Showing 6001 words to 9000 words out of 27098 words
Chapter 3 - SANADIN BESTY Complete Hausa Novels by hubby .txt
dawo ta gama abincin rana tunda tasan ko mutuwa za tayi Mommy ba zata barta ta fita yau ba.
A shagon Mansur tela suka haɗu, dan Besty ne ya buɗe shagon ma, Mansoor ɗin bai fito ba, sun shafe wajan awa 4 a shagon ba tare da sun farga ba, hirar su suka sha tamkar kar su rabu, tana duba agogon wayar ta taga ɗaya saura, ai da hanzari ta fara saka takalmi, cikin rudewa take fadin
"Na shiga uku na lalace, besty Wallahi nasan Mommy ta dawo kuma zata ga gidan ba kowa" ta karashe zancen tamkar ta fasa kuka,
"Ki kwantar da hankalin ki, insha'Allah ba ta dawo ba, zo muje na nema miƙi kake napep", Besty ya fada tare da kamo hannun ta, a haka suka jera har baƙin titi, hannun su na manne da juna, juyawar da Raudah za tayi ta hango Abba yana nufo wajan su, ai bata san lokacin da ta yi ihu ta hanƙada Besty ba, sannan ta kwasa a guje, ganin ta ruga da gudu shima Besty yabi bayan ta yana gudu tare da kiran sunan ta , ba tare da ya san gudun me take ba, dan shi bai san Abba ba sai a hoto kuma bai gane shi ba yanzu...
Yau za'a sha gudun famfalaƙi, ga Raudah, ga Besty ga kuma Abba 🤣🤣
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)
G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)
M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐
Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Ku yi hakuri da ni d'an Allah , biki ne ya sha kaina shi ya sa ku ka jini shiru, amma kuna raina a koda yaushe... Luv U oll...
💓💓∂σи'т ωαѕтє уσυя тιмє ωιтн ρєσρℓє ωнσ ѕєєк αттєитισи тнєу αяє נυѕт вσяє∂ ωιтн тнєяє ℓιfє.
✍️
яυвву
PⒶⒼⒺ 6️⃣
Ganin irin gudun da su raudah su ke yi ne ya sa Abba ya koma wajan motar shi, shiga ya yi shima ya tayar a dari ya bar wajan, ɗan yana da tabbacin gida Raudah za ta je .
Ganin Raudah ta ƙi dena gudun ne ya sa Besty fara yin ihun a tare_ a tare ɗan duk a na shi tunanin aljannun ta ne su ka tashi, ganin babu wanda ya yi yunkurin tare tan ne ya saka shi neman waje ya zauna ɗan shi dai Allah ya gani ba zai iya gudu da aljannu ba, koma mene ne ya je gidan su kawai.
Abba yana barin wajan gida ya nufa, dama yazo bada sako ne, saukar shi kenan a mota ya ga Raudah da wannan yaron da take cewa ɗan ajin su ne, Abin da ya ƙara mishi takaici shine ganin hannun su manne da juna.
Raudah kam duk nisan wajan nan bata gani ba sai da tayi rabin tafiya, gajiyar da ta yi ne ya sa ta tsugunna a gefen titi tana kuka, wayar ta ce ta ke ta ringing amma ba ta da nutsuwar duba wa balle ta iya ɗauka, yanke shawarar koma wa gida ta yi, d'an haka da sauri ta tsayar da me keke napep, da kyar ta iya faɗa mai inda zata je.
Ko a cikin keken ma babu abinda Raudah ta ke yi sai kuka, shi dai mai keke ya tsaya yana kallon ikon Allah, ganin budurwa santalelliya son kowa ƙin wanda ya rasa, amma ta zauna tana zubar da hawaye, koma me yake damun ki Allah ya yaye miki yan'mata, ya fada a zuciyar shi.
Raudah kam ba ta ma san ya na yi ba, gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta, addu'a ta ke yi Allah ya sa Abba ya koma kasuwa, babban tashin hankalin ta ma Mommy ce, in dai Mommy ta dawo ba ta same ta a gidan ba to ta kaɗe, ɗan yau ta san mai ƙwatar ta a hannun iyayen ta sai Allah, ƙara sautin kukan ta yi, ba ta biyo ta titi ba, sai ta saka mai adaidaitar bi ta saman layin su, hakan ne ya sa bata ga Abba ba, d'an shi har ya zai yi kwanar shiga gida wani abokin shi ya tare shi, akan wata muhimmiyar magana da za su yi, hakan ya sa Abba ya shiga gidan abokin d'an su tattauna, amma gaba ɗaya hankalin shi na kan Raudah.
A dai_dai kofar gidan su, Raudah ta ce mai adaidaitar ya sauke ta, sallamar shi ta yi, duk da gaban ta na dukan tara_tara hakan bai hana ta tunkarar gidan ba kai tsaye, da sanɗa ta shiga da saleem ta fara cin karo a bakin pampo ya na wanke hannu, da sauri ta karasa wajan da ya ke ta na tambayar shi
"Saleem, Mommy ta dawo?"
Bai amsa ma ta ba illa ɗaga ma ta kai da ya yi alamar eh
"Na shiga uku Saleem, ta riga ku dawowa" Raudah ta ƙara tambayar shi, duk ta bi ta rikice, har yanzu jikin ta bai bar rawa ba, kasa motsi ta yi jin muryar Mommy kamar daga sama ta na faɗin
"Daga gidan uban wa ki ke"
Tsaya wa ta yi, ta gaza furta komai sai rawar jiki, bata iya bama Mommy amsa ba d'an ta san ko giyar wake ta sha ba zata iya ma Mommy ƙarya ba, ganin ta yi shiru ne ya sa Mommy ta fara nufo wajan da ta ke ai da sauri bakin ta ya fara magana
"Mommy kar ki ƙara so wallahi shagon tela na je, kira na ya yi wai bai ga kayan da na kai ba, kuma ban dade da fita a gidan ba",
Ganin Mommy ta ki ce mata uffan ne ya sa ta ci-gaba da rantaɓa bayanai kamar an kunna rediyo kaduna
"Wallahi Mommy kuma da na je sai na samu ya fita,shi ne na kira shi ya ce na jira shi, shi yasa na dade"
Wata uwar tsawa mai sa yan hanji su kaɗa Mommy ta ma Raudah
"Dan uban ki ni sa'ar ki ce? Ni za ki kalla ki shirya ma karya Raudah? Tun sha daya da rabi na dawo gidan nan ba kya nan, kuma na kira wayar ki baki daga ba, to tukunna ma a ina Abba'n ku ya ganki?"
Ai tuni Raudah ta ji wani gudawa ya taho ma ta, jin ashe ma daddy ya dawo gidan, to amma ai ba ta ga motar shi s kofar gida ba, ƙila ya ajiye ne a kasuwa ya zo a mashin, ganin gudawar da ta ke rike wa na ƙoƙarin zubo ma ta a wando ne ya sa ta suri butar da ke kusa da Saleem wanda ya tsaya kallon su, ai Raudah ba ta tsaya a ko ina ba sai saman toilet, me Saleem zai yi in ba dariya ba, ana cikin haka sai ga Abba ya shigo gidan, a fusace ya ce ma Mommy
"Mommy'n yara Raudah'n ta dawo kuwa?"
Juyawa Mommy ta yi ta na ma Abba nuni da toilet, sannan ta ce
"Abba ta dawo ina mata magana ta shiga bayi, cemin tayi wai daga shagon tela ta ke", Mommy ta karashe maganar cike da takaici dan ita fa halayen Raudah yanzu sun fara ba ta tsoro".
Abba ya ciro wayar shi yana dannawa, sako ya tura sannan ya dago ya kalli Mommy, ya ce
" Kwarai daga shagon tela ta ke, amma ita da wannan ɗan iskan yaron da na raba ta da shi jiya, saboda ta nu na min ban isa ba shine ta je wajan shi har su na rike ma juna hannu"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!! Alh!! rike hannu fa? To Allah ne kaɗai ya san me yaron nan yake aikatawa da Raudah tunda a idon duniya ma sun iya riƙe ma juna hannu, to wa ya san me suke a ɓoye? Tin da dai ba'a shedar yaran yanzu" kana ganin Mommy ka ga wacce hankalin ta ya tashi, to ba dole ba ace an ga y'ar ka da wani hannun su manne da juna...
Ƙasa hakuri Mommy ta yi, dama Mommy ba sai zuciya ba, dan ba ta iya ɓacin rai ba, hanyar toilet ta nufa a zuciye, cikin ɓacin rai ta fara buga ƙofar, d'an Raudah da ta shiga sakata ta sa ka ta ciki, bugawa Mommy ta ke da ƙarfi tana ce wa
"Ki bude ki fito, yau sai kin faɗa min abinda kuke yi ke da wannan shegen yaron da ku ka ƙasa rabuwa da juna"
Jin Mommy na buga kofa kamar zata balla ne ya ƙara hautsina cikin Raudah, ai kuwa tana gudawar ta kara taho wa kamar pampo, ta na yi tana rusa ihu tare da magiya...
😂😂 Fan's ɗin Raudah yau fa besty ya ja ma mutuniyar ku gudawa, da alama sai Mommy ta ɓalla ƙofar za ta bude, Ni dai na tafi kiran besty mu kai agaji gwanda mu haɗu mu rarrashi Abba da Mommy kar su dakan ma na matar besty....
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)
G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)
M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐
Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
💓💓ѕмιℓє ιи fяσит σf ρєσρℓє ωнσ нαтє уσυ… υя нαρριиєѕѕ кιℓℓѕ тнєм…
✍️
яυвву
PⒶⒼⒺ 7️⃣
Abba ne ya umarci Mommy da ta bar Raudah ta ƙara sa uzurin ta, tunda ai dole zata fito a bayan gidan komai daɗewa, badan Mommy ta so ba ta shige cikin gida ba tare da ta ce uffan ba. Bin bayan ta Abba ya yi da kallo mai ma'anoni daban_daban, shi dai yana jin daɗin yadda Mommy ta ke tsaye a kan tarbiyyar gidansa, a kullum yana ƙara gode ma Allah da ya ba shi mata ta gari, ba kamar wasu matan ba da za kaga suna goyon bayan ya'yan su idan sun yi laifi, wasu iyayen ma idan an ma yaran su faɗa ko an hukunta su, koda kuwa mahaifin su ne ko yayun su, kai koda wani ne daban sai kaga sun ji haushi ko su nuna ran su bai so ba, wasu marasa hakuri ma sai sun mayar da martani.
Saleem dake tsaye har yanzu shima ya bi Abba da Mommy ciki ɗan daga shi sai Arya ne a gidan Mubasheer bai dawo ba, su sai karfe biyu da rabi suke tashi saboda lesson ɗin da suke tsayawa yi, tunda a shekarar nan zai zana SSCE.
Dee kam gajiya ya yi da zama a baƙin titi, gashi ya gaji sosai, shi anya ma zai iya zuwa gidan su Raudah yanzu? tashi ya yi jiki a sanyaye ya koma shago da zummar ya kwanta, in yaso zuwa yamma sai ya je gidan su Raudah.
Mahifin Noor na office ya ci karo da sakon Abba'n Raudah, hakan ne ya sa ya yanke shawarar kiran shi a waya, domin maganar ta shi mai muhimmanci ce, amma bai daga ba, ganin ya kira sau biyu bai dauƙa ba yasa ya hakura, ya san idan yaga ƙiran shi zai biyo baya, yanke shawarar kiran Noor ya yi, ringing biyu ya ɗaga wayar
"Assalamu alaikum Baba, Barka da rana"
Daga ɓangaren mahaifin Noor ya amsa cike da jin daɗi, yana son ɗan shi, kasancewar Noor yana da biyayya da sauƙin kai, cikin farin ciki Baba ya ce
"Son kana lafiya?".
"Lafiya lau alhamdulillah Baba, ya aiki?".
"To Alhamdulillah, komai na tafiya yadda ake so, amm...dama saƙo ne naga sirikin ka, ya turo min aƙan maganar bikin ku, to amma dai maganar ba ta waya bace, zan shigo a weekend ɗin nan insha'Allah, kai dai ka kasance cikin shiri".
Duk da Noor bai fahimci maganar ba, sai kawai ya sosa ƙeya tamkar yana gaban Baba, cike da ƙunya ya ce
"Allah ya dawo da kai cikin koshin lafiya da aminci Baba".
Sosai mahaifin Noor ya ji daɗin wannan addu'ar da gudan jinin shi ya yi, murmushi ya yi cike da farin ciki ya ke faɗin
"Amen Nuradden, Allah ya yi maka albarka, ka gaishe min da yan gidan , ko da yake kafin nan ma zan kira mahaifiyar taka".
"To shikenan Abba".
Noor ya amsa cikin ƙwantar da kai da nuna tsan_tsar biyayya ga Baban shi, ko wannen su ya ajiye waya cike da kewar junan su, ɗan akwai soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin iyalan Alh Mukhtar Baba, kan su a haɗe ya ke.
Nuradden shine ɗan su na fari sai Khadijah dake bin shi, sannan Hauwa'u ɗuk matan suna da aure Noor ne kaɗai ya rage ( shima kuma zai amarce da Raudah'n Besty🤣), mahaifiyar su, Mama Hajara mace ce mai dattako da mutunci, tana mutunta kowa, amma fa bata iya ɓoye soyayyar da take wa yaran ta a ko'ina, bata son Abinda zai taba su, duk da haka ba ta lalata yaran ba, ta basu tarbiyya dai_dai gwargwado, ɗuk gidan Alh Mukhtar Baba kowa yafi son Noor, ko dan kasancewar shi kaɗai ne namiji, shi yasa ake ma bikin shi tanadi na ban mamaki...
Sai da Raudah ta share wajan mintuna arba'in a toilet sannan ta iya fitowa, a hankali ta ke taƙawa tamkar wacce ta yi nakudar yan uku, Arya ce kaɗai a kofar kitchen da alama wani abin ta ke yi, ɗauke kai ta yi daga kallon Arya ta nufi hanyar shiga parlour'n su, a baƙin ƙofa ta ja ta tsaya jin Muryar Abba da Mommy suna magana
"Tabdijam! Yanzu Abba bai fita ba?, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wallahi na san yau ba mai ƙwata na a gidan nan".
Raudah ta faɗa, wasu hawayen baƙin ciki na zubowa a Idanun ta, jin an rangaɗa sallama ne ya sa ta juyo da sauri ɗan ganin waye
Ai kuwa da gudu ta karasa shigewa cikin parlour'n tamkar wacce ta ga mala'ikan mutuwa, ganin wanda Abba ya kira, ta san yau za taci ubanta.....
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)
G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)
M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐
Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Ina godiya sosai da addu'oin ku a gare ni bisa rashin lafiyar da nayi na kwana biyu, Allah ya saka muku da alkhairi, ina son ku sossai Sanadin Besty Fan's 1&2, Allah ya bar zumunci 👍
вєαυту fα∂єѕ αfтєя тιмє, вυт ρєяѕσиαℓιту ιѕ fσяєνєя!
✍️
яυвву
PⒶⒼⒺ 8️⃣
Ko da Raudah ta shiga parlour'n ma rasa inda zata nufa ta yi, gaba ɗaya ta rikice, cikin ta ne ya kuma kaɗawa ganin Mommy da Abba na bin ta da wani irin kallo, Allah ya so ta ma a iya kaɗawar ya tsaya.
Sallamar shi ce ta kuma ratsa dodon kunnen ta, ya na neman izinin shigowa cikin parlour'n, ai bata san lokacin da ta karasa gaban Abba ba, ƙafafuwan Abba ta kamo tana kuka tamkar ranta zai fita, hakan ya yi dai-dai da karasowar shi cikin parlour'n yana faɗin
"Yaya ai da tura ta kayi chan gidan ma ba sai na zo ba"
Murmushi Abba ya yi ya ce
"A'a Babangida, gata a nan ai ba inda ta isa ta je, naga ni ta raina ni ne shi yasa na ƙira ka, jiya-jiyan nan na gama mata kashedi a kan wannan ɗan iskan yaron, dake ban isa da ita ba shine ko awa ashirin da hudu ba a rufa ba ta tsallake maganar"
Kai da ganin yadda Abba yake magana kasan ran shi ya ɓaci sosai, yasan idan yace zai kuma mata hukunci to zai loosing control ɗin shi ne a kanta, baya son magana sau biyu, amma Raudah na neman chanja shi daga tsarin shi.
Babangida ne ya kalli Raudah da har yanzu jikin ta bai bar mazari ba , ya daka ma ta tsawa!!
"Za ki zo ne ko sai na zo wajan dan ubanki?".
Da rarrafe ta ƙara sa wajan da ya ke, tana gunjin kuka, hannaye biyu ta haɗa alamar roko cikin rawar murya ta ke faɗin
"Uncle dan girman Allah kar ka dake ni, wallahi ba zan kara ba na maka alkawari, kuma idan na kara..."
Ai uncle bai bari ta ƙara sa maganar ba ya buge baƙin ta da bayan hannun shi, kan kace kwabo kuwa bakin Raudah ya fashe sai jini da ke zuba, hannu ta sa ta tare jinin tana kuka, belt