Showing 3001 words to 6000 words out of 34154 words
Chapter 2 - ZUBAR HAWAYE Complete Document Writing By Maman Hanan.txt
kibani guri saura kwana 3 ayi saukar kowama yahuta"
Dagudu Aysher taba gidan dan gani takeyi kamar yadikko xata iya kai mata bugu.
Yarbingel takalli yadikko tace shawarar dana baki da ita zakiyi amfani bari idan zankoma zanzo nakarbi hoton a sakata cikin hotunan yan matan daxan tafi dashi abuja.
[10/9, 9:54 PM] Maman Hanan: πππππ
Ahmad yana zaune a falon innawuro suna taba hira yau asabar ba aiki.
Alh lawan yana zaune suna kallo gefe guda suna taba hiran saukar su Aysher da za'a gabatar gobe a makarantar NURUL HUDA
Alh.lawan ne yace zan bata gudunmawa sosai kuwa dan yarinyar tanada kokari bansan maiyasa aka turota aiki gidan nan ba dan mahaifinta naga yanada rufin asiri dai-dai gwargwado
Inna wuro tace kasani ko sunada wata matsala ta cikin gidan Alhaji.
Alh.lawan yace hakane kuma amman ina sha'war dabi'unta shisa ko kin bar yaran nan a gurinta hankalina baya tashi sam nasan yarinyace mai amana gata da halin manya.
Ahmad dayake jin hirarsu jin yadda ake yabonta yayi tsagal yana cewa a ina take Baffa
Innawuro tace nan gabanmu kadan gidansu yake gobe ne saukar karatunta ai duk zamuje tunda ba makaranta kaga hoton sticer dana buga mata kalleta kaganta kyakkyawa da ita takarasa fada tare da bama babban yarta Nafisa wayar tamikawa Ahmad.
Dammm kirjin Ahmad yabuga yayinda idanuwansa suka sauka akan wannan fuska ma'abociyar kyau da Haiba yadade yana kallon hoton kafin yakalli inna wanda hankalinta yake kan Tv yace"inna nima kibani guda d'aya zansa a bayan wayata"
Inna cikin mamaki takalleshi tace"Nabaka zakasa a bayan wayarka, daman manyan yara irinku suna amfani da sticer bayan waya ne"
Ga zahiri kingani idan zaki bashi kibashi banason dogon bincike cewar Alh.lawan
Inna tamike tadauko masa guda biyu akan friged dinta tabashi a nan take ya bude ya manna abayan manyan wayoyinsa guda biyu.
Cikin zuciyar inna cewa take banza bayakai zomo kasuwa mudai zamu gani.
Da daddare Ahmad kasa bacci yayi saboda tunanin aysher idonsa kuwa yakasa daukewa daga kallon hotonta dake bayan wayarsa
_Tabbas inason wannan yar kwai-kwai d'in soyayyar nata ma dabanne cikin raina zanbibiyeta har Allah yakai damo ga harawa_
Ahmad baya aikata zina amman ganin hoton Aysher yasashi canja tunani da cewa idan har zata sakar masa jikinta sujone to tabbas zaikwashe kairatin jikinta tsaf saidai kash daga gani ustaziyya ce tunda gashi sauka zatayima gobe amman badamuwa wuyarta yanganta yasan gidan su.
Can yayi murmushi daya tuna cewa a gidan daya sauka take aiki lallai takwana gidan sauki dan haka yadauko kwalbar codin dinsa ya kwan-kwade tas anan bacci yayi gaba dashi
MAMAN HANAN
[10/10, 11:55 AM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 7-8
*Allah sarki nagode da ziyararki gareni hakika bazan manta da 9-10-2017 ba Allah yabar zumunci nagode da yabawar dana samu daga gareki maman Amatullahi daga Rukuba barrack plateau state jos Sakhallau khair*
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP
Ranar saukar su Aysher Ahmad tare da mudan suka tafi dan Ahmad yagama bama mudan labarinta shima mudan din dokin son ganinta yake dan yadda abokinsa yake bada labarinta yaji sha'awar yarinyar da son ganinta yakamashi.
Gurin sauka yacika makil da jama'a mahaifin Aysher shima ya halacci gurin dan tunsanda saukar yarage saura kwana 3 yazo daga lagos.
Ahmad baiyadda sunzauna guri daya da Alh.lawan ba asalima tsayuwa sukayi a tsaye shida mudan yadda zasu hango daliban dakyau.
Fatima kawar Aysher itace tabude taro da karatun Alqur'ani sanda mudan yaganta ta6o abokinsa yayi yace"Ya akayi ne nawan ba ita bace wancan"
Ahmad tsaki yayi yace"mtswww Nawan kacika shirme bayan na nuna maka hotonta a waya koda yake time din naga alama kana sama"
Dariya mudan yayi kafin yace"Ohhh really ai lokacin naleka duniyar sahara"
Basu ankara Sukaji ankira Aysher Usman damare amatsayin Amiran makarantar kuma wadda tafi kowane dalibi tsafta da kokari.
Ahmad yakalli mudan yace"Shegen kasa yanzu zaka ganta zahiri ni bansan ma duk abinda ake gabatarwaba gashi har anzo bada kyaututtuka koda yake kaine kacikani da.........
Fitowar Aysher sanye da kalar ankon saukar da sukayi shadda Purple dinkin doguwar riga tasha aiki sanye da farin hijabi shine yadakatar da Ahmad daga maganar dayakeyima mudan
Wow what a beautiful lady gaskiya babyn nan tahadu she is xtreamly beauti.....bai karasaba yaji Ahmad yadaka masa tsawa tare da fadin Guys Watch ur mouth haba kacikamin kunne da she is beautiful so....so...and so toh wannan tafi karfinka kabarni nagama lafewata ka kwashi saura dan wallahi wannan baby akanta zan iya shige makadi da rawa zan iya kaiwa har cannn kaima kagane ai dan sha'awarta yashigeni dayawa....
Kai Mudan yafara girgizama Ahmad yana fadin "No nawan don't do this pls she is an innocent wallahi nacanja niyyata akanta nima kafin naganta a zahiri raina yabiya akanta but yanzu nahakura pls kaima ka hakura kabarmin ita mu dai-daita zan aureta.
Wani kallon *Baka isaba* Ahmad ya watsawa Mudan tare da bar masa gurin mota yanufa yashige yaja yatafi yabar mudan dan kafin su ankara antashi taron har an fara watsewa daga ganin yadda Ahmad Yaja motar zakasan cewa ransa a bace yake.
Dariya mudan yayi kafin yafada a bayyane cewa" Nasan halinka abokina kanason yarinyar nan dagaske nasan kai kanka bazaka cutar da ita ba nafadi hakan ne dan na gano abinda nakeso nagane dariya yayi yatare mai mashin yahau yamaidashi Apti.
πππππ
Haba Nura yaza'ayi kace min haka tayaya hankalina zai kwanta bayan kasan cewa idan har nafito takarar nan jama'a ido zasu sakamin makiya kuma sune nafarko da zasu tonamin asiri cewar banda aure.
Gaskiya banason aure a wani country dan haka zai iya zama koma baya agareni a harkar siyasa ta tunda kowa yasan matata ta farko tarasu kuma ansan cewa bani da wata matar zamanin yanzu baka damu da mutum ba amman yadamu dakai.
Wanda aka kira da nura shine yadafa kafadar abokin nasa yana fadin" calm down my friend yanzu nagano maka mafita....
Mafitar kuwa shine jiya a gidan cin abincin Hajiya.Falmata a Area 1 naji tana waya da wata mata cewar ta kawo mata hotunan yara guda 10 yan mata masu matukar kyau inajinta tana wayar amman nayi kamar banji abinda take cewa ba ayadda kuma naji tana magana kamar daga yola ne za'a taho mata da yaran dan haka ka kwantar da hankalinka dagaji yan matan da za'a kawo zasu zamo masu kyau amman ba wani cikakken ilimi dan haka kaga sai muje musameta kacikata da kudi tabaka hoto kafara zabar na aure kafin ayi duk abinda za'ayi da sauran.
Yakalli Nura tare da fadin kana ganin asirina bazai tonu ba ma'ana iyayen yarinyar bazasuyi dogon bincike akaina harsu gano matsalar danake tare dashi ba.
Nura yace "Haba Honourable Fulani basu da wani ilimi ballantana dogon tunani dazasu wannan shawarar ko binciken hakan akanka indai har zaka fitar da masu gidan rana toh angama.
Cikin farin ciki Honourable ya bawa abokinsa hannu suka tafa tare da mikewa a tare honourable yana fadin zo mutafi gurin Hajiya a Area 1 ba'abori da sanyin jiki dubu 100 zanbata yanzu a take....
*************
Hotunan Aysher wanda yadikko tabata kudi na musamman taje ta dauka guda uku sunyi matukar kyau yar bingel takalli Yadikko tace" gaskiya aminiya kinada jari a gidanki zantafi dashi yanzu gobe sammako zanyi zuwa abj idan har Allah yasa anzabeta sai kizo mutafi gidan boka hargitsa'u wanda dai muka saba zuwa gurinsa kinsan aikinsa kamar yankar wuka ne shizai mana aiki akan maigidanki yadda bazai mana musu ba idan anyukuro dan mijinki yanada kafiya ga naci akan karatu duk ya dora burinsa akan karatun yarinyar nan kamar itakadaice 'ya a gurinsa uwarta tatafi yawon dandi wai taje karatun jinya.
Yadikko tace"kedai Allah bar zumunci nagode da kokarinki gareni Allah kaiki lfy"
Har soro taraka yar bingel kafin takoma gida Aysher bata nan ta aiketa nan makota dan kartaji abinda suke tattaunawa akansa.
Hutun da Innawuro ta bata gobe ne zai kare.
_Yazata kasance tsakanin Aysher da Ahmad idan sun hadu_
_wane irin abu honourable yake dauke dashi_
_Shin hoton Aysher yana samun nasara a Abj_
*kukasance tare dani domin warware muku zare da abawa*
MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP
[10/10, 11:49 PM] Zeetty: [10/10, 11:10 PM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 9-10
*Duk wanda baiji tsoron Allah ba toh tabbas zaiji tsoron Abinda Allah ya halitta*
*Katuna kowane second daya wuce yana kusantar bawa zuwa ga mutuwarsa*
_Up up up yan group din Zauren littattafan hausa hakika ina alfahari daku zankuma cigaba da Alfahari daku nagode da addu'arku gareni_
_Admin Aunty jamila......Ammin Lagos Allah yabarku tare da oga ya Albarkaceku da zuri'a tagari_
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP
Aysher suna hutu a makarantar boko zata shiga s.s 3 dan haka
Ranar alhamis Aysher takoma aikinta dan a lokacin babanta yakoma lagos.
Tana zuwa dai-dai gate din gidan ta hangoshi yana zaune yana shan sigari tare da fesar da hayakin sararin samaniyya idanuwansu ne suka gaurayu da juna dasauri Aysher tadauke kanta cikin sauri takarasa shiga cikin gidan aranta tana cewa _Ohh ni ayshertu komeye yahada Inna wuro da wannan dan iskan oho dan naji fatima tacemin mamanta tace duk wanda yakeshan sigari dan iska ne_
Falon inna tafara sakai ta tarar da inna zata tafi aiki Aysher ta gaisheta inna tace "yauwa Aysher ya gidan, ga baba maiyimin wanke-wanke tadawo jiya daga ganin gida dan haka zataci gaba da aikinta kema zaki samu hutu nizan tafi idan kingama zaki iya zuwa gurin baba kizauna kafin lokacin daura abincin rana yayi idan kunkoma makaranta kuma Baba zata cigaba da girkin yanzun ma zatazo tadinga saka miki hannu a wasu abubuwa.
Aysher tace toh " Inna saikin dawo Allah ya tsare"
Inna tace "Ameen bawani matsala ko?..
Kamar aysher ta tambayeta wanda tagani tare da maigadi a waje saikuma tafasa ta gyada mata kai alamar bakomai.
A bangaren Ahmad kuwa yaji takaicin yadda Aysher tayi masa dakuma irin kallon datayi masa daga gansa kallo ne mai ciki da tsana da mamaki yakalli sigarin hanunsa aransa yace" Kodai dan wannan ne toh"
Take yaji sigarin yafita a ransa yajefar dashi yatake da kafarsa.
Ohh yausu Aysher meya rikitata haka bata gaishe da Baba ba tashige cikin gida _cewar maigadi_
_lallai nita gani ta firgita_ Ahmad yafada aransa wani bacin raine ya ziyarci zuciyarsa yakalli baba maigadi yace"Baba wato kuna shiri sosai da ita"
Kwarai kuwa ai Aysher yarinyace tagari duk sanda tazo nan zata gaisheni idan ta tashi tafiya gidama zatace Baba saida safe yaudai inagani akwai abinda yake damunta.
Ahmad baice masa komaiba yamike zaishiga gidan yaji horn Innawuro zata tafi gurin aiki baba maigadi yatashi dan bude mata gate lokacin Ahmad yasakai cikin gidan sunansa takira bayan tasauke glass din motar tace"Ahmad bakatafi school bane yau"
Yace"banda lecture sai 11 yanzuma shigowa nayi nashirya natafi"
Kanta ta gyada kafin tace okay Allah taimaka yace Ameen.
Taja motar tafice daga gidan.
Kai tsaye falon innawuro Ahmad yashiga tare da sallama Aysher dake goge dining table ta amsa tare da dago kanta tana ganin shine tayi saurin sauke kanta kasa batare data ce komaiba.
_Hakika ran Ahmad idan yayi dubu yabaci saboda itafa yau yayi loosing lecture nashi but gashi ko gaisuwa da alamar bazai samu gurinta ba_
Cikin batarai Ahmad yace"ke wace irin yarinyace baki iya gaisuwa ba kin wucemu awaje baki gaishemu ba nashigo baki yimin gaisuwaba.
Banza tayi masa taci gaba da aikinta
Mamaki ne ya lullube Ahmad dabadan yasan Aysher ba kurma bace dasai yace kurman ce.
Doguwar tsaki yaja tare da juyawa cikin takaici.
Wayarsa yadauka yakira mudansir
Mudan yana dauka yafara cewa"Kai saiyau zaka nemeni kahuce kenan naga ko school kazo kadaina nemana toh ya'akayi ne ko harka gama da itane nazo na kwashi sauran"
Wata uwar ashar Ahmad yamaka masa kafin yakatse kiran hanunsa ya dunkule kafin yakaima bango naushi _oh my God nakira Guy dinna yabani shawara but yakara kunoni tayaya zan fahimtar dashi cewa taki yimin magana ballantana nasamu hadin kanta_
[10/10, 11:26 PM] Zeetty: A bangaren Mudan kuwa dariya yafara yima Ahmad yace" Nizanyi maganin mai taurinka tare da fadin rai Nawan saikayi kuka akan wannan yar fulanin dan daga gani kafada dayawa"
πππππ
A Abj kuwa Yarbingel tana sauka gidan Hajiya falmata.
Aranar data sauka tabata hotunan yan matan datazo dasu a washe gari Haj.falmata takira Honourable Mahmoud akan yazo yazaba ankawo.
*WACECE HAJ.FALMATA*
Haj.falmata asalinta yar maiduguri ce amman tazo abj saida abinci takeyi gefe guda kuma takasance kawalin mata (dillaliya)
Saboda akwai manyan yan siyasa da take kawoma yan mata dan fasikanci wasu kuma masu kudin tana kawo musu kyawawan yanmata ne daga garin Maiduguri (Shuwa), cameron,manbila da yola saboda masu kudin sunason auren kyawawa dan su samu yara masukyau farare masu kama da larabawa basu damu da ilimi ko rashin ilimin yarinya ba kawai dai su aureta idan yaso daga baya saita waye.
Haj.Falmata tana hada aure kuma tana hada lalacewa danhaka take samun kudi masu tsoka yanzu wannan hotunan da aka kawo mata duk neman masu bukatarsu takeyi bisa kudi masu tsoka kuma duk hoton yarinyar da akazo dashi da yaddar ita yarinyar ne da iyayenta ko marikanta.
Wannan kenan
***********
MAMAN HANAN
[10/11, 6:19 PM] Zeetty: [10/11, 6:15 PM] Zeetty: [10/11, 6:10 PM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
Page 10-11
*INDABAWA O.H.W Ina godiya maman Hanan tama sonku kamar yadda kuke sona love u more*
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
Hankalin Ahmad yatashi dan ganin yakasa samundaman yin magana da Aysher akwai ranar data taso aiki tafito tatsaya gaisawa da baba maigadi cikin fulatanci takemasa magana.
Ahmad yakalleta tare da fadin ni bazaki gaisheni bane? Yana magana yana busa hayaki (sigari)
Takalleshi a tsorace kafin tace"Minanate hausare sai fulfulde"
Ahmad yarasa abinda take nufi dahakan ita kuma tana gama fadin haka tasakai tawuce abinta baba
Maigadi shine yakalleshi yace"Tana nufin batajin hausa sai fulatanci"
Daman batajin hausar ne dagaske? Ahmad yatambaya
Baba maigadi yace"Aradun Allah bansaniba nidai bantaba jinta tayi hausa ba naga alamar ma kamar tsoron wannan abin hannun naka take _Yafada tare da nuna sigarin hannun Ahmad_
Yakara da cewa nikaina abin yana cutar dani dan ance duk wanda yake shakar iskar hayakin yafi wanda yake sha cutuwa"
Jefar da sauran sigarin yayi kafin yace'waye ya fada maka haka"
Maigadi yace"Wani likita ne dayazo"
Ahmad murmushi yayi yace" shikenan nadaina daga yau baka fadamin dawuri bane dabazan cutar dakai ba ita wancan yarinyar inane gidan su? Ahmad yafada tare da nuna hanyar da Aysher tabi.
Mai gadi yace "Aysher wai".
Ahmad ya gyada kansa
Maigadi yace nan ne gana kadan wajen shagon da aka chargin wayar nan yarinyace mai hankali sharrin matar ubanta ta hadu dashi dan wannan aikin datakeyi a gidan nan ubanta mahaifi baisani ba tana zuwa makarantar arabi da boko nima agurin maidakina naji.
_Tab wannan shine fadi ba'a tambayeka ba_ Ahmad yafada cikin ransa kafin yace" Tana zance kuwa ina nufin tanada samari?
Wani dariya maigadi yayi kafin yace"Ina zansan wannan Ahmadu amman natabbata tsaleliyar yarinyar kamar wannan bazata rasa saurayi ba"
Doguwar tsaki Ahmad yaja kafin yamike yashige gida mota yadauko yafita wata yarinya yakira yake shaida mata zaizo da daddare sudan debi current din juna ma'ana yanaso yaji dumin jikinta he is bored"
[10/11, 6:11 PM] Zeetty: ******************
Hon.Mahmoud yana duba hotunan babu wanda hankalinsa ya kwanta akanta irin Aysher dan haka kai tsaye yanunama abokinsa nura hoton shima dai yayi na'am da wannan kyakkyawan yarinyar dan haka Haj.Falmata suka nunama hoton Aysher akan cewa itace zabin Hon mahmoud.
Yarbingel wanda tayi masauki a gidan Haj.Falmata suka kira tazo dasauri.
Takwana gidan sauki dan wannan diyar aminiyata ce bata dawani matsala yanzutake aji biyar a sakandire tayi saukar qur'ani sati daya daya wuce _wannan shine bayanin da yarbingel tayi musu a sanda suka nuna mata hoton Aysher amatsayin wacce Hon.Mahmoud yazaba_
Jin wannan bayani daga bakin yarbingel yasaH Hon.Mahmoud farin ciki ashe baiyi zabin tumin dare ba.
Nan dai suka gama magana akan cewar zasu tafi a satin saboda gabatowar zabe dan Hon.bayason ayi zabe bashi da aure kuma zaben saura watanni takwas.
πππππ
*Al-qarya* multi-media nan Ahmad yaje ya rera wakarsata hiphop batare da sanin abokinsa mudansir ba dan yadaina nemansa ko school kuma Ahmad din yadaina zuwa he is not serious about his study at all ayanzu.
Wakar tasa tasamu karbuwa a gurin samari da yanmata matasa kai harma da masu aure fadi suke ai wakar *A.A HAMEED* yahadu ba kadan ba.
Kasan cewar wakar yayisa da salon soyayya da bege a ciki dan haka ma'abota soyayya suka afka cikin kogin son wakar.
Wani abin mamaki kuma duk yadda Ahmad zaiyi su hadu da Aysher yayi amman takasa bashi fuska yadaina shansigari a gurin maigadi yakuma daina zuwa makaranta saboda ita dan kawai yaganta su hadu amman shiru ba labari.
Ranar dai lokacin saura kwana 2 Aysher su koma school ranar juma'a da yamma Ahmad yaci kwalliya cikin manyan kaya na shadda kansa hadda hula idan kagansa ahaka kamar wani mutumin kirki.
Dayamma yatare Aysher a hanyarta takomawa gida cikin tsoro Aysher ta tsaya tana kallonsa.
Ahmad yarasa da wani yare zai mata magana dan gaskiya bazai iyafula tanci ba dan haka can wata dabara tafado masa dayatuna abinda innawuro tafada masa lokacin dayaji 'yarta Nafisa tana Faransanci cewa tayi _Ai yawancin yaran garin nan namu na yola sunajin french dan ana koya musu sosai_
Dan haka Ahmad yace bari yagwadata yaji yace mata"Bonjour"
A tsorace Aysher ta dubeshi tare da cewa" Comment Allez vous (yakake)
Yace"Je suis bien Normal (ina lafiya)
Aysher tayi shiru tare da juyawa dan cigaba da tafiya taji Ahmad yace"Est ce que ont peux etre des amies?
(Zamu iya zama abokai?)
Tace "Nom y'a pas d'amitie entre une fille et unbgarcon" (Babu abota tsakanin mace da namiji).
Yace"d'accord je peux etre ton grand frere? (Zan iya zama yayanki)
Cikin hanzari dan ganin mutane suna wucewa suna kallonsu Aysher ta bashi amsa da cewa"O.k je suis d'accord" (Ok nayadda). Ta fada tare da zurawa aguje dan karasawa gida.
Wow Tayadda am happy today.
Ahmad yafada tare da tafa hannuwansa yana dariya.
********
[10/11, 6:19 PM] Zeetty: Ahmad cikin kwanaki kan-kani yayi suna ta ko'ina idan kazagaye garin yola saidai kaji wakar A.A Hameed yana tashi.
Alh.lawan baisan abinda yakefaruwa ba shidai yaji har yarinyarsa Nafeesa tana maganar wakar A.A Hameed dan tana yawan jinsa a gidan radio
Kaca-kaca Ahmad sukayi da Mudansir akan wakar daya fitar dan ran Mudansir idan yayi dubu ya baci.....
MAMAN HANAN
[10/12, 7:48 PM] Zeetty: [10/12, 7:12 PM] Zeetty: π
ππ
πππ
ππππ
πππππ
ZUBAR HAWAYE
Page 12-13
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP
Hakika A.A Hameed yayi suna agarin Yola da kewayensa 'yan mata kuwa sukace idan bakayi bani guri gurin tururuwan zuwa gurinshi a school wadan da sukasan shi yayi wakan kenan.
Wanda basu saniba kuma ido suka xuba sunatunanin hanyar da xasuga A.A Hameed.
Duk yadda 'yanmatan sukayi dan susan gidansu Ahmad yaki yadda yabasu fuska dan yana tsoron Alh.lawan