Showing 6001 words to 9000 words out of 28059 words
Chapter 3 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt
su har yazmana sun ɓace ɓat tamkar basu taɓa wanzuwa,
Wannan shi ne yafaru da su sarki shazwan bayan su saurayi Hizmal sun samu nasarar shiga gidan tsira,
Turƙashi ana wata sai ga wata, yanzu dai gashi manyan sarakuna
Sarki shazwan na birin zawatul-ifdal, sarki uslaim na birin Istanbul, sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran, sarauniya Nuwairat ta birin Garul-mausul.
Da matsafan duniya sun bazama farautar yaro Humair makaho domin saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Tabbas farautar wadannan abubuwa biyu dai dai yake da neman jaki mai ƙaho.
---
A birnin Rum dake yammacin duniya anyi wani gawurtaccen sarki da ake yiwa laƙabi da Baddadul-ulƙas
Sarki Baddadul-ulƙas yakasance gabjejen kato mai kirar samudawan farko mutum mai tsananin jarumtaka tagaban kwatance,
Ya bunƙasa a sihirin tsafi da da tarin dukiya,
Bokayen duniya da masu hasashe sun tabbatar dacewa a wannan ƙarni babu wani sarki mai da ya kai sa tarin dukiya dangin lu'u lu'u da zinare gami da dabbobin ni'ima,
Baddadul-ulƙas ya samu nasarar tara wannan dukiya ne saboda wata gasar jarumtaka da ake shirya wa a wani birni mai suna madinatul- shaja'a ma'ana BIRNIN MAZAN JIYA,
Fiye da sukaru goma sarki Baddadul-ulƙas ne ke cinye wannan gasa saboda jaruman da yake kawo wa sun kasance hatsabibai a fagen fama,
Duk jarumin da labarin jarumtakar sa ya shahara sai sarki Baddadul-ulƙas ya mallake sa kodai ta hanyar siyan sa da dukiya mai tarin yawa ko kuwa ta karfin tsiya,
Domin dai kawai ya saka sa a cikin gasar jarumtaka,
Duk sarkin da ya lashe gasar ana naɗa jarumin sa a matsayin GOGA SHA FAMA na shekara,
Wata rana sarki Baddadul-ulƙas na zaune a lambun shaƙatawar sa,
Sanye yake cikin shiga irin ta sarauta zaune abisa kujera ta ƙasaita gudanar da bincike bisa halarar tsafin sa abisa madubin tsafin sa,
Kwatsam sai yaga wani al'amari da ya sanya shi farin ciki kuma ya dugunzuma hankalin sa
Abin da ya sanya sa farin cikin shine akwai wani boyayyen jarumi da ake kira da suna Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Wanda yake a halin yanzu babu wani gwarzon mayaki kamar sa,
Abin da ya dugunzuma hankalin sa kuwa shi ne ta wace hanya zai mallaki SARKIN SADAUKAI Hibairu domin ya shiga gasar jarumtaka dashi,
Bayan cewa A halin yanzu Hibairu baya jin Yaren mutanen duniya baki ɗaya shi yana amfani ne da wani yare na musamman,
Wani abu da ya fi dugunzuma hankalin sa shine haƙiƙa sauran Yan uwan sa sarakuna abokan gaba zasu iya cin nasara akan sa matsawar su ka riga sa mallakar SARKIN SADAUKAI,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sa sai ya sake zurfa fa izuwa cikin Kogin tunani domin samun mafita,
Daga bisani ya samu mafitar, mafitar kuwa ita ce tun da a halin yanzu saura kwanaki ɗari biyu SARKIN SADAUKAI ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIn sa sannan ya fito daga dajin Baitul-shamshan to yazamana wajibi na yi ma za na ɗebi runduna ta domin na je bakin dajin Baitul-shamshan na kafa sansani har izuwa lokacin da SARKIN SADAUKAI zai bayyana
Fatana shi ne Hibairu ya samu nasarar cinye gasar jarumtaka ta duniya ya zamo GOGA SHA FAMA,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sai ya sake nutsawa bisa halarar tsafin sa domin yakara samun haske akan al'amarin,
Yana cikin wannan bincike ne sai kawai ya a bushe da dariyar farin ciki maral misaltuwa tamkar ba zai taɓa daina wa ba,
Bakomai ne yasan ya shi a cikin wannan farin ciki ba sai domin ya gano cewa HUBAIRU yaksance ɗa a wajen babban maƙiyin sa Barde Shabbaru
Wanda a halin yanzu yake bauta a ƙarƙashin masarautar sa,
A salin Shabbaru mutumin ƙasar Misra ne kuma sarki Baddadul-ulƙas ya farauto sa ne bisa yarjejeniyar cewa idan ya samu nasarar lashe gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA zai raba dukiyar da ya samu ya basa kaso biyu kuma zai nada shi wazirin sa,
Bayan Barde Shabbaru ya samu nasarar cinye gasar ne, sarki Baddadul-ulƙas ya ci amanar sa,
Kuma yayi umarni a hallaka matar sa domin bincike ya tabbatar masa dacewa jaririn da zata haifa ne zai kawo karshen mulkin sa,
Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yaga wannan al'amari sai ya sake cika da mamaki,
Amma sai ya tambayi kansa a cikin ransa yana mai cewa ya a kayi matar Barde Shabbaru ta rayu har ta haifi abinda ke cikin ta ?
Wani ɓangare a zuciyar sa kuma na cewa dashi yanzu ai zaka yi amfani da wannan dama ne wajen jifar tsuntsun biyu da dutse ɗaya,
Wato zakayi amfani da Barde Shabbaru wajen mallakar SARKIN SADAUKAI,
Koda cewar bata ganin bil'adama ballantana ya tuna wane mahaifin sa,
To amma soyayyar uba da ɗa ba wasa ba ce tilas zata yi tasiri,
Zaka samu nasarar sarrafa Hibairu yadda kake so har ya kai ga lashe maka gasar jarumtaka ta duniya,
Dazarar ka cimma burin ka sai ka hallaka su baki ɗaya da uba da ɗan na sa,
Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yazo dai dai nan a tunanin sa sai ya sake bushe da dariyar farin ciki tamkar bazai daina ba.
Tun a daren wannan rana sarki Baddadul-ulƙas ya fara shirya rundunar mayakan sa ta haɗar da dakarun bil'adama da aljanu haɗe da miyagun dabbobi
Alfijir na ketowa ya tashi hankalin rundunar sa ya durfafi dajin Baitul-shamshan,
Tirƙashi gaskiya masu iya magana da suka ce ba'a rabu da bukar ba an haifi habu,
Gashi duk waɗannan sarakuna da jarumai sun bazama farautar Hibairu tare da nasu hukumomin,
Jaruma Husnaila, saurayi Hizmal da aljani Marhutul-Azab suna tare da yaro Humair wanda shine kaɗai ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Sarauniya Nuwairat kuwa tana son kasance mace ta farko da Hibairu zai fara arba da ita domin ya kamu da ƙaunar ta domin ta iya sarrafa sa yadda take so,
Yanzu kuma ga sarki Baddadul-ulƙas wanda ya tawo tare da Barde Shabbaru mahaifin Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Domin yayi amfani da mahaifin na sa wajen mallakar sa,
To masu saurare sai muje zuwa Littafin na gaba domin muji yadda zata kaya tsakanin sarakunan duniya
Lokacin da tawagar sarki Baddadul-ulkas suka dauki hanyar da zata kai su izuwa dajin Baitul-shamshan,domin da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI.
Sai suka wanzu suna tsala Azababban gudu a bisa dawakansu,
Daya ke tafiyar ta manyan sarakai ce da suka yi shura a halarar tsafi sai ya zamana cewa,
Tafiyar da za'a yi ta a cikin kwanaki shida sai ayi a kwana biyu,
Kasancewar masu iya magana na cewa sarkin yawa yafi Sarkin Karfi dai yazamana cewa komai yawan abokan gaba da dakarun sumame,
Cikin abin da bai huce dakika ashirin ba ake hallaka su,
Wadansu ma cika wandonsu ke da iska domin tsira da rayukan su domin sun san cewa ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza.
Haka dai wannan tawagar ta wanzu tana ratsa duwatsu koramu haɗe kwazazzabai gami sarkakiyar bishiyoyi,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Baddadul-ulkas ya birnin Rum.
Gaskiyar masu iya Magana da suka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba.a je ba.
Akwana a tashi sai gashi jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI ya cika kwanaki ɗari uku da sittin da biyu,
Ma'ana saura kwanaki ɗaya kacal ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI,
A daren wannan rana ne aljani Marhutul-Azab ya sauke su saurayi Hizmal a bakin kofar shiga dajin Baitul-shamshan,
Bayan ya sauka a turba ne sai kowa ya yunkura ya sauko ƙasa,
A sannan ne kowa yasha jinin jikin sa bisa yin arba da yadda farkon shiga dajin Baitul-shamshan yakasance,
Duk da kasancewar a wannan lokaci dare ya tsala babu abinda kunne keji face kukan tsuntsaye da kananan dabbobi,
Jaruma Husnaila ta katse shirun da wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya a karo na farko tace"ya abokanan tafiya ta ahalin yanzu gashi mun iso dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu,
Kuma na ji a jikina cewa muna halitta ta farko da muka riga kowa zuwa wannan waje,
Shin yanzu mene ne abin yi?
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai ce kala'.
Sai daga bisani aljani Marhutul-Azab yayi''''' gyaran murya yace "yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wannan waje da muka iso shine waje mafi haɗari fiye da ko ina ,
Domin kuwa duka burikan sarakunan duniya, bokaye,da jarumai ya dogara da dajin Baitul-shamshan,
Ku sani cewa a subahin gobe ne nan da Sa'a uku Hibairu SARKIN SADAUKAI zai fito daga wannan daji na Baitul-shamshan,
Shawarar da zan ba mu ita ce mu dole mu kasance a cikin shirin ko ta kwana domin kowa ne lokaci sauran abokan gaba na iya iso nan,
Idan bamu mai da hankali ba zai zamo abin nan da masu iya magana ke cewa
Kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai kowa yayi na'am da shawarar.
Nan take kowa ya zare takobin domin shirin ko ta kwana,
Aljani Marhutul-Azab ya zare wani zabgegen Gatari a gadon bayan sa,Hizmal goye da yaro Humair makaho,sunaila da budurwar Nihla suka zare waɗansu takubba a damtsen su,
Kuma aljani Marhutul-Azab ya dunga rangadi yana kai komo a harabar wajen domin tabbatar da cikekken tsaro,
Ana cikin wannan hali ne sunaila ta dubi budurwa Nihla tayi gyaran murya tace da ita"yake wannan jaruma shin mene ne labarin rayuwar ki kuma mene ne dalilin daya sanya wannan azzalumar sarauniya ke farautar rayuwar ki? .
Ko da jin wannan tambaya daga bakin sunaila sai idanun Nihla suka suka ciko da kwalla,
Har ta buɗe baki da nufin ta ba wa sunaila amsar tambayar sai kawai a ka ji wani gurnani daga sararin samaniya,
Cikin hanzari kowa ya ɗaga kan sa izuwa sama domin ganin abin da zai wakana,
Nan take akayi arba da waɗansu halitta na sauka daga sararin samaniya,
Sannu a hankali halittun suka dunga sauko ƙasa,
Lokacin da suka sauka a turba sai aka fara kallon- kallo tsakanin su da su saurayi Hizmal,
Ba wasu ba ne halittun ba face aljani Haulatul-infal dauke da gimbiya Hushriba,sarki shazwan,sarkin bokaye Dargas,da tawagar matsafa biyar,
Halitta ta biyu kuwa ba wata ba ce aljani Darmanu ibn kauƙas dauke da sa sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar su
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma sunaila da yar uwar ta Hushriba,
Sarki sarki shazwan kuwa da saurayi Hizmal,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sa aljani Marhutul-Azab,
Gimbiya Hushriba ta taka da kafafun ta ta durfafi inda Sunaila ke tsaye yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma sannan taja ta tsaya,
Kana ta buɗi baki cikin matukar ƙiyayya tace"yake yar uwa ta kuma babbar abokiyar gaba ta har abada kiyi sani cewa nayi matuƙar baƙin ciki da na gano cewa mahaifin mu ya sanar da ke maganin da zai warkar dashi daga shirin da muka yi masa domin ki samu nasarar hawa Bisa karagar mulkin kasar mu,
Gashi Ni da dan uwana yarima zufair har kin riga mu mallakar yaro Humair makaho wanda shine kaɗai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Kuma kina tare da aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da taswirar fadar Sarkin bokaye inda anan ne za'a ɗauko tsumin tsafi da mahaifan mu zai sha ya warke,
Duk da waɗannan nasarorin da kika samu Ina mai tabbatar miki dacewa sun tashi a banza domin a yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ki kuma na mallaki yaro Humair makaho da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai jaruma sunaila tayi guntun murmushi mai tattare da takaici yace"kaicon ki yake yar uwa ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kike tunanin cewa zaki samu nasara akai na kwatar yaro Humair tare mallakar taswirar fadar Sarkin bokaye,
Ki sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA basa taɓa haɗuwa a waje guda, Domin kuwa keda ɗan uwan ki kuna kwaɗayin mulki ne domin ku zalunci talakawa,
Wanda akan dalilin hakan ku kayi yunkurin hallaka mahaifin mu, Ni kuwa ina so na warkar da mahaifin mu ne daga sihirin da kuka yi masa domin na samu nasarar hawa Bisa karagar mulki domin na gaji mulkin adalci irin na mahaifin mu,
Sannan da kike iƙirarin cewa za ki samu nasara akai na shin kin manta ne cewa a halin yanzu ina ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mahaifin mu,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hushriba ta cika da matukar baƙin ciki zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata kone,
Abangaren sarki shazwan kuwa bayan ya kammala karewa saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho kallo sai ya dube sa cikin matukar fushi yace "yakai Hizmal kayi sani cewa haƙiƙa ka aikata mini laifi mafi munin gaske sanadiyyar tseratar da rayuwar yaro Humair makaho da kayi wanda sanadin hakan ya jefa al'umma ta cikin gagarumar tashin hankali sakamakon GOBARAR DAJI,
Ina mai tabbatar maka da cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne,
Cikin ruwan sanyi ka damƙa mini yaro Humair domin na yanke maka hukunci cikin lumana ta hanyar daddatsa sassan jikin ka,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai saurayi Hizmal ya bushe da dariyar ƙarfin hali sannan daga bisani ya murtuke fuska yace"kaicon ka yakai wannan azzalumin sarki da bai damu da darajar ran ɗan adam ba face buƙatar kansa,
Ai a halin yanzu yaro Humair yayi maka nisa, domin bazaka taɓa samun nasarar hallaka sa ba matsawar ruhina yana tare da gangar jiki,
Da jin wannan batu sai takaici ya turnuƙe sarki Shazwan jikin sa ya kama tsuma,
Har ya sake buɗar baki da nufin ya furta wani abu sai aka ga wani haske na ratsowa daga sararin samaniya
Koda kowa ya mayar da duban sa zuwa ga wajen take aka yi ido biyu da wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance tare da wani dattijo mai tarin shekaru zaune abisa kan wata dardumar sihiri,
Mu haɗu a GOGA SHA FAMA littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Mansur Usman Sufi
GOGA SHA FAMA 2
BABI NA BIYU
Littafin yaki
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaki
Free book
Ba wasu ba ne face sarauniya Nuwairat tare da boka Jadwar dake farautar Budurwa Nihla domin su hallaka ta,
Domin Nuwairat ɗin ta samu nasarar kasance mace ta farko da Hibairu zai fara gani a rayuwar sa kuma ta samu soyayyar sa.
Nan fa sabon kallon kallo ya fara guda na tsakanin sarauniya Nuwairat da budurwar Nihla dake tsaye hannun ta riƙe da takobi,
Bisa mamaki a wannan karon sai sarauniya Nuwairat taga Nihla ta ƙura mata idanu babu tsaro ko fargaba a tare da ita duk kuwa da irin kwarjinin ta,
Abangaren jaruma Husnaila kuwa koda ta gama faɗin hakan sai yar uwar ta gimbiya Hushriba ta zare waɗansu tagwayen takubba guda biyu a gadon bayan ta ta falfala da azababban gudu izuwa kan ta, tana mai ihu da kururuwa mai firgitar wa, Koda ganin hakan sai sunaila ta falfala da gudun izuwa kan ta riƙe da takobi domin tarar juna,
Tamakar haɗin baki a lokaci guda jaruman kowane bangare sukayi kukan kura domin yin karon battar karfe,
Sarki shazwan da boka Dargas suka ruga izuwa kan saurayi Hizmal, Sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka ruga izuwa kan Budurwa Nihla,
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu suka tari juna,
Sarki uslaim da boka ƙarzum kuwa sai suka tari tawagar sarki uslaim domin ganin sun tseratar da yaro Humair domin shine abin buƙatar su.
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin jaruma sunaila da Hushriba,
Sarauniya Nuwairat,boka Jadwar da budurwa Nihla,
Saurayi Hizmal, boka Dargas, da sarki shazwan,
Aljani Marhutul-Azab da aljani Darmanu, sarki
Sarki uslaim, boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan,
A gabar shiga dajin Baitul-shamshan,
Sai yakin yazamo abin tsoro kuma tashin hankali ga kowa ne bangare.
Jaruman suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,
Ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihun mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya,
A bangaren jaruma sunaila da yar Uwar ta Hushriba kuwa,
Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi ta hanyar kaiwa juna sara da takubban su,
Cikin ɓakin zafin mama juriya da nacin tsiya,
Duk sa'adda takubban su suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da kara marar daɗin sauraro,
Babu abinda zai burge ka ga zaratan matan biyu sama da yadda suke kaiwa juna sara da suka tamkar jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba,
Abangaren sarki shazwan,boka Dargas da saurayi Hizmal labari yasha bamban,
Domin duk karfin damtsen zaratan sarakunan biyu sai yazamo ya tashi a banza.
Domin kuwa sun kasa koda lakutar jikin saurayi Hizmal da makaman yakin su.
Sai dai ga wanda yake kallon yadda artabun ke wakana zai iya fahimtar cewa ƙarfin damtsen Sarki shazwan da boka Dargas ya nun ka na Hizmal sau goma,
Saboda wasu lokutan idan su ka kai masa hari da takobin sa,
Idan ya sanya takobin sa ya kare sai kaga har durkushewa ƙasa yake yi,
Amma saboda da juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga ya taso sama ya mayar da martani.
Duk wannan fafatawa da akeyi tsakanin su Hizmal,