Showing 3001 words to 6000 words out of 28059 words
Chapter 2 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt
ne aljani Marhutul-Azab ya sauke su saurayi Hizmal a bakin kofar shiga dajin Baitul-shamshan,
Bayan ya sauka a turba ne sai kowa ya yunkura ya sauko ƙasa,
A sannan ne kowa yasha jinin jikin sa bisa yin arba da yadda farkon shiga dajin Baitul-shamshan yakasance,
Duk da kasancewar a wannan lokaci dare ya tsala babu abinda kunne keji face kukan tsuntsaye da kananan dabbobi,
Jaruma Husnaila ta katse shirun da wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya a karo na farko tace"ya abokanan tafiya ta ahalin yanzu gashi mun iso dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu,
Kuma na ji a jikina cewa muna halitta ta farko da muka riga kowa zuwa wannan waje,
Shin yanzu mene ne abin yi?
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai ce kala'.
Sai daga bisani aljani Marhutul-Azab yayi''''' gyaran murya yace "yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wannan waje da muka iso shine waje mafi haɗari fiye da ko ina ,
Domin kuwa duka burikan sarakunan duniya, bokaye,da jarumai ya dogara da dajin Baitul-shamshan,
Ku sani cewa a subahin gobe ne nan da Sa'a uku Hibairu SARKIN SADAUKAI zai fito daga wannan daji na Baitul-shamshan,
Shawarar da zan ba mu ita ce mu dole mu kasance a cikin shirin ko ta kwana domin kowa ne lokaci sauran abokan gaba na iya iso nan,
Idan bamu mai da hankali ba zai zamo abin nan da masu iya magana ke cewa
Kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai kowa yayi na'am da shawarar.
Nan take kowa ya zare takobin domin shirin ko ta kwana,
Aljani Marhutul-Azab ya zare wani zabgegen Gatari a gadon bayan sa,Hizmal goye da yaro Humair makaho,sunaila da budurwar Nihla suka zare waɗansu takubba a damtsen su,
Kuma aljani Marhutul-Azab ya dunga rangadi yana kai komo a harabar wajen domin tabbatar da cikekken tsaro,
Ana cikin wannan hali ne sunaila ta dubi budurwa Nihla tayi gyaran murya tace da ita"yake wannan jaruma shin mene ne labarin rayuwar ki kuma mene ne dalilin daya sanya wannan azzalumar sarauniya ke farautar rayuwar ki? .
Ko da jin wannan tambaya daga bakin sunaila sai idanun Nihla suka suka ciko da kwalla,
Har ta buɗe baki da nufin ta ba wa sunaila amsar tambayar sai kawai a ka ji wani gurnani daga sararin samaniya,
Cikin hanzari kowa ya ɗaga kan sa izuwa sama domin ganin abin da zai wakana,
Nan take akayi arba da waɗansu halitta na sauka daga sararin samaniya,
Sannu a hankali halittun suka dunga sauko ƙasa,
Lokacin da suka sauka a turba sai aka fara kallon- kallo tsakanin su da su saurayi Hizmal,
Ba wasu ba ne halittun ba face aljani Haulatul-infal dauke da gimbiya Hushriba,sarki shazwan,sarkin bokaye Dargas,da tawagar matsafa biyar,
Halitta ta biyu kuwa ba wata ba ce aljani Darmanu ibn kauƙas dauke da sa sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar su
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma sunaila da yar uwar ta Hushriba,
Sarki sarki shazwan kuwa da saurayi Hizmal,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sa aljani Marhutul-Azab,
Gimbiya Hushriba ta taka da kafafun ta ta durfafi inda Sunaila ke tsaye yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma sannan taja ta tsaya,
Kana ta buɗi baki cikin matukar ƙiyayya tace"yake yar uwa ta kuma babbar abokiyar gaba ta har abada kiyi sani cewa nayi matuƙar baƙin ciki da na gano cewa mahaifin mu ya sanar da ke maganin da zai warkar dashi daga shirin da muka yi masa domin ki samu nasarar hawa Bisa karagar mulkin kasar mu,
Gashi Ni da dan uwana yarima zufair har kin riga mu mallakar yaro Humair makaho wanda shine kaɗai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Kuma kina tare da aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye inda anan ne za'a ɗauko tsumin tsafi da mahaifan mu zai sha ya warke,
Duk da waɗannan nasarorin da kika samu Ina mai tabbatar miki dacewa sun tashi a banza domin a yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ki kuma na mallaki yaro Humair makaho da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai jaruma sunaila tayi guntun murmushi mai tattare da takaici yace"kaicon ki yake yar uwa ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tunanin cewa zaki samu nasara akai na kwatar yaro Humair tare mallakar taswirar fadar Sarkin bokaye,
Ki sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA basa taɓa haɗuwa a waje guda, Domin kuwa keda ɗan uwan ki kuna kwaɗayin mulki ne domin ku zalunci talakawa,
Wanda akan dalilin hakan ku kayi yunkurin hallaka mahaifin mu, Ni kuwa ina so na warkar da mahaifin mu ne daga sihirin da kuka yi masa domin na samu nasarar hawa Bisa karagar mulki domin na gaji mulkin adalci irin na mahaifin mu,
Sannan da kike iƙirarin cewa za ki samu nasara akai na shin kin manta ne cewa a halin yanzu ina ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mahaifin mu,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hushriba ta cika da matukar baƙin ciki zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata kone,
Abangaren sarki shazwan kuwa bayan ya kammala karewa saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho kallo sai ya dube sa cikin matukar fushi yace "yakai Hizmal kayi sani cewa haƙiƙa ka aikata mini laifi mafi munin gaske sanadiyyar tseratar da rayuwar yaro Humair makaho da kayi wanda sanadin hakan ya jefa al'umma ta cikin gagarumar tashin hankali sakamakon GOBARAR DAJI,
Ina mai tabbatar maka da cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne,
Cikin ruwan sanyi ka damƙa mini yaro Humair domin na yanke maka hukunci cikin lumana ta hanyar daddatsa sassan jikin ka,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai saurayi Hizmal ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan daga bisani ya murtuke fuska yace"kaicon ka yakai wannan azzalumin sarki da bai damu da darajar ran ɗan adam ba face buƙatar kansa,
Ai a halin yanzu yaro Humair yayi maka nisa, domin bazaka taɓa samun nasarar hallaka sa ba matsawar ruhina yana tare da gangar jiki,
Da jin wannan batu sai takaici ya turnuƙe sarki Shazwan jikin sa ya kama tsuma,
Har ya sake buɗar baki da nufin ya furta wani abu sai aka ga wani haske na ratsowa daga sararin samaniya
Koda kowa ya mayar da duban sa zuwa ga wajen take aka yi ido biyu da wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance tare da wani dattijo mai karin shekaru zaune abisa kan wata dardumar sihiri.
Mu haɗu a GOGA SHA FAMA 2
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
BABI NA ƊAYA
Al'amarin su sarki uslaim kuwa lokacin da suka kammala fafata yaƙi da wadannan ayarin gwaggwan birrai,
Sai sarki uslaim yayi umarni aka kafa tantuna domin ya da zango, nan fa kuyangi suka shiga aikin dafa abinci domin yin kalaci,
Sarki uslaim ya shiga izuwa nasa tantin domin ya ɗan samu nutsuwa,
A lokacin boka ƙarzum ya kebance ana sa tantin domin shiga cikin halarar tsafin sa domin gudanar da bincike na musamman,
Lokacin da ya baje alƙalumman sihirin yafara gudanar da binciken,
Abinda yafaru tsakanin sarauniya Nuwairat da boka Jadwar gami da su saurayi Hizmal ne yafara bayyana a madubin tsafin,
Tun daga lokacin da waɗannan miyagun halittun ke biye da wannan kyakkyawar budurwa, har izuwa lokacin da su Hizmal ɗin suka samu nasarar ceton rayuwar ta,
Sa'adda boka Jadwar yaga wannan al'amari sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu wanda ya firgita duk wata halitta dake filin sansanin kuma ya yi sanadiyar farkawar sarki uslaim daga gyangyaɗin daya ɗauke sa,ya mike tsaye zumbur daga kan gadon sa,
Ya zare takobin sa ya ruga izuwa waje bisa tunanin cewa koda dakarun sumame ne suka kawo farmaki
Ai kuwa koda fitar sa ya ruga izuwa kofar tantin da yaga dakaru na yin tururuwar shig,
Da isar sa izuwa wajen ya tusa kai izuwa cikin tantin
Nan take yayi arba da boka Jadwar zaune a bisa buzun tsafi fuskar sa a murtuke babu annuri,
Sarki uslaim ya dube sa cikin fushi yace yakai ƙarzum shin ina dalilin wannan kururuwa taka,
Koda jin wannan tambaya sai boka ƙarzum ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace "Ka gafarce ni ya shugaba na kayi sani cewa bakomai bane ya sanya wannan ihu ba sai bisa Abin da na gani a cikin madubin tsafi na,
Abinda na gani ɗin kuwa shine abinda muka fito farauta wato yaro Humair makaho sun samu nasarar ceton rayuwar wata jaruma da ake kira da suna Nihla,
Ya shugaba na kayi sani cewa a halin yanzu bincike ya tabbatar dacewa wannan budurwa itace mace ta farko da SARKIN SADAUKAI Hibairu zai fara gani a rayuwar sa,
Kuma tabbas da zarar yagan ta zai kamu da matukar soyayyar ta
Haƙiƙa jaruma Nihla ita ce zata zamo tana sarrafa Hibairu tamkar yadda ake sarrafa masa akan kasko saboda tasirin soyayyar ta a zuciyar sa
Wani abu daya kara dugunzuma hankali na shine al'ajanin dake ɗauke da su saurayi Hizmal shine ke ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye face ya mallaki wannan taswira,
Kaga kenan koda ace mun samu nasarar saduwa da Hibairu kuma ya amince zai ceto gimbiya zarifa to fa tilas ne yazo muna ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Sa'adda sarki uslaim yaji wannan batu daga bakin boka ƙarzum sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe,
Ya dubi ƙarzum cikin alamun tsananin damuwa yace yanzu mene ne abin yi ya masanin ilimin tsafi,
Boka ƙarzum yace "Mafita ɗaya ce tabbas dole mu yi kokari mu riski su saurayi Hizmal,
Domin a halin yanzu kwanaki ƙadan ne suka rage su isa dajin Baitul-shamshan,
Kuma yanzu haka sarauniyar kyawawan duniya Nuwairat tare da boka Jadwar na biye da su,
Baya ga su ɗin ma akwai sarki shazwan tare da tawagar matsafan sun bazama farautar yaro Humair tare wata hatsabibiyar jaruma mai Hushriba
Wacce takasance yar uwa ga jaruma Husnaila da ke tare da saurayi Hizmal domin tserar da yaro Humair makaho
Tabbas masu iya magana na cewa A bari ya huce shine ke kawo rabon Wani
Kuma tabbas da zafi zafi akan daki ƙarfe domin a sarrafa shi yadda ake buƙata,
Tabbas wanda ya daɗe zai ga daɗau,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan zancen sa sai sarki uslaim yace "Haƙiƙa zancen ka dutse ne ya dodon bokaye,
Yanzu dazarar mun yi kalaci za'a cigaba da tafiya ba zamu yada zango ba,
Koda gama faɗin hakan sai sarki uslaim ya juya ya fice da ga masaukin boka ƙarzum,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki uslaim da tawagar sa a lokacin da suka kammala artabu da gwaggwan birrai,
A ranar da tafiya dajin Baitul-shamshan tazo tun sa'adda alfijir ya keto SARAUNIYA ABIDATUL-AULIYA ta kammala shiri tsaf
Ta zauna tana jiran matsafi shubairu, tsawon daƙiƙa hamsin tana zaune a cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai matsafi shubairu ya bayyana a gare ta a cikin siffar wannan kyakkyawan tsuntsun da bayyanar sa sai ya rikiɗa izuwa ainahin siffar sa,
Sa.adda Abidatul-auliya tayi arba dashi sai ta miƙe tsaye cikin matukar farin ciki taje ta tare sa fuskar ta cike da annuri,
Matsafi shubairu ya dube ta cikin wani murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wata ya mace mai hankali ya buɗi baki cikin tattausar murya yace"Barka da wannan lokaci ya sarauniyar kyawawan duniya Abidatul-auliya bintu shafwaz,
Abidatul-auliya fuska cike da annuri tace cikin zazzakar murya tace "Barka da zuwa JARUMIN JARUMAI kuma sadaukin mazaje,
Tun tuni na kammala shirin komai kai kaɗai nake jira domin gudanar da gagarumar tafiyar mu ta zuwa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI ko zamu samu nasarar cika burin mu na mallakar tsumin tsafi dake fadar Sarkin bokaye domin warkar da lalurar kuturtar tsagin jiki da ta same mu,
Dajin wannan batu daga bakin Abidatul-auliya sai matsafi shubairu yace"Ai bakomai ne yasanya nayi jinkirin bayyana a gare ki ba sai domin a lokacin da kika fito ba lokacin sa'a a tafiya ba ne,
Bisa hakan ya sanya na jinkirin ta amma yanzu batare da bata lokaci ba zamu fara wannan tafiya,
Koda gama faɗin hakan sai matsafi shubairu ya buɗe bakin sa ya karanta wadansu dalasiman tsafi yake wani Dankareran tsuntsun tsafi ya bayyana a wajen,
Shi dai tsuntsun tsafin yakasance yana kama da mikiya sai dai kan sa irin na batoyi ne,
Koda bayyanar tsuntsun sai matsafi shubairu yayi wa sarauniya Abidatul-auliya nuni da ta hau bisa tsuntsun,
Batare da bata lokaci ba ta hau ta zauna, Shubairu yayi koyi da ita,
Kawai sai tsuntsun tsafin ya kaɗa fuka -fukan sa ya tashi izuwa sararin samaniya ya na mai keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran tare da matsafi shubairu daya bayyana a agare ta da siffar kyakkyawan tsuntsu.
Lokacin da sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da su yaro Humair makaho,
Sai suka wanzu suna tsala gudu a cikin gajimare bisa kan Dardumar sihiri
Tafiyar Sa'a biyu da daƙiƙa hamsin kacal suka yi su na wannan gudu,
Su na cikin wannan tafiya ne sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tayi gyaran murya tace "yakai Jadwar shin nan da wani lokaci ne za mu iya cimma su saurayi Hizmal?
Da jin wannan tambaya sai boka Jadwar yayi shiru gami da runtse idanun sa,
Daga can sai ya cire kai ya dubi sarauniya Nuwairat yayi gyaran murya yace"ya shugaba ta haƙiƙa cimmu su a wannan lokaci abu ne mai matukar wahalar gaske domin kuwa aljanin dake ɗauke dasu shine aljani mafi tsananin karfin gudu a cikin jinsin aljanu,
Sai dai duk da hakan akwai yiwuwar zamu iya cimmu su a lokacin da zasu yada zango,
Koda jin wannan batu daga bakin boka Jadwar sai sarauniya Nuwairat ta cika da matukar farin ciki
Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru babu wanda yakara cewa kala,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Nuwairat da boka Jadwar akan hanyar su ta farautar budurwa Nihla wanda ke tare dasu yaro Humair makaho,
---
Kamar yadda gimbiya Hushriba ta tsara haka al'amarin yaksance wato tun da duku-dukun safiya fadar sarki shazwan ta cika ta batse da al'umma maza da mata yara da manya suka yi cincirindo babu masaka tsinke,
Duk inda Mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu,
Tamkar dandazon kiyasai, tsawon daƙiƙa Ɗari biyu da ɗoriya ana jiran fitowar sarki shazwan tare jama'ar sa,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka jiyo bugun tambura da bushin algaita,
Sai aka hango sarki shazwan tare da bakuwar jaruma Hushriba da tawagar bokaye,
Nan take fadar ta rude da shewa da jinjina kuma kowa ya mike tsaye daga wajen zaman su domin girmama ga sarki,
Sai da sarki tawagar sa suka zauna abisa kujerun su,
Bayan yan majalissa sun kammala kwasar gaisuwa,
Sai sarki shazwan ya mike tsaye daga kan karagar mulki ya fuskanci jama'a kuma fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara
Sannan daga bisani ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace"Da farko ina yiwa dukkan waɗanda suka hallara a wannan fada mai albarka barka da zuwa
Bayan haka kuma ina taya al'ummar kasa ta alhinin abinda yafaru damu na ibtila'in GOBARAR DAJI,
Yaku jama'a ta kuyi sani cewa ina mai farin cikin sanar ɗaku cewa a yau ne zanyi gagarumar tafiya domin samo maganin dazai kare wannan birni namu daga sharrin bayyanar SARKIN SADAUKAI,
Sannan ina muku albishir dacewa bakuwar jaruma Hushriba zata baku wani muhimmin sirrin tsafi dazai kare ku daga sharrin GOBARAR DAJI har izuwa lokacin da zamu dawo daga abin da suka fita ne ma
Sa'adda sarki shazwan yazo nan a jawabin sai fadar ta sake rudewa da shewa a karo na biyu kuma jama'a suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa.
Batare da bata lokaci sarki shazwan ya ɗora waziri Rufyan a matsayin halifan sa,
Bayan ya shiga izuwa gidan sarauta yayi bankwana da yar sa gimbiya sulairat,
Sai aka dunga aka fito izuwa wajen fada, batare da bata lokaci jaruma Hushriba ta buɗe bakin ta takaranto waɗansu dalasiman tsafi,
Tsawon daƙiƙa goma, tana gama rufe bakin ta nan take wani irin haske kore ya bayyana a wajen ya duka shiga jikkunnan jama'a,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa Ɗari ba ya shiga jikin duk wani mahaluki dake wajen,
Sannan haske ya dawo ya cure waje guda ya tashi izuwa sararin samaniya ya tsaya cak,
Sai gashi yana bayar da wani irin haske tamkar fitila,
Koda kammala hakan sai sarkin bokaye Dargas ya kwalla wa aljani Haulatul-infal,
Jim kadan sai ga sa ya bayyana a wajen ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Cikin azama sarki shazwan ya hau kansa ya zauna,
Sarkin bokaye Dargas, gimbiya Hushriba, sarkin yaƙi tare da tawagar bokaye biyar suka yi koyi dashi,
Cikin sadaukantaka aljani Haulatul-infal ya naɗa fuka-fukan sa ya luluƙa izuwa cikin gajimare,
Tun jama'a na hango