Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 28059 words

Chapter 4 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

406

Ads at the middle of Article

yaro Humair makaho dake goye a gadon bayan sa yana jin duk irin fafatawar da akeyi,


A bangaren manyan aljanu biyu kuwa aljani Darmanu da Marhutul-Azab,


Sun wanzu suna ba wa hammata iska yazamana cewa,


Suna yin ragas idan Darmanu ya samu nasarar kaftawa Marhutul-Azab sara a hannu sai kaga shi ma ya mayar da martani ,


Ko iya hargagin su ma ya isa ya firgita lahittun


Dake wajen ,


Amma a bangaren sarki uslaim da boka ƙarzum da tawagar sarki shazwan kuwa,


Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi,


Duk inda sarki uslaim ya sanya gaba sai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan ,


Ita kuwa budurwa Nihla ta zamo tamkar wata shaiɗaniya a tsakanin sarauniya Nuwairat da boka Jadwar,


Domin sun kasa samun nasarar murƙusheta


Al'amarin daya fusata sarauniya Nuwairat da boka Jadwar kenan, zukatan su suka kama tafarfasa tamkar zasu ƙone


Abu na farko da ya dugunzuma hankalin su shine yaushe Nihla ta samu wannan gagarumin karfin damtse,


Har su gaza samun nasara akan ta a matsayin su na zaratan Jarumai masu juriya da bajinta,


Sannan idan har aka cigaba da wannan artabu a haka zasu iya yin biyu babu,


Domin abinda zai faru shi ne dazarar ɗaya daga cikin abokan gaba ya samu nasarar kashe a bikin faɗan sa zai iya rigasu saduwa da SARKIN SADAUKAI,


Kai ga kenan sunyi aikin banza, kura da shan bugu gardi da kwace kuɗi,


Sa'adda suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗan su.


Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza.


Faruwar hakan keda wuya sai yazmana cewa a wannan karon su boka Jadwar suna haɗawa da bugu da kafa da kai sara da takobi,


Nan fa suka fara haɗawa Nihla jini da majina,


A cikin wannan fafatawa ne Nihla ta kai musu wani sara da takobin ta a kirjin su,


Adai dai lokacin ne sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka kai mata duka da ƙafafuwan su ɗia ɗin,


Bisa Sa'a sai suka dake ta a kirji da dukkan karfin su,


Saboda karfin dukan sai da Nihla tayi katantanwa a sama sau uku sannan ya kife ƙasa da ruf da ciki,


Kawai sai sarauniya Nuwairat ta zare takobin ta ta durfafi inda take tana mai yi mata murmushi mugun ta,


Tana isa ta ɗaya takobin ta domin ta sare mata wuya.


Dai dai lokacin da jini ke kwaranya daga bakin. Budurwa Nihla kuma numfashin ta na sarkewa.


Kwatsam ! Bazato babu tsammani sai sarauniya Nuwairat taji an dankara mata wawan naushi a dagon bayan ta saboda karfin naushin sai Nuwairat ta tayi gundumbala sau uku sannan ta kife a ƙasa,


Amma sai ta miƙe tsaye zumbur cikin matuƙar fushi da zafin nama,


Ta wai ga bayan ta domin taga wane ne ya dake ta ɗin,


Ai kuwa koda juyawar ta sai tayi Turus, bawa Ni ta gani ba face,


Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa zaune a bisa kan wani tsuntsun tsafi tare da wani zabgegen kyakkyawan saurayi,


Ba wata ba ce wannan budurwa ba face sarauniya Abidatul-auliya ta birnin Tehran tare da matsafi shubairu,


Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarauniya Nuwairat da sarauniya Abidatul-auliya,


Tsawon wani lokaci sai daga bisani Abidatul-auliya ta a dubi Nuwairat ta daka mata tsawa sannan ta buɗi baki cikin kakkausar murya tace"yake tsohuwar azzaluma kuma abokiyar gaba tun iyaye da kakanni ina fatan a halin yanzu kin shaida Ni ko?


Dajin wannan tambaya sai Nuwairat ta bushe da dariyar ƙarfin hali sannan tace "Ai kuwa ni na gane domin na sanki fiye da yunwar ciki na,


Abidatul-auliya bintu shafwaz ta birnin Tehran,


Ban taɓa tsammani cewa akwai sauran zuri'ar mahaifin ki a doran ƙasa ba,


Abidatul-auliya ta ce"Idan barci kike sai ki farka a yanzu ne zuri'ar mahaifi na take gab da yaɗuwa a duniya,


Hakika ke da zuri'ar gidan ku kun dade kuna aiwatar da mulkin zalunci,


Amma ina so ki sani cewa a waje zan hallaka ki na tsira kokon kan ki,na tsire sa da mashi na ajiye sa a fada ta domin ya zamo inza ga sarakunan azzalumai,


Kuma ina mai tabbatar miki dacewa bazaki taɓa burin ki na saduwa da SARKIN SADAUKAI,


Ballantana ki cika burin ki, na sarrafa sa yadda kike so har ki sanya duniya a cikin musiba,


Koda jin wannan batu daga bakin Abidatul-auliya sai Nuwairat ta bushe da dariyar mugun ta sannan tace"Fiye da shekaru ashirin baya mahaifin ki yayi wannan furuci amma sai da Abba na yaga bayan sa don haka,


Wannan bayani naki tamkar a zuba ruwa a faifai,


Ina mai tabbatar miki dacewa a yanzu zan hallaka na zare ruhin ki daga gangar jiki,


Kuma na hallaka budurwa Nihla da kika ceci rayuwar ta a halin yanzu,


A bangaren matsafi shubairu da boka Jadwar kuwa koda suka yi kallon kallo


Sai boka Jadwar ya dubi matsafi shubairu yace"yakai shubairu kayi sani cewa zuwa wannan waje domin saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu domin ya tafi izuwa fadar Sarkin bokaye ya ɗebo maka Tsumin tsafi


Kayi maganin lalurar tsagin jikin da ta addabe ka,


Ka sani ya tashi a banza domin kuwa matsawar ina numfashi a doran ƙasa bazaka taɓa cika wannan buri maka ba Ballantana ka zama dodon bokaye na wannan nahiya,


Koda jin wannan batu sai matsafi shubairu yayi murmushi ya dubi boka Jadwar cikin kaskanci yace "Ai kuwa ina da tabbacin cewa zan cika wannan buri na wa domin dai masu iya magana na cewa


In da rai da rabo! Kuma tabbatar mai nema yana tare da samu,


Kuma ita karya fure take bata yaya tabbas rana dubu ta barawo ce rana ɗaya ta kai kaya


Na tabbata cewa da ace sarauniya Nuwairat tasan cewa ka shafe tsawon shekaru kana cin amanar ta da ta daɗe da sheƙaka barzahu,


Na sani cewa a duniya baka da burin da ya huce kaga ka mallake ta a matsayin abokiyar rayuwar ka domin a halin yanzu a duniya samun wata ya mace mai kyawun sura kamar ta abu ne mai wahala,


Baka san cewa hatta mafarkin da sarauniya Nuwairat tayi ba akan dole ne ta fara arba da SARKIN SADAUKAI domin tazamo mace ta Farko da zai gani yaji yana kaunar ta ba,


Duk kai ne. Ka shirya sa domin kawai ka yi amfani da ita wajen mallakar ta dashi kansa SARKIN SADAUKAI, domin ka kwashe sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN sa domin ka zama Sarkin bokaye na wannan nahiya,


Hatta zaluncin da sarauniya Nuwairat ke aiwatar wa kai ne ke sarrafa ta ta hanyar wani bakin aljani,


Na sani cewa Nuwairat ba zata taɓa gano wannan sirri ba face an karya sirihin dake tsakanin ta da masarautar su,


Abinda ba ka sani ba shine babban kuskuren da kayi shine,


Matsawar Nuwairat tayi arba da SARKIN SADAUKAI take dukkanin sirrikan tsafin dake jikin ta zasu lalace su daina aiki,


Domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN Hibairu duk wanda yafara arba da shi sai ya rasa nasa sirrikan tsafin,


Wannan shi ne fa abin da masu iya magana ke cewa karyar ƙasa wai malamin duba ya dubo ranar mutuwar sa,


Kuma idan za ka gina ramin mutunta to gina sa gajere,


Sa'adda matsafi shubairu yazo nan azancen sa sai idanun boka Jadwar suka kaɗa sukayi jajur har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita kai da gani kasan aiki ne na sihirin tsafi,


Kawai ya buɗi baki yace"Na rantse da kushewar mahaifina boka sahibul -ƙarnas sai na mai sheka gawa domin a halin yanzu kai ne kadai kasan sirri na,


Koda gama faɗin sai boka Jadwar ya ɗaya daga hannun sa izuwa sama,.sai ga wani narkeken Gatari ta bayyana a hannun sa mai matukar kaifi tamkar takobi,


Tamkar hadin baki a lokaci guda jaruman huɗu sukayi kukan kura suka afkawa juna ta hanyar ɗaga makaman yaƙin su,


Wato sarauniya Nuwairat ta afkawa sarauniya Abidatul-auliya,


Boka Jadwar kuwa ya afkawa matsafi shubairu,


Aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,


A dai dai lokacin ne akaga sararin samaniya tayi duhu dunɗum,


Kwatsam sai wata runduna ta bayyana mai ɗauke da dakarun bil'adama da aljanu haɗe da miyagun dabbobi.


Ba wata bace wannan runduna ba face rundunar Sarki Baddadul-ulkas na birnin Rum,


Daga cikin dajin Baitul-shamshan kuwa sai kaji wani kara ya cika wajen kuma wata irin guguwar iska ta bayyana ta dunga sanyawa bishiyoyi na karairayewa suna zubewa ƙasa,


Duwatsu suna karo da juna suna yin bindiga,


Wata irin walkiya na bayyana a sararin samaniya tamkar hadari ne ya hadu ake shirin ɓarkewa da ruwan sama,


Alamun dake nuna cewa HUBAIRU SARKIN SADAUKAI na gab da bayyana Daga cikin dakin Baitul-shamshan .


Kwatsam bazato babu tsammani sai akaji wani irin gurnani na fitowa daga dajin haɗe da waɗansu irin sauti ka da kunnawa ba su taɓa jin su ba,


Al'amarin daya sanya budurwa Nihla dake kwance a ƙasa ta ɗimauce kenan,


Bata san sa'adda ta kama rarrafe ba ta shiga izuwa dajin Baitul-shamshan saboda da ɗimauce wa,


Tsaye tayi arba dashi sanye da kayan fata riga da bante iya kaurin sa,


Kyakkyawan saurayi ne nagaban kwatance wanda kallon farko zai ɗimauta zuciyar duk wata ya mace mai hankali,


A gadon bayan sa yana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka hannun sa riƙe da wani dogon mashi mai baki biyu,


A gefen sa na dama wani irin tsuntsun tsafi ne mai ɗauke da siffar mikiya da girman sa bai huce na jakin dawa ba,


A gefen daman sa kuwa wani murgujejen zaki ne mai kwarjini daban tsoro,


Tsaye a bayan sa kuwa nau'ikan miyagun halittun daji ne gasu nan birjik har da ma waɗanda idanu basu taɓa gani ba,


Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI,


Sa'adda budurwar Nihla ta yi arba dashi sai ta sake ɗimauce wa bata san sa'adda jikin ta Yakamata tsuma yana kyarma ba,


Saboda tsananin tsoro, shi kuwa jarumi Hibairu sai ya ƙura mata idanu ko ƙiftawa baya yi,


Abu na farko da ya daɗo masa arai shine shin dama akwai wata halitta a wannan sararin dake ɗauke da halitta irin ta sa,


Sannan mene ne abin da ya kawo wannan halitta izuwa cikin dajin Baitul-shamshan,


Amsar tambayoyin da Hibairu ya kasa bawa kansa kenan a karon farko kawai yaji ya kamu da ƙaunar halittar wato Nihla,


Har yaji yana son yaga yaksance da ita a rayuwar sa har abada,


To amma mene ne ya janyo yaji ya damu da wannan halitta a cikin ran sa,


Koda wannan murgujen zaki dake tsaye a hannun sa na dama ya hango sunaila sai kawai ya dako wawan tsalle domin ya turmushe ta ya hallaka ta,


Kafin ya kai ga aiwatar da hakan Hibairu SARKIN SADAUKAI ya daka masa tsawa tayi yin wani furuci cikin wani irin yare,


Kawai sai zakin ya dawo da baya ya tsaya cikin ladabi,


Al'amarin daya sanya Nihla ta sake faɗuwa ƙasa a sume,


Cikin hanzari Hibairu SARKIN SADAUKAI ya riga izuwa inda take kwance ya busa mata wata iska daga cikin bakin sa,


Jim kaɗan sai Nihla ta fara buɗe idanuwan ta ,


Sai gashi ta mike tsaye zumbur cikin koshin lafiya tamkar Banu wani abu daya faru gare ta,


Kuma ta ƙurawa Hibairu idanu,


A karon farko taji Ta kamu da matsananciyar kaunar HUBAIRU,


Kuma dukkan tsoro da fargaba sun fita daga zuciyar ta,


Hakika so na da matukar tasiri wajen canza zuriyar bil'adama cikin kankanin lokaci,


A can bakin shiga dajin Baitul-shamshan kuwa,


Yaƙi yayi tsamari tsakanin kowa ne bangare,


Bangaren sunaila da yar uwar ta Hushriba kuwa,


Sun wanzu suna kaiwa juna hare - hare cikin zafin nama nagaban kwatance tamkar waɗansu ifritai,


Sai dai a wannan karon labari yasha bambam domin kuwa idan Sunaila ta kaiwa Hushriba hari da takobi idan ta yanke ta sai ka wajen ya dare jini ya zuba,


Sai kaga ita ma Hushriba ta mayar da martanin,


Kafin cikar daƙiƙa hamsin sun yiwa juna raunuka fiye da goma kuma kowanne na zubar da jini,


Har jiri yana ɗibar su suna faɗuwa ƙasa amma saboda nacin tsiya sai su miƙe tsaye zumbur su sake afkawa juna,


Kaji faɗan MAZAN JIYA masu tarwatsa maza a filin daga,


A bangaren sarki shazwan,boka Dargas da saurayi Hizmal kuwa,


Sun wanzu suna ɗauki ba daɗi a wannan karon sai yazamana cewa dakyar saurayi Hizmal ke iya kare hare haren da su ke kawo masa,


A wasu lokutan har faɗuwa ƙasa yake amma sai ya miƙe tsaye zumbur kuma bai taɓa yarda yaro Humair makaho ya daɗo daga gadon bayan sa ba,


Haƙiƙa inda ace mutum ya tsaye a wajen lokacin da ake wannan artabu Dole ne ya jinjina wa Hizmal ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon sadaukai,


Amma a bangaren boka Jadwar da matsafi shubairu kuwa ba a cewa komai domin komai kallon ƙurillar mutum bazai iya gane wane gwani a cikin artabun ba domin kowannen su yana yaƙin ne cikin baƙin zafin nama tamkar jikin sa bai kasance na jini da tsoka ba,


Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas da rundunar mayakan sa suka ja daga suna masu kallon fafatawar da ake yi tsakanin sarakuna bokaye da matsafa da suka kafa sansani a dajin Baitul-shamshan,


Sai Baddadul-ulƙas ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki,


Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar mutuwa ya dubi wani hadimin sa dake tsaye a hannun sa na dama yace dashi cikin kakkausar murya


"Yakai zawatu ban taɓa sanin cewa wadancan sarakuna, bokaye da matsafa da suka fafatawa yaƙi su na da taɓin hankali ba sai a yau domin in ban da rashin tunani yanzu idan suka hallaka kawunan su wane zai iya saduwa da SARKIN SADAUKAI Hibairu,


Da ace sun haɗa kansu kowa ya ajiye buƙatar sa a gefe sai kaga kowannen su ya samu nasara dazarar an samu haɗin kai.


Jira nake yi su kammala kashe kawunan su sannan na ni kuma na mallaki Hibairu cikin ruwan sanyi,


Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulkas sai hadimi zawatu ya jinjina kai yace tabbas maganar ka haka take yakai sarkin sarakuna mai duniya,


Ana cikin wannan fafatawa ne kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga Hibairu SARKIN SADAUKAI ya Bayyana a bisa kan tsuntsun tsafin sa hannun sa riƙe da wani dogon mashi,


Abangaren hannun sa na dama budurwa Nihla ce zaune a bisa wani murgujejen zaki


Sauran tawagar dabbobi da aljanu na take masa baya,


Wani irin koren haske na fita daga jikin ZOBEN SHIRIn dake hannun sa,


Lokacin da duka ɓangarorin sarakuna, jarumai, bokaye,da matsafa suka yi arba da SARKIN SADAUKAI Hibairu sai kowa ya tsaya cak da yakin da yake yi da abokin gwamin sa,


A kayi cirko cirko aka rasa wanda zai fara tunkarar sa yayi masa wata magana,


Ita kuwa sarauniya Nuwairat Sa'adda ta yi arba da budurwa Nihla tare da SARKIN SADAUKAI sai takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyar ta domin kuwa,


Ta tabbatar dacewa bazata taɓa samun soyayyar Hibairu tun da har Nihla ta fara arba dashi kuma a yadda alamu suka nuna sun kamu da soyayyar juna tun da gashi har ya ɗora ta a bisa kan ɗaya daga cikin dabbobin sa,


Koda Nuwairat tazo dai dai nan a tunanin ta


Sai hawaye suka kwaranyo daga idanun ta ,


Kuma a sannanne tsananin kyawun diri da sura na jarumi Hibairu ya sake bayyana a gare ta, nan take taji ta sake kamuwa da matukar begen sa,


Hibairu ya cigaba da bin jama'ar dake wajen da kallo yana mamakin yadda ake yi a kasa samu halittu masu siffa irin tasa,


Wai shin dama akwai wata halitta mai irin sura ta a wannan duniya,


Amsar tambayar da Hibairu ya kasa bawa kan sa kenan,


Kawai daga bisani sai ya juya ya dubi budurwa Nihla da wani irin kallo mai ɗauke da tsnatsar so da kauna,


Kuma ya buɗi baki da wata irin magana wacce shi kaɗai ce ke fahimtar abinda yake cewa,


Koda jin wannan batu daga bakin Hibairu, sai budurwa Nihla ta yiwa su saurayi Hizmal nuni da su gaba to da yaro Humair makaho izuwa gare ta,


Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa jaruma sunaila da Hizmal goye da Humair suka taka sannu a hankali suka durfafi inda SARKIN SADAUKAI ke tsaye,


Ko da ya rage saura kamar taku goma a tsakanin su


Sai suka ja suka tsaya Nihla ta sauko daga kan zakin da take akai,


Bayan Hizmal ya sauke yaro Humair daga gadon bayan sa sai taja hannun sa har izuwa daf da inda SARKIN SADAUKAI yake,


Har a wannan lokaci namun dajin dake take wa Hibairu baya suna ta hargagi jira kawai suke a basu umarni suka afkawa sarakunan,


Hibairu ya ƙurawa yaro Humair makaho idanu ko ƙiftawa baya yi,


A karo na farko yaji ya kamu da matukar tausayin sa bisa ganin cewa yakasance karamin yaro kuma makaho wanda baya gani,


Nan take ya tuna sa'adda wani daga cikin halittun dake dajin Baitul-shamshan ya makan ce, ya shaƙu matuka ainun da halittar gami da jin tausayin ta,


Nan take Hibairu yaji cewa a ransa tamakar wannan halitta ne ke tare da shi,


Hibairu ya sake buɗar baki a karo na biyu ya dubi Nihla yayi mata magana da Yaren sa,


Bisa mamaki caraf sai suka ji yaro Humair makaho ya mayar wa da Hibairu amsar maganar da irin Yaren na sa,


Al'marin da yayi matukar bawa Hibairu mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai bisa makahon Yaron na magana da irin Yaren,


Su kansu su jaruma sunaila sun cika da matukar mamakin Bisa jin yaro Humair makaho na magana da Yaren Hibairu,


Bata de wani bata lokaci ba yaro Humair makaho ya zayyane wa SARKIN SADAUKAI Hibairu dukkan abinda ke tafe dasu saurayi Hizmal izuwa gare sa dama bukatar da suke nema


Koda jin wannan batu daga bakin Yaro Humair sai Hibairu ya yi shiru yana mai dogon nazari,


Daga bisani ya dubi Nihla, sunaila da Hizmal sannan ya dawo da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads