Header Ads
Showing 21001 words to 24000 words out of 28059 words

Chapter 8 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

372

Ads at the middle of Article

sarki shuraih cikin tashin hankali ya tari yarsa gimbiya Rumaisat tare da duba halin da take ciki koda yaga cewa ta galabaita ainun sai hankalinsa ya dugunzuma ya umarci wadansu kwararrun likitoci suka shiga duba lafiyar ta,


Abangaren mai girma shaibat kuwa da kansa ya a shiga gasawa yarsa gimbiya haya'ul-nur fuskan ta ta ruwan ɗumi domin kumburin dake fuskantar ya sabe,


Sakamakon jinin da ya taru a fuskar saboda naushin da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih tayi mata,


Kuma duk bayan daƙiƙa uku ya tambaye ta shin ya a bar alfaharina a wane hali kike jin jikin ki yana sauƙi kuwa,


Al'amarin jaruma nihla, sunaila, Hizmal,yaro Humair makaho, sarauniya Abidatul-auliya, Nuwairat da matsafi shubairu kuwa,


Lokacin da suka ga yadda sarkin sadaukai Hibairu ya jigata ainun,


Sai hankulan suka dugunzuma ainun, suka dunga kai komo a bakin ɗakin da ake duba lafiyar Hibairu.


Kamar yadda sarkin yaƙi abu-Damraz ya faɗa haka al'amarin yakasance,


Wato rabin Sa'a na kammala cika sai dukkan jaruman gasa gami da sauran jama'a suka sake hallara a karo na biyu,


A lokaci guda jaruman gasa suka shiga izuwa Filin fama suna masu zagaye juna,


Amma a wannan karon babu jarumai biyu, wato sadauki lazwas da jarumi shazwas,


Har a wannan lokaci fuskar jaruma Amirat na sanye cikin rawani idanuwan ta kaɗai ake gani,


Koda ganin cewa Jaruman suna shirin fafatawa,


Sai wannan badakare ya sake ɗauko wannan gabgegen ƙaho ya kafa a bakinshi ya busa da karfi


Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan babu ƙasa nanne ake gardamar kokawa.


Kuma ranar bikin sarakai babu e fitowa ya taka rawa face wacce da wane,


Kafin sautin ƙahon ya kammala mamaye fadar


Sarkin sadaukai Hibairu yayi ɗauki izuwa kan jaruma Amirat,


Gimbiya haya'ul-nur kuwa ya ruga izuwa kan gimbiya Rumaisat,


Su dukan ukun suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,


Jaruma Amirat na ambaton sunayen Ubangiji a cikin ran ta,


Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa,


Jaruman huɗu suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa,


Cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka irin ta zaratan Jarumai


Nan fa ƙura ta turnuƙe, sautin naushi da ihun mazaje ya cika filin baki ɗaya


Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara gudana domin kuwa a wannan karon jarumi Hibairu da jaruma Amirat na tashi izuwa sararin samaniya suna yaƙar junan su,


Tamkar sun kasance masu fuka-fukai,


Nan fa filin gasar ya ruɗe da shewa masoyan Hibairu da jaruma Amirat nayi musu tafi,ihu da jinjina,


Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar mai girma shaibat kenan,


Zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata faso kirjinshi ta fito waje,


Ya dubi Sarkin matsafan masarauta yace dashi a cikin raɗa a fusace "shin mene ne amfanin alƙalancin da aka baku,


Shin bakwa ganin anyi amfani da karfin sihirin tsafi ga wadancan jarumai biyu,


Koda jin wannan tuhuma sai sarkin matsafa ya risina ya dubi sarki cikin ladabi da girmamawa yace"ya shugabana ai tuni dukkan tawagar alƙalanci sun gudanar da bincike bisa abinda ke wakana tsakanin jarumi Hibairu da jaruma Amirat,


Kuka kuma abin da Binciken ya tabbatar mana cewa sam wannan tashin saman da suke yi babu aikin sihiri a cikin shi.


Ni kaina al'marin ya firgita ni kuma ya ɗimauta domin ko da a tarihi ban taɓa ganin wanda yayi wannnan aikin almara ba batare da yayi amfani da sihiri ba,


Sai dai irin mutanen nan da ake wa lakabi da ma'abota addinin Musulunci,


Ka da jin wannan bayani daga bakin Sarkin matsafa,


Sai takaici ya sake turnuƙe sarki shaibat yaji tamkar ya zare takobin sa ya afkawa hubairu sarkin sadaukai ya hallaka shi,


Kuma ya tambayi kanshi a cikin ranshi yana mai cewa


Shin tsakanin HUBAIRU da Amirat wane ne yakasance ma'abocin addinin musulunci?


Amma kuma yadda sunan ya nuna Amirat suna ne Musulmi,


Amma shi hubairu ya ƙarbi addinin ne ko kuwa,


Taya ya yake yin wannan abin bajinta batare da yayi amfani da sihiri ba,


Haƙiƙa idan har ɗaya daga cikin su yakasance


Musulmi abune mai matukar wahala bazasu samu nasarar lashe wannan gasa ba,


Koda ya sake zuwa Nan a tunaninshi sai yaji tamkar ya kwala ihu


Abangaren sarki Baddadul-ulƙas kuwa sa'adda yaga yadda jaruma Amirat take yaƙar hubairu cikin gwanin ta da kwarewar yaƙi,


Kuma babu alamun dake nuna cewa HUBAIRU zai samu nasara akan ta.


Sai hankalin sa ya dugunzuma ainun kuma ya fusata


Abinda ya dugunzuma hankalin shi shi ne yadda alamu ke nuna cewa abu ne mai matukar wahala hubairu ya lashe wannan gasar jarumtaka,


Shin ko kuwa hubairu baya tare da zoben sihirin sa ne,


Abin da ya fusata shi shine shin wace wannan boyayyen jaruma Amirat dake ƙoƙarin ganin ta tozarta shi,


A wannan gasa ta sanya yayi muguwar asarar dukiya mai tarin yawa wacce ban taɓa yin kamar ta ba.


Me ne ne dalilin daya sanya halarar tsafi na bata bayyana mini jaruma Amirat ba,


Haƙiƙa matsawar jaruma Amirat ta lashe wannan gasa sai na shafe Birnin su daga doran ƙasa koda kuwa kiyashin birnin su bazan bari a raye ba.


Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunaninshi sai ya sake murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA.


A binda sarki shaibat da sauran jama'a basu sani ba shine


Bakomai yasanya Amirat take samun nasarar tashi sama batare da fuska fukai ba.


Sai domin ta na yin hakan ne bisa iko da karfin buwayar Ubangiji


Shi kuwa jarumi Hibairu yana samun nasarar tashi saman ne bisa sirrin tsafin dake jikin ZOBEN SHIRIN sa,


Abinda yasanya alƙalan gasar basu gane sihirin tsafin ba,


Sai domin bisa tsarin sirrikan tsafin dake jikin ZOBEN sune makarin dukkan sirrikan tsafin duniya,


Duk wani sirrin tsafi da ya haɗu da na jikin ZOBEN SHIRIN


Sai ya lalata sirrikan tsafin gaba ɗaya koda kuwa sun kai guda miliyan guda,


A tsakiyar filin fama kuwa an cigaba da yin ɗauki ba daɗi,


Jaruman sun wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu cikin matukar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance,


Ana cikin wannan fafatawa ne Hibairu da jaruma Amirat suka kaiwa juna wawan naushi a ciki,


A lokaci guda bisa Sa'a sai kowannen su ya samu ɗan uwan sa nan take su duka biyun suka sulale ƙasa,


Babu alamun rai a tare dasu har idanuwan su sun fara ƙafewa.


Lokacin da jama'a suka ga halin da manyan gwanayen biyun ke ciki,


Sai hankulan su suka dugunzuma ainun.


Har wasu daga cikinsu suka fara zubar da hawayen baƙin ciki.


Domin fargabar kada ace gwanayen su sun rasa rayukansu a wannan gumurzu.


A wannan karon ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka baje a ƙasa suna haki, gami da hararar juna tamkar waɗansu zakaru,


Abangaren tawagar sarki Baddadul-ulƙas kuwa,


Wato dukkan sarakuna da jaruman da sukayi masa rakiya su ka ga halin da gwanin su SARKIN SADAUKAI Hibairu ke ciki sai kwallar takaici ta


A dai dai wannan lokaci shugaban alƙalan gasa wato sarkin yaƙi abu-Damraz ya lura cewa lokacin da aka ɗibarwa gasar ya kusa ƙarewa gashi babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,


Sai kawai ya miƙe tsaye tsam daga kan karagar sa da nufin yace wani abu sai kawai ya jiyo gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat daga filin gasar,


Ai kuwa yana dubawa sai ya ga ashe dukkan su san sake zubewa ƙasa ne babu alamun nasara,


Daga can sai kawai akaga HUBAIRU da Amirat sun miƙe tsaye zumbur tamkar haɗin baki gami da kaiwa juna bugu da naushi,


Tamkar babu wani abu da ya sameshi,


Koda ganin hakan sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka ruɗe da shewar murna.


Jaruma nihla masoyiyar hubairu bata san sa'adda ta miƙe tsaye ba ta kama yiwa masoyin ta jinjina,


Sarki Baddadul-ulƙas da dukkan tawagar murna ce ta kama su ainun,


Ana fara wannan sabon artabu ne sai Hibairu ya shiga ambaton waɗannan kalmomi da yaji ameerat na ambata a duk lokacin da suka fara gumurzu wato Allahu Akbar!


Domin ya tabbatar dacewa tunda har nasara da jarumtakarsa bata sanya yayi galaba akan Amirat ba,


To lallai kalmomin da amirat ke amfani dasu zasu iya bashi nasara,


Domin dai ya samu nasara akan Amirat ɗin,


Amma wani abu daya fahimta shine tabbas jaruma Amirat Bata niyyar taga ta cinye shi a wannan gasa,


Domin sau arba'in tana samun damar da zata illatashi kada yayi nasara amma taƙi aiwatar da hakan,


Faruwar hakan keda wuya sai hubairu yaga cewa a halin yanzu yana samun nasarar kai Amirat ƙasa,


Har takai bata iya mayar da martani, ana cikin wannan hali ne hubairu ya shammaci ta ya gabza mata wawan naushi a gadon bayan ta.


Saboda da karfin naushi,


Sai da amirat tayi sama tamakar an janye ta da ƙugiya,


Sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! Hancinta da bakinta na yoyon jini,


Numfashin ta na fita sama-sama, adai dai lokacin ne gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat suka suka bajewa a ƙasa wanwar sakamakon naushin juna da sukayi a cikin su,


Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa hamsin acikin wannan hali batare da an ga ɗaya daga cikin jaruman uku ya miƙa tsaye ba domin cigaba da artabu,


Har sai da badakaren dake busa ƙahon gasa ya ɗauko ƙahon ya busa sau uku amma babu wanda yayi yunkurin miƙewa.


Nan fa magoya bayan jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur,da gimbiya Rumaisat suka shiga kiran sunayen gwanayen su domin su miƙe kafin wa'adin busa ƙahon ya cika.


Shi kansa sarki shaibat bai sa'adda ya shiga kwallawa yar shi gimbiya haya'ul-nur kira amma shiru kake ji.


Amma sai badakaren a kammala busa ƙahon gasar,


Abin da ya tabbatar dacewa sarkin sadaukai Hibairu shine ya zamo gwarzon daya lashe gasar GOGA SHA FAMA,


Nan fa fadar ta ruɗe da shewa, kide-kide da raye-raye kamar za'ayi shagalin nadin sarautar,


Saboda da murna,


Jaruma sunaila, Hizmal, Abidatul-auliya, Nuwairat,yaro Humair, matsafi shubairu,sarki shazwan da tawagar sa, aljani Marhutul-Azab da sauran dabbobi tawagar sarkin sadaukai basu san sa'adda suka shiga tiƙar rawa ba suna shewa da murna tamkar waɗanda suka zautu.


Sarki Baddadul-ulƙas kuwa kururuwar murna ya shiga yi tamkar wani tsohon mahaukaci,


Bisa ganin jarumin sa ya lashe gasar GOGA SHA FAMA ta sabuwar Shekara,.


Cikin hanzari dakaru na musamman suka shiga izuwa Filin yakin suka ɗauki


Jaruma Amirat, gimbiya haya'ul-nur da gimbiya Rumaisat abisa keken doki aka fice dasu daga filin gasar, domin duba lafiyar su,






Mu haɗu a littafi na 5 domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.


Daga Alkalamin


Mansur Usman Sufi


Sarkin Marubutan yaki


08137237071









GOGA SHA FAMA
End book


Writing by


MANSUR USMAN SUFI






Cikin kaɗuwa da matukar fushi da sarki shaibat bai taɓa yin kamar sa ba,


A wannan lokaci in da ace mutum yana tsaye a wannan waje sai ya rantse yace "garwashin wuta aka watsa masa akan fuskar tashi saboda yadda ya murtuke ta tamkar bai taɓa dariya ba.


Kawai ya miƙa tsaye zumbur daga kan karagar shi ya yabi bayan keken dokin da gimbiya haya'ul-nur ke ciki da sauri,


Dakarun shi na biye dashi cikin tashin hankali,


Sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa saboda tashin hankali dakyar ya samu dama yayi wa mutane bayanin cewa


A gobe ne za'a gabatar da bikin naɗin Jarumi Hibairu a matsayin GOGA SHA FAMA,


Tare miƙa kyautuka gareshi da bawa wakilin daya sakashi a cikin gasar dukkanin dukiyar sauran sarakunan da jaruman su sukayi rashin nasara a cikin gasar.


Yana kammala jawabin ya miƙe zumbur yaja tawagar dakarun shi suka fiye daga fadar,


Shi kuwa jarumi Hibairu koda yaga an fice da jaruma Amirat cikin halin dake tsakanin Rayuwa da mutuwa sai ya tsinci kanshi cikin alamun tsananin damuwa da tausayin halin da take ciki,


Nan fa jama'a suka fara darewa suna ficewa daga filin gasar,


Gaba ɗaya tawagar sarki Baddadul-ulƙas suka dunguma suka tari sarkin sadaukai Hibairu suna masu yi masa jinjina.


Kai tsaye suka dunguma suka fice daga filin gasar domin komawa izuwa masaukin su.


Lokacin da tawagar sarakuna da jarumai suka yiwa da suka yiwa Sarkin sadaukai Hibairu rakiya izuwa Filin Garsar goga sha fama,


Sai suka ci-gaba da tafiya acikin saƙo da lungu na birnin madinatul-shaja'a.


Duk inda suka zo giftawa sai kaga jama'a suna yiwa Hibairu jinjina suna ɗaga mashi hannu.


Haka dai suka shiga da tafiya acikin birin har suka iso izuwa masaukin su.


Kai tsaye aka dunguma izuwa ciki, bayan dakarun dake tsaron kofa sun wangame kofar shiga masaukin.


Da yake a wannan lokaci duhun magari ba ya kawo kai sai sarki Baddadul-ulƙas yayi Umarni aka kunna dukkan fitulun dake gidan ya kaure da haske ɗau!.


Lokacin da hubairu ya shiga izuwa masaukin shi sai ya kasa zaune ya kasa tsaye ya wanzu yana kai komo.


Bakomai na sanya shi a cikin wannan hali ba sai tunanin halin da jaruma Amirat ke ciki.


Nan take ya raya a ranshi cewa haƙiƙa komai tsananin duhun dare kafin wayewar gari sai ya ziyarci jaruma Amirat a sirran ce batare da wani ya sani ba.


Yana cikin wannan hali ne yaji an kwankwasa kofar turakar.


Kawai sai yayi gyaran murya da nuna bayar da umarnin shigowa.


Kofar tayi ƙara tana kammala buɗe wa sai yayi arba da ita ba wata bace face jaruma


Nihla,


Sannu a hankali ta iso daf dashi, tana sakarmashi ƙaytaccen murmushi,


Shima martanin murmushin ya shiga mayarta.


Fuskar ta cike da annuri ta dubeshi


tace "ya masoyiyina ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, hankali yakasa kwanciya, shi yasa ya yanke shawarar cewa dole sai nayi arba dakai sannan zan iya samun runtsawa.


Murmushi ya sakar mata bisa jin daɗin furucin nata, ya buɗi baki yayi gyaran murya.


Yace "ina matuƙar alfahari dake ya farin cikin zuciyata, haƙiƙa ina cikin ƙoshin lafiya.


Nihla cikin mamaki.


"Amma ina dalilin rashin barcinka a lokacin daya kamata ace ka kwanta domin warware gajiyar dake tare dakai, domin a gobe da safe ka tashi da kwarin jiki, a lokacin da za'a baka lambar girmamawa ta Zakaran GOGA SHA FAMA.


Koda jin wannan batu daga bakin masoyiyarshi sai hankalin shi ya dugunzuma bisa tsoron kada ta fahımcı akwai wata damuwa a tare dashi.


Sai yayi gyaran murya yace "ya rabin raina haƙika bakomai ne ya hanani rintsawa ba sai bisa ga dalilai guda biyu.


Na farko shine tunanin a wane hali mahaifina yake ciki a hannun sarki Baddadul-ulƙas.


Dalili na biyu tsaron kada sarki Baddadul-ulƙas yaci amanata ya yaudareni, a kowa ne hali dakarun sumame zasu iya kawo mini farmaki akoda yaushe.


Koda dai na mai girma shaibat ko na sarki shuraihu domin su hallakani.bisa jin haushi da baƙin cikin faɗuwar su gasar GOGA SHA FAMA.


Da jin wannan bayani sai Nihla ta gyaɗa kai alamar gamsuwa gami da tausaya wa.


Tace "tabbas maganar ka gaskiya ce amma baka ganin cewa duka gidan nan cike yake da dakarun tsaro, bana tunanin akwai hanyar da wani zai kawo farmaki.


Hibairu yayi murmushi yace "Zancen ki dutse ne amma kada ki manta masu iya magana na cewa.


"Komai sammakonka wani a hanaya ya kwana ".


"Kuma idan kana dakyau ka ƙara da wanka".


"Zance ka dutse ya sarkin sadaukai.


Nihla ta faɗa tana mai juyawa domin ficewa daga turakar gami da sakar mashi ƙayataccen murmushi.


Koda ficewar ta daga turakar sai ya shiga sanya waɗansu kayatattun tufafi baƙaƙ, ya rufe fuskar sa da rawani ya rataya wata zabgegiyar takobi a gadon bayanshi.


Yana kammala hakan sai ya kawai ya murza zoben sihirin dake hannunshi, take ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.


Ko da ɓacewarshi da kamar daƙiƙa goma ba sai ga waɗansu miyagun halittu ya ketowa daga jikin bangwayen turkar, tamkar yadda danshi ke tsattsafowa daga ƙasa.


Sannu a hankali suka dunga bayyana suna fitar da wani irin gurnani mai ban tsoro.


Yayin da suka kammala bayyana sai suka bincike turakar saƙo da lungu.


Al'amarin jarumai Hibairu kuwa, lokacin da ya ɓace daga turakarshi bai bayyana a ko ina ba, sai a nesa ƙaɗan da masaukin su.


Sannan ya cigaba da tafiya cikin ɗarɗar yana mai waige-waige, domin yana ganin cewa a kowa ne lokaci za'a iya kawo mashi farmaki.


Yana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai yaga waɗansu irin zaratan dakaru marasa adadi na fitowa daga cikin kowace kusurwar dake unguwar.


Kafin yayi wani yunkuri sunyi mashi ƙawanya suna gurnani da hargagi tamkar zasu ci babu.


Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, suna ɗauke da makamai na ƙare dangi.


Komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arba dasu dole ya ɗimauce saboda kwarjininsu.


Cikin matuƙar zafin nama HUBAIRU ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakanin su, na tsawon daƙiƙa arba'in.


Daga bisani wani garjejen ƙato,wanda da alama shine shugaban su ya buɗi baki cikin kakkausar murya tamkar saukar aradu yace.


"Yakai Hubairu ina so yanzu take ka miƙo mini zoben sihirin dake hannunka cikin ruwan sanyi,domin na yanke maka kisa mafi sauƙi ta hanyar tsinke maka wuya.


Idan kuwa kayi taurin kai, yanzu zan umarci tawagata ta gididdiba sassan jikinka, ta yadda kowa tsuntsaye basu damar tsatstsagar namanka ba.


Koda jin wannan batu daga bakin katon, sai hubairu ya bushe da dariyar mugunta, daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar ajali, ya dube sa yace "yakai wannan katon banza kayi sani cewa ka tafka babban kuskure da kake bani umarni.


Nine yafi cancanta na baku umarnin, yanzu kafin na zare ruhikan ku daga gangar jikkunan ku ina so ku sanar dani shin wane mai ɓatar basirar ne ya turoku domin ku hallakani?.


Kafin Hubairu ya gama rufe bakinshi, ƙaton ya tari numfashin shi yana mai daka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads