Showing 27001 words to 27791 words out of 27791 words
Chapter 10 - TAFARKIN TSIRA ORG.txt by Mansur Usman Sufi
farin ciki dakarun sarki Madsur suka gabatar da dinaren harajin dake cikin waɗansu akwatu na baƙin ƙarfe, sannan sarki ya ja ya koma ya gefe guda
Sarki na biyu mai suna Ashrum dake mulkin birnin Darul-Zabub ya faɗi ya kwashi gaisuwa ya buɗi baki ya yi gyaran murya kanshi a sunkuiye ya ce "Ya shugabana gani tafe da dukkan abin da aka buƙata, ina fatan dukiyata za ta zamo fansa gare ni da al'ummata"
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Ashrum sai Fitinatul-Amir ya fusata ainun ya daka mashi tsawa wacce ta sanya hantar cikinshi Ashrum ta kaɗa jikkunansu suka kama ƙyarma, cikin matuƙar fushi Fitinatul-Amir ya dube shi "Ya kai Ashrum shin wace dukiya gare ka da zata fansar da Jinin al'ummarka? Haƙiƙa ka yi Furuci mafi muni a gare mu da wajibi ne sai mun ganar da kai kuskuren ka,
Koda jin wannan batu daga bakin Fitinatul-Amir sai sarki Ashrum ya faɗi ƙasa yana neman gafara yana mai cewa "Ina tuba ya shugabana tabbas na yi kuskure....,
Kafin ya gama rufe bakinshi Fitinatul-Amir ya dako wawan tsalle daga kan karagarshi tamkar an harbi shi daga cikin baka ya shammaci Ashrum ya kirɓa mashi wawan naushi a wuya, saboda ƙarfin naushin nan take wuyan ya yi ƙara ya karye ji kake ruƙus! Ƙas jini ya yi tsartuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica! Nan waɗansu zaratan dakaru a fadar suka ɗauke gawar sarki Ashrum suka goge jikin da ya zuba, sannan suka tusa ƙeyar jama'ar shi izuwa kurkuku.
Sa'adda sauran sarakunan suka ga abin da ya faru ga sarki Ashrum sai cikinsu ya ɗuru ruwa domin sun san cewa a kodayaushe ɗayan su zai iya baƙuntar barzahu,
Bayan Fitinatul-Amir ya koma bisa kan karagarshi ya hakimce sai aka hango yara biyu mace da namiji sun shigo fadar sun durfafo inda karagar mulki take, ba wasu ba ne face Yaro Usaiba mai hatimin takobi tare 'yar uwarshi Hairat, lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bata huce taku goma kawai sai aka ga sarki Fitinatul-Amir ya miƙe tsaye tsam! Daga kan karagar mulki fuskarshi cike da annuri ya je ha tare su yaja hannayensu har izuwa kan karagar mulki suka zauna a tare.
"Wannan shi ne masu iya magana ke cewa idan rabo ya rantse... Kaico! Rashin sani wai Kaza ta kwana akan dami, haƙiƙa Fitinatul-Amir ya tafka babban kuskure da ya riƙi wannan yaro a matsayin magajin shi, shin ko bai gano cewa yaron shi ne Usaiba mai hatimin takobi SAIFUL-ZAYYAD da yake farauta dare da rana ba"
Wani daga cikin sarakunanne ya yi wannan furuci a cikin ranshi batare da ya bayyana ba,
Ana cikin wannan hali ne wani badakare ya matso daf da karagar mulki ya risina ya kwashi gaisuwa ga sarki ya ce " Ya shugabana an lissafa harajin sarki Madsur kuma tuni dakaru sun nufi Baitul-Mali domin su kai dukiyar domin haka sarki Madsur ta tawagar shi za su iya tafiya,
Koda jin wannan batu daga bakin badakaren sai Fitinatul-Amir ya gyaɗa kai alamar gamsuwa.
Nan take Madsur da tawagarshi suka miƙe tsaye suka durfafi ƙofar fita daga fadar, amma koda suka zo giftawa ta gaban Fitinatul-Amir sarki Madsur ya haɗa idanu da yaro Usaiba sai suka ƙurawa juna idanu, nan take Madsur ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi.
Jim kaɗan bayan ficewar su daga fadar sai yaro Usaiba ya dubi Fitinatul-Amir ya buɗi baki cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya abbana wannan sarki da ya fita daga wannan fadar ya shirya maka wata mummunar gadar zare ka sani cewa dukiyar da ya kawo maka a matsayin haraji bakomai ba ce face sinadaran tsafi, wadanda matsawar ka haɗa su da dukiyar ka dukkan abin da ka mallaka zai lale za ka dawo sarkin da ya fi kowa talauci a duniya"
Koda jin wannan batu daga bakin yaro Usaiba sai Fitinatul-Amir ya cika da matuƙar mamaki ainun ya dubi Usaiba ya ce "Ya aka yi kasan da hakan ya ɗana?
Usaiba ya ce "Ya abbana ka duba idan har ka tabbatar da abin da na faɗa ba gaskiya ba ne na yarda cewa na yi kuskure".
Koda jin wannan batu sai Fitinatul-Amir ya zira hannunshi a aljihunshi na riga ya ɗauko madaidaicin madubin tsafi ya shafe shi da hannun shi na hagu ya shiga gudanar da bincike, Nan take ya gano gaskiyar abin da yaro Usaiba ya faɗa game da mugun tanadin sarki Madsur.
Koda ganin wannan al'amari sai Fitinatul-Amir ya taƙarƙare ya kurwa wawan ihu da ya ɗimauta duk wata halitta dake fadar.
Mu haɗu a ƘARYA DA GASKIYA Domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071