Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 27098 words

Chapter 4 - SANADIN BESTY Complete Hausa Novels by hubby .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ɗin jikin shi ya kunce, ganin haka Raudah ta ƙwalla uban ihu tana ƙara bashi haƙuri, nufar in da Mommy ta ke zaune ta yi,


"Mommy wallahi zai kashe ni, Mommy dan Allah ki bashi haƙuri ba zan sa ke ba, Please Mommy".


Duk da Mommy ta tausaya ma ta ganin irin kukan da ta ke yi, amma bata nuna tausayin na ta a fili ba, saboda ko ba komai gidan miji za su kai Raudah, kuma ba zata so ta bar musu abin kunya ba, ko ta janyo musu magana a gari tunda har sun iya riƙe ma juna hannu da namijin da ba muharramin ta ba, to gwanda su yi wa tufkar hanci tun wuri, to idan Raudah ba ta dena waɗannan halayen da ta tsiro da su ba ai kuma ba'a san a inda abin zai ƙare ba, tashi Mommy ta yi ta bar parlour'n dan ba zata iya zama ba, shima Abba miƙewa ya yi ya bi bayan Mommy, ɗan ya lura da halin da ta ke ciki, kuma shima hakan ya ke ji a ranshi, sai dai fa ba zasu ƙi hukunta Raudah ba saboda suna son ta, inaaaaa!! Ai a irin tsarin gidan ma babu ɗan da zai gagare su hukunci ko da nan gaba ne, saboda idan suka goyi bayan yara a kan rashin gaskiya to fa a karshe sune za suyi kuka, tare da dana sani mara amfani.



A mamakin Raudah sai ta ga uncle ya zauna, ajiye belt ɗin ya yi a gefen kujera, ganin ta ƙura mai ido ya sa shi faɗin


" Ba za ki zo ba sai na zo wajan na cire Waɗannan shegun idanun na ki masu kama da na mujiya".


Ai da sauri Raudah ta tashi, ƙaraso wa ta yi wajan da ya ke ta tsugunna tare da sunkuyar da kai ƙasa kamar wata ta arziki...


"Waye wannan yaron da ki ka maƙale mai, wanda har yaya da kanshi zai raba ku amma kiyi kunnen uwar shegu?"


Uncle ya tambaye ta cikin daka tsawa


Cikin shesheƙar kuka ta fara magana


"Uncle wallahi ba komai a tsakanin mu da shi, class mate ɗina ne lokacin muna secondary school, bayan haka babu komai, kaji na rantse".


Kallon ta uncle ya ke cike da son gano gaskiyar abinda ta ke faɗa, ya yi tunanin ba iya dukan bane kadai zai wadatar musu, dole sai an hada da yi ma ta nasiha da tunatar wa, gyaran murya ya yi sannan ya ce


"Raudah kin ga wannan abun da muke miƙi? Wallahi shine gatan ki, baki da waɗanda suka fi iyayen ki duk duniyar nan, riƙe mutuncin ki abin alfahari ne a wajan su kamar yadda zubar da mutuncin ki abin takaici ne da tozarci a gare su, dan haka kece kadai mafitar gidan nan, darajar gidan nan ke zaki daga ta a wajan al'ummar da suke ganin ƙima da darajar iyayen ki, kuma ke kan ki kin sa ni, wanda za ki aura wato Nuradden ɗan manyan mutane ne, to da'a ce yau mahaifin Nuruddeen ne ya ganƙi a yanayin da Abba'n ki ya ganki ya zai ji? To wallahi fasa auren za'a yi duk kuwa son da kuke ma juna da yaron na shi, kuma shi wannan sha-sha-shan ba da kuke yawon gantali a gari ba zai taɓa auren ki ba".


Haƙika maganganun sa sun ratsa zuciyar Raudah, jikin ta ya yi sanyi laƙwas, cikin sanyayyar murya wadda har ta fara dashewa saboda kukan da ta yi, ta ce


"Uncle kayi hakuri insha'Allah ba zan ƙara ba, kuma zan bama Abba da Mommy hakuri, kai ma ɗan Allah ka taya Ni basu haƙurin".


Jin-jina kai uncle ya yi, ganin jikin Raudah ya yi sanyi fiye ma da yanda yake tunani, kamo ta ya yi ya zaunar da ita ɗan da a tsugunne ta ke,


"To shikenan Raudah in dai kin kiyaye babu wanda zai kara taba lafiyar jikin ki, kuma zan taya ki bama Abba da Mommy haƙuri, sai dai Raudah akwai wani hanzari ba gudu ba..."








Ba'a iya haka Adnan ya so su tsaya da Fadeelah ba amma wannan Mallam Sule'n ya kwafsa mishi, ko da ya koma gida kiran ta ya yi a waya ta na daga wayar ya sauke ajiyar zuciya


"Fadeelah Baba Sule ya kwafsa min wallahi, ba ki ji yadda na ji ba, ko kaɗan ban ji daɗin yadda ya katse mana jin dadi ba, a hannu na ke".


Fadeela ma cikin yanayin rashin jin dadi wanda daga muryar ta ma zaka fahimci hakan ta ce


" Wallahi kuwa Bestynah, amma fa na ji dadi da Allah ya rufa mana asiri bai gan mu ba, ɗan wallahi da ya gan mu tare sai ya tara mana jama'ar anguwa"


Shi dai Adnan a zuciyar shi yasan yau tarkon shi zai iya cimma Fadeelah, dama haka ya ke so ta fara muradin shi da ƙanta, yasan dama wataran da ƙanta za ta kawo mishi kanta a ruwan sanyi, cikin nuna isa ya ke faɗin


"Kinga Fadeelah gobe ki fito mu hadu, kuma ba romancing na ke so ba, so na ke na karɓi budurcin ki a gobe, idan ba haka ba ki manta da ni a rayuwar ki, kuma ko a hanya kar ki nuna kin sanni saboda ba kya sona kamar yadda na ke son ki"


Yana gama faɗar haka ya kashe wayar






Chabdi jam!!!!🤣🤣🤣 Chakwalkwalin chakwakiya kenan, shin Fadeelah zata amince ta mallaka wa Besty Adnan budurcin ta kafin Aure kuwa?


Ga kuma Raudah'n Besty an ce akwai magana a kasa... Ko me Uncle zai faɗa ma ta....




Ku ci-gaba da bina dan jin yadda za ta kaya.....






VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH


💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




PⒶⒼⒺ 9️⃣


Kallon mamaki Fadeelah ta bi wayar hannun ta da shi, a iya zaman da suka yi da Adnan bai taɓa mata haka ba, Ita dai ta san ba soyayya suke ba amma kuma ta bashi muhimmanci sossai a zuciyar ta, ta yadda ko ɓacin ran shi ba ta so ballantana kuma a ce ita ce sanadi, number shi ta ƙara gwada wa amma sai ta ji a kashe, saƙo ta rubuta mai sanan ta kashe wayar ta gaba ɗaya, shirin bacci ta yi, sai da ta gama shirin ta hau gado, wata sha'awa ce ta fara damun ta hakan ya sa ta dauko wayar da ta kashe ta kunna, wani group ɗin su na mata da maza ta shiga, babu abinda ake yi a group ɗin sai batsa, ai kuwa tana hawa ta ci karo da wani hira da a ke yi mai ta da hankali, karantawa ta shiga yi cikin nutsuwa da mayar da hankali, tana cikin karatun kuma aka sako wasu zafaffan vedio masu ɗaga hankali, da kallon da tayi ne dai har ta samu relief sannan bacci mai daɗi ya kwashe ta.




A ɓangaren Adnan kuwa shima bai samu bacci ba ɗan yana cikin yanayin da in dai bai rage abinda yake damun shi ba to tabbas akwai matsala, ganin lokaci na tafiya ne ya sa ya shirya cikin kananun kaya masu kyau da daukar hankali, wayar shi ya dauka ya kira Farouk, sai da ya kira sau uku sannan ya ɗaga wayar


"Hello freind kana ina ne ina ta kiran ka baka ɗauka?"


"Mtseww kaii dan iskaa ne mutum yana tsakiyar jin dadi ka katse shi, ai dai kasan ina gida ko?" Farouk ya faɗa cike da jin haushi ɗan da yasan wannan banzar tambayar zai mai da ba zai ɗauki wayar shi ba.




"Ah lallai shine ɗan ka samun jin dadi ko ka kira ni muyi kashe mu raba kamar yadda aka saba, to gani nan zuwa dan wallahi a hannu na ke".


Bai ma jira cewar Farouk ba ya kashe wayar, ɗakin ya kulle ya fita, tunda yasan babu mai neman shi a cikin iyayen na shi koda kuwa zai kwana uku baya gida ne, ɗan iyayen shi basu cika damuwa da inda yaro yaje ba, a cewar su ai ya na da hankali zai iya kare kan shi, shi yasa bai cika kwana a gida ba.


Mashin ya dauka ya nufi gidan su Farouk, babban gida ne sosai, dake me gadi ya san da shi bai sha wahalar shiga ba tunda dama sun saba kwana a gidan, direct sashen Farouk ɗin ya nufa sai dai a kulle kofar ta ke, door bell ya danna har tsayin mintuna biyar amma ba alamar za'a bude mishi kofar, a ran shi ya ce


"Lallai Farouk ɗan iska ne ya, wato ya samu mace ai dole ya manta da ni", wayar shi ya ciro ya kira shi, ganin kiran Adnan ya sa Farouk miƙewa da wayar a hannunsa dan ya san ya zo ne shiyasa ba zai daga wayar ba, kofa ya je ya bude mishi, kutsa kai Adnan ya yi shiga


"Kaii ka ga idanun ka kuwa lallai yau akwai tada ƙura..." Adnan ya faɗa cike da zolayar abokin na shi. Wata uwar harara Farouk ya mishi yana faɗin


"Eh ba gwanda ni ba duk jarabata ai ban kai ka ba, kai kam wallahi matar da zaka aura, oh sorry Fadeelah da zaka aura ta shiga uku", ya karashe maganar yana dariya ƙasa-ƙasa, ai kuwa a ƙufule Adnan ya ce


"Kar ka ɓata min rai Mallam, na taɓa ce maka Fadeelah ce matar da zan aura? Allah ya sawwaka!! Me zan yi da wannan balagazar yarinyar da bata jin maganar kowa, kada ma ka sake haɗa ta da matar da zan aura, domin ni matata mai nutsuwa ce kuma mai tarbiyya, kamila sannan Malama, irin matar da zan aura kenan, so you better stop comparing me with that stupid"




Tin da Adnan ya fara magana Farouk ya ke kallon shi, dake a tsaye suke a cikin parlour'n, basu Karasa ciki ba suka fara wannan hirar, shi wallahi Adnan mamaki ya ke ba shi, ba wani mamakin wacce yake da burin aure ba a'a mamakin yadda ya ke deceiving yarinyar mutane kuma a bayan idon ta yazo yana zagin ta, girgiza kai kawai Farouk ya yi bai ƙara ce masa uffan ba ya nufi hanyar bedroom, ganin haka ya sa shima Adnan jan dogon tsaki ya bi bayan shi, saboda ya lura Farouk na son lalata mishi mood ɗin shi ne.


Yana shiga ɗakin yaga wata budurwa a kwance, dama Farouk ya riga shi shiga hango su ya yi a kwance cikin bargo, kallo daya ya ma yarinyar ya ga idon ta a soye ya ke, zama Adnan ya yi a kujerar da ke bedroom ɗin, yana iya ganin kallon da yarinyar take mishi, a ranshi ya ce "mayya kar ki cinye ni".




Adnan ne ya kalli Farouk ganin bashi da niyyar tashi ya basu waje gashi dama shi a mugun matse yake ya ce


"Guy ka ɗan bamu waje mana".


Ko kallon shi Farouk bai yi ba sai ma baya da ya juya musu yana faɗin


"Hmmm bana son munafurci yau ka saba yi a gabana? Nifa iyayi ne bana so, kasan dama haushin ka nake ji, idan kaga dama ka ɗauke ta kuje parlour amma nikam ba inda zan je" yana gama faɗar haka ya ƙara jan bargo ya rufe jikin shi, shi kuwa Adnan jawo hannun yarinyar ya yi wadda ko sunan ta ma bai sani ba, yasan ita ma ba baƙuwa ba ce a harkar daga ganin yanayin ta, ai kuwa narke mishi ta yi a jiki , daga haka dai labari ya chanza ( ban ga komai ba Fan's kar Fadeelah ta soka min wuka 😜).








Shiru Raudah ta yi ta bama uncle dukkan nutsuwar ta, da alama maganar da zai faɗa mata tana da muhimmanci sossai, qasa ta kara yi da kanta ta ce


"Uncle mene ne ya faru, Ko laifin nawa ba daya ba ne?".


Girgiza mata kai uncle Babangida ya yi, ganin hankalin ta ya tashi ne ya sa shi faɗin


"Ki kwantar da hankalin ki Raudah, dama Abba'n ki ne ya bani sako na baki, akan maganar auren ku da Nuradden, kin san dama kowa a shirye yake, kuma da tuni an dade da yin auren naku sai aka miki uzurin ki kammala jarrabawa a makaranta tunda kun zo ƙarshe, haka ne?"


Daga mishi kai Raudah tayi ba tare da tayi magana ba, ya ci-gaba da faɗin




"To mahaifin ki ya tsayar da bikin ku nan da sati Biyar masu zuwa idan Allah ya kaimu, sai kije ki fara shirye-shirye, kuma shima a ban'garen Nuruddeen ɗin Abba ya sanar da mahaifin shi".


Dammm!!! Raudah taji.ƙirjun ta ya buga, rasa wanne yanayi take ciki ta yi, murnar auren ta da masoyin ta da za'a yi ko kuma baƙin cikin an raba ta da Besty ɗin ta, kawai sai ta faɗa jikin kujera ta fashe da matsanancin kuka...




😂😂🤣 Raudah'n Besty Meye na kuka? Fan's ɗin Raudah ku ce mata amarya bata kuka fa ahto kar tayi ma Noor asarar hawaye.....












VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH


💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




PⒶⒼⒺ 🔟


Ganin Raudah ta ƙi dena kukan ne ya sa uncle haɗe rai, yaga yarinyar na neman raina shi, to in ba raini ba daga magana sai ta kama yi masa kuka? Tsawa ya daka mata hakan ya sa ta yi gum da baƙin ta


"Kukan me kike yi?" Ya tambaya yana zaro mata dukkan idanuwan shi, dama a kaf cikin familyn su babu wanda ake tsoro kamar uncle Babangida, yana da sauƙin kai amma yana da zafi, kuma a jinin su ne shi da Abba'n Raudah Allah ya basu baiwar kwarjini a idon mutane, shiyasa a lokuta da yawa su ne masu hukunci a cikin familyn...


Ƙasa bashi amsa ta yi hakan ya sa uncle tashi ya fita a parlour'n yana faɗin


"Kya ji da shi munafuka, ki na son mutum amma kin saka shirme da wasa a maganar aure kina son ki mayar da mu ƙananan mutane".


Haka dai ya ci-gaba da mita har ya bar parlour'n gaba ɗaya ba tare da ya nemi Abba da Mommy ba, Raudah na ganin ya fita ta miƙe, ta nufi ɗakin ta, zama ta yi a kan bed sai kuma tunanin besty ya faɗo mata a rai, kawar da tunanin ta yi ta hanyar tunawa da nasihar da uncle ya ma ta, ganin kanta na ciwo ne ya sa ta dauƙo magani ta sha, sannan ta ƙwanta, ko a baccin ma babu abinda ta ke yi sai mafarkin Besty, wai gasu a wani lambu mai korayen ganye, tana zaune a saman cinyar shi yana bata hollandia milk a baki sai zuba shagwaba ta ke yi shi kuma yana biye ma ta, suna cikin wannan yanayin ne sai ga Abba da Noor ai kuwa ta ƙwalla ƙara ta farka a gugice ta na share zufa, jin ihun Raudah ya sa Mommy shigowa da gudu cikin ɗakin tun da ta tabbatar Uncle Babangida ya tafi, saboda yana fita ya kira su a waya ya shaida musu yadda su kayi da Raudah'n da kuma roƙar su yafiyar ta, kuma suna gama wayar shima Abba ya koma shago, a guje Mommy ta ƙara so ɗakin, ganin Raudah na zaune a bakin gado tana haɗa zufa ne ya sa ta jingina da jikin Mirror, kallon mamaki Mommy ta ke bin Raudah da shi, a ranta ta ke tunanin ko dai yarinyar nan tana da aljannu ne? Saboda abubuwan da ta ke yi wasu lokutan na bata mamaki ko kuma dai tsabar iskanci ne ohooo, cike da mamaki Mommy ta kalli inda Raudah ta ke zaune, har yanzu bata bar haɗa zufa ba, duk da ta ga shigowar Mommy, sai da Mommy ta gama nazartar ta sannan ta ce


"Wai ke Raudah me yasa kike abu kamar ƙaramar yarinya ne? Ko Arya ba zata yi abinda kike yi ba, ke kenan kullum sai an miki magana? To wallahi ba zan iya ba na gaji da halin ki gwara ma ayi-ayi auren kowa ya huta ki tattara kayan ki ki bamu space ni da mijina ni ma".


Karshen maganar da Mommy ta yi ne ya sa Raudah kallon ta gami da sakin murmushi tana faɗin


"Kai Mommy kun gaji da ni kenan?"


Harara Mommy ta galla ma ta, gaba ɗaya lamarin na Raudah sai addu'a


"Eh ba dole muyi Allah-Allah ki tafi na ki ɗakin ba, Raudah yanzu kin fara chanza halin ki, tun da ki ka haɗu da wannan ɗan iskan yaron ni ƙaina hakuri na ke yi da ke, Ni dai shawarar da zan baki ita ce gwara ki rufa ma kan ki asiri ki rufa mana mu ma iyayen ki, ki samu ayi auren ki lafiya qlau ba tare da an samu wata matsala ba"


Murmushi Raudah ta yi har da rufe idanu alamar kunya, ganin haka ya sa Mommy girgiza kai kawai ta fita a daƙin tana addu'ar Allah ya raba Raudah da wannan Besty'n, Mommy bedroom ɗin ta ta koma ta fara ninke kayan Arya da almajirin gidan ya wanke.


Mommy na fita Raudah ta tashi, parlour ta fito bata ga kowa ba, hakan ya tabbatar mata da yaran sun tafi madrasah, tunowa ta yi da wayar ta, da sauri ta nufi tsakar gida, a gefe kusa da pampo ta hango jakar ta a yashe a wajan ba zata iya tuna lokacin da ta yar da jakar ba tsabar ƙiɗimewa da ta yi, Allah ya so ta ma ba'a mata dukan da tayi tsammani ba,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads