Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 28059 words

Chapter 5 - GOGA SHA FAMA Complete by Mansur Usman Sufi .txt

Ads the beginning of article before Image

01 Jun 2024

370

Ads at the middle of Article

duban sa ga Humair makaho yayi masa bayani abinda zai faɗa


Sannan Humair makaho ya juya ya dubi su sunaila yace


"Ya abokan tafiya ne kuyi sani cewa abinda sarkin sadaukai yace a cikin bayanin sa shine ya amince da dukkanin bukatun ki kuma zai biya muku su,


Amma bisa sharadi guda ɗaya sharaɗin kuwa shine bazaku taɓa cutar da wata dabba ba,


Kuma zaku taimaka masa wajen kare martabar su da kuma zaku masa wajen yaƙar dukkanin bil'adama dake doran ƙasa,


Koda jin wannan batu daga bakin Yaro Humair makaho sai hankalin kowa ya dugunzuma ainun,


Kuma cikin su ya ɗuri ruwa , tsawon daƙiƙa goma babu wanda ya ce ƙala a cikin su,


Sai daga bisani ne,


Jaruma sunaila tayi gyaran murya sannan tace"yakai Hizmal kayi sani cewa a halin yanzu ba lokaci ne da zamu tilasta Hibairu ya janye ƙudirin sa na yakar bil'adama ba tare da shafe su daga doran ƙasa ba,


Domin kada ka manta cewa akan hakan ya rayu, bai san cewa akai wasu bil'adama ba,


A can gaba za mu samu nasarar canza masa ɗabi'un sa ta hanyar Budurwa Nihla da a halin


Yanzu ya kamu da matukar kaunar ta,


Tare da yaro Humair makaho da shi kadai ne ke iya jin Yaren sa a halin yanzu,


Sannan wani abu da baka sani ba shine,


A lokacin da Hibairu ya fito daga dajin Baitul-shamshan na fara arba dashi naga ɗumbin tausayi da jin kai a tattare da fuskar sa,


Wanda hakan ya tabbatar mini dacewa mahaifan sa sun kasance mutanen kirki masu adalci,


Haƙiƙa dole ne Hibairu ya kasance yana tare da wannan dabi'u kyawawa nasu domin kuwa masu iya magana na cewa,


"kyan ɗa ya gaji uban sa


Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Hizmal ya cika da farin ciki yace "yanzu zai mu ce masa mun amince ko


Koda jin hakan sai Humair makaho ya juya ya dubi Sarkin sadaukai Hibairu yace "yan uwa na sun amince da sharaɗin ka sannnan dukkanin wadancan mutane da ka gani,


Su ma sun zo gare ka ne domin bayyana maka nasu bukatun,


Kafin yaro Humair makaho ya gama rufe bakin sa sai kawai gani akayi a suri yaro Humair anyi sama dashi,


Sai ga zaune a daf da keken dokin da sarki Baddadul-ulƙas ke zaune,


Sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariya mugun ta,


Sannan bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa yace


"ya ku masu jiran gawar shanu kuyi sani ceqa a halin yanzu gashi na mallaki yaro Humair,


Tare wani abu da gaba ɗayan ku baku dashi,


Wanda yazama dole saboda shi


HIBAIRU ya zamo mai biyayya a gare Ni,


Sa'adda sarkin sadaukai Hibairu yaga cewa sarki Baddadul-ulƙas ya kwace yaro Humair makaho,


Sai ya fusata ainun kawai sai ya zare kwarin dake gadon bayan sa,


Ya ciro kibiya ɗaya daga cikin kwanson ya saka a cikin bakan sa ya taɓe take ya harba kibiyar izuwa kan dakarun sarki Baddadul-ulƙas,


Kibiyar ta tafi cikin matsanancin gudu a iska,. Ya yin da ta sauka akan dakarun take wata irin guguwar Wuta ta bayyana


Kafin dakarun suyi wani yunkuri wutar ta hallaka dakaru dubu biyu cikin abin da bai gaza daƙiƙa Ɗari ba sun ƙone ƙurmus,


Al'amarin daya fusata sarki Baddadul-ulƙas kenan ya takarkare ya kwarara wawan ihu irin na hamshakan sarakai da suka saba gwagwarmaya da maza a filin daga,


Ya nuna yaro Humair makaho da ɗan yatsan sa na hagu,


Take wadansu irin sarkokin tsafi suka ɗaure sa tamau hannu da ƙasa a jikin keken dokin Da yake akan sa


Kawai sai ya dako tsalle daga kan keken dokin sa tamkar an janye sa kungiya, yana tafiya a cikin iska ya durfafi inda SARKIN SADAUKAI


Yana saman ya saman ya zare wata sharbebiyar adda a damtsen sa,


Koda ganin hakan sai Hibairu ya zunguri cikin tsuntsun tsafin sa da kafafun sa biyu,


Take tsuntsun ya kaɗa fuka -fukan ya durfafi Sarki Baddadul-ulƙas domin tarar juna yana aman wuta daga bakin sa,


***


Lokacin da SARKIN SADAUKAI Hibairu da da sarki Baddadul-ulƙas suka ruga izuwa kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,


Lokacin da suka haɗu da juna sai suka kacame da azababban yaƙi mai matukar kwarjini, muni ban tsoro da tashin hankali,


Ga dukkan mai kallo.


Wohoho haƙiƙa idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu wanda ke tunkarar ta face GOGA SHA FAMA da ya saba gwagwarmaya a DUNIYAR MAYAKA


Tabbas faɗa yan MAZAN JIYA na JARUMAN DUNIYA ne,


Ana fara wannan artabu ne fa kallo ya koma sama,


Domin du ka bangarorin sarakuna bokaye da matsafan da suka hallara a wajen sun zuba idanu domin su ga abinda zai wakana,


Duk sa'adda sarkin sadaukai ya kaiwa sarki Baddadul-ulƙas hari da kashin sa idan Baddadul-ulƙas ya zillewa harin sai kaga duk inda mashin ya sauka a ƙasa wajen ya rufta idan bishiya ce ko duwatsu sai su kama da wuta


Idan kuwa makaman nasu suka haɗu da juna sai kaga wata irin tartsatsin wuta yana tashi haɗe da walkiya,


Nan fa dawakai suka firgice suka dunga jefar da mahayan su suna nausawa izuwa cikin daji saboda firgita,


Sa'adda da halittun dake bayan Hibairu suka ga cewa shugaban su ya garƙame da azababban yaƙi da sarki Baddadul-ulƙas sai kawai su kayi kukan kura suka afkawa dakarun sarki Baddadul-ulƙas,


Nan fa waje ya sake rincaɓewa da ɗauki ba daɗi,


Nan fa halittun suka zamo tamkar guguwar annoba a tsakiyar dakarun,


Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa hamsin ba gawarwakin dakarun sun watsu a ko ina,


Waɗansu kuma na faɗa wa izuwa cikin wannan rami ka dake faruwa sakamakon nutsewar makamin Sarkin sadaukai,


Lokacin da sarki Baddadul-ulƙas yaga cewa an shafe tsawon Sa'a Arba'in ana wannan fafatawa batare da ya samu nasarar lakutar koda jikin sarkin sadaukai da takobin sa ba,


Sai takaici ya turnuƙe sa ya faɗa izuwa kogin tunani,


Abu na farko da ya faɗo masa arai shine mene ne dalilin daya sanya ya kasa samun nasara akan Hibairu,bayan cewa a kaf jinsin sarakunan duniya babu sarki mai karfin damtse kamar sa gami da karfin sihirin tsafi,


Sannan idan har a ka cigaba da wannan artabu miyagun halittun dake fafatawa yaƙi da dakarun sa zasu iya samun nasarar hallaka Barde Shabbaru mahaifin Hibairu


Don haka dole ya samu mafita


Koda kammala tunanin hakan sai sarki Baddadul-ulƙas ya yi yuf ya kaiwa HUBAIRU wani nagartaccen sara da kafaɗa,


Cikin zafin nama Hibairu ya zille tare da mayar da martani Cikin zafin nama,


Bisa Sa'a sai gashi ya soke Baddadul-ulƙas a cinyarsa saboda karfin sukar sai mashin ya fasa sulken yaƙin dake jikin sa ya jini yayi tsayuwa


Baddadul-ulƙas yayi taga taga zai fadi amma sai ya turje,


Kawai sai ya shafi wani gurun tsafi a damtsen sa kawai sai riƙiɗa izuwa wata baƙar guguwa, guguwar ta tashi izuwa sama ta nufi keken dokin dake tsakiyar dakarun yaƙi,


Daga bisani guguwa ta bayyana a daf da inda SARKIN SADAUKAI ke tsaye sai ta riƙida izuwa sarki Baddadul-ulƙas tare da wani dattijo ya ɗora kaifin takobin sa akan wuyan dattijon yana mai yi Hibairu murmushin mugunta,


Sa'adda HIBAIRU yayi arba da Dattijon sai ya tsaya cak yana mai ƙura masa idanu ko ƙiftawa baya yi,


Bakomai yagani ba face yadda kamannin sa dana dattijon suka zo iri ɗaya sai tamakar an tsaga ƙara,


Nan take yayi tausayin Dattijon yakama sa bisa ganin yadda aka ɗaure dattijon da sarkokin tsafi kuma Baddadul-ulƙas ya ɗora kaifin takobin sa akan wuyan sa,


Abangaren su jaruma sunaila,sarki uslaim,sarki shazwan, sarauniya Abidatul-auliya, Nuwairat da su aljani Marhutul-Azab kuwa,


Sa'adda da suka yi arba da wannan dattijo mai matukar kama da sarkin sadaukai sai suka cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki,


Su na masu cewa a cikin ran su an ya kuwa wannan dattijo bashi ne mahaifin Hibairu ba lallai tsananin kamannin surar su yayi yawa!


Idan kuwa har haka ne tabbas wannan baƙon sarki da ya bayyana zai iya samun nasarar mallakar HUBAIRU cikin ruwan sanyi


Shin wane ne wannan sarki, menene alaƙar sa da Hibairu?


Amsar tambayoyin da su ka kasa ba wa kansu kenan,


Kawai su ka zuba idanu suna kallon abin da zai wakana


Kallo ne ya wakana tsakanin sarkin sadaukai da dattijo na tsawon daƙiƙa talatin daga bisani sai hawaye suka zubo daga idanuwan dattijon yana mai sakarwa Hibairu murmushi mai taushi


Bisa mamaki HUBAIRU bai san sa'adda da ya mayar masa da martanin murmushin ba,


Sarki Baddadul-ulƙas ya katse shirun daya wanzu ta hanyar buɗar baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya dubi dattijon a lokacin da kara rikon wuƙar dake kan maƙogaron sa yace


"Ya kai Barde Shabbaru bin sha'asanul-haibar kayi sani cewa ban kawo ka nan ba sai domin na nuna maka ɗan ka na cikin ka tsawon shekaru ashirin kenan yau


Wato Hibairu nasan cewa ko ba'ayi maka bayanin komai ba


A halin yanzu gaji a jikin ka cewa HUBAIRU ɗan ka ne wanda matar ka layizat ta haifa wannan daji mai ban al'ajabi,


Ka sani cewa ban fito dakai daga kurkukun Darul-barzak ba sai domin na yan taka daga KANGIN BAUTA a karkashi tsahon shekaru masu yawa,


Amma fa hakan bazai tabbata ba face ka amince ka biya mini wata buƙata guda biyu


Kamar haka.


Da farko Wajibi ne ka janyo hankalin ɗan ka HUBAIRU akan lallai ya amince ya zai shiga gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,


Idan yayi nasara ne kawai zai sanya na yan taku kai da ɗan ka daga KANGIN BAUTA a karkashi na,


Sannan tilas ne ka sanya Hibairu ya zamo mai biyayya a gareni,


Yakai Shabbaru kayi sani cewa matsawar ka cika mini waɗannan to bayani ya zo karshe,


Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai fuskar Shabbaru ta canza daga walwala izuwa ɓacin rai,


Ya daga kai sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai ɗauke da karfin zuciya yace"ya kai Baddadul-ulƙas kayi cewa nafi kowa sanin wane ne kai,


Kai mutum ne maci amana kuma mayaudari nasan cewa ko da na cika maka waɗannan sharudda ko ban cika ba baza ka taɓa bari na da rai ba,


Kuka kuma tilas ne sai ka ci amanar ta shin ka manta da zaluncin da kayi mini,


Ka raba ni da kasar mu, yan uwana, sannan ka zo ka raba ni da mata ta da na fi kauna fiye da komai,


Ai har abada ba'a taɓa canzawa tuwo suna kuma mai hali ba ya canza halin Sa,


Koda jin wannan batu daga bakin Barde Shabbaru sai sarki Baddadul-ulƙas ya bushe da dariyar mugunta,


Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa wasikar mutuwa yace"shin yanzu ka zaɓi ka rasa rayuwar ka da ɗan ka guda ɗaya jal ai ko babu komai kaso zuri'ar ka su ci gaba da wanzu a doran ƙasa,


Kada ka manta cewa HUBAIRU shi kadai ne ya rage maka a cikin zuri'ar ka,


Koda jin wannan batu sai hawayen bakin ciki suka zubo daga idanun Shabbaru


Ya sake ƙurawa Hibairu idanu nan take yaji cewa tamakar matar kuwailat ce yake tare da ita ,


Sarki Baddadul-ulƙas ya yi nuni da hannun sa izuwa inda yaro Humair makaho yake nan take wata iska mai karfi ta jimimiyo sa ta kawo sa izuwa daf da inda SARKIN SADAUKAI Hibairu yake tsaye,


Sannan sarkin sadaukai Hibairu ya dubi yaro Humair ya buɗi baki ya fara yi masa Magana da irin nasa yaren,


In da yake cewa dashi "yakai wannan yaro ɗan baiwa shin wane ne wancan mutumin mai matukar kama da Ni,


Kuma me yasa wannan azzalumin sarki yake son hallaka sa


Haƙiƙa ina ji a zuciya ta cewa wannan mutumin wani ne na musamman a cikin rayuwata.


Koda jin waɗannan tambayoyi sai budurwa Nihla ta matsa daf da in da Humair makaho yake da ya ke taji dukkan abinda sarki Baddadul-ulƙas da Barde Shabbaru ke tattaunawa,


Nan take ta zayyane wa yaro Humair dukkan abinda ya wakana tsakanin su,


Shi kuma ya shiga yi wa HIBAIRU bayani tun daga farko har ƙarshe,


Sa'adda Hibairu yaji bayanin abinda yafaru tsakanin sarki Baddadul-ulƙas da dattijon,


Kuma dattijon ba wani bane face Mahaifin sa Barde Shabbaru


Da irin zalunci da cin amanar da yayi masa har ya yi sanadin mutuwar mahaifin sa,


Kawai sai a kaga Hibairu ya fashe da kuka mai tsuma zuciya,


Tsawon daƙiƙa goma yana zubar da hawayen,


Sai daga bisani ne ya sanya hannun sa na hagu ya murza zoben dake hannun sa sai ga wani irin koren haske ya fita daga zoben ya bayyanar da wani Hoto wanda dukkan wanda ke wajen yana iya gani,


Majigin wata mata ne ya bayyana ɗauke da juna biyu ya bayyana ta na cikin tafiya a dajin Baitul-shamshan ta yanke jiki ta fadi kasa


Kallo ɗaya zaka yi matar ta kamu da matukar tausayin ta har ka zubar mata da waye,


Saboda yadda raunukan dake jikin ta ke zubar da jini,


A wannan hali ne nakuda ta kamata tasha wahala sosai matuka kafin ta haife abin da ke cikin ta,


Bayan ta Haihu ne numfashin ta ya ɗauke ta mutu nan take sakamakon jinin ta da ya zuba a jikin ta


Jim kaɗan da faruwar hakan sai wani aljani ya bayyana a wajen a lokacin da jaririn da matar ta haifa ke tsala kuka,


Kukan na sa ya amsa amo izuwa cikin dajin


Aljanin ya sunkiya ƙasa ya ɗauki jaririn sannnan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,


Haka dai Hoton ya cigaba da bayyana yadda Hibairu ya rayu a cikin dajin Baitul-shamshan tare da dabbobi da aljanu,


Daga farko har ƙarshe ya bayyana,


Sa'adda Barde Shabbaru yaga wannan al'amari sai ya sake fashe da kuka a karo na biyu, tamkar bazai daina ba,


Shi kuwa SARKIN SADAUKAI Hibairu yana zubar da hawaye ne bisa halin da yaga mahaifiyar sa da Yadda akayi ta rasa rayuwar ta


Kusan dukkan jama'ar dake wajen sai kwallar takaici da tausayi ta zubo musu,


Ina ban da boka Jadwar da aljani Darmanu


Da Hushriba,


Ita kan ta sarauniya Nuwairat da ta kasance azzalumi tagaban kwatance sai taji tausayin ya kamata,


Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne,


Sarki shazwan katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yaro Humair makaho ya ce" yakai Hibairu matsawar kana son ka tsira da mahaifin ka wanda a halin yanzu shi kaɗai ne ya rage maka a duniya to ya zama wajibi ka bi dukkan sharuddan dana bayyana wa mahaifinka na shiga gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA.


Da kuma bin umarnin dukkan abinda nake da buƙata,


Koda jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-ulƙas sai yaro Humair ya dubi Sarkin sadaukai ya bayyana masa abinda sarki Baddadul-ulƙas yake nufi da irin nasa yaren,


Dajin wannan batu sai hawaye suka sake zubowa HUBAIRU,


Sannan ya dubi Humair makaho yayi masa magana da irin nasa yaren shi kuma ya juya ya dubi Baddadul-ulƙas yace "A bin da Hibairu yake nufi shine zai bi dukkan umarnin ka matsawar zaka bar mahaifin sa a raye,


Amma bisa sharaɗin cewa bazaki yaudare sa ba, matsawar hakan ya faru zai yaƙe ka,


Sa'adda sarki Baddadul-ulƙas yaji wannan batu sai ya bushe da dariyar farin ciki maral misaltuwa


HUBAIRU ya tako da kafafun sa har izuwa inda mahaifin sa yake yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce ta ku ɗaya ba,


Sa'adda suka ƙurawa juna idanu sai Hibairu yaji wani irin abu ya roki zuciyar sa,


A karon farko yaji gaba ɗaya yanayin ɗabi'ar sa ta sauya,


Nan fa ya cika da mutukar mamaki da al'ajabi


Abin da Hibairu bai sani ba shine wannan abu daya ji a zuciyar sa bakomai ba ne face


Akwai wani sirrin tsafi na musamman dkaek da ke ɗauke a cikin idanun Shabbaru wanda ya gada tun iyaye da kakanni,


Bisa tsarin tsafin Dazarar mutum ya kai Shekaru hamsin shafin zai rabu dashi ya tafi izuwa jinin sa,


Sinadarin tsafin na ɗauke da dukkanin sirrikan nasara, adalci, tausayi da sauya al'amura,


Wani abu da Hibairu bai sani ba shine a halin yanzu yana dauke da dukkanin yaren mutanen duniya na kowa ne jinsi ,


Bisa mamaki koda Hibairu ya buɗi baki da nufin yace wani abu sai yaji yana magana da Yaren irin na jama'ar dake wajen,


In da ya dubi mahaifin da Barde Shabbaru Yace"ya abbana kayi sani matsawar ina numfashi a doran ƙasa bazan taɓa bari na rasa ka ba kamar yadda na rasa ummana,


Zan bi dukkan umarnin da sarki Baddadul-ulƙas yake buƙata,


Koda jin wannan batu daga bakin Hibairu sai Barde Shabbaru yayi murmushin karfin hali,


Sannan yace "ya ɗana abin alfahari kayi a halin yanzu kana ɗauke da dukkan sirrikan tsafin mu na gado,


Don haka ina da tabbacin zaka samu nasara akan dukkan abin da ka sanya a gaba,


Yanzu abin da kawai nake bukata a gare ka shine.


Dukkanin waɗancan mutane dake wannan waje sun zo gare ka ne domin ka share musu hawaye,


Don haka dukkanin su zaka cika musu burikan su bayan ka samu nasarar cinye gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA,


Domin kuwa cika burikan nasu tamkar shafe duk wani zalunci ne da azzalumai a doran ƙasa,.


Wanda ke bukatar ya bi ka izuwa birnin madinatul-shaja'a zai iya yi,


Wanda kuma zai koma izuwa birnin sa ya jira har izuwa lokacin da zaka dawo daga gasar jarumtaka ta GOGA SHA FAMA to ,


Koda jin wannan batu daga bakin Shabbaru sai Sarkin sadaukai yace "An gama ya abbana dukkan abinda ka faɗa shi za'ayi.


Dajin hakan sai Barde Shabbaru ya cika farin ciki jin Hibairu ya kira da Abban sa,


Hibairu ya juya izuwa inda sarakuna bokaye da matsafa suka yi cincirindo suna kallon abin da ke wakana,


Ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace"ya ku jama'ar dake wannan waje kuyi sani nasan cewa dukkanin ku kun taru ne anan domin na cika muku burikan ku,


To na amince zan biya kowannen ku buƙatar sa, amma sai bayan na dawo daga birnin madinatul-shaja'a,


Duk wanda zai biyo ni zai iya wanda kuma zai jira na dawo shi ma zai iya,


Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin sadaukai sai kowa dake wajen ya cika da matukar mamaki Bisa jin Hibairu na magana da Irin Yaren su,


Shin Yaushe Hibairu ya iya wannan Yaren


Amsar tambayar da dukkanin su suka kasa bawa kansu kenan.


Nan take kowannen su ya amince cewa zai bi Hibairu izuwa birnin madinatul-shaja'a domin yaga irin wainar da ake toya wa,


Domin idan suka bari sarki Baddadul-ulƙas ya tafi da SARKIN SADAUKAI yaushe suke da tabbacin zai dawo gare su bayan cewa dukkanin su sun shaida azzalumi ne nagaban kwatance bayan dukkanin su sun amince da hakan sai sarki Baddadul-ulƙas ya sake nuna Barde Shabbaru da ɗan yatsan sa na hagu nan take ya dawo izuwa cikin wannan keken doki


Sannan sarkin sadaukai yaje inda tsuntsun tsafin sa yake yakama ya hau,


Tare da goya yaro Humair makaho akai cikin hanzari ya bi bayan Sarki Baddadul-ulƙas a lokacin da tawagar su suka fara cigaba da tafiya,


Koda

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads