Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 27098 words

Chapter 9 - SANADIN BESTY Complete Hausa Novels by hubby .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kasancewar suna da kuɗi sosai, sai a wajen mai gadi suka samu lambar Adnan ɗin da ƙyar, a ƙofar gidan mijin Anty ya mai kira har guda uku amma bai ɗaga ba hakan ya sa suka tafi zuwa police station kai ƙarar Adnan, motar police ɗaya aka haɗo su da shi ta biyo su har gidansu Adnan ɗin aka sanar da mahaifinsa, motar shi ya shiga ya bi su station ɗin yana iƙirarin duk wanda ya ma ɗansa sharri sai ya yi Shari'a da shi, 'yan sandan ne suka ba shi umarnin ya kira Adnan ai kuwa yana liƙe da Zeenat suna ta faman abu ɗaya kiran Daddyn ya shigo da ƙyar ta bari ya fito a gidan bayan ta gindaya mai sharuɗa.....














VOTE






COMMENTS






SHARE


✍️
BADAWEEYERH


💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*
💐💐S͆A͆N͆A͆D͆I͆N͆ B͆E͆S͆T͆Y͆ 💐💐



L͆a͆b͆a͆r͆i͆/R͆u͆b͆u͆t͆a͆w͆a͆✍️


R͆A͆B͆I͆'A͆T͆U͆ A͆H͆M͆A͆D͆ M͆U͆A͆'Z͆U͆
(R͆U͆B͆B͆Y͆)




G͆a͆j͆e͆r͆e͆n͆ l͆a͆b͆a͆r͆i͆
(S͆h͆o͆r͆t͆ s͆t͆o͆r͆y͆)




M͆y͆ w͆a͆t͆t͆p͆a͆d͆ l͆i͆n͆k͆👇🏻


https://www.wattpad.com/1190086089?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
💐💐💐💐💐💐💐💐


Dᴇᴅɪᴄᴀᴛᴇᴅ ᴛᴏ


Mʏ ʟᴏᴠᴇʟʏ ᴍᴏᴍ (Hᴀᴊ Rᴜᴋᴀɪʏʏᴀ), Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ᴍɪᴋɪ ʟᴀғɪʏᴀ ᴅᴀ ɴɪꜱᴀɴ ᴋᴡᴀɴᴀ ❤️❤️




Sᴘᴇᴄɪᴀʟ ɢɪғᴛ ᴛᴏ


Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀ'ꜱ ᴀꜱꜱᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ


Aʟʟᴀʜ ʏᴀ ƙᴀʀᴀ ʜᴀᴅᴀ ᴋᴀᴡᴜɴᴀɴ ᴍᴜ ᴀ ᴅᴜᴋ ɪɴᴅᴀ ᴍᴜᴋᴇ 🤗






*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*




PⒶⒼⒺ 1️⃣5️⃣

(Last page)


Ko da ya iso police station ya ga Fadeelah sai da gabansa ya faɗi, shi ya ma manta da ita Wallahi, tana ganin shi ta tashi ta cukume rigarsa tana ihu tana faɗin:


" Ka cuce ni Adnan haƙiƙa na ga "SANADIN BESTY" Wannan abin kunyar ina zan kai shi?" Haka dai take ta sambatu da ƙyar aka ɓamɓare ta a jikinsa, bayan DPO ya saurari bayananta ne ya tambayi Adnan shin da gaske ne? Shiru ya yi bai ce komai ba Daddy ya ce:


"Ka yi magana Adnan ba shiru za ka yi ba mutanen nan so suke su ƙulla maka sharri, shirun ka ba mafita ba ne don wallahi muddin sharri suke maka sai na ɗaure su", mahaifin Adnan na ta kumfar baki ya tsinkayi muryar ɗansa yana faɗin:


"Daddy ciki na ne, tabbas Fadeelah budurwa ta ce kafin na yi aure".


"Aure? Aure fa ka ce ?" Fadeelah ta faɗa da ƙarfi saboda kalmar ta razana ta, Adnan ya ci gaba da cewa:
"Gwara na faɗa maka gaskiya daddy cikina ne a jikinta ba sharri take yi min ba"
A zabure Daddy ya tashi yana cewa "ko ka sha ƙwaya ne Adnan? Ina kai ina yarinyar nan mai zubin mayu? To wallahi ka dawo cikin hayyacinka don ba a gidana ba", yana gama faɗin haka ya miƙe zai tafi, DPO ne ya tsayar da shi ta hanyar nuna masa illar abin da yake yi gwara a bi komai a hankali kada mutuncinsu ya zube, da haka ya koma ya zauna suka tattauna yadda zasu ɓullo ma lamarin, shi dai Adnan ban da ƙyarma babu abin da jikinsa ya ke yi domin minti talatin Madam Zeenat ta ba shi ga shi an hura awa ɗaya yanzu, yana ta jin vibration ɗin wayarta amma ya kasa ɗagawa, matsaya aka samu a kan cewa zai ɗauki nauyinta har sai ta haihu, kuma duk wani dawainiya shi ne zai yi, godiya mijin Anty ya yi wa DPO suka koma gida, ita kam Fadeelah kuka kawai take yi da nadamar abin da ta aikata , ko a yanzu Adnan ya gama da ita ya ma ta illar da ba za ta taɓa gogewa a jikin ta ba, ta bi son zuciya ai kuwa yau ta tabbatar da "SANADIN BESTY" ta ga babban darasi a rayuwarta.




A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da daɗi gobe babu har cikin Fareedah ya shiga wata huɗu, ba ƙaramar wahala cikin yake bata ba, ga shi mijin Anty ya koma, tsakanin ta da Anty kam abin ba sauƙi, tana gida babu inda take zuwa kuma tun daga ranar da suka je police station har yau Adnan bai sake zuwa ba, tsananin da ta ke ciki ne ya sa ta fara tunanin hanyar da za ta bi ta zubar da cikin, Google ta shiga ta fara browsing ai kuwa ta ci karo da magani kala-kala ba tare da tayi tunanin komai ba ta rubuta su a wata yar ƙaramar takarda ta ɓoye, tunanin inda za ta samu kuɗi ta yi, can sai ta miƙe tana murmushi ta nufi dakin anty domin ta ji fitar ta daga gidan, purse dinta ta buɗe ta ga kuɗi a ciki dubu biyu ta zara sannan ta fice a gidan, machine ta hau ta tafi wani babban pharmacy ta siyo maganin ta dawo, dama sun saba siyar da illegal magani a wajen shi ya sa ba tare da tunanin komai ba suka bata, gida ta koma ta ƙara duba yadda ta ga an rubuta a wayar yadda za tayi amfani da shi ai kuwa haka ta yi amfani da shi tana mai farin cikin za ta rabu da wahala..




Zaman Zeenat kam da Adnan abin ya ci tura, ba wanda yake iya zuwa gidan domin amarya ta hana, shi kam ya ma zama mijin kan ta ce domin kuwa mugun tsoron ta yake ji, ko ba ta ce ya yi abu ba sai ya yi jikinsa na rawa, sai dai ta tara ƙawayen banza su yi ta shaye shaye har maza suke tarawa a gidan, tun da an mayar da mai gida hoto, Farouk ne ya yanke shawarar zuwa ya ga abokin nasa tunda ko wajen aiki ma ba ya zuwa, ai kuwa zuwa ya yi ya tarar da shi kwance ba lafiya ita kuwa uwar gantali ta fita da ƙawaye ta bar shi jiran gida. Asibiti Farouk ya kai shi, a nan aka ba shi gado sannan aka diɓi jininsa don a yi masa gwaji domin gano me ke damun shi, sai dai gwajin farko likita ya tabbatar wa da Farouk cewa abokinsa na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (HIV), ƙiris ya rage Farouk bai faɗi a gaban likita ba, haka ya kira Daddyn ya sanar da shi suna asibiti, ko da suka iso shi da mahaifiyar Adnan results ɗin ya basu ba tare da ya ce komai ba, zufa daddy ya shiga sharewa yana maimaita kalmar innalillahi a fili, ɗakin da aka kwantar da Adnan suka shiga yana bacci shi kam bai ma san wainar da ake toya wa ba, zaune suke jugum jugum, can mahaifiyarsa ta ce:


"Farouk ni kam ina Zeenat? Na ga tun da muka zo ban gan ta ba?"


"Mommy wallahi ni ma ko da na je gidan ban tarar da ita ba, shi na samu zazzaɓi ya rufe shi, shi ne na kawo shi asibiti. Ina ganin ta je unguwa ne" Farouk ya ba ta amsa domin shi kam ya san halin da abokinsa yake ciki, kawai ba zai iya faɗa musu ba ne. Haka suka zauna a asibitin cike da damuwa don mahaifiyarsa sai kuka take yi, jira kawai suke ya farka su ji daga gidan uban wa ya kwaso wannan ciwo, ai shi Farouk tun da ya ji wannan maganar hankalinsa ya dawo jikinsa, sai istigfari yake yi yana neman gafarar Allah , shi kam ma aure zai yi kar shima ya jono ma kansa masifa.




Raudah na zaune a gidansu tsawon lokacin nan ba wanda ya ce mata koma gidanki, abin duniya duk ya ishe ta ta rasa makomar aurenta, ko ta kira Noor ba ya ɗagawa, kullum sai ta tsine ma Besty a fili da zuciya, ta yi nadama mara adadi ga shi ba ta jin daɗin jikinta, komai idan ta ci sai ta yi amai, lura da haka ne ya sa Mommy ta sanar da Abba suka kira wata likita a unguwarsu mai suna DR. Zainab ta gwada ta, ai kuwa gwajin farko ta tabbatar musu da zaman ciki a jikinta, farin ciki a wajen Mommy da Abba ba a magana, nan da nan suka rungumo 'yarsu suna saka mata albarka kuka ta fashe da shi, bayan DR. Zainab ta tafi take ce musu:


"Shikenan Abba Noor ya tsane ni, ga shi ina ɗauke da cikinsa, na san ya daina so na, kuma komai daren daɗewa zai rabu da ni" ta faɗa tana kuka kamar ranta zai fita , Mommy ce ta buga bayanta tana cewa:


"Ki yi haƙuri Raudah, Noor yana son ki, ya yi hakan ne don ganin kin shiryu kuma mu ma mun ba shi goyon baya don mu ga ko kin hankalta, kuma tabbas kin yi nadama insha'Allah Noor zai zo ya gan ki kuma za ki koma ɗakinki kin ji? Gata muke miki" hannu Mommy ta sa ta share mata hawaye sannan Abba ya fita ya siyo maganin da Dr ta rubuta mata, kunu Mommy ta dama mata ko da ta sha sai ta ba ta magani sannan ta kwanta , nan da nan barci ya yi awon gaba da ita.


Abba ne ya kira Noor ya shaida masa albishir, ai ba shiri ya taho gidan cike da farin ciki, Mommy ce ta ce ya shiga ɗakin Raudah'n don ya sa Mommy a gaba yana ta sunkuyar da kai, ai kamar jira yake yi ya miƙe har da ɗan gudunsa ya shiga, barci ya tarar da ita tana yi , hayewa saman bed ɗin ya yi ya kama kissing ɗin ta, kamar a mafarki Raudah ta ji ana ma ta kiss, tana buɗe ido ta ga Noor nan da nan hawaye suka fara zubo ma ta, harshe ya sa yana lashe mata yana faɗin:


"Haba maman baby kar ki sa baby ya ce na ci zalin mamansa, i am sorry! ko kishi ne ya rufe min ido na yi abin da na yi amma ki yi haƙuri komai ya wuce tashi mu koma gida", ƙoƙarin miƙar da ita yake yi ta noƙe, fita ya yi ya je ya samu Mommy ya ce "umm amm...Mommy zan tafi da ita gida tana buƙatar kulawa", ya faɗa yana sosa kai, murmushi Mommy ta yi tana faɗin Allah ya tsare hanya ga ka ga ta nan, tashi ya yi ya koma ɗakinta ya haɗa mata kayanta da maganin da Dr ta bata suka yi wa Mommy sallama ya mayar da ita gidansa, ai kuwa a ranar ta durzu kuma ta sha gata, ita ma ta zage ta nuna mai soyayya domin ƙara samun matsayi a zuciyarsa, Noor haka ya dinga kiran yan'uwansa yana sanar da su labarin cikin Raudah kowa ya yi farin ciki har mahaifinsa da mahaifiyarsa da kansa ya faɗa musu, addu'a suka musu da fatan Allah ya sauke ta lafiya, haka dai suke rainon cikinsu cike da soyayya da tattalin juna.




A gadon asibiti Fadeelah ta farka, ganin hannunta ana mata ƙarin jini ya sa ta rufe ido tana ƙoƙarin tuno abin da ya faru, ta dai san ta sha magani ta kwanta, can kuma ta ji mararta kamar za ta fashe daga nan ta ƙwalla wata ƙara ba ta sake sanin inda take ba sai yanzu, Anty ce a gefenta tana share hawaye, kamo hannunta Fadeelah ta yi tana faɗin:


"Anty da kin bar ni na mutu, rayuwata ba ta da amfani sam, na cuci kaina, kullum cikin baƙin ciki nake, rayuwata ba ta da wani amfani" ita kan ta Anty kuka take yi sai yanzu ta yi nadamar ƙin
jan ƙanwarta ta a jiki da ba ta yi ba, ga shi nan a garin zubar da cikin ta sha magani ba bisa ƙa'ida ba har ta rasa mahaifarta gaba ɗaya, nasiha mai ratsa jiki Anty ta yi mata tare da nuna ma ta muhimmancin yarda da ƙaddara, sannan daga bisani ta faɗa mata matsalar da zubar da cikin ya ja ma ta, domin ita ma Anty ta shigo kenan daga unguwa ta gan ta kwance cikin jini shi ne ta kwaso ta zuwa asibiti da ƙyar aka tsayar da jinin, Allah Ya yi tana da nisan kwana ne amma da yanzu wani labari ake ba wannan ba, sosai jikin Fadeelah ya ƙara sanyi da lamarin duniya ta san Adnan ya gama da ita ya kuma cuce ta, haka dai ta zauna a asibiti aka yi ta jinya har ta samu sauƙi suka tattara suka koma gida ...






A ɓangaren Adnan kuwa ko da ya farka babu wanda ya iya faɗa masa halin da yake ciki, sai dai mahaifiyarsa ta saka shi a gaba ta yi ta kuka, ya rasa abin da zai ce ma ta, idan ya tambaye ta sai ta ce ba komai, Zeenat neman shi take cike da tashin hankali, don babu wanda ya sanar da ita inda yake ga shi boka ya ce kada ta yarda ya yi nisa da ita na tsawon awa arba'in da huɗu, komai zai iya lalacewa, hankalinta sam baya jikinta, shi kam jin shi yake sakayau, ko da mahaifiyarsa ta tambaye shi ina Zeenat ɓata rai ya yi domin ba ya son jin ko sunanta, sai da ya cika sati ɗaya a asibiti aka sallame shi, Farouk ne mai kwana da shi, direct gidansu aka wuce da shi sannan Daddy ya zaunar da Adnan ya faɗa masa halin da yake ciki, cikin firgici yake kuka da maimaita kalmar innalillahi a bayyane, ihu yake yana cewa Zeenat ta cuce shi, bai tsaya jiran kowa ba ya miƙe ya zari key ɗin motar Daddy da ke gefen kujera ya fice daga gidan a ɗari da talatin, bai tsaya a ko'ina ba sai cikin parlour'n gidansa, ai kuwa ya iske Zeenat da ƙawayenta suna ta rawa kamar yadda ya saba, ido rufe ya yi kanta gadan gadan bayan ya kunce belt din jikin shi, karfe belt ɗin ya samu ya dinga dukan ta da shi har sai da gefen idon ta ya fashe, ihu take amma babu mai taimako domin ƙawayen nata ma tuni sun tsere, sai da ya tabbatar ya mata illa sannan ya rubuta mata saki uku ya cilla ta wajen gidan ya rufe gidan ya yi gaba abin shi ....






A haka dai rayuwa ta gangara abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar Zeenat wadda ta yi hatsarin mota a yawon bin bokaye don su mayar da ita gidan Adnan, iyayenta sun yi baƙin ciki sosai da mutuwarta, shi kuma Adnan yana nan yana karɓar magani, kuma ya je gidansu Fadeelah ya roƙe ta gafara bayan ya sanar da ita halin da yake ciki, tana kuka ita ma take faɗa mai abin da ya same ta na rasa mahaifa da ta yi gaba ɗaya, yanzu ma wani ɗan maƙocin su Baba Saleh ne zai aure ta a unguwar yake matansa biyu ita ce ta uku, kallon ta Adnan ya yi ya ce:


"Hmmmm lallai Fadeelah SANADIN BESTY bai haifar mana da komai ba sai sharri, har yau ina nadamar kasancewa ta a matsayin Besty domin na san abin da muka shuka a lokacin da muke ƙawance shi muke girba yanzu", a haka dai suka gama hira suka yafi juna ta koma gida...




Bayan wata tara Raudah ta haihu inda ta haifi 'yarta mace santalleliya mai kama da Noor, shagali kam an sha a ranar sunan yarinyar nan, inda SANADIN BESTY FANS suka taka rawar gani a sunan nan, don kuwa shinkafar Noor kam haka suka saka buhu guda a gaba suka cinye, ko da Noor ya gan su a gefe suna harraka abinci harara ya dinga zabga musu, a haka aka yi shagali aka watse inda yarinya ta ci suna Hafsat wato ƙanwar Mamman Noor kenan....






Bayan shekaru goma,
Wani na hango sanye da kakin soja da wata mace a gefensa sun shiga shopping mall, wata yarinya ya gani kyakkyawar gaske tana bin wani yaro da gudu za ta amshi teddy, buge shi yaron ya yi ganin ya buge baban mutum ya saka shi yin rau-rau da idanu yana cewa:


"Sorry uncle, Hafsa ce ta ture ni", murmushi wanda aka kira da uncle ya yi ko kafin ya yi magana ya hango wata hamshakiyar mace a tare da wani babban mutum suna ƙarasowa wajan da suke, kallo ya bi ta da shi ya ce:


"Raudah?" Tana dago kai ta ce "Dee" harara Noor ya zabga musu yana cewa:


"Malama ki zo mu tafi ko?" Hannu Dee ya ba shi suka gaisa cikin wasa da dariya bayan sun gaisa yake tambayar Noor waɗanan yaran fa? Noor ya ce mai yaransu ne macen sunanta Hafsa, namijin kuma Muhammad, albarka ya sanya musu sannan shima ya gabatar musu da Fa'iza yarinyar da ya aura wata uku da suka wuce kuma yanzu two star ne shi a aikin soja, murmushi suka yi, nan take Raudah da fa'iza suka ƙulla zumunci, Dee ne ya biya musu kuɗin siyayyar gaba ɗaya sannan suka fito a tare kowa ya shiga motarsa zuwa inda ya fito...
Anyi bikin Fadeelah da maƙocin su Sani kuma suna zaune lafiya da shi, duk da wani lokacin matansa na mata gorin haihuwa sai dai ta shiga ɗaki ta yi ta kuka, shi ma Adnan ya damu wata mata ya aura a asibitin da ya ke karɓar magani....


Zaman Raudah da Noor kam sai son Barka hankalin iyayenta a kwance, ƙannenta ma duk sun girma, wani lokaci idan suna zaune da Noor sai ta tuno da lokacin da Abba ya biyo ta ta shige bayi ta dinga zawo, sai Raudah ta yi dariya tana faɗin:


"Ai SANADIN BESTY ya so ya raba soyyayya, da mun bi ta BESTY da yanzu Allah bai bamu yaranmu sanyin idaniyarmu ba".


Dee ya ce "ai da kuwa na ga asalin SANADIN BESTY dan ni za a cuta, duk abin da Allah da ManzonSa suka hana to guje mai ya fi wayewar duk na banza ne".








Alhamdulillah!

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads