALA WABARA KATUHU,INAMUKU SALLAMA IRIN TA ADDININ MUSULUNCI!




kamar yadda kukasani ba mutaru a nan domin komai ba, face dan taron walimar auren Aysher da angon ta Ahmad wanda muke musu fatan samun zaman lafiya.






To Aysher nasiha ta gare ki da sauran mata baki d'aya shine ki kula da mijin ki, yi nayi bari na bari, kuma shi aure ki d'aukesa a matsayin ibada domin hakan ne zaisa kiyi hak'uri da juriya akan zaman gidanki.


Sanan basai na fad'a miki ba kasan cewar daga ganinki nasan ked'in mai tsafta ce saidai in k'ara miki tuni daki k'ara akan wanda kike dashi, sanan abu mafi wuya kuma mafi so shine kizama mai 6oye fushin ki da yafiya, karki zama mace mai gaba da mijinta in yamata wani abu, kizama mai taushin hali, kuma banda rainuwa, duk k'ank'antar abu mijin ki yakawo kizama mai yaba masa koda ba haka bane a zuciyarki, domin zaiji dad'i da karfi gobe yakawo wani, sannan Allah zaiyi farin ciki dake a ranar gobe k'iyama.


Mafi akasarin mata sai kiga mazajen su sun zauna dasu tsawan shekara goma sha suci dasu, su sha dasu amma rana d'aya in magana ta taso sai ace mekata6a mun to wallahi 'yan uwana mata mukiyaye domin Manzon Allah S.A.W lokacin dayaje sama yaziyarci gidan wuta yaga mafi yawan su mata ne, sanan an tambaye sa, meyasa mata ye sukayi yawa a wuta?
Abun da yace"shine:-


*Suna sa6awa mazajen su.*


*Suna yawan tsinuwa.*


*Suna bayyana saraici.*


Dan haka mata mukula wallahi duniya fa ba gidan zama bane kamar yanda kake zuwa bak'unta in kagama adadin kwana kinka kakoma to haka kake zaune duniya, sannan babban tashin hankalin mu yanzu yanda mutuwa bata mana alama kana tsakiyan rayuwar ka sai kajika kwatsam a cikin kabari, an tashi da kai amma kan dare ka kwana a cikin kabari.


Karna cika ku da surutu domin in zan kwana bazan gama ba.


Amma jan kunnen da zanyi mana shine kiringa tausasa muryarki yayin da kike cikin bacin rai, ko kuma karkiyi magana sai kin huce domin babu alkairi acikin maganar da za a fad'e ta cikin fushi.






Mata dan Allah mudena sa turare in zamu fita haramun ne duk namijin daya ji k'amshin kuma ya burge sa to kina da lefin zina dai-dai kuke da wanda yayi, dan Allah akiyaye, kituna wanda fa kikayi domin kibirge su wallahi randa kike cikin azaba ba mai iya cetan ki suma takansu sukeyi.


Mata murike iyayen muji duk da ba a musu gwaninta amma a fita hakin su, arike su kamar 'yan uwa.


Sanan mata kunga shigan dakukeyi to wallahi kuyi hankali, shiyasa yanzu matan aure idan kuka fita kiga maza na muku magana kamar 'yan mata, sabida irin shigan 'yan mata da kukeyi kizama mai 6oye surarki, shiyasa a yanzu bamu da daraja a idan duniya sabida tsiraicin mata abayyane yake ba abinda ba a sani ba ko ba a ganiba akiyaye.


Abu na karshe kunga tsinuwa to wlh kubari domin duk gidan ma da ake tsinuwa, albarka basa zuwa gurin, katsinewa d'anka ko kace Allah tsinewa wane bakyau yana kai mutum jahanna ma mukiyaye kuma muyawaita sadaka.


Gamu mata munfi maza wahala ko gun haihuwa, rainon ciki, raino bayan haihuwa matsalolin rayuwar aure amma ace munyi sakacin da zamushiga wuta, to dan Allah mukiyaye.




Allah yarabamu da Jahannama, inawa duk 'yan group dina ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA fatan Alheri, Allah kasa dukkan mu 'yan Aljanna ne, ka k'ara shirya mu kan dai-dai ameen.




Sannan kuma 'ya'yanki ki koya musu ladabi da biyayya, su dunga girmama na gaba dasu, ki nuna musu suyi da'a ga Allah da manzonsa, sannan sai iyayensu.




Ki koya musu yadda za suyi zumunci da tausayin junansu. Ki kassance mai yiwa mijinki addu'a dan samun bud'i ki rok'i Allah ya d'aukaka mijinki, zuriyarki, d'aukakar addini, ki zamo mai k'yakk'yawan mu'amala da mak'otanki


Aysher ina so ki zamo matar k'warai abin alfahari a gurin mijin ki domin shine Aljannarki shine abin alfaharin ki.


Zan tak'aitane sabida lokaci, Aysher Allah yabaku zaman lafiya keda angon ki kula da addini Allah ya Albarkaci Auren ku da zuri'a d'ayyiba. Ameen Allah maida kowa gidan sa lafiya




*WASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH*




Addu'a akayi kafin aka tashi walimar bayan anyi rabon abubuwa na biki.




Nasiha sosai masu shiga jiki da zaman takewar aure Ammee Jamila tayi ma Aysher.


Aysher kuka take tayi cikin alkyabbar ta Ahmad kuwa sai kiranta awaya yakeyi harya gaji da nemanta, yafara kiran na K'anwarsa ta sanar masa suna gurin walima kuma ba damar d'aukar waya, rok'onta Ahmad yayi da cewa"ta taimaka masa da daddare ta had'ashi da Aysher a waya idan ba haka ba wallahi zai shigo gidan har inda matar sa take sai dai a ce masa yayi rashin kunya"


Dariya tayi kafin tayi masa alk'awarin had'asu da daddaren.........








MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/27, 9:41 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*






Page 55-56






Ahmad yana zaune cikin abokan sa (A gidan su Mudansir) amman hankalin sa gaba d'aya yana gurin matar sa dan haka wayar Amatullah k'anwarsa ya kara kira yaji shiru, mik'ewa yayi yafito daga gidan su Mudansir d'in batare yayima kowa magana ba ya mike yabar gidan, kai tsaye motar da yake amfani da ita, tun bayan dawowan sa (daga saudi'a) ya nufa bayan ya shiga yajata bai tsaya a ko'ina ba sai gidan Mahaifinsa.




Ku tsawa yakeyi ta ko'ina abokan wasa suna ta tsokanar sa da cewa"Ango kasha kamshi", bai kula da abinda suke cewa ba kai tsaye falon Mahaifiyarsa ya shiga yana zazzare ido sai da ya tabbatar Umma bata falon sai wasu danginta, hankalin su yana kan kallo basu lura da shigowar shi ba dan haka yayi amfani da wannan damar cikin zafin nama ya shige d'akin da yake tunanin nan aka sauke matarsa.


Aikuwa yayi sa'a dan kuwa a d'akin Umma dake falon k'asa akayi masu masauki, dan kuwa Ahmad yana bud'e k'ofar yaji wasu mata suna fulatan ci, dan haka yajuya da sauri.


Dole bayadda Ahmad zaiyi a wannan ranar bai ga Aysher ba, ya cika fam ya k'ullaci Amatullah k'anwarsa (Ahmad ba hak'uri)







**********
Washe gari dinner za'ayi daga nan a wuce da amarya gidan ta, da daddare kowa ya gama shiri 'yan uwa da abokan arziki duk an tafi.




Hakik'a dinner ya yi kyau Amarya da Ango sun had'u ba k'arya, anci, ansha da abubuwa da aka tanadar domin taron.


K'arfe tara aka fara d'auko mutane ana dawo da su gida, Ahmad mikewa yayi ya kalli Amaryan sa cikin shauk'in so da k'auna yace"Ina zuwa kijirani tare zamu koma ba zaki bi su Aunty Khadija ba (K'anwar maman sa)".
Kai Aysher ta d'aga masa dan bazata iya mishi magana ba saboda tunda aka shigo Hall d'in yake rik'e da hanun ta duk inda zasuje har gurin fita rawa yak'i sakin hanun ta, ita kuma kunya take ji duk iyayen su ne a gurin.
Saboda haka taji dad'in wannan fita tashi daya ce zaiyi saboda duk a takure take.




Cikin taron ta kutso kai tsaye gurin Aysher ta nufo waya tacire a kunnen ta, takalli Aysher tace "Ahmad yace kizo muje ta wancan k'ofar kutafi".
Waigawa Aysher tayi taga ba kowa a kusa da su duk an fita waje dan komawa gida, ganin budurwan yarinyar da ankon dinner a jikinta yasa Aysher mik'ewa tsaye, budurwan tace" Laaa naga kinayin abu sanyi-sanyi ko dan baki gane ni bane sunana Safiya daga Gombe mukazo ni family yaya Ahmad ne.




Tunawa da Aysher tayi cewar Ahmad suna da family a Gombe yasa ta mik'ewa cikin kwarin jiki suka bi ta hanyar da budurwan ta nuna musu, suka fice (Hanyar ba jama'a kwata-kwata)




Wani had'ad'd'iyar mota budurwan ta bud'e ma Aysher gidan baya ta shige da sauri cikin k'warin gwiwa danjin kamshin turaren mijinta a cikin motar, zama tayi batare da takalli na kusa da ita ba, domin kanta yafara mata ciwo saboda hayaniyar jama'a da kuma gajiya, budurwan ta bud'e gidan baya ta shiga direba yaja motar sa ya figeta da gudu suka fice daga haraban hotel d'in.


Aysher sai da taga tafiya tak'i k'arewa idon ta daman a rufe yake dan haka ta bud'e a hankali takalli na kusa da ita, wani k'atoton mutum tagani ya zaro mata ido tare da saita kanta da bindiga yana mai yi mata nuni da cewar tayi shiru ko ya harbeta....................










MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/28, 9:11 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*




Page 57-58








A gurin dinner kuma bayan Ahmad ya gama abinda zaiyi ya dawo gurin zaman sa da Amaryan sa, wayam yagani Aysher bata gurin dan haka sai ya fara dudduba cikin Hall d'in amman duk bata nan gashi iyaye suna ta jira awaje zasu tafi su wuce da Amarya gidanta (Kamar yadda aka tsara).


Jin shirun Ahmad yayi yawa bai fito ba yasa akace Amatullah ta shiga ta kira shi iyaye zasu zo su wuce da Aysher gidan ta ana jiranta a waje.


Amatullah ganin Ahmad tayi duk a firgice dan haka ta fara tambayar sa da cewa"Yaya lafiya kuwa, ina Aysher ana jiranta dare yanayi?".


Bakwa tare da ita ne Amatullah? (Ahmad ya tambaya cikin rawar murya)


A'a yaya bama tare da ita daman kasan ai yadda aka tsara, tun a gida cewar iyayen ta zasu zo gurin dinner a wuce da ita. Ni ban ganta ba bata waje ma at all, yaya da ace tafita da zamu ganta a..........




Cikin tsawa Ahmad ya dakatar da ita kafin yace"Kina nufin bata nan?."




Kai ta gyad'a masa dan ta tsorata da yanayin sa.


Da sauri Ahmad ya fice, duk inda aka tunanin za'aga Aysher anduba bata gurin, har gida ankira a waya bata je ba. Toh Aysher ina ma tasani a garin cewar K'anwar umma, nan da nan hankali yatashi ba'aga amarya ba.




Kuka danginta suka fara yi, Fatima tana salati tana fad'in waye zai musu haka? Dan Allah kar a cutar mata da 'yar uwa.


Ana cikin haka Ahmad ya yanke jiki ya fad'i ko motsi bayayi, nan guri ya k'ara rikicewa da koke-koken mata da sauri Mudansir da wasu abokan Ahmad suka d'auke shi sai ZEEMAN'S HOSPITAL.


***********




Tafiya mai nisa sukayi kafin Aysher taji an tsayar da motar, wannan dai k'aton mutumin shine ya jawo Aysher ya shigar da ita wani gida mai shegen duhu, kwata-kwata babu alamar hasken wani abu waishi wutar lantarki a cikin gidan.




Wannan budurwan yarinya itace ta wanke fuskan Aysher da mari lokacin da Aysher tafara kuka tana rok'onsu dasu taimaka mata su mayar da ita gida...... Dan ubanki baza'a mayar dake gidan ba tunda kika shiga gonar mu (Budurwan ta bata amsa da hakan).




Wani d'aki suka jefar da Aysher kamar kayan wanki suka kunna mata wani fitila budurwan yarinyar nan tace" zamu tafi sai gobe zakiji dalilin zuwan ki gurin mu, za kuma kisan komu su waye". Muta fi Idi, suna gama fa'din haka suka kullo k'ofar da d'an mukulli suka fice.


Mikewa Aysher tayi a hanzar ce tafara kallon d'akin da take ciki, bakomai a cikin sai wata k'aramar tabarma, gefe guda wata k'ofa ce da sauri Aysher ta k'arasa k'ofar tare da bud'e k'ofar, ban d'aki ne (Toilet) dan haka a hanzar ce Aysher ta shige dan d'auro alwala tayi sallolin da suke kanta tare da rok'on Allah ya kawo mata agaji, dan kukan ma ya gagara zuwa idanuwanta sun bushe.........






Kuyi hak'uri da wannan.










MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[10/29, 7:50 PM] Zeetty: [10/29, 7:12 PM] Maman Hanan: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*




*Member's na mace mutum writers ina jin dad'in zama da ku Allah bar mana zumunci*





Page 59-60




Yanda Aysher taga dare, takasa bacci idon ta k'amas babu alamar wani abu waishi bacci.


Washe gari da sassafe suka shigo d'akin, 'yan mata ne guda uku harda budurwan yarinyar nan ta jiya saura guda biyun kuwa Aysher bata san su ba, d'aya dagaa cikin su tajawo kujerar roba guda d'aya dake falon ta zauna, fito tayi tare da mik'a hannuwan ta d'aya daga cikin 'yan matan ta ciro kwalin sigari daga jaka ta kunna shi tare da mik'awa wacce take zaune a kujerar, ta kar6a tafara zuk'a kafin ta fara magana cikin isa da tak'ama tafara da cewa"maraba da zuwa amarya wanda nake mata fatan k'are rayuwar ta a cikin gidan nan dafatan kin tashi lafiya cikin walwala da anna shuwa kamar yanda ko wacce amarya take kasan cewa washe garin tarewarta a gidan miji?, sai dai ke naki salon yazo da abin al'ajabi ( sigarin ta k'ara zuk'a kafin taci gaba da cewa"Sunana FEEDO ni budurwan mijin ki na da ne, ido Aysher ta zaro tana yunkurin mikewa amman takasa, kai Feedo ta gyad'a ma Aysher kafin tace"Ofcourse ni budurwan mijin ki ne da baya, kuma duk duniya babu wanda ya isa yarabani da Ahmad domin nafi kowa son shi hatta Uwar daka kawoshi duniya.




Dan haka za'a cigaba da kullemin ke a gurin nan, har sai ranar da kika zama mushe mu fitar da gawanki, ku bata abincin ta taci (ta k'arasa fad'in haka tare da mikewa ta ficewa daga d'akin).




Aysher tana kallon su takasa cewa komai, sai binsu da ido kawai takeyi, budurwan data yaudari Aysher jiya itace ta matso kusa da Aysher hanun ta d'auke da wani roba ta ajiye a gaban Aysher suka juya dan barin d'akin.




Roban abincin Aysher ta bishi da kallo kafin ta bud'e, Alala ce guda uku da manja da yaji, bayadda Aysher zatayi haka ta wanko hanun ta, ta fara cin abincin dan tsananin yunwar da takeji, alala guda ukun nan da Aysher ta cinye ba inda yaje mata ga cikin ta da ya k'ulle saboda ruwan da ta bankawa cikinta, dan haka kwanciya tayi akan tabarman d'akin tana dafe da cikin ta na salati saboda wani irin murd'awa da cikin nata yakeyi, tana daga kwance tafara ta mik'e da sauri ta nufi band'aki tafara kwarara amai, duk alalar da taci yafita yabar cikinta, dakyar ta yunk'ura ta koma d'akin tana dafe bango, kan tabarman ta koma ta kwanta tana murk'ususu.
[10/29, 7:50 PM]

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads