Showing 3001 words to 6000 words out of 27098 words
Chapter 2 - SANADIN BESTY Complete Hausa Novels by hubby .txt
nufa, a kofar shagon ya ga Abba zaune da abokan shi suna hira, cikin girmamawa da kunya ya tsuguna ya gaishe su , ganin yanayin shi yasa Abba tashi yace su shiga shago
"Nuru me yake damun ka na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?" Abba ya tambaya yana tsare shi da ido
"A'a Abba , kawai na kasa hakuri ne ma shi yasa na ga ba zan iya jira ba har sai nazo na fada maka abinda ya faru yanzu, saboda banji daɗin abin ba"
"Subhanallah, Nuru faɗa min mene ne ya faru ɗan Allah"
"Abba dama ba wani abu bane so nake kawai ka ma Raudah magana akwai wani yaro sunan shi Kamaludeen tana ce masa Dee, to abokin ta ne, sam Abba bana son alaƙarsu kuma nasan da wuya idan kana da masaniyar suna tare, shi yasa nace bari na faɗa maka domin ayi wa tufkar hanci" cewar Noor yana kara russunar da kanshi ƙasa.
Ran Abba ba ƙaramin baci ya yi ba kuma Noor ya kula da hakan , ƙara kwantar da murya ya yi
"Abba ba wani abu bane fa kawai dai magana zaka ma ta" ya fadi haka ne ɗan ya ga Abba ya dauki abin da zafi dama yasan halin Alh Adamu mahaifin Raudah baya ɗaukar raini kuma mutum ne da yaƙe tsaye tsam akan iyalinsa, sa'annan baya magana biyu idan yace eh to eh ne haka idan yace a'a to fa a'a nan ne, shi ya sa mutane su ke ganin girman shi da kimar shi"
Abba ya ce
" Kar ka damu Nuru, ai kai da Raudah duk ɗaya ku ke a wajena, insha'Allah zata gane ƙuskuren ta, kayi hakuri, ina ga ma zan kira mahaifin ka, idan ya shigo ƙarshen satin nan mu zauna a saka ranar auren kawai hankali na zai fi kwanciya"
"To shikenan Abba Allah ya ƙara girma"
"Amen Nuru, Kai kuma Allah ya maka albarka"
"Amen Abba"
Ganin ba wanda ya ƙara cewa komai a cikin su yasa Noor tashi ya ma Abba sallama, ya koma office.
Ko a cikin adaidaitar hira suke cike da nishadi, tabbas suna jin daɗin kasancewar su tare a lokuta da yawa, koda suka sauka Raudah ce ta biya kuɗin, kasancewar shi Dee ba wani kudi ne da shi ba, ɗalibi ne ya na ajin karshe a jami'ar ATBU Bauchi, jakar hannun Raudah ya karba ya riƙe har suka karasa shagon tela, kai idan ka gan su zaka ɗauka masoya ne, dama telan abokin Besty ne haka suka zauna suka sha hira sai wajan ƙarfe uku na rana suka bar shagon a tare suka tafi, sai da ya rakata har ƙofar gida sannan ya juya ya tafi yana ta wurgo mata kiss da hannu, wasu samarin anguwan ne da su ke zaune a saman dakali su ke gulmar Raudah ƙasa_ƙasa, kallon su Raudah ta yi ɗan tabbas taji me suke faɗa a kanta, harara ta galla musu ta yi shigewar ta cikin gida.
Gidan su Raudah matsakaici ne dai_dai zaman mutum daya, akwai flowers wanda aka ƙawata gefe da gefe compound din gidan, sai rijiya da pampo duk a waje ɗaya, daga chan gefe wajan ƙarshen gidan a nan toilet yake, flat biyu ne a gidan sai daƙin tsakar gida da kitchen madaidaici, a gefen kitchen ɗin store ne da yawanci tarkacen su suke ajiye wa, ba za'a ce da gidan su Raudah gidan masu kudi ba, amma suna da rufin asiri ɗan ba abinda suke nema su rasa a wajan Mommy da Abba, kasancewar Abba ɗan kasuwa, Mommy kuma malamar makarantar primary'n gwamnati ce.
Raudah ce ƴa ta farko a wajan Alh Adamu sai Mubasheer da ke binta, sai Salem sannan auta Arya, Raudah nada shekara ashirin, tana zuwa school of nursing, shi kuma Mubasheer shekarar shi 17 yana SS 3 , sai Saleem ɗan shekara goma sannan auta Arya mai shekara biyar ta na nursery three, suna samun kulawa da tarbiyya yadda ya kamata kasancewar mahaifin su da mahaifiyar su basa ɗaukar wargi, suna da wasa da dariya da yara amma kuma hakan baya hana su tsawatar musu idan su ka yi ba dai_dai ba..
Wajen ƙarfe takwas na dare a lokacin Raudah ta iddar da Sallah, tana zaune suna chart da Besty, sai ga Salem ya shigo dakin ta
"Anty Abba yana kiran ƙi"
Damm gaban ta ya faɗi na ce "na shiga uku Salem me nayi?"
Dariya Saleem ya sheke da shi ya na tafa hannu tare da faɗin
"Kaiii Anty!! Kinga yadda kika zaro ido kuwa, sai kace an ka ma kaza za'a yanƙa" yana fadar haka ya fita ya bar ma ta ɗakin, jiki a sanyaye ta tashi bayan ta kashe data ta ajiye wayar a kan daddimar salla ta fice, a hankali ta ke tafiya kamar wata munafuka, kasancewar ba wuta, a haka ta karasa falon Abba.
Da sallama ta shiga, ganin Mommy a wajan yasa gabanta kara faɗuwa, gefe ta samu ta zauna ta raƙube tare da cewa
"Sannu da dawowa Abba"
"Ba abinda na kira ki kimin ba kenan" Abba ya fada a hasale, ya cigaba da faɗin "dan ubanki waye Kamaludeen?"
Cikin In inaa Raudah ta ce
"A...a Abba ɗan makarantar mu ne, tare mu ka gama secondary" ta karashe zancen baƙin ta na rawa
Mommy ta ce
"Makarantar ubanki, yanzu Raudah kaf a cikin ƙawayen ki mata ki tasa wacce za kiyi ƙawa da ita sai namiji? Kisa mahaifin ki yana ganin kamar da haɗin bakina?"
"Mommy dan Allah kuyi hakuri"
Abba ne ya tashi a fusace ɗan jin zuciyar shi yaƙe kamar zata fashe saboda baƙin ciki ya kalle ta ya ce
"Raudah abota!! Abotar ma da namiji", girgiza kai ta shiga yi ganin Abba na matsowa da bulala yasa ta fara ja da baya tana kuka da faɗin ya yi hakuri baza ta ƙara ba, ai kuwa sai da ya zane ta tas, ko hakuri Mommy bata bayar ba a cewar ta ita ta jama ƙanta, sai da Abba ya gaji dan kan shi ya kyale ta.
Tana ta shesheƙar kuka Abba ya ce;
"Yimin shiru!! Ba zaki mayar da ni mutumin banza ba kuma wlh babu ke babu wannan yaron, Kada na sake ji ko ganin ku tare" Yana gama fadar haka ya yi shigewar shi ɗaki, Mommy ma ta bishi bata ko kalle inda Raudah take ba..
Dafe kirji Raudah tayi ɗan kalaman Abba sun razana ta, kuma suna ma ta yawo a kwakwalwa, tashi ta yi tsaye tare da faɗin
Kaiii!!! Innaaa!!! Wallahi ba zai taba yiwuwa ba ace na rabu da Dee, munafukin da ya faɗa ma Abba a kan shi zan sauke...
😂😂Toh fa da alama Noor ya jama soyayyar shi
Ku ci-gaba da bin alƙalamina ɗan jin yadda zata ƙaya...
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)
G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)
M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐
Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
💓💓 ∂σи'т ¢αяє fσя тнσѕє ωнσ αяє ιgиσяιиg уσυ
¢αяє fσя тнσѕє ωнσ αяє ιgиσяιиg σтнєяѕ fσя уσυ
✍️
яυвву💓
PⒶⒼⒺ 4️⃣
Da kyar Raudah ta iya koma wa ɗakin ta, ko Arya da ta ke ma ta magana a falon Mommy bata kula ba, so kawai ta ke ta ƙira Noor ta mai rashin mutunci, ɗan kawai yaga tana son shi , shine zai fara hadata da iyayen ta, har ya sa Abba ya ɗake ta, to ba zata saɓu ba bindiga a ruwa.
Haka dai ta yi ta kullawa da warware wa har ta isa ɗakin, ko kallon gaban ta ba ta yi ba,tsabar takaici da baƙin ciki, waya ta dauka ta na kiran Noor amma har wayar ta tsinƙe bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ƙular da ita ya kuma yi ba, bata gaji ba ta ci-gaba da kira amma still bai dauƙa ba, sai da ta ƙira shi wajan sau goma sannan ta hakura, number Besty ta ƙira ringing biyu ya daga
"Hello sarauniyar ya kike?" Jin tana shesheƙar kuka ne ya hana shi ƙara sa maganar da ya yi niyya tuni ya rikice da faɗin
"Haba baby what's wrong kike kuka? Ko wani abu na miƙi? Dan Allah ki fada min" ganin Raudah taƙi dena kukan yasa Dee fadin "gani nan zuwa gidan tunda ba za ki faɗa min ba"
Da sauri Raudah ta ce ,"a'a ba sai ka zo ba zan faɗa maka"
Duk yadda suka yi da Abba Raudah ta faɗa ma Dee, ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin
" Wlh Raudah ban da kin nace da rabuwa ki ka yi da Nuru, mutum sai ɓakar zuciya da baƙin hali kamar kafuran farko, Ni wlh taurin kan shi ne ma na ke jiye miƙi"
"To ya ka ke so nayi ne Besty" ni fa ba wannan bane damuwa ta, babbar damuwa ta maganar da Abba ya min ne, cewa fa ya yi wai bani ba kai, kuma kafi kowa sanin bazan iya rabuwa da kai ba" ta ci-gaba da shesheƙar kuka
"To kiyi hakuri ki dena kukan mu yi magana ta fahimta, idan ina jin kukan ki har jijiyar ƙaina tashi ta ke yi" da kyar da kalamai masu ɗadi da ratsa zuciya Besty ya rarrashi Raudah ta dena kukan,
"Ko kefa" ya faɗa cike da tsokana
Murmushi ta sakar mai sauti kamar ta na tare da shi, dama tasan shi ne zai saka ta farin ciki, ɗan ba shi da burin da ya wuce hakan a ko da yaushe, in ta tsinci kan ta a damuwa, to wannan fa aikin Besty ne ya yi ƙoƙarin samar mata da farin ciki komai wahalar shi, shi yasa Raudah ba ta shayin fada mai ko mene ne ya same ta ko ya ke damun ta, abokin shawarar ta ne babu abinda ta ke iya boye mishi, ta riga ta sabar ma da ƙanta fada ma Besty damuwar ta ko farin cikin ta...
"Kiyi hakuri kin ji Raudah!! insha'Allah ba zamu rabu ba, haba ni da ke ba rabuwa sai dai mutuwa ce za ta raba mu, muna nan tare har da ke har abada" Besty ya faɗa cike da son kwantar ma ta da hankali
Ajiyar zuciya Raudah ta sauke,
"Nima haka na ke fata my Better half, Allah ya ƙauda idon maƙiya"
"Kaiii!! Raudah Abba'n ne maƙiya?lallai baki da hankali ashe" ya faɗa cike da fushi har ya na hura hanci kamar tana gaban shi
Da sauri Raudah ta ce "a'a bestyna nifa ba da Abba na ke ba, da Noor na ke, ɗan nasan shine ya kai gulma wajan Abba kuma wallahi sai na mishi magana zai gane ya sa an dake Ni" Raudah ta faɗa cike da tsiwa
Dariya Besty ya kwashe da shi, sai da ya yi mai isar shi sannan ya ce
" Kar ki yadda ki mai magana, ki saƙa shakku a zuciyar shi, ko a fuska kar ki nuna mai anyi wannan maganar hakan zai rage mai ƙwarin gwiwar ƙara tarar Abba da irin wannan maganar koda wataran zai ƙara ganin mu tare, sannan maganar haɗuwa kuma zan san yadda za'a yi mu dinga haduwa ba a layin ku ba"
Murmushi Raudah ta sake ɗan ta ji daɗin wannan shawarar, kuma ta gamsu da hakan, hira suka ci-gaba da yi har Arya ta shigo ta, dangwarar ma ta da book ɗin assignment ɗin ta tayi ta ce
"Anty!! Mommy ta ce na kawo ki koya min kuma ta ce kar ki yadda ki dake ni"
Sakkowa Raudah ta yi daga kan gadon ta fara koya mata assignment ɗin ba tare da ta ce ma ta komai ba kuma hakan bai sa ta yanke wayar ba...
Misalin ƙarfe takwas da rabi Adnan ya iso kofar gidan su Fadeelah, sauka ya yi a kan mashin ɗin shi, kasancewar layin nasu shiru ne, ba shi da hayaniya sossai, karasa wa ya yi wajan wata barandar da ake kiwon shanu, akwai wani waje ta gefen barandar kamar lungu a inda ake ajiye abincin shanun, wayar shi ya zaro a aljihhu ya kira Fadeelah ya sanar ma ta ya iso.
Bayan minti biyar sai ga Fadeelah ta fito daga gida da wani zumbulelen hijabi, taku taƙe cike da yanga dan dama ita akwai ƙaudi, iyayi, rawar ƙai, uwa uba kuma yanga,
Idanu ya tsira ma ta har sai da ta ce "matsa mana na shiga ƙar wani ya ganni" ai da sauri ya matsa mata ta shige cikin lungun, tana karasa cire hijabin da ke jikin ta, daga ita sai pant da bra, ganin haka ya sanya Adnan sakin murmushi, janyo ta ya yi, ya fara aika mata da sakkoni, sun yi nisa cikin jin dadin su kawai sai ganin hasken wuta suka yi yana nufo wajan da suke da alama za'a shiga wajan abincin shanun ne...
Toh fa reader's, 🤣😂 wannan shi ake kira da dirimm babban motsi!!!
Yau fa ƙaryar Adnan da Fadeelah ta ƙare dan nasan zasu daku a wajan nan...
VOTE
COMMENTS
SHARE
✍️
BADAWEEYERH
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐
L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️
R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)
G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)
M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻
https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐
Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ
Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️
Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ
Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ
Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Nα rαѕα dα wαccє írín kαlmα zαnчí αmfαní wαjαn nunα fαrín cíkí nα α gαrє ku mαѕσчα líttαfín ѕαnαdín Bєѕtч, ѕhαrhín ku nα ѕαkα ní níѕhαdí, nα gσdє ѕσѕαí, Allαh чα вαr mu tαrє Bαєѕtíєє'ѕ Dínα🤪
яєѕρє¢т fσя тнσѕє ωнσ ∂єѕєяνє ιт,иσт fσя тнσѕє ωнσ
∂ємαи∂ ιт 💓💓
яυвву✍️
PⒶⒼⒺ 5️⃣
Da sauri Fadeelah ta mayar da hijabin ta jiƙin ta na ƙyarma, gani haka shima Adnan ya rikice, dagan ganin hasken ya kusa ƙaraso wa wajan da suke, yana daga da karyo kwanar lungun wayar shi tayi ringing
Tsaya wa Mallam Sule ya yi yana amsa ƙiran da aka mishi a waya, hakan ya bama Fadeelah damar fita da sauri ta bayan lungun kasancewar aƙwai maɓoya ta baya,
Ganin haka yasa Adnan matsowa daga wajan lungun shima ya dawo dai_dai rumfar shanun, haska shi Baba Sale ya yi ganin yana zufa kamar sabon ɓarawo yasa ya kasa yadda da shi, gaba ɗaya Adnan ya ruɗe da ganin irin kallon da Baba Sale yaƙe mishi.
"Saurayi me ka ke yi a nan? Baba Sale ya tambaye shi
Cikin in ina da rawar murya Adnan ya ce;
"Am im, da da dama amm ina jiran wani ne"
Ƙara haska shi Baba Sale ya yi sannan ya ce " yaro alamun ka sun nuna kamar baka da gaskiya, kodai irin barayin yaran nan ne kai"?
Da sauri Adnan ya girgiza mai ƙai yana faɗin
"A'a Baba wlh ka yadda da ni, ni ba mugu bane wallahi kaji na rantse maka"
Goro Baba Sale ya ɓantara tare da cewa
"Ahaf!! Yoo mugu yana da kama ne? Ai da yana da kama da matsalar tsaro ta ragu a ƙasar mu"
Ganin maganar ba zata ƙare ba ne ya sa Adnan ciro dari biyar a aljihu ya miƙa ma Baba Sale, Yana murmushi ya ce
"Ga wannan ba yawa Baba, a siya goro"
"Chabdi jam!! Niii na karɓi kuɗi a hannun ka? A'a ba haka nake ba, haka kurum ban san ka ba, ban taɓa ganin ka ba, kai ko me kama da ƙai ban taɓa gani ba, ai hakan ba zai yiwu ba" Baba Sale na gama faɗan haka ya shige cikin lungu ɗan dama ya manta bai saƙa ma shanun da yake kiwo abinci band shine ya fito sai kuma babban ɗan shi ya kira shi a waya.
Adnan na ganin shigar Baba Sale lungun ya sauke ajiyar zuciya, bai ko tsaya ƙara neman Fadeelah ba ya yi tafiyar shi.
Noor yana kwance a ɗakin shi da daddare, babu abinda yake yi sai tunanin halayen Raudah, shi dai yasan yana son ta so na haƙika, kuma itama ya tabbatar tana son shi, to amma wannan yaron da yake barazana da farin cikin shi yana kawo masa tsaiko da ruɗani a cikin soyayyar shi da Raudah, dole ne fa ya nemi mafita tun ƙafin dare ya mishi, wata zuciyar ce ta ce mishi;
"Ai kuna yin aure zata dena tunda a lokacin ta zama mallakin ka gaba ɗaya, kaga sai yadda kayi da ita"
Da wannan shawara da kwarin gwiwa da ya samu daga zuciyar shi ya saka hankalin shi kwanciya, ya ci-gaba da ayyukan shi a laptop hankali kwance...
Sai da Raudah da Besty suka kwashe wajan awa uku suna chatting tare da alƙawarin za su haɗu washegari a shagon aɓokin shi tela, sannan suka kwanta bacci kowa zuciyar shi cike da farin ciki...
Da safe tun da asuba Raudah ta tashi daga bacci, bata sake koma wa ba, kasancewar yau tasan Mommy na fushi da ita shiyasa ta fara ayyukan gidan da wuri, karfe takwas ta gama komai har Arya da saleem sun tafi school, Abba ya tafi kasuwa, Mommy ce kaɗai ta rage bata fita ba kuma ita ma yanzu take shirin fita.
Mommy na tafiya maƙaranta Raudah ma ta shirya ta fita, dan tun wuri suka tsara haɗuwar su da besty kafin time ɗin da su Mommy za su dawo daga school tasan har ta