Showing 18001 words to 21000 words out of 28059 words
Chapter 7 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt
yaƙi abu-Damraz yazo nan azancen sa sai hankalin sa ya sake dugunzuma fiye da ko Yaushe ya dubi hadimi Amirul-bait yace dashi ina so ka ɗebi dakarun leƙen asiri guda dubu su bazama ko ina a wannan birni kuma su saka idanu akan duk wani motsi na sadauki Hibairu,
Koda jin wannan umarni sai Amirul-bait ya miƙa tsaye ya fice daga cikin harabar.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya ciki da waje na birnin madinatul-shaja'a ya cika ya batse da baƙi daga sassan duniya,
Domin halartar bikin gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.
Tun ketowar alfijir jama'a suka fara cincirindo shiga filin gasa domin samun wajen zama,
Nan fa yazamana cewa duk inda Mutum ya kalla a wajen gasar dakaru ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen su riƙe da miyagun makamai suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro,
Kuma duk wanda zan shiga filin gasar sai an buga masa wani hatimi a tafin hannun sa
Idan kuwa mutum guda ne yake ɗauke da tawagar mutane a bayan sa zai bayyana takardar shaidar halartar sa gasar,
Daga cikin wajen gasar kuwa tuni an tsara komai yadda ya kamata wajen zaman sarakuna daban,jaruman gasa, attajirai da sauran su.
Kowa dai an tanadar masa wajen zaman sa dai dai da matsayin sa,
A cikin wannan hali ne aka hango tawagar wani basarake ta shigo filin gasar,
BASARAKEN yakasance gabjejen kato mai kirar samudawan farko,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa,
Sanye yake cikin ado na sarauta a gefen hannun sa na hagu wata irin tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance kai kace ita ce ta tsara kanta yadda take bukata domin tsayawa masalta kyawun ta ya huce hankali.
Tana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke, tun daga ƙasa har sama.
A gadon bayan ta ta rataya waɗansu zaratan takubba,
A gefen hagu da dama dakaru ne gami da hadimai ke take musu baya
Ba waɗansu ba ne waɗannan sarakai ba face
Sarki shuraih ibn shaslam na birin Iskandar tare da yar sa gimbiya Rumaisat,
Fiye da shekaru goma sha biyar sarki shuraih ya shafe yana sanya ana bawa yar sa gimbiya Rumaisat rohon yaƙi a can birin Kisra domin dai jiran wannan rana da zata shiga gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA domin ta kafa tarihi a can nahiyar su ta gabashin duniya.
A lokacin da gimbiya Rumaisat ke karɓar horon yaƙin sai da yazamana cewa ta zarce kowa ne jarumi karfin damtse gami da sanin dabarun yaƙi,
Har yazamana an bata lambar girma mawa ta gwarzon mayaƙi,
Lokacin da mahalarta gasar su kayi arba da sarki shuraih ta tawagar sa fadar ta ruɗe da shewa masoyan sa nayi masa jinjina.
Waɗansu ma tsananin kwayun surar gimbiya Rumaisat ne ya ruɗe su.
Har sa sarki shuraih da tawagar su ka je suka zauna abisa kujerun da aka tanadar musu sannan fadar ta ɗan samu nutsuwa,
Haka dai tawagar sarakuna suka dunga shigowa fadar rukuni-rukuni kafin wani lokaci filin ya kammala cika maƙil,
Ana cikin wannan hali ne aka hango tawagar sarki Baddadul-ulƙas ta shigo filin gasar nan take fadar ta ruɗe fiye da ko yaushe kuma mutane suka cika da matukar al'ajabi bisa ganin yadda a wannan karon tawagar ta sa har da miyagun dabbobi su ma sun samu halartar gasar.
A wannan lokaci sarkin sadaukai Hibairu ya rufe fuskar sa da rawani idanun sa kaɗai ake gani don haka babu wanda ya shaida cewa wane ne gwarzon mayaƙi acikin tawagar sarki Baddadul-ulƙas,
Bayan Baddadul-ulƙas sun zauna bisa kujerun zaman su,
Sai mai girma shaibat ya miƙe tsaye ta hanyar ɗaga hannun sa sama fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta
A wannan lokaci yana sanye cikin shigar alfarma ta hamshakan sarakai,
Sannan daga bisani ya buɗi baki yayi gyaran murya yace
"Da farko ina yiwa dukkan mahalarta wannan GASAR jarumataka Barka da zuwa wannan birni mai albarka.
Nayi matuƙar farin cikin yadda manyan sarakuna, bokaye, attajirai,sadaukai haɗe da talakawa,
Su ka fito kwan su da kwarkwatar daga ko ina a sannan duniya domin halartar wannan gasa mai ɗumbin tarihi da ake gudanarwa tsawon shekaru,
Da wannan nake yiwa dukkanin mahalarta Barka da zuwa tare da fatan ayi taro lafiya a tashi lafiya,
Yanzu sai a samu nutsuwa a saurari sauran bayanin yadda gasar zata kasance daga bakunan alƙalan gasa.
Koda Gama faɗin hakan sai sarki shaibat ya koma bisa kan karagar sa ya hakimce,
Kawai sai sarkin yaƙi abu-Damraz ya miƙe tsaye yayi gyaran yace
"Bayan jawabin mai martaba yanzu abinda ke gaban mu shine gabatar da dokokin gasa ga dukkan jaruman da zasu fafata,
Amma kafin hakan yanzu za'a kira wo sunayen jaruman domin su wajen wajen zaman su dake daf da filin fama.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Sarkin yaƙi abu-Damraz ya sanya hannun sa na dama ya ɗauki wata jimammiyar fata dake ajiye a bisa teburin dake gaban sa,
Ya ɗora idanun sa akan ta sannan ya fara karanto sunayen jaruman kamar haka
Gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat
Koda jin an ambaci sunan yar mai girma shaibat sai fadar ta ruɗe da shewa,
Lokaci guda ta sauko daga kan karagar ta ta durfafi wajen zaman alkalan gasar,
Nan da wasu da ya wa daga cikin mazaje suka ɗimauce bisa ganin tsananin kyawun sura da diri nata,
Haka dai sarkin yaƙi ya cigaba da kiran sunayen sadaukan ɗaya bayan ɗaya
Jama'a nayi musu jinjina,
Har yazamana an ambaci sunan Jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI
Koda jama'a suka yi arba da Hibairu sai fadar ta kaure da ihu da shewa fiye da ko yaushe,
Zukatan al'umma cike da matukar mamaki da al'ajabi suna masu cewa wai shin dama Barde Shabbaru yana raye bai mutu ba,
Amma kuma ai Shabbaru ai a halin yanzu dattijo ne kuma ma labarin mutuwar sa ya watsa ko ina a duniya
Haka dai hubairu ya cigaba da tafiya har ya zamana ya zaune a bisa kujerar sa,
Koda ya zauna sai ya hangi wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ta ƙura masa idanu ko ƙiftawa baya yi,
Ba wata ce wannan kyakkywar budurwa ba face gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih,
Koda gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat taga yadda Rumaisat ke ƙuruwa hubairu idanu sai ta daka mata harara kuma tace a cikin ran ta tabbas idan kin kamu da soyayyar Hibairu ne to kin so gawa mara amfani,
Domin na rantse da darajar iyaye na sai na hulakanta hubairu kamar yadda mahaifin sa ya wulakanta Abbana.
Kuma tabbas Ni ce zan zamo ajalin sa bayan na cinye wannan gasa ta GOGA SHA FAMA.
Sarkin yaƙi ya kira sunan jaruma ta karshe wacce ake kira Amirat bintu Hamza ta birnin madinatul-barnawiy.
Koda fitowar jarumar sai kowa ya cika da mamaki Bisa ganin jarumar bata ɗauke da alamar SADAUKANTAKA,
Kuma fuskar ta rufe take da rawani Nan fa daya wa daga cikin jihar jama'a suka kama yi mata dariya wasu kuma tausayin ta ne ya kamu bisa ganin cewa ita da bata kasance Basadaukiya ba amma ta shiga gasar mai haɗarin gaske da zata iya rasa rayuwar ta.
Bayan dukkanin jaruman gasa sun zauna a bisa kujerun da aka tanadar musu,
Sai sarkin yaƙi abu-Damraz ya cigaba dacewa
"Kafin mu kai ga shiga cikin shagalin yana dakyau dukkan jarumai su san da wadannan dokoki na gasar jarumtaka,
Doka farko ita ce Ba'a yarda ayi amfani da sihirin tsafi ba
Wajen samun nasara, koda mutum ya aikata acikin alƙalan gasa akwai bokaye dasu gane cewa yayi tsafin,
Dukkan jaruman da aka haɗa ku faɗa dashi babu damar a canza.
Kuma kamar yadda aka sani cewa dukkanin jaruman zasu dunga gwagwarmaya a tsakanin su har sai an fitar da gwarzo wanda shi ne babu wanda yakasance a saman shi.
Dukkan wanda yayi kisa za'a haramta masa shiga gasa na tsawon shekaru goma tare da tara mai tsauri,
Idan kuwa ya lashe gasar to za'a bawa yan uwan wanda ya kashe dukkan kyautuka da za'a ba shi,
Lokacin da sarkin yaƙi abu-Damraz yazo nan a jawabin sa sai ya koma kan kujerar sa a ya zauna,
Kawai sai wani garjejen kato mai sanye da jajayen tufafi masu yalwa ma'abocin tarin ƙasumba da gemu baƙaƙe siɗik
Ya miƙe daga cikin alƙalan gasar ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace
"Yanzu dukkan jaruman gasa zasu hallara a Filin fafatawa dake tsakiya bayan ambaci sunayen su,
Da farko akwai mai girma gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat
Tare da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih
Sannan sadaukai Hibairu ibn Shabbaru
Tare da jaruma Amirat bintu Hamza ta birnin madinatul-barnawiy
Sadauki lazwas ibn shaslam na birnin Laufas
Da Jarumi nazwar ibn gaurus na birnin shasrad.
Koda kammala karanto sunayen sai filin gasar ya sake kaurewa da shewa da ihu fiye da ko yaushe,
Ɗaya bayan ɗaya jaruman suka dunga tashi suna isa zuwa filin,
Jim kaɗan sun kammala hallara.
Nan take kowa ya shiga kallon abokin gwamin sa kuma suna masu gazaye juna,
Dai dai lokacin da waɗansu dakaru ke buga waɗansu tambura da ganguna dake ziga dukkan mazaje da tsuma zukatan su a filin fama,
A bangaren gimbiya haya'ul-nur tsananin takaici ya turnuƙe zuciyar ta da a karon farko na gasar ba'a haɗa ta da hubairu sarkin sadaukai ba,
Ita kuwa gimbiya Rumaisat tsananin farin ciki ne ya kamata bisa ganin cewa ba'a haɗa saurayin da ta kamu da kaunar sa da abokiyar gabar ta gimbiya haya'ul-nur ba.
Daga can sai wani garjejen kato na daban ya ɗauki wani zunguren ƙaho a jikin sa ya kafa a bakinsa ya busa shi da ƙarfi,
Tamkar haɗin baki a lokaci guda jaruman kowanne bangare suka yi ɗauki kan abokanan gwamin su,
Suna masu ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAKA a filin daga,
In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda jaruman takwas suka yi ɗauki kan junan su dole abin ya firgita shi domin yasan ko ba'a ce komai ba haƙiƙa za'ayi KARON MAZA,Kuma za'a sha ɗauki ba daɗi.
Yayin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini muni,tashin hankali da ban tsoro,
Wohoho haƙiƙa idan kaji ƙidan farauta sai GWARAZAN JIYA ke amsa gayyata,
Idan garken zakuna suna fito fagen artabu babu masu tarar su ayi gaba da gaba face manyan giwaye,
Nan fa ɓangarorin suka shiga kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance tamkar jikkunan su basu kasance na jini da tsoka ba
Abangaren mahalarta taron gasa kuwa, lokacin da jaruma Nihla, Sunaila,saurayi Hizmal, sarauniya Abidatul-auliya,Nuwairat da yaro Humair makaho suka ga an kacame da azababban yaƙi tsakanin sarkin sadaukai Hibairu tare da jaruma Amirat bintu Hamza sai hankalin su ya dugunzuma ainun,
Duk da cewa a zahiri sun san cewa HUBAIRU ya nunka Amirat fiye da arba'in a SADAUKANTAKA da ƙirar jarumtaka,
Amma bisa ganin yadda Amirat ɗin ke yakar Hibairu cikin zafin nama juriya na ɓacin tsiya tamkar wata shaiɗaniya sai hankulansu suka dugunzuma ainun,
Domin dai matsawar Hibairu ya faɗi wannan gasa,
Tamkar rushewar cikar burikan su na duniya ne baki ɗaya,
Abangaren sarki Baddadul-ulƙas kuwa zuciyarsa babu yabo babu fallasa,
Domin yana ganin cewa tamkar Hibairu ya samu nasara ne akan jaruma Amirat,
Sai dai inda kizo ke saƙar shi ne don HUBAIRU ya samu nasara akan Amirat to lalle bane yakai ga nasara akan sauran jaruman,
Wani ɓangare a zuciyar kuma a zuciyar sa kuma yace dashi kada ka manta cewa nasara da Sa'a a jinin Hibairu take haƙiƙa sai ya samu nasara a wannan gasa,
Domin a halin yanzu babu gwarzon mayaƙi kamar shi a faɗin duniya,
Koda sarki Baddadul-ulƙas yazo nan a tunanin sa sai ya bushe da dariyar farin ciki,
Al'amarin da ya sanya sarki shuraih dake zaune daf dashi ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA,
ya dubi Baddadul-ulƙas da wani irin kallo mai ɗauke da alamar tamabaya,
A bangaren mai girma shaibat kuwa ya zuba idanu ya kallon yadda gasar ke gudana,
Zuciyar sa na dukan uku-uku,
Domin yana ganin cewa haƙiƙa koda yar sa gimbiya haya'ul-nur ta samu nasara gimbiya Rumaisat bai zama tilas ta samu nasara akan Hibairu ɗan Barde Shabbaru ba,
Abangaren teburin alƙalan gasa, al'marin sarkin yaƙi abu-Damraz kuwa ana fara wannan fafatawa tsananin jaruman sai hankalin sa ya dugunzuma ainun ya kasa samun nutsuwa, domin a halin yanzu yana cikin tsaka mai wuya,
Idan sarkin sadaukai Hibairu ya cinye wannan gasa,
Gimbiya haya'ul-nur ta faɗi, dai dai yake da ya rasa rayuwar sa,
A Ɓangaren dabbobin dajin da suka yi Hibairu rakiya izuwa Filin gasa,
Sa'adda suka ga yadda shugaban su Hibairu ya kacame da azababban yaƙi da jaruma Amirat sai suka dunga yin gurnani suna hargagi,
Dake nuna fatan nasara ga sarkin sadaukai Hibairu,
Nan fa mamaki Yakamata jama'ar dake filin gasar bisa ganin yadda dabbobin ke nuna alamun fatan alkairi ga Hibairu,
Abin tambaya anan shine mene ne alaƙar HUBAIRU da waɗannan miyagun dabbobi,
Me ne ne alaƙar dake tsakanin HUBAIRU da Barde Shabbaru tabbas a yadda alamu suka nuna lokacin da aka ambaci sunayen jaruman ya tabbatar dace wa Hibairu ɗan Barde Shabbaru.
Tabbas kyan ɗa ya gaji uban sa,. Nanfa jama'a suka dunga yiwa gwanayen su jinjina,
Amma sai ya zamana fiye da rabin jama'a hubairu suke ɗagawa hannu suna yi masa kirari, masu wake nayi masu shewa nayi.
Nan fa zuciyar sarki shaibat ta kama tafarfasa tamkar zasu ƙone,
Bisa ganin yadda jama'a ke nuna goyon baya ga Hibairu,
A tsakiyar filin gasar kuwa jaruman sun wanzu suna kaiwa junan su sara da suka cikin ɓakin zafin nama juriya da jarumtaka irin ta JARUMAN DUNIYA,
Duk wanda ya gaɓzawa ɗan uwan sa nashi sai kaga shi ma ya mayar da martani Cikin zafin nama tamkar suna casar hatsi.
Kai kace wata na'ura ce ke sarrafa su ba da jini da tsoka ke gudana a jikkunan su ba.
Lokacin da zaratan Jaruman gasar GOGA SHA FAMA suka wanzu suna kaiwa Juna naushi da bugu cikin matukar zafin nama juriya da jarumtaka ta gaban kwatance,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa arba'in ana wannan fafatawa babu sassauci,
Nan fa wani abun mamaki ya fara wakana,
Domin bangarorin jaruman ana samu ragas ma'ana karfi yazo ɗaya,
Duk sa'adda ɗayan su ya gaɓzawa abokin faɗa sa naushi sai kaga ya shanye dukan,
Shi ma ya taƙarkare ya mayar da martani Cikin gwanin ta da zafin nama.
Nan fa jama'a suka shiga yin shewa da tafi bisa ganin cewa har yanzu babu alamun nasara ga dukkan bangarorin jaruman,
Wannan fa shine abinda masu iya magana ke cewa kyan faɗa akwana ana yi.
A ɓangaren Jarumi Hibairu da jaruma Amirat kuwa sun wanzu suna bawa hammata iska,
Suna kai wa juna hari ta ƙasa da sama,
Wasu lokutan har daka tsalle sama suna kaiwa juna harin.
Lokacin da Hibairu sarkin sadaukai yaga cewa an shafe tsawon Sa'a sittin batare da ya samu nasarar kai Amirat ƙasa ba,
Sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun,
Abin da ya bashi mamaki shine yadda akayi ya kasa samun nasara akan Amirat bayan cewa a zahiri ya nunka a karfin damtse da ƙirar jarumtaka,
Abin da Ya dugunzuma hankalin sa kuwa shine matsawar ya faɗi wannan gasa shi kenan bazai taɓa samun nasarar fansar rayuwar mahaifinshi daga hannun sarki Baddadul-ulƙas ba,
Sa'adda sarkin sadaukai yazo dai-dai nan sai kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kaiwa Amirat naushi da bugu da wani irin salo na musamman.
A ɓangaren gimbiya haya'ul-nur yar mai girma shaibat da gimbiya Rumaisat yar sarki shuraih kuwa
Labari yasha bambam domin sun fara haɗawa junan su jini da majina suna rangaji jiri na ɗibar su amma saboda juriya da bajinta irin ta JARUMAN DUNIYA sai suka ƙi yarda su faɗi ƙasa,
Su ka cigaba da faɗan a haka kawai,
Abangaren sadauki lazwas ibn shaslam da Jarumi nazwar kuwa,
Sun tara zufa sun jiƙe sharkaf saboda yadda suke naushi da bugun juna cikin gwaninta da salon yaƙi mai matukar kwarjini,
Domin idan lazwas ya gabzawa nazwar naushi a fuska ya kife ƙasa,
Sai ya ɗan huta na yan daƙiƙa sannan ya taso sama ya mayar da martani,
Lokacin da Sa'a ɗaya ta cika da fara wannan artabu sai salon yaƙin ya canza salo,
Kasancewar rana tayi tsananin zafi ainun sai sadaukan suka fara galabaitar da juna,
Ana cikin wannan artabu ne sadauki lazwas ya kaiwa jarumi nazwar naushi a wuya a lokacin da shi ma yakai mishi harin a kirji,
Cikin nasara kowanne su ya samu nasarar samun ɗan uwan sa nan take suka kurma wawan ihu suka sulale ƙasa
Babu alamun rai a tare dasu,
Al'amarin da ya sanya fadar ta kaure da shewa da tafi kenan kuma ya dugunzuma hankalin attajiran da su ke ɗauke da alhakin sanya jaruman a cikin gasar
Shin yanzu jaruman nasu sun rasa rayukansu ne ko kuwa doguwar suma su kayi
Cikin hanzari waɗansu zaratan dakaru suka shigo filin Ɗauke da keken doki suka ɗauki jaruman biyu suka ɗora su akai,
Suka fice daga filin gasar domin basu taimakon gaggawa a ceto rayuwar su,
Ana cikin wannan fafatawa sarkin sadaukai Hibairu tare da jaruma Amirat suka kaiwa juna naushi a fuska,
A lokacin da suka Daka tsalle izuwa sama,
Cikin Sa'a kowanne ya gabzawa ɗan uwan sa naushi a fuska,
Take suka hantsilo suka rikoto ƙasa, amma saboda gwanin ta kafin su kai ƙasan sai kowanne su ya ware kafafunsa biyu ya turje a cikin ƙasa,
Sannan suka kaiwa juna karo da kawunan su jika ke gau,
Amma a wannan karon sai suka kife a ƙasa suna haki tamkar waɗansu zakaru,
Koda ganin irin gwanintar da sadaukan ke yi sai filin fadar ya kaure da shewa da jinjina haɗe da ihu,
Al'amarin gimbiya haya'ul-nur da Rumaisat kuwa,
An cigaba da yin kare jini biri jini babu alamu dake nuna cewa ga gwanar dake da nasara a cikin su,
Lokacin da alƙalan gasa suka cewa an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan artabu babu alamun nasara ga dukkan bangarorin sai wannan badakare daya busa ƙahon yaƙi ya sake ɗauko wannan ƙaho ya busa da karfi,
Take kowanne jarumi yaja ya tsaya cak yana haki da hararar abokin gwamin sa.
Sarkin yaƙi abu-Damraz ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yayi gyaran murya ya fuskanci jama'a yace"yaku mahalarta wannan gasa mai albarka kuyi sani cewa duba da yadda har sa'o'i uku suka shuɗe babu alamun nasara ga dukkan bangarorin,
Bisa tsarin wannan gasa za'a tafi hutu na rabin Sa'a domin jarumai su sake kimtsa wa suyi sabon shiri domin yin karon batta ta biyu wacce a cikin ta ne muke sa ran za'a ƙarƙare wannan gasa domin fitar da gwarzon mayaƙi,
Koda jin wannan jawabi daga bakin Sarkin yaƙi abu-Damraz sai fadar ta sake ruɗewa da shewa cikin Hanzari dukkan jaruman huɗu suka fice daga filin gasar,
Kai tsaye sarki Baddadul-ulƙas ya sanya hadiamn sa suka shiga duba lafiyar jarumi Hibairu domin ya samu wartsakewa kafin a koma zagayen gasa ta biyu,
Shi kuwa