Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 28059 words

Chapter 6 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

374

Ads at the middle of Article

ganin hakan sai budurwa Nihla zaune bisa kan wannan zaki, tare da tawagar namun dajin Baitul-shamshan suka mara masa baya,


Saurayi Hizmal da sunaila suka hau bisa kan Aljani Marhutul-Azab,take kowa ya hau bisa kan abin hawan sa aka karawa sarki Baddadul-ulƙas baya a ka fara tafiya , domin durfafar hanyar da zata Sada su da birnin madinatul-shaja'a,





Mu haɗu a littafin GOGA SHA FAMA na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen labarin.


Dagaa mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.


Mansur Usman Sufi






Goga Sha Fama 3


Littafin yaki


Rubuta Labari


MANSUR USMAN SUFI


Sarkin Marubutan Hausa


Wthapp Number


08137237071






Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas,ya jagoranci tawagar matsafa,sarakuna bokaye da jarumai,


Tare da SARKIN SADAUKAI Hibairu,


Domin isa izuwa birnin madinatul-shaja'a don halartar gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,


Sai aka wanzu ana ratsa dazuka da tsaunuka


Babu sassauci,


Kai idan kaga yadda tawagar suke tafiya sai kayi tsammanin cewa gaba ɗaya sarkaunan duniya ne suka taru waje guda suke shirin yakar duniya baki ɗaya,


Ana cikin wannan tafiya ne sarauniya Abidatul-auliya ta dubi matsafi shubairu cikin alamun matukar damuwa tace "ya amini na shin yanzu mene ne makomar mu a wannan tafiya,


Yanzu muna ji muna gani haka sarki Baddadul-ulƙas zai dunga sarrafa musu kamar yadda zai sarrafa Hibairu,?


Wai shin ma Wane ne a cikin mu yake da tabbacin cewa Baddadul-ulƙas bazai ci amanar Hibairu ba?


Ko da jin wannan batu daga bakin SARAUNIYA ABIDATUL-AULIYA sai matsafi shubairu yayi murmushin karfin hali sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye yace"ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa Ni kai na na yiwa kai na waɗannan tambayoyi sai dai ban iya bawa kai na amma sa ba,


A halin yanzu bamu da wani zaɓi da ya huce mu bi sarki Baddadul-ulƙas domin ta wannan hanya ne zamu samu nasarar bayyana cika burin mu,


Domin a halin yanzu Hibairu tamkar farin ingarman doki ne a tsakiyar bakaken dawakai,


Abin nufi anan shi ne farautar sa abu ne mai matukar wahala da rabo,


Saboda kowa muradin mallakar sa yake a


Kawai dai abin da zamu yi riƙe a wannan tafiya domin samun nasara shine


Rike amana,gaskiya da tausaya wa ga wanda muka sani da ma wanda ba mu sani ba,


Sannan ƙoƙarin mu yakasance kullum cikin taimakon Hibairu,


Waɗannan abubuwan sune tabbatar nasarar mu idan mun riƙe su.


Lokacin da matsafi shubairu yazo nan azancen sai sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar farin ciki,


Daga wannan batu kowannen su yayi shiru suka shiga hirar da ta shafi rayuwa,


Kamar yadda ya wakana tsakanin su shubairu haka al'amarin yaksance,


Abangaren jaruma sunaila da saurayi Hizmal a in da sunaila ta dubi Hizmal tace"yakai Hizmal har yanzu kayi sani cewa har yanzu ina ji a jikina cewa tabbas zamu samu nasara a wannan tafiya,


Domin dai babu wani mahaluki da zai iya zuwa fadar Sarkin bokaye face yana ɗauke da taswirar dake hannun aljani Marhutul-Azab,


Duk da cewa a halin yanzu Ban San mene ne abin da zai kasance a birnin madinatul-shaja'a ba,


Shin Hibairu SARKIN SARAKAI zai iya cika sharaɗin da sarki Baddadul-ulƙas ya ginda ya masa ya cinye gasar jarumtaka,


Har ya yan mahaifin sa Barde Shabbaru Daga KANGIN BAUTA,


Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hizmal ya ce "Naji a jiki na cewa HUBAIRU zaiyi nasara a gasar jarumtaka


Hujja ta na faɗin hakan shi ne kada fa ki manta cewa HUBAIRU shine SARKIN SADAUKAI na duniya a halin yanzu babu wani jarumi mai karfin gaske kamar sa,


Sunaila ta ce"Ko da hakan amma kasan cewa Sa'a da rabo ake bukata a Kowa ne al'amari ba wai tarin karfi ko sihiri ba,


Komai karfin damtsen ka idan baka da Sa'a da rabo kenan kayi aikin banza,


Hizmal yace"Tabbas zancen ki dutse yake sunaila,


Amma ai Sa'a da rabo na tare da gaskiya da adalci,


Sunaila"tabbas zancen ka haƙƙun ne yakai Hizmal.


Amma a ɓangare sarauniya Nuwairat da boka Jadwar kuwa,


Nuwairat ce ta dubi boka Jadwar cikin damuwa da ɓacin rai tace "yakai abin dogaro yanzu gashi dukkanin shirin mu ya tarwatse yanzu ina amfanin tafiyar mu tare da tawagar sarki Baddadul-ulƙas,


Tun da budurwa Nihla ta samu nasarar fara yin arba da SARKIN SARAKAI,


Kuma a yadda alamu suka nuna tuni ya kamu da matukar kaunar ta,


Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi ya mai sunkiyar da kan sa ƙasa daga bisani ya ɗago da kansa ya dube ta cikin girmamawa, da kakkausar murya yace


"Ya sarauniya kyawawan mataye kiyi sani cewa har yanzu kina da damar mallakar HUBAIRU har ma ki sarrafa shi yadda kike so


Matsawar kina bukatar hakan to wajibi ne ki mallaki zoben sihirin dake hannun jarumi Hibairu ki sanya shi a hannun ki,


Domin duka sirrin zuciyar sa ya tattara a cikin wannan zobe,


Daga nan har izuwa lokacin da za'a kammala gasar jarumtaka a birnin madinatul-shaja'a,


Dole kisan hanyar da zaki bi domin ki ga kin raba Hibairu da zoben,


Ko da wasa kada kiyi yunkurin cewa za ki hallaka Nihla domin hakan zai iya kawo miki cikas wajen mallakar zoben,.


Sannan dole ne mu kasance a cikin shiri domin tayi a cikin abokanan gabar mu akwai masu muradun zoben.


Musamman abokiyar gaɓar ki sarauniya Abidatul-auliya,


Nan gaba zan sanar dake waɗansu muhimman abubuwa game da zoben.


Sa'adda boka Jadwar yazo nan azancen sa sai sarauniya Nuwairat ta cika matukar farin ciki maral misaltuwa


Har bata san sa'adda murmushi mai taushi ya suɓuce mata ba,


Amma a bangaren sarki shazwan kuwa ya shiga tattaunawa tsakanin sa da gimbiya Hushriba da sarkin bokaye Dargas akan hanyar da zasu ba wajen mallakar sarkin sadaukai a wannan tafiya,


Haka dai tafiya taci gaba da wakana kwanaki banin kwanaki, Mako banin mako,


Sai a wuni cire ana tafiya batare an yada zango ba,


A iya tsawon wannan tafiya soyayya da shaƙuwa ta kara shiga tsakanin sarkin sadaukai Hibairu da jaruma Nihla, sarauniya Abidatul-auliya da matsafi shubairu,


Sunaila da saurayi Hizmal,


Kuma ba a haɗu da waɗansu abubuwa masu cutar wa,


Koda yan fashi da darun sunane da miyagun dabbobi,


Domin tsananin yawa da kwarjinin tawagar kafin su haɗu da su suke cika wandon su da iska,


Kuma a wannan tafiya ne dukkan sarakunan suka samu nasarar bayyana bukatar su ta hanyar kamun ƙafa da yaro Humair makaho


In da kusan dukan bukatun sarakunan ya dogara akan tafiya izuwa fadar Sarkin bokaye,


Sarki uslaim domin ceto yar sa gimbiya zarifa,


Jaruma Sunaila, Hushriba, sarauniya Abidatul-auliya da matsafi shubairu dake buƙatar su shine mallakar tsumin tsafi domin samun waraka,


Aljani Marhutul-Azab kuwa domin ta ceto ruhikan kabilar su dake ajiye a cikin akwatin baƙin ƙarfe dake hannun Sarkin bokaye.


Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas ya cigaba da jagorantar tawagar sarakuna,bokaye,jarumai haɗe da matsafa domin halartar bikin gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA da za'a gudanar a birnin madinatul-shaja'a,


Sai yazamana cewa ana tafiya dare da rana Babu sassauci da yake harka ce ta gawurtattun matsafa cewa tafiyar da za'a iya a cikin kwana ashirin, an yi ta a cikin kwana shida kacal,


A ranar kwana na sha takwas ne da la'asar sakaliya aka iso kofar birnin madinatul-shaja'a


Nan fa kowa ya cika da matukar mamaki,


Abin da ya ba su mamakin shine yadda kofar shiga birnin madinatul-shaja'a takasance cike da zaratan dakarun tsaro na jinsin mutum da aljan, ɗauke da miyagun makamai.


Saboda da kwarjinin su bazaka iya tantance dakarun mutum da aljan a cikin su ba,


Duk inda Mutum ya kalla daga saman kofar da katangun birnin dakarun birjik Babu adadi,


Nan take wani gabjejen kato mai tsawo da kwarjini tamkar toran Giwa ya dako da kafafun sa izuwa inda suke.


A lokacin da sarki Baddadul-ulƙas ya fito daga cikin keken dokin sa,


Ya dube sa cikin ladabi kansa a sunkuya yace"marhaban da zuwa BIRNIN MAZAN JIYA ya


Dodon sarakai, hadari ma'anar duniya,


GOGA SHA YAƘI"gagarau uban kan garau,


Ka ci dubu sai ceto , ANNOBA DARI mai saukar da GOBARAR DAJI,


FARGABAR SADAUKAI,


Lokacin da badakaren yazo nan a kirarin sai sarki Baddadul-ulƙas ya sake jin izza gami da ƙasaita ta ƙara shiga cikin ƙoƙon kan sa,


Har jikin sa na tsuma


Ya dubi badakaren yace"An gaisheka yakai


Himaru haƙiƙa ka cancanci kyauta mai tsoka,


Bayan na samu nasarar lashe gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.


A wannan karon zaka samu adadin dinaren da baka taɓa samun kamar su ba,


Koda Gama faɗin hakan sai Baddadul-ulƙas ya yiwa wani badakare inkiya ta wutsiyar idanu.


Badakaren ya gabato da wata jakar fata,


Ya risina a gare shi,


Sarki ya umarce sa ya miƙa wa badakare Himaru ya karɓa ya buɗe jakar, aikuwa sai yayj arba da dinare masu yawa a ciki,


Nan take ya sakarwa sarki Baddadul-ulƙas wani ƙeƙashasshan murmushi wanda babu abinda ya ƙarawa fuskar sa face muni,


Kuma ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Baddadul-ulƙas.


Daga bisani ya ɗago da kan ya dubi waɗansu dakaru yayi musu inkiya da sannu,


Take zaratan dakarun su hamsin suka shiga wangane kofar birnin,


Sannu a hankali sai kofar ta buɗe aka kunna kai izuwa ciki, ana shiga nan fa kowa yakara cika da mamaki, yakama kalle kalle,


Bakomai ne ya bawa Kowa mamaki ba sai bisa ganin yadda birnin madinatul-shaja'a yakasance kasaitacce tamkar aljannar duniya,


Gine - ginen birni anyi su bisa tsari mai kayatarwa, gwanin ban sha.awa kowace unguwa kalar tsarin ta daban iri ɗaya sai !


Ko ina a tsaftace yake a birnin babu wajen da ake zuba shara ko kazanta,


Hatta manyan sarakuna dake cikin tawagar wato sarki uslaim,shazwan, sarauniya Nuwairat da Abidatul-auliya sai da suka re na kan su,


Domin sun tabbatar da cewa gaba da gaban ta aljani ya taka wuta.


A dai dai lokacin ne aka hango tawagar wani mutum ma'abocin sarauta ya durfafo inda ake tsaye,


Tun da ga nesa mutumin ya ƙura wa Hibairu SARKIN SADAUKAI idanu ko ƙiftawa baya yi,


Lokacin da ya karaso sai tari sarki Baddadul-ulƙas suka rungume juna daga bisani mutum ya janye jikin shi daga na sarki Baddadul-ulƙas suka fuskanci juna


Cikin kakkausar murya mutumin yace "Lale marhaban da zuwan sarkin sarakuna, baban attajirai da matsafa,


Sarki Baddadul-ulƙas ya dube sa yace"yakai Abu - Ɗariƙ ina Fatan


A tanadar mana dukkanin abinda muke da buƙata da ya danganci masauki,


Abin kalaci har izuwa lokacin da za'a kammala gasar jarumataka,


Koda jin wannan tambaya sai Abu-Ɗariƙ yayi gyaran murya yace"An tanadar komai ya shugaba na yadda ka bukata,


Sai dai a wannan karon tsarin gudanarwar gasar ya canza,


Ina da a wannan karon dole ne dukkan wanda zai shiga kallon gasar ya bayar da bayanan sa,


Sannan ya shugaba nayi mamakin yadda kake tafe da wannan tawagar haka,


Koda jin wannan batu sai Baddadul-ulƙas ya bushe da yar karamar dariya yace


"Wannan ai ba abin damuwa ba ne ya Abu-Ɗariƙ


Game da tambayarka akan tawagar da nake tafe da ni wannan bayani mai girma,


Nasan dai abinda kake muradi shine kana so kasan wane ne GOGA SHA FAMA da nake tafe dashi ko,


Ya Abu-Ɗariƙ kayi sani cewa haƙiƙa a wannan karon nazo da jarumin da babu kamar sa a duniya a halin yanzu


Ba wani bane jarumi na ba face HIBAIRU SARKIN SADAUKAI na duniya,


Ɗa ga Barde Shabbaru tsowon GOGA SHA FAMA na shekaru ashirin da suka gabata,


Koda jin wannan batu sai Abu-Ɗariƙ ya sake ƙura wa Hibairu idanu,


A wannan karon sai yaji kirjin da ya buga da karfi tsoro ya kama shi,


Don haka sai ya kawar da duban sa daga hubairu izuwa ga Baddadul-ulƙas cikin ladabi yace dashi


"Haƙiƙa kyan ɗa ya gaji Uban sa ya shugabana kayi sani cewa tun sa'adda da na hango nake yiwa wannan baƙon jarumi kallon sani,


Nasan cewa Barde Shabbaru bashi da aure ballantana nace ɗan sa ne na cikin sa domin tsananin kamannin su ya ɓaci tamkar an tsaga ƙara,


Amma ya shugaba na dama Shabbaru ya na da ɗa ne a boye ban sani ba?.


Koda jin wannan tambaya sai Baddadul-ulƙas ya yayi murmushin mugunta yace "Mu ƙara sa izuwa masauki za ki dukkan yadda al'ummarin yaksance,


Abu-Ɗariƙ ya risina yace an gama ya shugaba na yana Gama faɗin hakan sai sarki Baddadul-ulƙas ya koma izuwa cikin keken dokin sa ya hakimce,


Abu-Ɗariƙ ya shige gaba take aka sakarwa dawakai linzmai aka cigaba da tafiya.


Nan fa jama'a suka dinga bin tawagar sarki Baddadul-ulƙas da kallo cike da matukar mamaki da al'ajabi,


Abu na farko da ya basu mamakin shine yadda tawagar Baddadul-ulƙas takasance mai tsananin yawa, da ta haɗar da aljanu da miyagun dabbobin daji,


Abu na biyu da ya fi basu mamakin yadda suka ga fuskokin baƙin sarakuna waɗanda ba'a taɓa ganin fusakun su a halartar gasar ba,


Haka dai tsoho Abu-Ɗariƙ ya cigaba da jagorantar tawagar sarki Baddadul-ulƙas suka wanzu suna masu ratsa unguwanni gami da saƙo da lungu na birnin,


Tafiyar daƙiƙa saba'in a kayi aka iso wata ƙasaitacciyar unguwa,


Unguwar an jima ta manyan gine gine benaye Masu tsawon ainun,


Idan mutum ya ɗaga kansa sama sai yaga cewa tamkar benayen sun shige cikin gajimare saboda Tsawon su,


Hatta kayan ƙawa da zanen tambarin gidaddajin irin ɗaya ne sak gwanin ban sha'awa,


Duk inda Mutum ya kalla dakaru ne shirye shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban daban ɗauke da miyagun makamai suna ta kai komo domin tabbatar da tsaro,


A ta dai wannan unguwa ana kiran ta da suna


Manazil-tijjar


Bisa wani katafaren gida aka ɗauke su sarki Baddadul-ulƙa,


Tun kafin su karaso waɗansu samudawan dakaru suka wangame musu kofar birnin ana zuwa aka kunna kai izuwa ciki,


Duk inda Baddadul-ulƙas ya gifta da tawagar sa sai dai kaga dakaru, kuyangi,da bayi na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa Cikin ladabi,


Bayan an shiga ne sai a Kowa aka basa nasa masaukin,


Saurayi Hizmal, yaro Humair makaho da sunaila a bangare guda kowa da turakar sa,


Sarki shazwan, boka Dargas , sarkin yaƙi da tawagar bokaye a bangare guda,


Hushriba ,sarauniya Abidatul-auliya da sarauniya Nuwairat a sauki guda,


Sarki uslaim da tawagar sa,


Aljani Marhutul-Azab da boka Jadwar da matsafi shubairu da aljani Darmanu


Hibairu SARKIN SADAUKAI da budurwa Nihla,


Tare da tawagar dabbobi da aljanu da sukayi masa rakiya a masauki ɗaya ,


Sauki Baddadul-ulƙas kuwa masaukin sa daban,


Sai dai masaukin kowa yana bisa saman benayen ma bambanta,


Jim kaɗan sai ga waɗansu irin tsaka-tsalan kyawawan yan mata sun shiga rarraba abin kalaci da abubuwan sha da tanɗe -tanɗe a Kowa ne masauki.


Sai da aka shafe tsawon kwanaki huɗu ana gudanar da shirye - shiryen tunkarar gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,


A iya tsawon waɗannan kwanaki soyayya mai karfi ta ƙullu tsakanin HUBAIRU Sarkin sadaukai da budurwa Nihla,


Kuma Hibairu ya fahimci Yaren sauran mutane ainun, sai dai a Kowa ce rana sau ɗaya kacal sarki Baddadul-ulƙas yake yadda Hibairu ya gana da mahaifin sa Barde Shabbaru,


Tun a daren ranar da za'a gudanar da gasar jarumtaka,


Birin madinatul-shaja'a ya cika ya batse da al'umma manyan sarakai, attajirai, jarumai da bokaye sukayi cincirindo,


Kuka kuma a daren wannan rana ne aka aika da sunan dukkan tawagar dake tare da sarki Baddadul-ulƙas zuwa ga sarkin yakin birnin wanda shine ke kula da harkokin gudanar da gasar,


Lokacin da sarkin yaƙi abu-Damraz yaga jerin sunayen tawagar sarki Baddadul-ulƙas tare da jarumin da zai kasance wakilin sarki Baddadul-ulƙas wato SARKIN SADAUKAI Hibairu.


Sai ya shafe tsawon daƙiƙa goma yana nazarin sunayen,


Sa'adda ya ɗora idanun sa akan sunan hubairu sai yaji zuciyar sa ta buga da karfi, tsoro ya ɗari su a cikin ta.


Al'amarin da yayi matukar ba shi mamaki kenan yace a cikin ran sa,


Shin wane ne wannan baƙon jarumi Hibairu mene ne yasanya dukkan binciken da na gudanar bisa halarar tsafi bai bayyana mini shi ba.


Mene ne yasanya zuciya ta buga da na yi arba da sunan sa,


An ya kuwa wannan jarumi ba shi ne abin farauta ta ba?.


Amsar tambayar da ya ka sa bawa kan sa kenan,


Kawai sai ya dubi wani hadimi dake tsaye a gefen sa a durƙushe ƙasa bisa gwiwar sa cikin kakkausar murya yace dashi "yakai amirul-bait shin wane ne wannan jarumi kuma daga wace nahiya a ka taho dashi.


Ko da jin wannan tambaya sai Amirul-bait ya buɗi baki cikin ladabi yace"ya shugabana wannan jarumi da ake kira da suna Hibairu nayi leken a siri akan sa,


Abin da binciken ya tabbatar mini shi ne jarumin ya rayu ne a cikin daji tun yana jariri har ya cika saurayi,


Mutun ne mai ɗauke da abubuwan al'ajabi da jarumtaka,


Domin bokaye da matsafa haɗe da sarakai na yi ma shi laƙabi da SARKIN SADAUKAI


Domin bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu GWARZON MAYAKI kamar sa


Kuma dukkanninsu waɗannan sarakuna da ka gani da Jarumai sun biyo shi ne izuwa gasar jarumtaka domin ya cika burikan su,


Wani abu na mamaki da na gano ga me da wannan jarumi shi ne yakasance ɗa ne a wajen Barde Shabbaru wadda a duk shekarun da aka shafe ana gudanar da gasar jarumtaka ba'a taɓa samun gwarzo tamkar shi ba.


Ko da jin sunan Barde Shabbaru sai Sarkin yaƙi abu-Damraz ya miƙe tsaye zumbur daga kan kujerar sa a dubi amirul-bait yace dashi


Shin ya kayi Shabbaru ya kasance a raye har ya samu Haihuwar ɗa namiji,


Bayan cewa a sani na ya daɗe da mutuwa,


Tabbas wannan fa shi ake cewa ana wata sai ga wata,


Tabbas ba'a rabu da bukar ba an haifi habu yakai amirul-bait kayi sani cewa fiye da shekaru talatin barde Shabbaru ya cinye mai girma shaibat a gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,


Sarki yayi kukan baƙin wanda sai da ya kamu da rashin lafiya


Tsawon shekaru domin ya ɗaukar wa mahaifin sa alkawarin cewa sai ya zamo GWARZON MAYAKI na gasar jarumtaka,


Bisa hakan ya sanya ya bani wani sinadarin tsafi na sanyawa Barde Shabbaru a cikin barasa a lokacin da ake gudanar da shagalin nadin sarautar GOGA SHA FAMA,


Nayi mamaki da ka ce mini Shabbaru na raye Tabbas koda wani ya canza sinadarin dana sanya masa a cikin barasar ko kuwa waɗanda na umarta ne da aikin su ka ci amana ta,


Cikin biyun nan dole ɗaya ya faru.


Tsawon shekarun da aka shafe da faruwar wannan al'amari


Mai girma shaibat bai manta da wannan abu a zuciyar sa ba,


Bisa wannan dalili yasanya yasha alwashin cewa yar sa gimbiya haya'ul-nur


Ta sha alwashin sai ta cika wa sarki wannan buri na sa,


Yakai Amirul-bait kayi sani cewa ahalin yanzu gimbiya haya'ul-nur na cikin jerin sunayen jaruman da zasu fafata a gasar GOGA SHA FAMA,


Tabbas a halin yanzu a cikin tarko guda biyu,


Na farko shine yayin da sarki ya gano cewa HUBAIRU ɗa ne ga Barde Shabbaru zai tuhume ni akan aikin da ya bani na hallaka Shabbaru ya akayi ya rayu,


Abu na karshe shine tsoro na kada gimbiya haya'ul-nur ta faɗi a wannan gasa


Tabbas a tsakanin waɗannan abubuwa da na lissafa faruwar ɗayan su dai dai yake da na rayuwa ta


Haƙiƙa zama bai same ni ba matsawar Hibairu na numfashi a doran ƙasa,


Sa'adda sarkin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads